Showing 87001 words to 90000 words out of 259716 words

Chapter 30 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

13

su Jidda suka shiga gaida Yashjub cikin girmamawa da mutuntawa.

Da kulawa ya

amsa yana tsokanr Muhsin da d’an lukuti

kafin ya amsa gaisuwar Aisha da y’arta daganan suka gaisa cikin mutunta juna shi da su Ya Musbah.

Yunk’urawa Manubiya ta yi tace “bara ta kawo musu ruwa” da sauri Ya Musbah yace “A’a sauri fa mukeyi”

Aisha ce

ta kalli Yashjub tace

ga gara nan mun kawo da kayan zak’i,Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya.”

Murmushi Yashjub yayi kafin yace”kun dage dai Aisha,har da wannan wahalar itama?. wannan fa duk bidi’a ne”

Sai kuma ya ce”An gode!haka ake cewa ko?



Ya yi musu tambayar yana kallonsu.

Duk dariya sukayi kafin su fara mik’ewa da niyyar tafiya,da sauri yace”Au wai dama da gaske kuke?tafiya da wurwuri haka kamar ana korar ku?”

Wayar sa ce ta d’auki k’ara dan haka ya yi excusing kansa ya matsa gefe dom

in amsa kiran Mommy.

Yana wucewa Manubiya ta d’ago kai ta kalli Aisha wadda har yanzu bata zauna sosai ba tace”Wai da gaske tafiya zakuyi haba mana”

Ta fad’i hakan kamar zata fashe da kuka.

Murmushi Aisha ta yi ta na shirin yin magana muryar ya Musb

ah ya katseta jin yana cewa”Manu, kuka kikayi ne?”

Saida ta sunkuyar ta kanta k’asa na d’an lokaci tukunna ta d’ago ta kalle sa tace “A’a”

Sai kuma hawaye sharr suka b’alle mata a take kamar an kunna famfoo.

Cikin rashin jin dad’i Aisha tace

“King

a dalilin da ya sa mukeson tafiya kenan!

Yanzu dan Allah in ya dawo ai sai yayi tunanin mu muka ce wani abun ko.Taya zaki sa kuka haka

So kike ki janyo mana bak’in jini?”.

Zuwa yanzu Ya Musbah ya tamke fuska tamau tsabar takaici!duk rashin hak’urin B

araka sai da ta yi wata goma sha d’aya a gidansa tukunna ta fara kuka a ranar sunan mai sunan baba dan ba’a yanka mata rago da tunkiya ba instead an yanka iyaka rago.

Amman shi kalli k’anwar sa ko sati d’aya ba ta yi a gidan miji ba amma har ta fara kuka

!ba ma hawaye ba.

A hankali ya mik’e ya k’arasa inda take ya zauna a gefenta

yana jin tsananin tausayin ta yana ratsashi,cikin nutsuwa ya bud’e bakinsa ya fara magana”Manu ko ma menene ya faru ki yi hak’uri kinji ko?ki daina kuka,

haka auren yake sai h

ak’uri..”

Ajiyar zuciya Ya Nafi’u wanda ya ke shirin tsaida Ya Musbah ya sauk’e dan a tunanninsa tanbayar ta Ya Musbahn zai kuma yi akan ‘mai akayi mata’

amman sai yaga yayi lissafin manya dan haka ya d’an ji

sanyi aranshi saboda shima ba kad’an ba

ya ji ba dad’i game da yanayin da suka tadda Manu d’in a ciki.”

Dakyar Ya Musbah ya sake cewa”Mun so mu d’an zauna amman kukan nan naki ya koremu”

Da sauri ta dag’o kanta ta shiga goge hawayenta tana cewa “Allah na daina”

Murmushi yayi yana mai jin i

nama ace yanada ikon da zai iya goge mata koma wanne irin takaici ne yake addabar zuciyarta haka.Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna yace”Next time idan mun zo sai ki yi k’ok’arin k’in yin kuka ko?idan har ba ki yi ba sai mu zauna,kin ji?”

Ya fad’i hak

an cikin d’aga mata gira d’aya.

Dai dai nan Yashjub ya k’araso wajen, tun d’azu ya gama waya da Mommy amman ya kasa komawa wajen su..tun da yake bai tab’a jin kunya da nauyi irin wannan ba,dan tun d’azu tun da ya d’ago ya ga Manubiya tana kuka ya ji wata

kalar kunyar ta da nauyin su Ya Musbah sun yi masa kawanya.He’s not supposed to make her cry,ever!.

Yana k’arasowa Ya Musbah ya mik’e ya k’arasa inda yake ya mik’a masa hannu,da kyar

duk su biyun suka k’ak’alo murmushi kafin Ya Musbah yace “Kayan sun

a varender anan muka jere su ,mun so mu shishshigo da su har kitchen mu d’an zauna to amman wannan shagwab’abb’iyar matar taka ta kore mu…daga

ganin mu ta hau kuka.

Bara mu wuce

Allah ya sanya alkahairi.”

Wani abune ya tokare k’irjin Manubiya ganin

yadda duk cikinsu babu wanda ya damu ma ya tambaye ta me akayi mata sannan kuma bama za su tsaya ma ta gansu sosai su yi hira ta d’an ji sanyi ba,har zasu tafi..ga kuma kishin Kausar da zuwa yanzu haka kurum ta ji ya sake turnik’e ta

dan haka kawai sai t

a mik’e da kyar ta je ta yi hugging su Siyama tace “na gode”

daga haka ta wuce sama da sauri mai kamar d’an gudu dan

bataso ta sake sakin wani kukan a gaban su kar su ce sun fasa dawowa next time d’in ma gaba d’aya.

Tun kafin ta kai ga k’arasawa d’ak

in nata ta saki kuka.

Yashjub ne ya rakasu har mota yana ta musu sannu da godiya da basu sak’on gaisuwa a Baba da Inna,dauriya ce kawai yake yi dan gaba d’aya jin sa yake wani iri duk ba da’di.Sai da ya ga fitarsu tukunna ya kira masu gadi yace su shiga

r da komai ciki.

Kasa tsayawa ya yi har su gama,hakanan ya barsu anan k’asan ya nufi d’akin Manubiya ransa duk a jagule…ya lura bayan cin fuskar da su Yassira suka yi wa Manubiya da kuma zancen Kausar tabbas akwai shagwab’a da tab’ara a lamarin ta,ya san

sai ya yi lallashin da gaske tukunna za ta sak’k’o…gashi Mommy ta kira sa tace “ya zo shi da Manubiya yanzun nan!…..”

Kamar d’azu yanzun ma a zaune ya same ta a bakin gado

tana kuka.

A hankali ya k’arasa inda take ya durk’usa a gaban ta….shi fa b

ai iya lallashi ba wallahi bai ma san ta Ina zai fara ba!.

Tun lokacin da ya durk’usa a gaban ta gaba d’aya sai ta ji ba dad’i!no mattar what komin takaicin da take ji bai kamata ta bar sa ya d’urkusa haka da sunan bata hak’uri ba dan ta san hak’urin z

ai bayar.

A hankali cikin sharar hawaye tace”Ka tashi,ba kuka nake yi ba”

Murmushi yayi kafin ya ruk’o k’afafunta ahankali yace “Dan Allah ki yi hak’uri…”

Da sauri ta zamo daga kan gadon ta fara k’okarin kwace k’afar ta tana cewa”Ni dai dan Allah ka d

aina!babu kyau.”

Y’ar guntuwar dariya ya yi yana kallonta yace

‘’babu kyau miji ya bawa matar sa hak’uri?’’

Cikin tarar numfashinsa tace

‘’A’a babu kyau ka durk’usa kamar haka,dan Allah ka daina kana sakawa Ina jin ba dad’i”

Ta fad’i hakan tana

mai goge ragowar hawayen da sukayi saura a fuskar tata.

Cikin kwabe fuska tare da kwaikwayar muryar ta yace

“To ke ba ki san babu kyau ki yi ta kuka kina d’aga min hankali ba?sannan kalli fa a yadda su Siyama suka tafi na san duk hankalin su a tashe y

ake za ayi tunanin ko har na fara cutar da ke ne tunda daga ni sai ke a gidan.Ni addua ta d’aya ma kar su gayawa su Baba”.

Shiruu ta yi tana sauraron sa

ganin haka yasa ya matso kusa da ita sosai ya tallafo fuskarta a tafin hannun sa yace “Hawayen ki

tsada gare su,dan Allah dan Allah Baby ki daina saurin zubar min da su

kalla idanunki gaba d’aya kin wahalar min da kanki ba tare da kin tsaya kin ji kan zancen ba ma.”

Shiruu ta yi kawai ta kasa cewa komai,haka shima yayi shiru ya zubawa kyakkyawar

fuskar ta ido…kad’an kad’an ta ji yana matso da fuskar ta ta garesa yana d’an murza gefen kumatunta,ta san inda ya nufa shiysa ta yi saurin mik’ewa ta juya masa baya tana kallon gadon tana mai gyara d’aurin dankwalinta.

Lumshe ido ya yi ya bud’e kafin y

a mik’e tsaye ya na kallonta,lokaci d’aya ya saka hannu ya yi hugging nata tsantsan ta baya a hankali ya d’aura kansa a kan dokin wuyanta yana mai shak’ar k’amshin jikinta mai sanyaya zuciya had’i da dimauta sa a ko da yaushe.

Cikin tsananin mutuwar jiki

ya ce “ki yi hak’uri ban gaya miki asalin maganata da Kausar ba

dalili kuwa shine a time d’in da na ji maganar sam ban dauk’i abun serious ba shiyasa kikaga ban saka shi a fannin da yake important na rayuwata ba.Dukkannin abunda na gaya miki kika sani g

ame da ni tou shine important duk abunda kika ga ban gaya miki ba tou bashi da amfani shiyasa amma naga kamar rashin gaya miki maganar Kausar d’in yana neman janyo wani labule a tsakanin mu wanda ba zan bada k’ofar hakan ba.”

A hankali ya juyo da ita ya

na facing d’inta rik’e da k’ugunta ya fara zaiyyano mata yadda ranar ya ji Kausar tana gayawa Mommy ‘tana sonshi’

sannan ya d’aura da cewa”Wallahi Wallahi apart from Kausar d’in da Mommy sai kuma Yahanasu da ya gayawa sam shi bai ma san wani a ciikin su

Yassira ya san zancen ba,bai san maganar ta je kunnuwansu ba ta yadda har suke tunanin zai aureta,shi a mazaunin shirme da rashin tunani ma ya d’auki maganar tata shiyasa bai bawa abun importance ba.Amman yana so ta yi masa alfarma d’aya!’ta manta da komai

da kowa

ta yi trusting d’insa akan abunda zai fad’a mata yanzu

‘Tun yana Yaro shi tsarin mace d’aya garesa kuma Kausar is the last parson da zai iya aura

saboda kwata kwata jinin sa bai d’auke ta ba tun yarinta,

ko da ace su biyu ne kad’ai suka rage

a duniya ba ya jin zai iya rayuwa da Kausar a matsayin matarsa’….’’

A hankali Manu ta sunkuyar da kanta tana jin wani sanyi da nutsuwa yana lullub’eta dan tabbas maganganun sa sun rufe kusan kaso arba’in na damuwarta zuwa yanzu ta fahimci ba b’oye mata

yayi ba.

Dukda tana fargaba da kuma kishin yadda Kausar d’in take son Mijinta amman still ta d’an ji sauk’i da ya fito ya gaya mata komai,sannan she has chosen to trust him akan lamarin,kamar yadda ya buk’ata.

Cikin son sake kwantar mata da hankali ya

d’ago da fuskarta yana mai kallon kwayar idanunta yace”Mannubiya ce kad’ai a cikin zuciyar Yashjub!Ba ki san yadda kika tare gaba da baya ba shiyasa kike wannan tunanin amma inda ace kinsan yadda kikayi bake bake a cikin zuciyata da ko ni da kaina in nace

miki zan k’ara aure ko zan kula wata na san ba za ki tab’a yarda ba

I love you only you no one else!

So idan ma akwai wani tunanin zan auri wata ko zan kula wata a ranki gara ma tun wuri ki cire

saboda wahalar min da zuciyar ki kawai kike yi

as far

as I know u are the only one for me kuma na san su Daddy ba za su tab’a yi min auren dole ba

So..pls Baby! ki daina b’ata ranki…um?!..”Ya k’arashe maganar ta sa cikin sa hannu ya janyota jikinsa sosai kafin ya d’aura da cewa” ko amarci na ma ban fara ci

ba har Amarya ta fara shiga damuwa ta fara fushi da ni,Pls ki daina Plssssss”ya fad’i hakan kamar zai fashe da kuka yana sake sakata a jikinsa.

Shiruu Manubiya ta yi a ranta tace”au bai ma fara cin amarcinba a hakan…”

Tana wannan tunanin ta ji yanayin na

sa yana shirin sauyawa dan haka ta d’an yi y’ar dabara ta goce dakyar tace”Ya wuce fa!

Ni ba fushi na yi ba kuma na daina kukan ai”

Cikin sake ruk’ota yana dariya dan ya fahimci zillewa ta ke son yi yace”ba wani nan!fushi kikayi mana bayan k’iri k’iri

d’azu aka yi denying d’ina kiss yanzu kuma hug anjima kuma Allah kad’ai ya san mai za a hanani…”

Da ga haka ya janyota ya fara aika mata da sak’onninsa ma su zafi da tsada……

Addua ta fara yi Allah ya kawo mata ceto dan a yadda ya fara sakin layikan nan

ta san k’aniyarta za ta ci.

Allah kuwa ya amsa adduar ta dan tashi d’aya wayar sa ta fara k’ara…sai da aka kira har sau biyu bai kula ba jin kiran yak’i k’arewa ne ya sa yace”Ohh God!”kafin dakyar ya samu ya sa hannu ya zaro wayar daga aljihu da niyyar k

ashewa amman sai idanuwan sa suka hango masa sunan Mommy b’aro b’aro…shi fa sai yanzu ma ya tuna da neman nasu da takeyi wallahi shaf ya manta…sai da ta tsinke ta sake kira tukunna dakyar cikin k’ok’arin daidaita muryarsa ya d’auka ya ce”Mommy gamu nan zuw

a”

daga haka ya kashe wayar ya kalli Manu yace”Bamu je ba gashi Mommy har ta fara neman mu,kece kika k’i ki warke da wuri shiyasa mukayi letti”ya fad’i hakan yana dariya k’asa k’asa yana mai sake kissing d’inta tukunna ya mik’e da kyar….

Yasan idan suka

zauna a d’aki d’aya suka ce za su shirya ba za su yi sauri ba,gashi ya d’an jiyo fushi a muryar Mommy

hakan ya sanya ya ce mata”ta shirya da wuri bari shima yaje ya shirya”

Daga nan ya koma ya sake kissing nata daga haka ya fice da sauri dan ji yakeyi

kamar akwai wani magnet d’in da yake jansa gareta.

Yana fito ta sauk’e ajiyar zuciya had’i da ta’a’uzi dan tashi d’aya taji wani tsananin kishi ya lullub’e ta sakamokon tuno wa da tayi zata had’u da Kausar idan taje gidan.

Cikin nutsuwa tana ta kora

r shed’an a hankali ta shiga shiryawa…wanka ta fara yi tukunna ta fara d’auko kayan da za ta saka.

A ganin ta gidan surukai za ta je shiyasa ta yanke shawarar saka kayan da suka yi mata a cikin lefe ta san in suka ga ta saka za su ji dad’i kwarai.

Wata d

andatsetsiyar atamfar exclusive ta saka kalar royal blue da ratsi ratsin silver da red an zuba mata d’inkin riga da skirt na zamani da sukayi asalin amsarta…ita kanta tasan d’inkin ya fito da ita ras matsalar ta d’aya yadda d’inkin ya matseta rabin k’irjin

ta a waje sannan skirt d’inma ya kamata ga waist d’in ya fito sosai shima…d’inkin ya fito da surar jikinta gaba d’aya.

dama tun jiya da ta zo zab’ar kaya ta lura da yanayin d’unkunan gaba d’aya sun yi fitting dayawa,gaskiya idan ta samu lokaci zata ce

su mayar musu a dan bud’a mata dan ba zai yiu a kashe uban kud’i ba kuma a yi mata d’inkunan da ranta bai so ba….

Dama tanada abun d’auri na ture kaga tsiya dan haka ta d’auko ta saka a cikin dankwalin nata ta ajjiye kafin ta koma gaban madubin ta d’auk

a powder ta shafa ta saka eye liner ta d’auko lipstick ta shafawa labb’an ta.

Ita kanta tasan tayi kyau irin sosai d’innan..murmushi ne ya sub’uce mata ta san Yash yana shigowa zai hau mita yace mugunta ta had’a masa dan ta san ba zama za suyi a gidan ba

shiyasa ta chab’a wannan uwar kwalliyar.A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya tana jin tsantsar k’aunar mijin nata tana sake shiga jikin ta tana ratsa ko’ina.

Tana tunanin sa tana murmushi ta shiga tufke gashin kanta a ta baya chan k’asa ta kanainaye sa ta s

aka d’an siririn ribbom black gudun kar ya sunce daga nan ta d’auko dannkwalin data saka abun daurin a cikin ta d’aura sa perfectly.

Saida ta san yadda ta yi ta b’oye uban tulin gashin ta da ya fito ta k’asan d’aurin tukunna ta tafi closet ta bud’e wardro

be ta zaro mayafi jaka da takalmi kafin ta d’auko iyaka y’an kunne zobe da agogo kawai dan ba ta cika son sark’a da awarwaraye ba.Y’an kunnenta,zobe agogo da Mayafinta silver yayinda jaka da takalminta suka kasance red colour.

Tana shirin yafa mayafi ya t

uro k’ofar ya shigo..dama k’ofar take facing dan a kan gadon nata ta jere jaka da mayafin nata.

Saida numfashin Yashjub yayi sama ya dawo bai san lokacin da a fili yace”MashaaAllah,Ubangiji mai halitta.”ba.

Kamar had’in baki shima sanye yake da kaftan

blue nasa da farar hula da farin takalmin da agogo,wanda hakan ya yi kamar anko sukayi.

Ahankali ya taka ya shigo cikin d’akin idanunsa a kanta.

Gaba da’ya Manubiya sai ta diririce sakamokon kallon da ta ga yana mata…so take ta ware mayafin ma ta rufa

amman sai ta kasa.

Murmushi yayi kafin ya maida k’ofar ya rufe ahankali ya k’arasa inda take still idanunsa suna a kanta.

Saida ya gama k’are mata kallo tukunna ya sa hannu ya karb’i mayafin sannan ya zagaya ta bayanta ya tsaya tukunna ya ware mayafin g

aba d’aya ya rufa mata shi a saman kanta gefe da gefen kuma ya zagaya dashi ya rufe mata gaba d’aya jikinta dashi wanda hakan ya basa damar yin hugging d’in ta

A tare shi da ita suka sauk’e ajiyar zuciya kamar ta saani dama aikuwa ta ji yace

“Wannan da

i tsokanata akayi amman kar ki damu zan fanshe idan muka dawo”.

Daga haka ya manna mata wani dogon peck a kumatunta kafin yayi saurin cikata dakyar yana mai sauk’e ajiyar zuciya.Jakarta ya d’auka daganan ya ruk’o hannunta suka fita tare gwanin ban sha’awa

. Wani Irin shauk’i da so ne suke jan Yashjub game da ita ji yakeyi kamar ya had’iye ta ya kora da ruwa ko ya samu sauk’in abunda yake ji. Gaba d’aya robobin kayan zak’in garar Manubiya tace su tafi da shi a su Mommy ita za ta raba har su sai ta basu nasu

haka akeyi. Sai da ya bud’e mata mota ya sakata a ciki tukunna ya kira masu gadi suka kwasa suka sanya a boot da seat d’in baya sannan ya shiga motar ya ajjiye Jakarta da ya yake rik’e da ita ya zauna tukunna ya kunna mai gadi ya bud’e musu suka fice.

Har suka k’arasa gidan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login