Showing 90001 words to 93000 words out of 259716 words
Daddy yana rik’e da hannunta..da hannu d’aya yayi tuk’in sai dai in zai chanja gear ne ya ke d’an cikata yana chanjawa kuwa ya ke sake ruk’ota kamar wani zai kwace masa ita ne.
Haka kurum suna zuwa bakin gate d’in gidan data ga ya
danna horn ta ji gaban ta ya yanke ya fad’i sosai..da kuma ta tuna su Yassira da Kausar sai ta ji ranta ya b’aci…..salati ta shiga yi a cikin zuciyarta da ikon Allah sai ta ji fad’uwar gaban da b’acin ran suna raguwa.
Tunda suka shigo gidan ta shiga al
ajabi da mamakin tsantsar girman gidan,ita
tana ganin gidanta Babba ashe ga mansion anan!
MashaaAllah masu kud’i suna hutawa..tashi d’aya ta fara addu’ar ‘Allah itama ya bata ikon fara aiki ya bata kud’i ta samu ta siyawa su Baba gida ko d’an flat ne su
ma su ji dad’in rayuwa.
A parking space sukayi poarking kafin ya kashe motar ya d’auki jakarta ya fita da niyyar zagayawa ya bud’e mata,da sauri ta juya ta bud’e ta fito kafin ma ya zagayo.
B’ata rai ya yi sosai kafin
yace”Why?!”
Murmushi kawai ta
yi tace “yi hkr”….
Da kyar ya d’an saki fuska ganin ta masa kalar tausayi tukunna suka wuce suka nufi main parlour.
A bakin k’ofar shiga suka ci karo da Yassir wanda ya zo shiga shima..bai dad’e da dawowa daga office bama jakarsa kawai ya ajjiye a sid
e d’insa ya zo da niyyar ganin Kausar dan kwana biyu karantarta kawai yake yi…ya fi
minti d’aya tunda ya hangosu har suka k’araso suka tsaya yana k’are musu kallo yanajin yadda zuciyarsa take wani irin tafarfasa!a ransa yana aiyyana”how can Yashjub be th
is lucky!ta ya
zai fi sa sa’a ata ko wanne b’angare ata ko wanne fanni
na rayuwa!….”
Da mamaki Yashjub yake kallosa yana la’akari da yadda idanuwansa suke sauya kala dan lokaci guda yaga sun fara rinewa suna chanzaa kala zuwa jajajaja…
Baban abunda
ya b’ata masa rai game da Yassir d’in shine yadda ya kafe Manubiya da idanuwa ko kiftawa ba ya yi.
Ashe haka take!wacce iriyar kyakkyawar halitta ce wannan mai tafiya da imanin d’an Adam…tabbas ya zama dole Yashjub ya mutu kwanan nan
ta yadda cikin sa
uk’i zai had’a Kausar da Manubiya a matsayin matansa ya yi rayuwa mai dad’i.Dan bayan Kausar ba ya jin akwai wata da ya ji yana so ya yi rayuwar aure da ita bayan wannan baiwar Allahn.
“Yasir’’
d’in da Yashjub yace maasa a d’an zafafe ne ya dawo dashi
daga duniyar da ya lula.
Wani lumshe idanuwa yayi wanda hakan ya kuma k’ular da Yashjub kafin ya bud’e ya ce
“Welcome”
Sai kuma ya juya ya kalli Manubiya wadda tashi d’aya ta ji kamar ta rufe sa da duka ganin irin kallon da ya shiga yi mata.Murmushi y
a d’an yi yace “antyn mu barka da zuwa bismillah”
Ya fad’i hakan yana nuna mata k’ofa kafin ya d’aura da cewa
‘’Yau dai ya Yash ya bari anga fuskar ki”
Da kyar da mugun kyar Manubiya ta k’ak’alo wani d’an guntun murmushi wanda ya tsaya a iyaka labb’a
nta ne tukunna ta bi bayan Yash wanda ta ga ya juya kawai ya ruk’o hannunta suka nufi cikin parlourn.
Bayan su kawai Yassir ya bi da kallo yanajin yadda k’irjin sa yake wani irin bugawa…yadda
ya kafe Manubiya da ido yana k’are mata kallo hatta yanayin k
walliyar stones d’in jikin rigar ta sai da ya gani ya haddace ta cikin mayafin ta.
Suna shigewa ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya ya jin jina kan sa kafin yace “da sake!”
daga haka ya sa kai shima ya nufi cikin parlourn
A main parlourn gidan su
ka samu Mommy Baba larai Ya’isha da Kausar a zaune suna magana da alama mai mahimmanci ce,sallamarsu su ce ta sanya sukayi sauri duk suka d’ago suka zuba musu ido….tashi d’aya yanayin fuskar Ya’isha ya sauya ganin Yashjub d’in ne ma ya ruk’o wa Manubiya ja
ka.
Da sauri ita kuma Kausar ta mik’e ta wuce sama
Yayinda baba larai ta mik’e ta fara cewa “Lale marhababiki Amarya surukar mu
Yashjub bismillah mana k’araso!ku shigo ciki ya ka barta nan bakin k’ofa a tsaye”
Ta fad’i hakan tana nufar su tana Isa ta
kamo hannun Manubiya ta zare a cikin na Yashjub ta ja ta suka nufi cikin parlourn.
Dakyar Manubiya ta iya janye idanuwanta a kan Baba larai
sarai ta shaida ta itace suka ce sai ta d’urk’usa sannan duk wani mai hankali yana kallon fuskarta tashi d’aya
zai shaida ba farin ciki takeyi da auren ba,amma kalli yau itace kamar zata cinye ta! tabbas waennan shaid’anu ne wato idan a gaban Yashjub ne ba za su nuna mata k’iyayya ba kenna dan ta lura da Yasira ma d’azu saida ta bari babu Yashjub a wajen tukunna ta
gaggaya mata maganganu.
A gefen Mommy daff da ita Baba larai ta zaunar da Manubiya kafin tace”bari in je in kawo muku ruwa,sannu Amarya lalle marhaba”
Ta fad’i hakan tana wucewa da sauri har da d’an yin tuntub’e. Yashjub ne ya d’an tsani da ita ya san
ar da ita batun kayan zak’’i dan haka ta karb’i makullin motarsa tace bari ta nuna su gwaggo su kwasa su saka a kitchen.
A hankali Ya’isha ta mik’e kamar ba itace ta baro gidan d’azu tana fushi ba ta k’arasa wajen Yash tace “kawo jakar ni in rik’e mata”
Ta fad’i hakan tana mai amsar jakar.
Tashi d’aya kawai sai ya ji kunyar Mommy ta kama sa dan haka ya cika mata jakar ya k’arasa inda Mommyn take ya zauna a gefen ta dai dai nan su Yassira ma suka fara sauk’owa da alamar Kausar ce ta gaya musu Yash d’i
n ya zo,tare suka sauk’o gaba d’ayansu har da Daddy da alamun tare suke da shi a saman,shi Yashjub ma bai yi tunanin Daddyn yana nan ba ya d’auka yana office duba da yadda shi baya nan Yasira ma ya ga yau ba ta je ba.
A hankali Manubiya wadda tun d’azu
ta ke jin nauyin zama a kusa da Mommy ta d’an sullub’o daga kan kujerar tace “Mommy Ina wuni”
Saida Mommy ta yi namijin k’ok’ari dagasken gaske tukunna ta iya dafa kanta a hankali tace “lafiya y’ar albarka ya bak’unta”
“Alhamdulillah”tace a ranta tan
ajin wani sanyi dan yadda Mommyn ta yi mata ta ji dad’i sosai ta fahimci itan tana sonta ba kamar su Yassira ba..ta san dama zuwa d’auko ta da kai lefe ba hurumin Mommy bane amma da aka d’aukota tace “a wuce da ita ba sai ta zo ta gaida ita ba!” da kuma y
adda take kiranta a waya amma ba ta amsawa ya sa ta d’an ji tsoro ta shiga damuwa da tunani..
Muryar Daddy ce ta katseta jin yana cewa”Manubiya mik’e ki zauna a kan kujera mana,tashi
kinji”
Murmushi ta yi sai da Yashjub wanda shima yaketa zuba murm
ushi dan ba kad’an ba ya ji dad’in yadda iyayen nasa suka nuna kulawar su ga matar tasa,tukunna a hankali ya d’an sunkuya ya kalli Manu yace “mik’e ki zauna mana
Daddy yana magana”
Tukunna ta mik’e ta zauna a kusa da Mommy inda take tun farko tanajin wa
ni nauyi da girmanta yana ratsa ta,dai dai nan su Daddy suka k’araso suka zazzauna,shima saida ta durk’usa har k’asa tukunna ta gaidashi ya amsa da kulawa.
Da sauri yace”Ummi bata sauk’o ba Yassira jeki ki kirata”
sai kuma ya zaro waya yace “Bari in kira
ta”ya fad’i hakan yana dialing number Ummi,ba ta dad’e tana ringing ba ta d’auka.
Tana d’auka yace “ki zo munyi bak’i”daga haka ya katse kiran yana mai tambayar Manubiya “ya bak’un ta”
Cike da girmamawa da kunya suke amsa shi.
Suna a haka Munirat suka s
auk’o ita da Ummi.
Da sauri Munirat ta k’arasa ta je ta zauna a kusa da Manubiya tana “oyoyo antyn mu ashe kune Ina wuni”
sai kuma ta kalli Yash ta gaidashi.
Kamar yadda Manubiya ta yiwa Mommy da Daddy haka ta zamo ta gaida Ummi itama,
ta kuwa ji dad’i
dan haka ta shiga tambayar ta ya sabon waje ya su Innarta…. mik’ewa Yash ya yi yace”Bara mu lek’a Yahanasu,ya jikin nata?.”
Da sauri Mommy tace”da sauk’i!.Munirat ta kai Manubiya wajen Yahanasu kai kuma ka zauna munada magana da kai!”
Shiruu ya d’anyi d
a sam bai ji dad’i ba ya san Manubiya zataga kamar an ware ta ne…
Yana cikin wannan tunanin suka mik’e ita da Munirat suka nufi d’akin Yahansu jiki ba kwari.
Lumshe ido Yashjub ya yi har suke shige bai bud’e ba..
Muryar Daddy ne ya dawo da shi daga du
niyar tunanin da ya lula jin yana cewa”Yash,mai ya faru yau ka koro k’annen ka daga zuwan su na farko?”
Da sauri ya bud’e idanuwansa ya kallesa sai kuma yayi kan Yassira a zuciye.
Da sauri Mommy ta mik’e ta tsaya a gaban Yasirar tace”ai ni za ka daka b
a ita ba!tunda nice nan na gayawa Daddyn naku ba ita ba!”
Ummi ba ta san kan labarin ba
ba kuma ta san abunda ya faru ba amman tashi d’aya ta fahimci laifin su Yassira ne…baya ga haka saboda Allah ta ya Daddy zai biyewa Mommy a zuwan Yashjub da Manubi
ya na farko gida a fara da case!
Su da ya kamata ace sun saka su a gaba sun yi musu fad’a da nasiha sannan sun yi k’ok’ari wajen basu chance su fahimci juna amman kalli yadda tun farko aka sallami Manubiya akace a rakata d’akin Yahanasu saboda Allah wanne
irin rashin lissafi ne wannan?,ya suke tunanin Yarinyar za ta ji saboda Allah…..
Ta san inhar ta zauna to tabbas za a yi fad’a da ita
shiyasa ta mik’e tace
‘’Am Daddy bara in d’an baku guri dan Allah”tana gama fad’in haka ta wuce sama bata yadda ta k
uma had’a ido da Daddyn ba….sai da ta had’a da sauk’ar AlK’urani da addu’o’i tukunna ta daina jin matsananciyar tsanar sa,haka kurum ta samu sun shirya shima ya daina fushi da ita da kyar !
ba ta ga dalilin da zai sa ta zauna a wajen da zata fad’i abunda
zai ji haushi su yi fad’a su sake komawa ruwa ba.
“Ta fi Nono fari”Mommy tace a cikin zuciyar ta kafin ta maida hankalin ta ga Yashjub wanda ya ke cewa Yassira da ta b’oye a bayan ta “k’ara ta kika kawo?
ke ba ki fad’i abunda kuka yi ba?”
Cikin ta
rar numfashin sa Daddy yace
‘’Mai sukayi?’’
Tun kafin Yash yayi magana
Ya’isha tace
‘’Wallahi Daddy bamuyi komai ba,dama tun da mukaje ta tare hanya ta hanamu wucewa sai da ya zo tukunna ta matsa.
Ina ga yanayin fuskar ta ya kalla dan tanata fama
n kumbure kumbure shine ya kira Yasira ya ce ta kwashemu mu tafi’’
Wani irin takaici ne ya lullub’e Yashjub wanda ya sa ya ji kamar ya finciko Ya’isha daga kusa da Daddy ya feffella mata mari…ya godewa Allah da ba a kusa da shi take ba dan ya san yau da
sai ya illatata!
Ganin Yaran suna neman haukatasa ne yasa ya koma ya zauna ya dafe kansa da ya fara sara masa.
Gyaran murya Daddy ya yi kafin yace”Yashjub!!tun wanchan ranar a asibiti na fad’a maka kar ka bada k’ofar da matar ka za ta raina y’an uwank
a!and again a washegarin ranar da ka yi aure ma sai da na rok’ek’a da kaina akan kar ka bada k’ofar da kawunan ku zai rabu a ta dalilinta amman naga that’s exactly what you are trying to do. Sam!ban ga dalilin da zai sanya dan ka yi aure ka tsame y’an uwan
ka a jikin ka ba ba zai yiu ba ba zan zauna in zuba ido zumuncin ku ya tarwatse ba saboda rashin tunanin ka da kuma gigin giyar soyayyar da ka kurb’a.”
Yashjub ji yayi kamar ya d’aura hannu aka yayi ta faman zunduma ihu…ta ya Daddy zai biyewa waennan Ya
ran ya hau kan maganganunsu ya zauna daram sannan ji fa tone d’insa sai kace na mace yana magana kamar ta mata
yanzu wannan d’an k’ank’anin abun har ya kai a titsiyesa a gaban su haka…….
Muryar Daddy ce ta katsesa jin yana cewa”ina sauraron ka,
ka f
ad’amin exactly abunda ya faru.
Ku kuma”
yayi maganar referring to su Yassira yace”kar in ji bakin ku
har ya gama magana.”
Wato dai a gaban Yaran nan za a yi masa haka!alk’alanci kenan Daddy zai yi musu shi da k’annen sa….
“Ina jin ka mana!”
Ya
ji muryar Daddyn a d’an zafafe.
A hankali ya d’ago ya kalli Daddyn yace”Ba su kula ta ba.
Kaff cikin su saida na yi magana tukunna Yadira ta gaida ita‘’
Da takaici Mommy tace
“Saboda ba su gaida matar ka ba shine ka koro su daga gidan ka??’’
Ci
kin son fahimtar da ita yace
‘’Mommy saboda sun rainani kuma sun ki su yi abunda nace a gabanta sun nuna min ban Isa ba shiyasa na koro su
Baya ga haka Mommy taya za su je har gidan ta su k’i su kulata sannan kuma ni da kaina in ce su yi su k’i yi
Ma
atata ce fa!’’
Ai ko da ace ba za su gaida ita ba da ko ‘Hi’ ya kamata su ce mata…..”
Cikin tarar numfashin sa Ya’isha tace
‘’Daddy cewa ya yi duk sai mun gaida ita har Yasira da Kausar,kuma fa ita ma bata kula mu ba how yake expecting mu mu gaida i
ta?.”
Throw pillow Daddy ya jefawa Ya’isha cikin fad’a yace
“Ba na ce bana son jin bakin kowa ba?”
Da b’acin rai sosai ya juya ga Yashjub ya ce
“Yashjub’’
Ahankali Yash ya kalle sa ya ce
‘’Na’am Daddy’’
Cikin bada umarni da fahimtar wa Daddy
ya fara magana
‘’kamar yadda na fad’a d’azu
ba zan bari giyar soyayyar da ka sha ta lalatamin zumuncin dake a tsakanin ku ba!ba zan bari wata mace ta shiga tsakanin ku ba dan bakasan yadda muka sha fama ni da mahaifiyar ka wajen ganin mun daidaita kank
u ba!”
Ahankali Yash ya lumshe ido yana mamakin yadda su Daddy suka d’auki laifi gaba d’aya suka d’aura wa Manubiya…ta yaya Manubiya za ta shiga tsakanin sa da su Yasira shi kuma ya yarda..
Dan mai ya sa tun farko idan irin haka ta faru a tsakanin su b
a’a d’abbak’a abun sai yanzu da yayi aure?
Kuma shi rainin da suka yi masa a gabanta ne ma ya sake harzuk’a sa ya koro su a
tunanin sa ya Isa da su.
Inda ace ci musu fuska ya so yi ai da a gaban Manubiyan zai fatattake su…Ita Manubiyan ma da suke ta c
ewa ‘za ta shiga tsakanin su’ bama ta san da case d’in korar sun da yayi ba.
Ahankali tunanin sa ya dawo cikin parlourn jin Daddy yana cewa “Inaso ka sanar da Manubiya idan kuma ba za ka iya ba ni zan sanar mata cewa
‘Ya’isha da Yusra za su gaida ita w
annan dole ne!amma
tun daga kan Ya’isha har zuwa kan Yassir har Kausar ita ce zata gaida su tunda duk sun girme ta.’”
Da mugun sauri Yashjub ya d’ago sosai ya zubawa Daddy idanuwan sa.
“Kwarai kuwa”Daddy yace shima yana kallonsa kafin ya d’aura da ce
wa
“Ba wai nace dole in sun had’u sai ta gaida su ba,ruwanta ne idan taga dama ta kula su in bata ga dama ba karta kula su
amman kasancewarsu yayyu a gareta yasanya bazai yiu ace su su fara gaida ita ba.
Idan ta kula su ta gaida su su amsa
In kuma b
ata kula su ba
wannan alhakin yana a kanka
na ganin ka daidaita alak’ar dake a tsakaninta da su
kaine za ka nuna mata cewa yayun ta ne kuma ta dinga gaida su saboda a samu a zauna lafiya a raya zumunci.
Sai kuma magana ta biyu
‘Daga yau har gaba
n abada idan su Yasira za su je gidan ka a rana sau goma to baka da iko sannan baka Isa ka kore su ba!na san gidan ka ne nasan kai ka siya ka zuba furnitures ka yi komai da kanka amman ni kuma nine uban ka!
dan haka in dai ni na haife ka,to Yassira,Yahana
su,Ya’isha,Yadira,Yasmeen,Yusra,Yassir kai har ma da Kausar za su je gidan ka a duk lokacin da suke so
In ma hutu suke so su yi za su je su yi har sai sun gaji dan kansu tukunna su dawo amma kai dai baka da ikon koro su…in har kuma kace za ka yi taurin k
ai to zan sa ka had’omin spare key na kaff gidan naka in rabawa ko wanne a cikinsu….
Ban d’aura auren da zai tarwatsamin kan ya’ya na ba wallahi.!”
Yana gama fad’in haka ya mik’e ya ce
‘’a kiyaye” daga nan ya wuce sama.”
Shiruu Yashjub yayi ya ma k
asa cewa komai
Har sai da Mommy tace
“Sai magana ta uku!Yadira ta had’a kayan ta tun d’azu
In kun zo tafiya ku wuce da ita
za ta zauna a gidan naka for sometimes.”
Saida ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna ya ce
“To Mommy ba damuwa,amma jiya
na gaya miki za mu tafi Cyprus..y not a bari sai mun dawo t….”
Cikin tarar numfashinsa tace
“Ka wuce da ita,idan kun zo tafiya sai ka dawo da ita in kuka dawo sai ku koma tare da ita”
Ahankali yace”Mommy, jibi ne ai…”
Cikin fushi tace
“Ka san A
llah Yashjub in ka gwada min taurin kai idan bance ku tafi honeymoon d’in tare da ita ba ka chanja