Showing 237001 words to 240000 words out of 259716 words

Chapter 80 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

29

lura tafiya za su yi Wallahi da a yau zata had’a har da nata…..

“Ya’isha sannu da zuwa!”

Muryar Manubiya ta katsewa duk su ukun tunani…ko juyawa Najeeb bai yi ba Siyama kuma haka kurum

gabanta ya yanke ya d’an fad’i yayinda Ya’ishan ya d’an yi murmushi tace”yauwwa”kawai,daga haka ta yi gaba ba tare da ta san wanne a cikin flat biyun za ta shiga ba,dan ba za ta iya jurar ganin Siyama tsaye jikin Najeeb ba suna wannan rahar ta san tsaf zat

a iya mutuwa..shi kuma ta lura har wani sake ruk’o hannunta ya yi……

Tana wucewa Najeeb ma yace”bari su tafi”

Hakanan suka rabu Manubiya tana masa tsiya akan ‘gaskiya itadai bata gama ganin k’anwarta ba haka kurum ya zo da wuri!’

shi kuma yanata dariy

a.

A tsaye ta sameta gabn flats d’in dan haka suka sake gaisawa tukunna suka nufi ciki.

Ba yabo ba fallasa Ya’isha ta gaisa da kowa har Hadiza da Baraka kafin ta nemi ganin Manu in private…a ranta tana addu’ar Allah ya sa komai ya zo mata da sauk’i.

Suna shiga d’akin Manubiya ta cire hijab d’in jikinta ta linke ta ajjiye,sanye take ta wata riga y’ar kanta mai k’aramin hannu pink da hula pink mai d’an karen kyau.

Sosai Ya’isha ta ji dad’in ganin hular dan haka ta shiga tunanin ta Ina za ta fara!y

a za ayi ta samu!…

Da kyar ta iya yiwa Manubiya bayanin yadda suka shirya ita da Mommy d’azu a Napep tana yi tana hawaye itama Manubiyan sai da ta yi hawaye tace mata ta kwantar da hankalinta inshaaAllah zata saka Baki a al’amarin Mommy kar ta damu itam

a Mommy ai uwa ce a gareta…sam bata ce zata yi komai a case d’in Yassir ba dan babu ruwanta a case d’in Yassir.

Sosai ta girgiza da ta ji ance Baba Larai ta rasu

A take ta gayawa su Inna aka kira su Mommy itama Ya’ishan aka yi mata gaisuwa sannan suka f

ara shirye shiryen zuwa amma sai Ya’ishan tace”ba komai su bari sai gobe”dan ta san Mommy ba ta gidan yanzu.

Hakanan shima Yash da ta kirasa ta tanbayesa yace ta bari sai gobe a ransa yana mamakin mai ya kai Ya’isha gidan su Manu!!.

Kiraye kirayen

sallar Magrib aka soma dan haka duk aka tashi aka shiga alwallah ana gabatar da salla,a d’aki Ya’isha ta yi alwallah ta fito waje domin yin sallah,zuwa yanzu hanakalinta ya fara tashi dan tun d’azu Manubiya ba ta cire hula ba bare ribbom..

Sai da ta ji

kamar ta doka tsalle sakamokon pink d’in hular Manu da ta hango a kan hannun kujera itakuma ta d’aura k’aton jilbab d’inta na d’azu a kanta ya rufe ko’ina tana sallah ita da Inna a gefenta.

Ba ta yi wata wata ba ta k’arasa dan parlourn babu kowa tana

zuwa ta zauna a kan kujerar ta d’au hular ta danna a jaka jikinta har yana karkarwa.

Ko sallar ba ta yi ba, suna idarwa ta cewa Manubiya za ta tafi da aka tambayeta ta yi sallah tace “eh”

Ba yadda basu yi da ita akan ta tsaya ta ci abinci ba nan ma ta

ce”ba komai,ta koshi”

Hakanan Manubiya ta yi mata rakiya suna fita ta samu Napep,har ga Allah sosai tausayinsu ya lullub’e manu wai yau Ya’isha ce ta zo neman alfarma a wajenta tabbas daman idan mutum ya yi hak’uri komai ya yi farko zai yi k’arshe….

Fad’an kalar murnar da Mommy ta yi da Ya’isha ta kai hular b’ata baki ne..hakanan ta yi ta sanya mata albarka…

A gabansu tsohon ya d’auko wata k’atuwar babyn roba ya sanya mata hular Manubiya a kanta bayan ya yanka kaza a kan hular jinin ya gama zuba a ka

i! daganan ya nemo allurai ya caccake zuciya da kan y’ar tsanar ko Ina uku uku guda d’aya kuma ya chaka a mak’ogwaronta….…haka dai ya yi ta abubuwa abun tsoro akan y’ar tsanar ya fi minti talatin,yana aiki a kan y’ar tsanar nan kafin ya nad’e ta ya tambay

esu cikakkun sunayen Manubiya suka sanar maasa ya ambata sau uku tuukunna ya mik’e ya ce musu “mu je”….

Hakanan suka zagaya bayan gidansa inda yake kiwon kayan daji kala kala har da macijizai suna zuwa ya nufi wani k’aton biri kamar gunki,suna zuwa birin

ya tashi daga kan dutsen da yake tsohon ya d’aga dutsen ya saka Babyn robar a k’asan dutsen ya mayar ya ajjiye birin ya koma kai ya zauna..

With full confidence ya ce musu “an gama!!.. kar ma su biya sa sai sun tabbatar an kai Manubiya kabarinta…….

H

akanan suka nufi gida ransu fess…ko da suka je su Yasira suka nemi d’aga musu hankali ce musu suka yi ba su yi abun ba Ya’isha har da rantsuwa dan haka suka yarda da su.

A b’angaren Kausar ma tana chan tana ta shirinta…akwai wata k’awarta y’ar babban

jami’in tsaro mai fad’a a ji a Nigeria da kewaye da ta ga hoton baba larai itama tazo yi mata gaisuwa,

Ta yi mamakin ganin ta da ciki tsoho dan haka ta tambayeta ba’asi itakuma Kausar d’in tace”Yashjub ta aura amma har yau kishiya ta hanata tarewa”

Dan h

aka k’awar tata tace ta kwantar da hankalinta za ta taimaketa.. yanzu haka

Ita kanta tanada sojojin da idan ta saka suka k’ulle mutum Wallahi ba Yashjub ba ko

waye bai Isa ya fito da shi ba,yanzu abunda za a yi ta bari idan ta haihu ranar suna za su k’u

llawa Manubiya sharrin sata inshaaAllah indai sojojinta suka tafi da ita ba a Isa a karb’ota ba sai ta dad’e sosai in lokacin sakinta ya yi suka ga dama sai su sakota kafin nan ita kuma Kausar d’in inshaaAllah ta gama samun Yashjub ta saka shi a corner har

abada…”.

Sosai Kausar ta ji dad’in plan d’in dan haka ta bari akan sai ta haihu d’in sai ta had’a har da abunda suka shirya ita da Abbakar za su yi d’azu a yita duk a lokaci d’aya ta yadda ko bibiyarta ma Yash d’in ba zai yi ba kuma dama still akwai abun

da ta shirya zata yi wa Manubiya a kan Yaron nan ma ta san dole abun ya sake zama effective…

InshaaAllah kafin ta fito ita kuma ta san yadda ta yi ta ko wacce hanya ta aure Yashjub,tunda har ga d’a a tsakani kuma babu Manubiya ta san aurensa ba zai yi mat

a wahala ba inshaaAllah.

Sosai ta ji dad’I hakanan suka rabu ita da k’awar tata tana ta murna ranta fess kamar an yi mata bushara da gidan Aljannah.

A b’angaren Yassir shima yanzu ya sake hawa ya koma gidan jiya..saboda da farko ya ji tsoro matuk’a a

mma yanzu da ya d’inke da Abokinsa ya gaya masa komai ya samu goyon baya d’ari bisa d’ari daga wajen Abokin sai zuciyarsa ta sake bushewa especially ma daya tabbatr video d’in a iyaka family yake yawo bai je ga hukuma ba tashi d’aya tsoronsa ya kau!

Kuma

ya ji Mommy tana cewa sharri aka yi masa dan haka zai fake da sharrin aka yi masa ya dage har sai su Daddy sun yarda ya samu su shirya.. da ga nan zai yi mai kankat dan Abokin nasa yace”InshaaAllah zai tsaya masa zai taimaka masa su ga bayan Yashjub kuma b

a za su sake tura wani ya kashesa ba!saboda kar a sake samun matsalak kamar lokutan farko! Next time kawai sakawa za su yi a d’auko musu shi su kashe sa da hannunsu.

But first ya samu ya fara wanke kansa ya shirya da su Daddy daga nan sai su k’addamar da

shirinsu saboda yanzu wani abun yana samun Yash shi za a zarga.”

A ranar da daddare Ya’isha tana tafiya daga gidan su Manu itama Baraka ta je ta karb’o garin maganinta wanda za ta barbard’a ta haukatar da Inna dan yanzu tace ba za ma ta sakata jinya b

a haukatata za ta yi dan sai ta fi wulak’anta idan ta haukace akan jinya.

Sam ba ta da mu da sharad’in bokan ba da yace mata”idan ta b’arbad’a abun Inna ba ta bi ta kai ba to itace za ta haukace”

Tashi d’aya tace masa “ta amince!”

Hakanan ta zube masa m

ak’udan kud’ad’e ta amso ta taho saboda ta san a inda za ta zuba ta yadda dole innar sai ta bi ta kai, ai abun ma ya zo mata da sauk’i tunda yace”kowa zai iya bi kawai dai ta tabbata itama Innar ta bi ta kai.Kuma awa ashirin da hud’u abun zai yi bai lalac

e ba saboda yana da k’arfi.”

Dan haka ta gama tsarawa a bakin k’ofar ban d’akinta za ta zuba ta san ko cikin dare ko da safe ko da rana dole ta shiga ta yi uzuri ta yi alwallah!ai Inna ta tafka babban kuskure da ta bata access da bedroom d’inta…hakanan ta

na ta sak’e sak’e a ranta ta iso gida jakarta kawai ta ajjiye, ta nufi cikin gidan…a nan ta samesu duk d’insu gaba d’aya har Baba ana hira,inna kuma tana zaune a kan darduma tana lazimi dan har ta yi shirin barci.

Tana shiga suka fara tambayarta ya jikin

maman Abbakar d’in tace da sauk’i,daga nan ta fara rarraba ido lucky for her Manubiya tace mata”ya yi barci yana d’akin Inna,in kun zo tafiya sai in d’auko miki shi.”

Ita ba ma shi take nema ba amma daga jin hakan ko gama rufe Baki ba ta bari Manubiya

ba ta yi ba ta yi wuff ta mik’e ta afka d’akin tana mai cewa”ai

yanzu za mu tafi ma bari in d’auko sa!”

Tana shiga ta tura k’ofar ta mayar ta rufe,sai da ta zuzzuba tukunna ta mayar cikin bra d’inta ta d’auki mai sunan Baban ta fito ta yi musu sallama ta

tafi yau ko jiran ya Musbah ma

Bata tsaya ba…shima kuwa ya zauna sai da ya gama zancensa da Hadiza tukunna ya koma kuma da ya je ya balbaleta da masifa dan bai

san da zancen zuwanta dubo maman Abbakar da daddare ba sam ba ta tambayesa ba,sannan yace”id

an Inna tana cikin d’akinta to za ta iya shiga in har kuwa ba kowa a cikin d’akin kar ta sake afka mata d’aki kamar yadda ta yi d’azu tun da d’akin ba na sa’arta bane ba!”

Saboda shi har ga Allah haka kurum bai yarda da shigar tata da ta yi ba da yanayint

a na yau gaba d’aya bai yarda da shi ba.

Ga mamakinsa har k’asa ta durk’usa tace”ya yi hak’uri ba zata k’ara ba!”

Ita kuwa a ranta cewa tayi “kar ka damu,zuwa gobe mai karekan ba za ta sake samun dama ba!daganan wallahi ko

kara idan na ajjiye baka i

sa ka shallaketa ba.!!”.MANNUBIYA

(Book 2)

Page 43

Na

Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Ya Musbah yana tafiya su Inna ma suka fara k’ok’arin shiga domin suma su samu su kwanta barci, dan Baba shi ka

m ya jima da wucewa d’akinsa tun lokacin da suka gama yiwa Yash da Daddy gaisuwa,ya wuce abunsa…

Hijab d’inta ta cire ta linke ta ajjiye a kan dardumar tukunna ta d’auka ta had’a ta yi folding d’insu tare ta tsaya tana kallon Hannun kujerar inda ta ajji

ye hularta tun d’azu da Magrib da zata yi sallah amma da ikon Allah har yanzu ba ta ganta ba.

Manubiya ta kalla ta kalli hular kanta wadda gwaggwo Suwaiba ta basu tsarabarta su biyu iri d’aya tace”Manu hular ki ce a kanki ko?

Ni Ina tawa??”

Murmushi Man

ubiya ta yi tace”

Dama na sani!”sai kuma ta d’aura da cewa”ai dama kinsan Siyama tace itama kalar take so..ba ta son kalar tata ita da Jidda!

bani da tantama itace ta d’auke takin a tunaninta tawa ce na ajjiye shine ta d’auke ta tafi da ita!”.

Shiru I

nna ta yi kafin tace”Anya kuwa?

Kuma inda ace ita ta d’auka ai da na san za ta ajjiye tatan..

kuma ai kafin Magrib Siyama ta tafi,ni kuma sai da na zo yin sallar Magrib d’infa tukunna na cire!.”

Cikin tarar numfashinta gwaggo Suwaiba tace”To,watak’ila

n mai sunan Baba ne ya d’auka ya saka a wani wajen

,yanzu mu je mu yi barci idan Allah ya kaimu gobe da safe sai a duba!

Idan ma ba a samu ba sai in je kasuwa in siyo yadi kalarsa ai ba za a rasa ba duk ku hud’un sai in had’a Hadiza ta kai tela ya d’ink

e a yi muku iri d’aya,kinga an huta ai ko?”

Dariya Manubiya ta yi kafin tace”Allah ni fa Ina tunanin Siyama ce ta d’auke! ta yi tunanin tawa ce saboda fa tun da ta ga tamu(ni da Inna) tace ita za ta yi anko da Inna kuma kalar ta fi so shine favorite col

our d’inta shiyasa ni kuma tun d’azun har yanzu da ta tafi ma ban yarda na cire ba!”tana dariya ta ci gaba da cewa”wuyan Hijab d’ina ma ya yi mini kad’an fa amma haka nake d’aurawa a kan hular ina yin sallah tun d’azu”.

Ta fad’i hakan tana dariya…..daga h

aka suka nufi d’aki gaba d’ayansu…ita dai Inna abun ya d’aure mata kai saboda har bayan tafiyar Siyama fa hularta tana kanta…amma kawai sai ta tsaya akan watak’il mai sunan Baban ne ya d’auka ya jefa a wani wajen dan haka ta bari akan gobe da safe idan All

ah ya tashemu lafiya sai ta duba!!!!.

Manubiya da gwaggo Suwaiba ne kawai suka shiga suka kama ruwa suka yi alwallah dan ita Inna da alwalarta,dardumarta da Hijab d’in kawai ta ajjiye ta kwanta saboda haka kurum ta ji ta wani iri ga kasala!!!

da mugun

kyar ma ta iya kaiwa kan gadon,tana kwanciya kuwa wani wahalallen barci marar dad’i ga takura ya yi awon gaba da ita.

Su kansu su Manu sun yi

mamakin baccin da Inna ta yi nan da nan gashi a karkace ma ta kwanta amma sai sukayi tunanin maybe ko gajiya ce,

Manu ce ta d’aura mata Kai a kan pillow tana mamakin yadda take fitar da numfashi da kyar daga haka ta rufa mata abun rufa ta d’an rage k’arfin ac dan a tunanin ta sanyin ne ba ta so…daga nan suka d’an tab’a hira ita da gwaggo Suwaiba suka yi addu’o’i suka

bi gado suma.

Da asuba!!…kiran sallar farko ne ya farkar da Manubiya da Gwaggo Suwaiba.

Band’aki gwaggwo Suwaiba ta wuce yayinda Manubiya ta d’an zauna a kan gadon ta yi shiruu sai da ta wartsake sosai tukunna ta juya cike da mamakin Inna ta shiga

tashinta dan kullum idan suka farka a zaune a kan darduma suke tadda ita.

Sau uku ta kira sunanta tana mai d’an tab’a mata Hannu amma shiruu…cikin tashin hankali ta mik’e ta k’arasa ta kunna wutar d’akin ta koma gareta da sauri ta shiga k’are mata kallo

tana kiran sunanta kafin ta zauna a daidai kanta a firgice ta d’an shafa fuskarta ta ajjiye Hannunta daidai saitin hancinta.

A firgice cikin tsananin masifaffen tashin hankali firgice da tsoro ta tashi da ga kusa da ita da mugun sauri ta ta d’an ja baya

ta tsaya a kanta tana ci gaba da kallonta jikinta yana wani irin karkarwa!

Daidai nan gwaggwo Suwaiba ta fito daga band’akin…yanayin Manubiyan ne ya sanya ta yi saurin k’arasawa inda take ta ruk’o hannunta itama idanunta suna a kan Inna tace”me ya faru?”

Ta yi mata tambayar jikinta itanma yana karkarwa dan yanyin yadda Innar take a yashe da kuma yanayin Manubiya sun mugun firgigita.

Juyowa Manubiya ta yi ta kalleta dai dai nan hawaye suka samu damar b’alle mata cikin tashin hankali tana magana da kyar

tace”ba ta numfashi kuma jikinta ya yi sanyi”

Ta yi mata maganar tana mai nuna mata Innar da yatsa…

Da kyar Gwaggo Suwaiba ta samu ta yi namijin k’ok’ari wajen k’arasawa inda Innar take ta zaune a gefenta ta shiga dubata…..tashi d’aya ta fashe da wani

irin rikitaccen kuka ta shiga ambaton “innalillahi wa inna ilaihirrajiun!

Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!!

Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!!!”.

Luuu!!! haka Manubiya ta tafi ta zube a wajen sumammiya…….

Sama sama take jin muryar ya Musbah shi

ma yana kuka yana

yayyafa mata ruwa yana kiran sunanta!

A hankali ta shiga k’ok’arin bud’e idanunta kanta yana wani mahaukacin sarawa…dishi dishi ta fara gani kafin ta samu idanunta suka ware tarr take kallon fuskar ya Musbah shab’e shab’e da hawaye wan

da hakan ya sake tabbatar mata tabbas Inna ta rasu!!!

Mik’ewa ta yi ta zauna ta shiga k’are musu kallo kowa ya hallara har da mai sunan Baba ya Nafi’u da Aisha da Likita yana duba Inna.

Fashewa ta yi da wani irin kuka kanta yana wani kalar mahaukacin

sarawa ta samu ta mik’e daga kan sofar dake a d’akin(inda suka d’aurata)

da mugun kyar ta wuce Ya Musbah ta k’arasa inda Likitan yake duba Inna tana shirin yin magana dai dai shi kuma ya d’ago ya kalleta tukunna ya kalli su Baba cikin karyewar zuciya yac

e”rai ya yi halinsa!sai dai mu yi mata addua!!..i’m so sorry…..”

Gaba d’ayansu har mai sunan Baba da Khairat fashewa suka yi kuka Yayinda ita kuma Manubiya ta nemi nata kukan ta rasa hawayen idanunta suka k’afe k’aff!!! tsabar masifa da tashin hankalin da

ta tsinci kanta a ciki wanda ba ta tab’a jin kwatankwacinsa ba tunda Inna ta kawo ta duniya!!tabbas zafi rad’ad’i zugi da d’acin rashin Mahaifiya daban yake!ta yi going through hell a rayuwarta amma ba ta tab’a jin kalar bala’in da ta ke jinta a ciki a h

alin yanzu ba.!

Ita ba ta fad’i ba ita ba ta zauna ba hakanan ta tsaya musu k’ememe ta k’ame kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login