Showing 243001 words to 246000 words out of 259716 words
Allah Yasira ki
bar ni in huta mana bakiga situation d’ina ba???
Ki huta kema ki zo ki je mini pharmacy ki siyo min maganin ciwon Ido saboda wannan d’ayan har na daina gani da shi sannan ki fita ki nemo min chargi ina buk’atar in yi waya da gaggawa….Yusra ke kuma ki d’au
ra girki…”
Tana gama fad’in haka ta juya ta rufo k’ofarta hankali a masifar tashe………
Sai azahar tukunna Yash ya zo…zuwa wannan lokacin kowa ya fara jin tausayin gwaggo Suwaiba saboda sun fahimci zafin abun ne ya sanyata yin hakan dan kwata kwata ta k’i
bari a nad’e inna a yi mata sutura…..ta zama kamar wata tab’abb’iya.
Manu tana zaune a parlourn ita da su Siyama da su anty Umma suna kuka su mama kuma sunata lallab’a gwaggo Suwaiba Baba ma yana gefe shi da Ya Musbah in banda hawaye babu abunda suke yi
sun ma kasa tsawatar mata!
Suna a haka Muhsin ya shigo yace wa Manubiya “ga Ya Yash a waje yace ta je…”
Manu tana mik’ewa Gwaggo Suwaiba tace mata “tace masa tana son ganinsa ya shigo”
Sannan ta kalli su Baba tace “dan Allah tana buk’atar magana da Yash
shi kad’ai…….”
Sai da suka gama kukan su shi da Manu ya lallab’a ta da kyar tukunna ta iya gaya masa sak’on gwaggo Suwaiba ya d’an yi mamaki amma kawai sai ya bi bayan Manu ta yi masa rakiya zuwa cikin parlourn.
Manubiya ta so zama amma itama Gwagg
o Suwaiba ta sallameta parlourn ya rage daga ita sai Yash sai Inna….
Sun jima sosai sun fi 1 hour dan
har mota Yash d’in ya fita ya shigo da ita kafin ya tafi ko sallama bai yiwa Manubiya ba!
Ta ji mamaki matuk’a dan tun d’azu dama da ya zo ta Lura
da yanayin da yake a ciki na tashin hankali firgici tsoro da kuma rud’ani tun da yazo tana kallon idanunsa ta fahimci ya ci kuka ba na wasa ba,da farko ta yi tunanin rasuwar inna ce ta tab’asa haka amma yanzu yadda ya tafi kuma ya k’i d’aukar wayarta ya s
anya ta fahimci tabbas wata matsalarce ta sake tasowa bayan waenda suke a ciki.
Bayan tafiyar Yashjub suna shiga suka tarar Gwaggo Suwaiba har ta shirya Inna an sakata a makara ma wanda hakan ya sanyasu sake rushewa da kuka ko zama ba suyi ba ya Musbah ya
shigo yace Baba yace “su ake jira.”
Da kyar aka b’amb’are Muhsin da Manubiya daga jikin gawar Hakanan Ya Musbah shi da Ya Nafi’u suka d’auketa a cikin makarar aka je a ka yi mata sallah suka mik’ata gidanta na gaskiya…..
Ana tafiya kaita su Yaha
nasu sukazo dukkansu har Yasmeen Yadira da Hajiya Mama da su Daddy.
Hajiya mama ba su had’u da Mama ba saboda da wuri suka tafi tare da su Daddy ita da su Yasmeen,Yahanasu ce ta zauna.
Ita kuma Mama a lokacin ta koma gida suka d’an kimtsawa tukunna suka
taho ita da Ammi.
Yahanasu tana zaune a d’akin da Manubiya ta ajjiyeta kawai ta ga Mama ta shigo wadda dama ita maman ta san tabbas yau kam za ta
had’u dasu amma fa dukda haka sai da ta kusan fad’uwa a lokacin da sukayi ido biyu ita da Yahanasun,Yahan
su kanta ta kusan suma gashi lokacin babu kowa a d’akin sai ita
A hankali jiki ba lakka ta mik’e tsaye bakinta yana wani irin karkarwa tace”maa maa!”sai kuma ta tafi da gudu ta fad’a jikinta ta fashe da wani irin kuka…
Itama Maman kuka ta saka a nan waj
en ta yarda tray d’in hannun nata ta rungumeta a cikin jikinta!
Ba abunda ya fi yiwa Yahansu dad’i kamar yanzu da ta san whereabout d’in mama shikenan za ta had’a Yash da mahaifiyarsa cikin sauk’i
nauyin da ya ke a kanta shekara da shekaru yanzu zai
sauk’a.
Cikin sharar hawaye ta d’ago ta kalleta tace”Mama dama kin san su Manubiya?ya aka yi kuka had’u?”
Ta yi mata tambayar waensu hawayen suna sake zubowa…..
Hannu ta saka ta share mata hawayen nata kafin ta ja hannunta suka k’arasa bakin gadon suk
a zauna…nan ta faiyyace mata duk wata alak’a da take tsakaninta da su Manubiya
Tana kuka tana hawaye sannan tana dariya at the same time tace” da ma kece mama da nake yawan jin sunanki a bakin Manu?
Alhamdulillah!!
Mama na ji matuk’ar dad’in ganinki ba
ri Manu itama ta zo na san zata ji dad’in jin wannan labari kwarai!”
Ta fad’i hakan cikin sake rungumeta.
Da sauri Mama tace mata “A’a Yaha kar ki gaya mata komai!”
Cikin rashin fahimta tace”ko
me yasa Mama?”
A take wasu hawaye suka zubo mata ciki
n ruk’o hannun ta tace”Yahanasu a halin yanzu ba zan iya fuskantar Hajiya mama da sharrin tarin abun kunya da aka yi mini ba,sannan mahaifinku ya sanar mini muddin ya ganni ko da a kusa da ke ne to fa abunda zai aikata a gareni mummuna ne!!”
Cikin tarar n
umfashinta Yahanasu ta d’ago tace”Mama duk sharri ne ba shi ne ya fad’i waennan maganganunba!duk makircin su Momny ne!”
Da mamaki ya kalleta tace”su Mommy kuma?”
“Tabbas ita ta had’a Baki da mai makarantarmu a wannan lokacin sannan asalin abunda ya far
u shima duk laifinta ne!
Kar ki hukunta Daddy ta hanyar cewa kar a gaya masa an ganki na tabbatar shima neman naki yake yi yanzu haka.
Cikin gyara zama da sake ruk’o hannunta ta d’aura da cewa”
Akwai abubuwa da yawa da nakeso in faiyyace miki but first
yanzu bari in kirawo su Daddy su zo Allah kad’ai ya san kalar murnar da zasu yi idan suka ganki!”
Shiruu Mama tayi dan ba kad’an ba ta shiga shock da jin sunan Mommy a cikin lamarinta!!!Mommy Mommy dai??an ya kuwa?
Sai kuma ta kalli Yaha kamar mai naza
ri kafin cikin hanzari ta sa hannu ta karb’e wayar hannu Yaha ta kashe kiran….
Da mamaki Yahanasu ta kalleta kafin tace”Mama pls dan Allah ki bari in…..”
Cikin tarar numfashinta tace”Yahanasu ki yi mini alfarma guda d’aya a matsayina na mahaifiyarki kar
ki gayawa kowa kin ganni,inaso ace Daddy ya nemo ni ya maidani cikin zuri’arsa da kansa kamar yadda ya yi mini yankan k’auna da kansa…shekaru kusan talatin Yahanasu amma ace har ke da kanki kin fahimci sharri aka yi mini ta ya zan yarda Daddy da kansa bai
fahimci hakn ba sannan meyasa bai neme niba???
Ni dai kawai inaso ya kasance ya nemo ni
ya mayar da ni da kansa da hannunsa Akan ace kece kika mayarda ni ba tare da yarda da amincewarsaba kuma inajin tsoron had’uwa ta da shi ban san ya zata kasance ba ki
nce abun da mai makarantaar ku ta fad’a sharrin su Mommy ne ko?
To na ji na yarda amma kuma wat if ya yi mini kamar yadda suka ce zai yi d’in?dan na san zai iya aikata hakan Yahansu mutumin da ya kashe ni zai iya aikata fiye da abunda suka k’aga suka fad
’a suka ce ya ce zai yi.”
Ciki girgiza kai Yaha tace
“Na tabbata idan na yi masa bayani zai fahimta zai yarda.
Kumafa Mama shi a tunanin sa kin rasu ne muma a da duk hakan muka d’auka,ki bari a yi masa bayani”
“Yahanasu idan ace ya damu to ya kam
ata ace by now ya fahimci gaskiya kamar yadda kema kika fahimta”
Yahansu zata yi magana Mama ta katseta ta hanyar cewa”dan Allah kar ki yimin jayayya bana son musu daga gareki ki yi yadda nace hakan shine farin ciki na.
Na fi so ya fahimta da kansa ya ne
moni da kansa,hakan shine kad’ai zai goge mini abunda ya faru
Sannan bamuda tabbacin zai karb’eni Yahansu idan aka yi rashin sa’a ya tozartani Ina riba?
Ba zan so a ci mini mutunci a b’atamin suna ba dan haka na rok’ek’i da girman Allah kar kiyi komai k
ar kice komai,alfarmar mutunci da daraja ta a idanunki ki bari mu yi addu’a ya yi yadda nakeso d’in ko na samu peace of mind da sauk’in radadin da nakeji a cikin zuciyata!”.
Da kyar Mama ta samu ta yi convincing Yahanasu ta hak’ura ba zata gayawa kowa b
a har sai Daddy ya huce ya nemota da kansa ya fahimci komai…ba dan Yahansu ta so ba ta yarda da hakan amma InshaaAllah bazata yi k’asa a guiwa ba har sai ta nuna masa hanya shi kuma ya gane gaskiya ya nemi sanin inda take da kannasa kamar yadda Maman takes
o.
Washegari Jidda suka zo ita da Al’ameen nan kuwa komai ya dawo wa su Manubiya sabo fil…..sun ci kuka kamar ransu zai fita Jidda da Siyama masu d’auke da juna biyu wata uku uku kam sai da aka dangana da kwantar da su a asibiti tsabar kuka
da damuwa.
A ranar ne kuma Gwaggo Suwaiba ta tashi tafiya babu yadda basuyi da ita ba amma firr tace musu ita tafiya zata yi
Wanda hakan sam bai yiwa kowa dad’i ba dan kai tsaye hakan rashin kyautawa ne…hakanan su Ya Nafi’u suka kaisu tasha ita da Hadiz
a suka kama hanya gidan ya rage daga Manubiya sai su Jidda abun tausayi dan ma Anty Umma tana tare da su dan Siyama ba ta wani dad’e ba aka sallamota daga asibitin,Mama kuma ita take tare da Jidda a asibiti itakam sai da ta yi sati biyu a kwance dama cikin
nata ya zo da laulayi sosai tun usulinsa.
Yahansu har asibitin take zuwa ta duba Jidda su tattauna da Mama amma har yau bata samu ta yi convincing maman ba,ganin fa bazata tab’a yarda ba ne ya sanya ta mayar da hankalinta ga tunanin ta yadda za ta ba
wa Daddy ko da clue ne a samu ya fara bincikenta dan maman ta sanyata ta yi mata alk’awarin ba zata tab’a cewa kowa komai ba.
Sosai mama ta ji dad’in ganin kamal a matsayin wanda Yahanasun zata aura dan shima ya je ya duba Jidda kuma ya je ya yi gaisuwa
.
Sai da aka yi kwana ashirin da rasuwar Inna tukunna su Manubiya suka koma gidajensu anty Umma ma ta koma gida gidan ya rage daga mai sunan Baba sai Baba Muhsin da Ya Musbah dan Bararka tunda ta fita da gudu har yau ba’a ganta ba cigiya har a gidan rad
io mahaifiyarta ta bayar amma shiru…shi ya Nafi’u ma ya d’auka da ta ji labarin zata yiwa mutane hauka amma sai ta big’e da bada hak’urin abunda Barakar ta yi tace dan Allah a yafe mata a tayata addu’ar nasarar samun ganin ta……..
….
Bayan kwana goma..
Yau kwanakin Inna talatin da rasuwa su Manubiya kuma goma da komawar su gidajen mazajensu…Jidda ma a nan Al’Ameen ya barta ya tafi dan saura kwana sittin ya kammala abunda ya je yi kuma exams ne Masu zafi a gabansa shiyasa tace masa tana son zama a nan
su Ammi ma suka ce ya barta a nan saboda jikin nata ya yi tsanani sosai….
Ya siya mata gida mai kyau a Na’ibawa ya zuba kaya ya yi komai amma dai a hannun Ammi ya barta for now saboda kusan kullum sai an k’ara mata ruwa..sosai kuwa Ammi da Mama suke kula
da ita dan abunda suke yi mata ko Inna iyakacin abunda zata yi mata kenan.
Siyama ma ta koma gidanta lafiya k’alau itakam bata wannan fitinannen Laulayi kamar na Jiddah.
A b’angaren Manubiya kuwa gaba d’aya ta gagara gane kan Yash!!tun ranar da Inna
ta rasu ya chanja gaba d’aya kuma ba wai ita kad’ai ba kowa yake yiwa hakan….haka kurum sai dai ya yi shiruu ya zauna ya tusa mutane a gaba babu um babu um’um ya yi ta kallon kowa amma iyaka idanuwansa kad’ai idan ka kalla tashi d’aya zaka fahimci yana ci
kin masifa da tashin hankali…
Hatta office ma da Najeeb ya zo zai yi masa handing over cewa ya yi ya cigaba kawai ba zai iyaba……..
Shima da so ya yi ya chanjawa Manubiya gida amma sai Hajiya mama tace”kawai ya zo Mansion d’in Daddy su zauna a side d’insa
na da dan tabbas yanayinsa yana mugun bawa har su su Hajiya maman tsoro gashi an yi tambayar duniya yace musu”he’s fine!!!”
Mommy kuwa har yau bata cire raiba……Ya’isha dai ta tafi dahirr ta ma cire rai….….amma tsohon yace mata”ta kwantar da hankalin
ta indai hular Manu aka d’auko
akayi aikin da ita to fa ta zuba ido
Anytime labarin rasuwar Manu zai risketa!!watak’il inna itama ta saka hular shiyasa abun ya shafeta kuma shiyasa aka samu delay na mutuwar Manubiya amma tabbas tana hanya itama….Su Yasir
a kuwa zuwa yanzu sun dawo daga rakiyar Mommy…babu Ya’isha babu labarinta zuwa yanzu idan suka yi mata maganar Ya’ishan ma fad’a take rufe su dashi…dukda sun san itama tana cikin masifa amma sam wannan ba abun da za su yi shiru bane dan haka Yasira ta shir
ya akan zata je ta samu Daddy tace masa ba fa su ga Ya’isha ba kuma Mommy ko maganar ba ta so ayi!!!
Ta san ko da matsalar ganin da take fama da shi aka barta ya isheta(dan zuwa yanzu kwata kwata idonta na dama ba ya aiki na biyun shima ya tab’u sosai)am
ma fa ba zata iya cigaba da yin shiru ba wallahi,dan this is a serious case.
A lokacin da Yasira suke maganar za su je su samu Daddy ita da Yusra Mommyn tana jinsu…
Shiyasa hankalinta ya sake tashi matuk’a,dama masifar rashin gani da tsohon ya ke ta
amshe kud’inta ana ta yin magani amma a banza ta isheta ga Manubiya da ranta har yanzu Yash ma haka…a halin da take ciki dai yanzu ta ajjiye komai a gefe a samu ta fara gani tarr tukunna sai a yi komai su kuma su Yasira ta san ta rufe musu Baki a kan case
d’in Ya’isha to amma kuma gashi yanzu kwatsam! Suna shirin jik’a mata aiki,har fa su Yasmeen ta hana zuwa gidan duk dan kar a tambayi Ya’isha a waya kuwa da suka ji shiru tace musu bata da lafiya ne ita kanta sai yanzu ta san tanada matsala fa dan Bata sa
n me zata ce game da Ya’isha ba a gaba dan ba zai yiu ta yita b’oye b’oye forever ba.
A b’angaren Abbakar shima tunda aka yi rasuwar kusan kullum sai ya je musu gaisuwa da daddare lokacin da ya tabbatar ba zai had’u da Yash ba!
Ita dai Manu gaisawa
kawai suke yi daga haka ta wuce d’aki dan abu da Abbakar sam ba ta so…to yanzu kuma ya isheta a waya yanason taimakon ta,ta yi blocking d’insa amma a banza a rana sai ya kirata sau bakwai da different layuka ga messages,dan ma Allah ya taimaketa Yash bai
tab’a gani ba saboda shima he’s
not himself kwana biyun nan daina hankali kawai. …Ta san watak’il akan rashin lafiyar mahaifiyarsa ne da ya k’i ci ya k’i cinyewa (saboda ta ji anata maganar ciwon nata)
amma ita har ga Allah tsoron d’aukar wayar sa ma tak
e yi,Shiyasa jiya da ta je gida ta tura Muhsin gidansu ya karb’o mata accnt number sa ta tura masa dubu d’ari amma kuma dukda haka Abbakar bai bar kiranta da tura mata sak’onni ba.
A b’angaren Kausar kuwa,tana nan cikin tashin hankali dan ga Yash da M
anu a cikin gidan kusa da ita amma kamar basa nan…..ba ta Isa ta je inda suke ba kuma tun da suka zo
ko ganinsu bata yi ba,Yasmeen dai tana zuwa wajensu har Yadira idan sunzo amma shi kam saboda ita ko lek’owa bayayi itama Manu ya hanata shiga main cikin
gidan kuma su Hajiya mama sun yarda da hakan,Daddy dai da asubah suke gaisawa Hajya mama kuma ta kan je musu da kanta…….
Tun daga kan Hajiya Mama har zuwa kan Yadira da suke yawan zuwa duk y’an gidan mamakinta suke yi dan ta ma fisu energy,Kwata Kwata b
a ta jin nauyin cikin sannan babu alamun ciki ya d’auko tsufa a tartare da ita…….
Kwatsam yau suna zaune aka yi musu waya daga asibiti Kausar ta haihu ta haifi baby boy! Ba ma su san lokacin da ta fita ta tafi asibiti ba.
Ummi da Yasmeen ne kawai suka
je asibitin…sai da Ummi ta firgita a lokacin da ta d’auki Yaron sakamokon tsananin kamannin da suke yi ita da Yaron hatta Yasmeen sai da ta lura da hakan dan haka kanta ya sake d’aurewa tamau da al’amarin Kausar da haihuwarta…
Basu dad’e da zuwa ba su M
ommy suka k’araso dan haka suka yi mata sallama suka wuce gida kawai ko Yasmeen ma da Ummi ta yi tunanin zata d’an zauna bata zauna ba binta kawai itama ta yi.
Su kansu su Mommy sun yi mamakin tsananin kamannin Yaron da Ummi amma kawai sai suka bari a k
an watak’il saboda tana yawan kallon ummin kullum ne,Mommy har da cewa”akwai wani d’an makwaftan su itama da ya tab’a yin kamanninta lokacin suna yawan shiga gidan!!”.
Daganan kuma suka hau murna aka fara zab’e zab’en suna aka zab’i ‘Alan’, ba kad’an ba s
un ji matuk’ar dad’i da Yaron ya kasance Namiji dama tun tuni mommy take cewa ta yi scanning ita kuma tace bazata yi ba,gara kawai ta Haifa a gani.
Kausar ba ta b’oye musu abun da ta k’ullawa Manubiya ranar suna ba!
Su dai su Yasira basu ce komai ba,da
n zuwa yanzu komai ya fita a kansu
Mommy ce ta bada goyon baya dama tana neman ta inda zata rage bak’in cikin Manubiya kafin a samu asirin ya kamata ta tafi forever…
Idan kuma ma ta mutu kafin ranar sunan to falillahilHamdu!!!
Daganan kuma suka shiga
tattauna akan kud’in da zasu had’a bayan suna a samu Mommy ta ga likitan ido,dan suma zuwa yanzu al’amarin idon