Showing 165001 words to 168000 words out of 259716 words

Chapter 56 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

71

ta wuce ta koma wajen zamanta ta zauna.

Da kulawa suka gaisa da Mommy har da Baba larai,suka tambayeta ya jikinta tace “

Alhamdulillah”daga haka suka yi sallama dai dai nan Yadira ta shigo mata da abinci.Babu yadda ba su yi da ita ba amma ta k’i ci Siyama ma ta ji dad’in k’in cin da tayi dan itace ma ta fara yi mata signal da ido saboda yadda suka dage ya sa suka fahimci in

ba da kyar ba sun mata abu a cikin abincin ne…shiyasa ta k’i yarda ta ci iyakaci ta d’auki ruwanta na bohole da ta d’ura a gora jiya wanda taga har ya yi k’ank’ara k’ank’ara ta bud’e ta yi bismillah ta kai baki..kalar ruwan bai chanja mata ba hakama taste

d’in shiyasa hankali kwance ta sha sosai ta ajjiye tana sauk’e ajiyar zuciya…

Murmushi Yusra ta yi a ranta tace”in kin san wata ai ba ki san wata ba!”.

Ba su fi minti ashirin da zama ba Inna ta kira Manubiya ta sanar mata halin da ake ciki tace”nan da

11 za a d’aura aure”

Daga Manubiya har Siyama duk kuka suka saka…gashi sunata kiran Jidda ta ma k’i d’agawa.

Sama Manubiya ta je ta sanar da Yash halin da ake ciki dan haka ya mik’e yace bara ya shirya sai su tafi”

shima duk hankalinsa a tashe.Ba yadda

ba ta yi da shi ya tsaya ya karya ba amma ya k’i yarda yace”su je da wuri kawai ba su da ishashshen lokaci,ya san idan ya yiwa Baba magana inshaaAllah zai d’aga k’afa”

A gaggauce ya yi wanka ya shirya cikin wata had’add’iyar b’akar jallabiya daga nan suk

a d’auki hanyar gandun albasa gaba d’ayansu har Yusra da Yadira.

A mota Yusra ta yi chatting Yassira ta tura mata har da number Abbakar…Ya’isha Yasirar ta kira ta tsara mata komai yadda za ta yi kafin tace”idan ya k’i yarda ta kira ta za ta san abun yi”

.

A b’akin gate d’in gidan suka tarar da Baba Ya Nafi’u da kaka mallan da wasu mutane su uku.Da mamaki su Ya’isha suka shiga kallon juna ita da Yusra dan basu san sun chanja gida ba kuma za su iya dafa Al’Qurani akan cewa Yashjub ne ya basu gidan!tabb!a

ikuwa yanzu ba sai anjima ba za su gayawa su Mommy dama sun san irin haka ce za ta yi ta faruwa,gashi kuwa har an fara.

Suna wannan tunanin suka k’arasa suka gaida su Baba daga haka ya Nafi’u ya ce bari ya bud’e musu gate su shiga da motar amma sai Yash y

ace ya barshi bari ya bar motar tasa a waje kawai.

Shi ya bud’ewa su Manu k’aramar k’ofa suka shige ciki daganan suka juya wajen su Baba da shi da Yash.

Manya manyan flat house ne guda biyu iri d’aya gate d’insu d’aya ko wanne yana d’auke da 4 bedroom

da 2 parlours da kitchen da dining area,ga babban tsakar gidan da ya ji interlock wanda atleast sai a gina irin gidajen uku a cikinsa.Har da d’akin mai gadi a kusa da gate d’in.

Ba kad’an ba gidan ya burge su Manubiya tashin hankalin da suke a ciki ne ya

sa ba su tsaya santin gidan ba suka afka b’angaren da suka ga k’ofarsa a bud’e.

A chan waje kuwa sai da Yash ya tsaya tukunna ya fahimci limaman masallacin area d’in ne Baba yake tare da su…

Sai da suka gama suka yi sallama suka wuce tukunna Yash ya yu

nk’ura da kwarin guiwa zai lallab’a Baba amma instead sai Baban ya rigasa ya shiga had’a sa da Allah yana neman alfarmar indai ya d’aukesa a matsayin uba kuma yana ganin girmansa to kawai ya bar maganar ya yi wa su Jidda addu’ar samun zaman lafiya.

Sai da

Baba ya tabbata ya d’aure Yash da jijiyoyin jikinsa tukunna ya barshi jiki a sanyaye…..

Tun daga nesa da ya taho ya Nafi’u ya fara murmushi dan ba kad’an ba ya ji dad’i a cikin ransa matuk’a

Dama d’azu da sassafe da ya je ya yi masa magana a take

ya yi masa alk’awarin inshaaAllah zai zo,kuma dama tun a d’azun ya lura wannan karon ya Musbah ya ji fad’an da ya yi masa sosai shiyasa tun a lokacin ya ji sanyi da dad’i a ransa dukda kuwa uwar ramar da ya ga

Abokin nasa ya yi.

Sai da ya gama parking

mashin d’insa tukunna Baba ya lura da shi ya gane sa…..k’uraaa masa ido ya yi gaba d’aya tashi d’aya tausayinsa ya lullub’esa dan kana ganinsa ka san yana cikin matsananciyar damuwa.A hankali Baba yake jin duk wani takaicin Ya Musbah da ya k’unsa yana warw

arewa sakamokon fahimtar da ya yi tabbas ba yin kansa bane kuma shi kansa ba ya jin dad’in abunda yake yi d’in dan gashi gaishe da shi yake yi amma sam ya kasa kallon cikin idanunsa kamar ma kuka yake son yi.

Ahankali ya had’iye wani k’ululun abu da ya to

kare masa mak’oshi yace”Alhamdulillah Musbahu”still yana kallonsa yana karantarsa.

Sai da ya sake yin k’asa da kansa kafin yace”ya k’arfin jiki ya fad’i hakan a hankali.

“Alhamdulillah”Baba yace daga haka ya maida dubansa ga Ya Nafi’u yace”Nafi’u na tu

ra maka kud’in,ka je ka siyo gadon,kaka mallan kai yake jira tun d’azu ku kai gidan.”

A hankali Ya Musbah yace”Baba ba za a hak’ura da maganar nan ba,ka yi hak’uri dan Allah ka….”

Cikin fushi Baba yace”kai har yaushe ka zo ka ji halin da ake ciki da

har za ka tsomo mini baki a cikin al’amurana?Kar fa ka kaini bango Musbahu kulaka da ka ga na yi ba shi yake nufin na manta abubuwan da ka tafka ba!”

Da sauri kaka mallan ma ya tsomo baki,dama d’azu ma saboda Yash ne ya yi magana shiyasa bai tanka ba dan

haka yanzu ya samu bakin magana harda cewa “a cikin duhu aka kama Jidda da Al’ameen amma shine saboda rashin sanin ciwon kai still suke da bakin k’orafi ga Yusuf wanda ya ji ya gani ya rufe ido zai aureta a hakan.”

“Yashjub mu je ciki”

Baba ya ce,daga ha

ka ya juya,har Yash zai bisa sai wayar sa ta d’au k’ara ganin sunan Daddy yasa yace”Daddy yana kirana bari in je in dawo kafin d’aurin auren.”

“To”kawai Baba yace daga haka ya shige cikin gidan dan yana so ya yi wanka ya shirya da wuri gashi har 9:00 ta y

i.

Su Ya Musbah sun san shawo

kan Baba ba abu mai sauk’i bane dan ransa ba a b’ace ba ma idan ya turje babu mai sa shi ya bari ballantana yanzu da yake a fusace shiyasa gaba d’aya hankalinsu ya sake tashi suka cigaba da addu’a kawai..dan tunda har Yas

hjub ya sa baki ya k’i yarda to addu’a kawai za suyi ta yi su jira Ubangiji ya yi ikonsa ya ceto rayuwar Jidda.

28 September 1994

….zaune take a tafkeken parlourn gidan da ya ji kayan alatu daban daban…a cikin shekarun da ba su fi hud’u ba Mijin nasu b

ud’u yake samu ta ko ina Alhamdulillah..sun chanja gida ya gina musu bungalow guda biyu tafkeke iri d’aya a cikin gate da compound d’aya ko wacce da b’angarenta sai kuma boysquaters babba shima a ta gefe…ya siya musu gwala gwalai har motoci ya siya musu gu

da biyu iri d’aya zani kuwa mafi tsada na wannan zamanin shi suke d’aurawa ita da Abokiyar zamanta!sai dai fa ita duk wannan daula da ake ciki sam hankalinta ba a kwance yake ba zuciyarta babu dad’i nutsuwarta ba ta tare da ita sakamokon juya mata baya da

Mijinta masoyinta abun k’aunarta ya yi tun lokacin da ta haihu shekaru hud’u kenan.

Tashi d’aya ya chanja mata ba tare da ta san laifin ta garesa ba.A yadda yake nunawa kamar har yanzu yana k’aunarta tunda yana masifar kishinta har yanzu kishi mai tsanan

i amma kuma ko kusa da shi baya so ta je..hantara kyara da tsangwama ne kawai yake shiga tsakaninta da shi gashi tsabar kishi ya maida ita kamar prisoner ko baranda ta fita indai mai gadi ko mai wanki wani ya ganta to fa ta shiga ukunta a ranar,hakanan tan

a ji tana gani Abokiyar zamanta za ta tambayi fita a barta amma ita ba ta Isa ba kitso kawai ta san tana zuwa bayan layi shima tare ita da Abokiyar zamanta.Ita sam ta kasa gane kan Imam kwata kwata dan kamar ma zarginta yake yi watak’il saboda ya san ba ya

sauk’e hakkin ta da ya rataya a wuyansa shiysa yake zargin za ta je ta nema a waje…

A take hawaye suka shiga sintiri a kan kyakkyawar fuskarta,shin wannan wacce iriyar rayuwa ce??gashi ba ta da gurin zuwa da ma Imam d’in shine Uwa shine Uba kuma Masoyi a

gareta yanzu kuwa abubuwan da yake nuna mata ita kanta ta san kora da Hali ne k’arara yake yi mata,ya gaji ita!

A da tana tunanin ta yi sa’ar Miji yanzu kam tabbas ta san ba ta yi ba,instead Ubangiji ya had’ata da mugun Miji Mugu ajin farko!

“Khadija wa

i har yanzu ba za ki bar kukan nan ba?na gaya miki addu’a itace mafita…wallahi Imam har yanzu bai yi miki rabin abunda ya yi mini ba,haka yake zai daina wata rana dan Allah ki yi k’ok’ari ki cire damuwa a ranki mana.”

Muryar Abokiyar zamanta wadda shigowa

rta cikin b’angaren nata kenan ta katse mata tunani.

A hankali ta d’ago ta kalleta daidai tana zama da Yaronta a hannunta.

Cikin sharar hawaye tace”ba komai Mommy,kar ki damu na san wata rana sai labari.”

Cikin son kawar da maganar dan zuwa yanzu ko lal

lashi ba ta so a cika yi mata gaba d’aya sai ta sake zama emotional dan haka ta d’an k’ak’alo murmushi tace”Yassir! Ina ka baro Yasira?ko tana chan tana sana’ar?”.

Ta fad’i hakan tana mai mik’awa Yaron hannu alamun ya zo gareta.

“Kamar kuwa kin sani..t

un da Baba larai ta yi musu wanka ita da Yahanasu suka koma bacci har yanzu ba su tashi ba..”

Murmushi ta yi tace”Allah ya yi albarka ya had’a kawunansu”

“Am khadija ko za ki yiwa Hajiya Mama magana a samu Yashjub ya dawo..ya yi k’ank’anta a zuwa Hutu

ya dad’e haka a wata k’asar gashi an koma makaranta.”

Dariya ta yi kafin tace”yanzu Mommy sai in kira Hajiya Mama in ce mata Yashjub ya dawo ya yi k’ank’anta?ai sai a ga rashin karar mu..ki yi hak’uri ita kanta na san nan ba da jimawa ba za ta dawo da s

hi..ke da ya kamata ace yanzu fafutukar ta yadda za ku shirya ma kike yi! idan ta ji mun ce Yash ya dawo ai bak’in jini za ki sake gogawa kanki har ni sai ta shafa….”

Shiruu Mommy ta yi kafin ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya tace”Allah ya sa mu dac

e”

“Ameen”Khadija ta yi ta fara yiwa Yassir wanda ta karb’a wasa shi kuma yana dariya.

“D’azu dai Daddy ya kori mallan lawal,ai dama na gaya miki yadda ya sakawa Yaron nan k’ahon zuk’a ba zai barshi ba.”

Shiruu Khadija ta yi kafin tace”yanzu kenan ta

tabbata Daddy zargin na yake yi?”

“Ba zarginki yake yi ba Khadija masifar kishi ne kawai,ke dai ki yi ta addu’a sannan kamar yadda kika fad’a wata rana sai labari..

Ki yi ta sallar dare kina gayawa Ubangiji na san kina yi amma ki k’ara,jikina yana bani i

nshaaAllah yana dawowa daga Abuja za ku shirya komai ya zama labari…”

A hankali Khadija tace”Au ya tafi?”.

Jin jina kai Mommy ta yi kafin tace”bai yi miki sallama ba?”

Sai kuma ta kawar da zancen tace”bari in je in had’o y’an kud’ad’e in bawa mallan

lawal,Yaron yana bani tausayi wallahi bashi da kowa fa maraya ne gaba da baya.”

Tana gama fad’in haka ta mik’e ta bar mata Yassir ta nufi k’ofa tana cewa “bari na je na d’auko.”

Daga haka ta fice….

Tana fita itama ta mik’e ta nufi bedroom d’inta da Ya

ssir a hannunta…wajen ajjiye kud’ad’e ta d’aga ta zaro masu nauyi da niyyar idan Mommy ta dawo ta bata tace ta bawa mallan lawal d’in dan ko ba komai shima maraya ne kamarta kuma saboda ita a ka koresa….tana d’aukowa ta jiyo kenan suka yi ido biyu da shi,d

a farko tsoro ya bata saboda ta san mallan lawal d’in da ta sani ko giyar wake ya sha bai Isa shigo mata har cikin bedroom ba,ganin yana magana yana matsota ne ya sa ta fahimci tabbas fa shi d’in ne dan haka cikin tsoron gudun a gansu fushi da hargowa ta f

ara ce masa”ya fice mata daga d’aki”

Ba tare da b’ata lokaci ba.

Gadan gadan ta ga ya nufo ta

daga haka bata sake tuna komai ba…sai farkawar da ta yi

wadda ta ji inama ba ta farka ba inama wucewa lahira kawai ta yi da ya fiye mata kwanciyar hankali.

Daga ita sai under skirta kwance a gado d’aya lullub’e cikin bargo d’aya da mallan lawal wanda shima wando ne kawai a jikinsa yana kwance yana sharar baccinsa peacefully.

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”

Ta shiga ambato ba k’ak’k’autawa tana jin wani

irin bak’in ciki da tashin hankalin da bata tab’a jin kwatankwacin irin sa ba.

Tashi d’aya ta fashe da kuka ta fara k’ok’arin tashi amma sai ta kasa motsi kwata kwata saboda wani masifaffen tashin hankalin da ya sake mamaye ta sakamokon muryar Daddy da ta

ji yana cewa”har fa na kama hanya kuka saka ni na dawo saboda takardun! ke da kika gansu a hannun Yarinya ai kamata ya yi ki amshe ki kawo mini.”

Cikin kwantar da murya ta ji muryar Mommy tana cewa”to ai Daddy ban yi tunanin naka bane ni na d’auka na Mam

an nata ne da na ga ta yo

nan d’in da su,ba dan yanzun ka gaya mini kalar envelope d’in ba ma da yanayinta da ba ganewa zan yi ba….”

A hankali Khadija ta koma ta kwanta ta ja bargon ta lumshe idanuwanta kawai saboda no way out dan a halin da ake ciki

ma key ta ji Daddy yana murzawa ta waje zai bud’e k’ofar ya shigo yana cewa”yau kuma Khadija rufe kanta ta yi ta ciki kenan!Allah ya kyauta!”.Gashi ba ta ga makulli a jikin k’ofartata ta ciki ba.

Tsabar tashin hankali sumewa ta yi,ruwan da Mommy ta s

hek’a mata ne ya sa ta farka a gigice chan ta hango Daddy ya nufo ta gadan gadan da wuk’a a hannunsa kafin ta yi wata wata har ya Burma mata a ciki………

Sama sama ta ke jin Mommy tana kuka tana rok’on Daddy tana cewa”kar ka yi haka Daddy,Ubangiji kad’ai ne

ya Isa ya yanke hukunci kar ka yi abunda zaka kai kanka prison ka bud’e musu su fito dan girman Allah…..”

K’aurin wuta ta fara ji kafin hayak’i dga haka ta ga wuta tana ci wanda hakan ya tabbatar mata tabbas Daddy wuta ya cinna musu.

Kamar d’azu yanzun m

a ba ta yi yunk’urin yin komai ba dan ba za ta iyaba gashi jikinta ba kwari ba ma ta gani sosai ga tashin hankali..ko yatsarta ba ta iya d’agawa.

…..Ba ta san Ina Mallan lawal ya yi ba ita dai ta ji an d’auke ta sannan muryar wani yana cewa”ta nan za ku

bi”

Wanda har gobe ta kasa tantance muryar mutumin ballantana ta yanke hukunci.

A cikin wani d’an madaidaicin gida ta farka ta ganta ana yi mata k’arin ruwa ga likita a gefenta da mallan lawal.

Rufar mata suka yi suna tambayar ta ya jikinta itakam

bak’in ciki da tsananin tashin hankalin da take a ciki ma bai barta ta ko kallesu ba…duddubata likitan ya yi ya cewa mallan lawal “idan wani abun ya tashi ya nemesa” daga haka ya yi musu sallama da Allah ya k’ara sauk’i ya fice.

Yana fita mallan lawal ya

gyara zama ya fara magana”Khadija ki yi hak’uri dan girman Allah..wallahi sharrin shaid’an ne amma inaso ki san cewa babu abunda ya shiga tsakaninmu dan ko da na yunk’ura kasa aikata komai na yi a gareki….na san kin tsaneni ba kya son jin ko murya ta ma sh

iyasa na zab’i in yi nesa da ke daga yau har abada.

Ga gida nan ki zauna a ciki kar ki tambayeni a ina na samu kud’in kawai inaso ki san wannan gidan na ki ne ga takardun nan a cikin wachchar drawer!ki yi hak’uri ki yi hak’uri ki yafe mini dan girman Alla

h”.

Yana gama fad’in haka ya mik’e yace mata”a cikin garin Abuja muke ba a kano ba.”

Daga haka ya sa kai ya fita.

Sai da ta tabbatar da ya yi nisa tukunna ta mik’e tsaye..d’inki ne a cikinta amma kawai tsintar kanta ta yi da fara takawa a hankali a ha

nkali a haka har ta fice da ga d’akin ta fice daga cikin gidan gaba d’aya,ta ya ma za ta fara zama a gidan da lawal ya ajjiyeta?! ba zai yiu ba!.

Dare ya yi a lokacin gashi unguwar shiruu babu ma mutane sosai…..

Tafiya kawai take yi ba ta san ina za ta j

e ba ba kuma ta san abunda ya kamata ta yi ba…wani ikon Allah zuwa yanzu ta nemi zafin da cikin nata yake yi ta rasa amma kuma ko ba ta kalla ba ta san d’inkin ya warware dan tana jin yadda jini yake bin jikinta…ta lura da yadda wata mota take ta binta a h

ankali sai da aka yi kusan tafiyar minti ashirin da mutumin ya ga ba ta da niyyar tsayawa gashi sai faman zubda jini take yi yayi parking motar a daidai gabanta ya fito yana k’are mata kallo.

Sai a lokacin wata juwwa ta kwasheta ta tafi ta zube a wajen.

Sai da ta yi kwana biyu tukunna aka samu ta farfad’o da mugun kyar.

A asibiti ta bud’e ido ta ganta,wannan mutumin da ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login