Showing 231001 words to 234000 words out of 259716 words
zunubin da kika yaudareni kika sanya na aikata …..
Kukan da ya kufce masa ne ya sanya ya gagara cewa komai kafin da kya
r ya samu ya ci gaba da cewa”zamu had’u da ke a lahira!!!but for now Khadija bana k’aunar in sake jin ko da labarin ki ne dan haka ki bi Yassir ku b’ace mini da ga gani har gaban abada ba na so in sake jin ko da muryoyinku ne!!!!!”
Tabbas wannan itace r
ana mafi muni a rayuwar Mommy…wani irin kuka take yi tana janyo numfashinta da mugun kyar….duhu duhu kawai take gani!!
tabbas ta san Idan ta biyewa Daddy tsaff zai sake ta a take a yanzu shiyasa ta yanke shawarar tafiya kamar yadda ya buk’ata tun kafin ta
b’intike igiyoyin aurenta ta tonawa kanta asiri ta tarwatsa kanta….gara ta samu ta je ta yi sabon shiri a samu ya biyota ya rarrasheta ya d’aukota da kansa ya dawo da ita gidan, daga nan kuma ta san abun yi saboda ta riga ta san ba kowa bace silar wannan
bala’in da take a ciki face Manubiya,dan haka dama ta gama tsarawa tunda ta k’i fita daga rayuwar Yashjub gara kawai su mutu tare cikin gaggawa……tun kafin su zamo ajalinta…..
Tana cikin wannan tunanin kamar a mafarki ta ji muryar Daddy yana cewa”kwanak
i da kika tarwatsa auren Yassir da Kausar na sake ki!!
Da na fahimci abunda kika koyawa y’ay’ana kika turasu suka je suka aikata a gidan Yashjub shima a take a wannan lokacin na sake sakinki!!!
Kuma na san baki manta da sakin farko ba.. dan haka yanzu ni
da ke babu maganar aure har abada!.”
…..Da farko duhu Mommy ta gani ya mamaye ganinta,sai kuma ta daina ji gaba d’aya kafin ta ji k’afafunta da hannunwanta da duk wani sassa na jikinta kamar ma babushi!!finally kuma ta tafi luuuuu ta zube a wajen suma
mmiya.MANNUBIYA
(Book 2)
Page 42
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
Gaba d’aya Yaran kanta suka nufa har Junior,babu kalar ruwan da ba su yayyafa mata ba amma ko gezau!
Dan haka Yasira ta kalli Ju
nior hankali a masifar tace”Junior taya ni mu d’auketa mu kai ta sama sai in kira Dr…”
Ko gama rufe bakinta ba ta yi ba Daddy yace”amma ba ku ji abunda na fad’a ba ne?!!
Wanne saman za a kai ta?”
Cikin tsananin mamaki Yasira ta d’an cika Mommyn ta d
’ago tana kallonsa idanunta jazir tace”Daddy suma fa ta yi?a hakan still baka hak’ura ba so kake ta fitar maka daga gida?
Atleast ka tsaya a samu ta dawo cikin haiyyacinta mana sai a yi komai dan girman Allah.”
Hajiya Mama ta so ta saka musu baki tun d
’azu amma kuma sai ta ga wannan decision d’in Daddy ne to make, ita dai ta basa shawara dan haka kawai sai ta ja bakin ta ta yi shiru.
Cikin d’aci Daddy yace”Yasira ban bawa kowa ikon ya hau mini da ita sama ba sannan iyaka minti biyar na bayar a fitar
mini da ita daga cikin gidana!”.
Sosai zuciyar Yasira ta hau tafarfasa ta fusata sosai dan a ganinta no matter what ko dan darajarsu bai kamata ace ya kori Mommy ba on top of that kalli halin da take a ciki amma ya dage kawai shi a fitar masa da ita dag
a cikin gida kamar wata annoba!!
Idan ta gaskiya za a bi ai ba ita ta sanya Yassir ya yiwa Yashjub abunda ya yi ba!…..
Cikin sharar hawaye ta mik’e zuciyarta a iyaka wuya tace”Daddy muddin fa Mommy
ta fita muma binta za mu yi tabbas!!!
Cikin matsowa
kusa da shi tace”are you still willing to loose us too??akan dai ka tsaya a yi magana a yi sulhu??”
Shiruu ya yi kamar ba zai ce komai ba (dama wannan shine abunda shi da Hajiya mama suke gudu!!!)
kafin chan ya d’ago ya kalleta yace mata”time d’in da n
a baku ku fitar da ita ya kusan cika…Yasira nan gidan ku ne feel free ki zab’i wajen Mahaifiyarki sannan ki dawo nan a duk lokacin da kika ga dama no body will stop you.
Iyaka abunda na sani na kuma tsaya akai shine a yau a yanzu sai Khadija ta bar cikin
gidana ta bar rayuwata har abada!!!!.”
Wani irin kuka Yasira ta fashe da shi ta juya ta fita daga parlourn gaba d’aya rai a b’ace hankali a masifar tashe…….
Tana fita Daddy ma ya sa hannu ya share hawayen sa ya wuce sama da sauri…..
Hajiya mama ta
bisa…..A tsaye ta same sa yanata faman safa da marwa yana ganinta ya k’arasa gareta ya rungumeta ya fashe da wani irin kuka yace”ki yi hak’uri na gagara ci gaba da tolerating Khadija gashi kuwa abunda kike gudu shi zai faru da ni ‘za ta rabani da y’ay’ana
Maamaa’!”.
Cikin tsananin jin tausayinsa Hajiya mama ta shiga rarrashinsa tana cewa”kar ka damu ba komai…dukda ba haka na so ace ka yanke hukuncin da wuri cikin fushi ba amma ba komai inshaaAllah komai zai yi dai dai,mai gaskiya shi ke da riba a ko da
yaushe inshaaAllah za su dawo gareka za su gane gaskiya mu dai namu addu’a!!”.
…..
Har sama su Yadira suka bisa suka d’urkusa suka rik’e k’afafuwansa suna kuka akan ya yi hak’uri ko ba aure a tsakanin sa da Mommy ya barta ta ci gaba da zama a gidan ko a
k’asa ne ya bata d’aki amma furr!!Daddy ya k’i yarda ya k’i amincewa k’arshema a gaban su ya kira y’an sanda ya ce su zo gidansa!
Yana gaama wayar ya kallesu yace”Wallahi idan Mommy da Yassir ba su fice masa daga gida ba har suka bari y’an sandan nan suka
zo to sai ya sa an tafi da su cell!”.
Kuka sosai Yaran suke yi suna magiya amma Daddy ya sam ya k’i sauraronsu,Hatta Ummi wadda suka zo suka tarar da ita tare da shi a d’akin sai da Yadira ta rik’e hannunta tana kuka tana cewa”dan Allah ta saka baki ta
tayasu bashi hak’uri.”
Hakanan Ummin ta fara bawa Daddyn hak’uri itama dan sosai zuciyarta ta tab’u da al’amarin gwanin ban tausayi,ta san Mommy ba ta kirki amma ko dan Yasmeen da Yadira da ta tabbatar sun shiryu sosai tun kwanakin baya yanzu kuma suke i
rin wannan kukan ya kamata a tausaya musu……
Sai dai fa duk wannan abun da suke yi ko a kwalar rigar Daddy fad’a musu yake yi yana sake maimaitawa “wallahi idan har suka bari y’an sanda suka zo to
sai sun tafi da su Mommy.!”
Suna cikin wannan halin Y
a’isha ta kira su tace”idan za su bi su su sauk’o,ita da Yasira suna k’asa suna jiransu!”
Dan ita dama tun lokacin da Yasira ta kira ta ta sanar mata ko yunk’urin lallab’a Daddyn ma ba ta yi ba kuma wallahi ta gama sakawa a ranta sai ya nemesu ruwa a jall
o!!!.
A b’angaren Yassir kuwa yana chan side d’insa yana jiran azo a ce masa ai Mommy ta wankesa komai ya wuce amma kawai sai ganin Yasira ya yi a hargitse tace masa”Mommy ta suma Ashe Daddy yanata sakinta ita ba ma ta sani ba yanzu babu aure a tsakanin
su sannan su Yasmeen suna chan suna ta lallab’ata Daddy amma ya k’i yarda su ci gaba da zama a gidan ya ma kira y’an sanda ya ce “a zo a tafi da su(shi da Mommy)”
Dan haka kawai ya taho su tafi gidan Mommy dake a tudun a Yola Ya’isha ta kwaso keys a samu
a kira Likita Mommy ta farfad’o dan Yasmeen ta kasa yin komai kuka kawai take yi,idan ta farfad’o suka nutsu sai su san abun yi!.”
Da farko dafe kai Yassir ya yi da mugun k’arfi da hannunsa duka biyyn kafin ya cika ya fara fatali yana fashe fashe har ha
nnuwansa sai da ya farfasa!
Hausahinsa Yasira take ji d’azu amma har ga Allah zuwa yanzu duk sai ya bata tausayi dan haka ta matsa ta rungume sa wanda hakan ya sa ya fashe a wani Irin kuka ya sakar mata dukkannin nauyinsa suka zube suka durk’ushe a waje
n duk su biyun suna kuka!!
Cikin wani irin kuka yace”Yasira ba laifina bane ba,Daddy ya fi fifita Yashjub ya bashi duk dukiyar family d’innan bayan kamata ya yi ace ni da shi munada equal right….”
Muryarsa ce ta sark’afe sakamokon kukan da ya ci k’arfins
a ya sake sakinsa sa da mugun k’arfi…
Tabbas zuwa yanzu kam Yasira itama ta yarda idan Yassir yanada mugun mugun laifi tou Daddy ne silar komai shiyasa tausayinsu ita da y’an uwan nata da Mommy ya sake lullub’eta ta kuma rushewa da wani kukan….
Sun jim
a a haka suna kuka kafin dakyar Yasira ta d’ago fuskarta tace”Yassir a situation d’innan da kake a ciki kar ka bari ka shiga case da hukuma,kamar yadda ya fad’a ka tashi mu bar masa gida!
Tabbas abunda ka yi ba ka kyauata ba Yassir amma kar ka damu kana d
a mu!kana da y’an uwa tunda na fahimci pushing d’inka aka yi…ka taso mu tafi mu je mu fara ji da Mommy a samu ta farfad’o sai a san abunyi…..”
Kamar wani k’armin Yaro hakanan ya shiga d’aga mata kai dan a mugun tsorace yake bai saba shiga masifa da tashin
hanakali irin wannan ba…
Important abubuwa ya kwasa daga nan ya rufo side d’in nasa suka nufi motocinsu.
Dai dai nan Yusra ta sauk’o itama da akwatinta dan Yasmeen tace a nan ita za ta zauna,already Ya’isha da Junior sun saka Mommy a motar Ya’ishan
shiyasa tana ganin su ta kunna motar amma sai fitowar Kausar data gani a gigice ya sanya ta kashe motar ta fito.
…..
Da kyar suka yi convincing Kausar ta hak’ura da binsu a cewarsu ta zauna a nan ta zame musu ido a nan d’in kafin su dawo sannan ta samu
ta haihu a nan d’in sai ya fi tunda ga Yash nan ya dawo inshaaAllah za su san abun yi Akan duk wata matsala tasu ta kwantar da hankalinta komai zai gyaru!za su dinga waya suna communicating,kar ma ta soma binsu yanzu gudun kar Daddy ya samu damar korarta
itama…..
Sun ci kuka sosai Yassir ma ce mata ya yi kawai za su yi waya daga haka suka shige motocin su suka fice daga gidan Yasmeen kuma da ba ta bisu ba ta kamo hannun Kausar d’in suka koma ciki dan ta yi nauyi sosai…duk su biyun suna kuka wiwi haka na
n suka nufi cikin gidan…
Su Yadira kuma direct gidansu suka wuce dan kukan da yake yi sosai ya d’agawa Junior hankali Shiyasa ya hanata binsu ma saboda condition d’inta.
A tunanin Kausar Daddy zai koreta itama amma ko kallonta bai yi ba hakanan ya wuc
e ta ya fita wajen y’an sandan da suka k’araso yanzun domin ya sallamesu a ransa ya gama tsara’itama zai koreta ne but sai ta haihu tukunna bayan sun karb’i d’an sun bawa Manubiya….’
Yashjub tun d’azu yake ta jin k’arar bud’e gate ana rufewa shiyasa han
kalinsa ya sake tashi dan tashi d’aya kwakwalwarsa ta bashi Allah dai ya sa ba harda Mommy aka bar gidan ba.
……
Duk yadda suka yi tunanin abun zai yiu a gida gagara ya yi dan bayan sun kai kayyakinsu,abun ya ci tura,sai da suka dangana Mommy da asibiti t
ukunna ta farfad’o da kyar.!
Ai kuwa tana tari tana hawaye hankali a tashe kamar tab’abb’iya ta shiga tambayarsu “ya ake ciki?a ina take?”
Ya’isha ce ta iya yi mata bayani Aikuwa cikin masifa da tashin hankali ta rufe su ta fad’a tace “dan meyaasa suka y
arda suka fitar da ita daga cikin gidan??..”
Sai kuma ta fashe da kuka ta fara jero Allah ya isa a Hajiya Mama da Manubiya dan sam batajin haushin Daddy kamar yadda takejin masifaffiyar tsanarsu a cikin ranta!
Hatta su Yasira ma sai da ta dasa musu matsa
nanciyar tsanar su Abhi da Hajiya mama a cikin ransu bayan ta Manubiya da suke zaune daram a kai.
Duk yadda suka so su lallashi Mommy sam abun ya gagara gashi dama suma a wuya suke shiyasa kawai suka fashe mata da kuka…ba ta damu da kukansu ba ballanta
ta sarara musu magana kawai take yi kamar tab’abb’iya kuma ta nace akan Itafa sai sun d’auketa sun mayar gidan Daddy dan Kwata Kwata jikinta babu kwari itan so so ta kasa tashi da kanta,shiyasa kawai Yassir ya juya ya fita ya je ya kira likita yana zuwa ya
yi mata allurar bacci da kyar dan sai da su Yassir d’in suka danneta tukunna aka samu aka yi sam ta k’i tsayawa.
Sosai Yassir yake jin tsanar Yashjub yana dad’a shigarsa ga tsoro ga tashin hankali…
Suma su Yasira sun ji haushin rashin zuwan Yashjub d’
in asibiti ya ga Mommy matuk’a.
Sai chan dare tukunna Mommy ta farka…tashi d’aya komai ya dawo mata sabo wanda hakan ya sanya ta ji inama ba ta farka ba.
One by one ta fara kallonsu tashin hankalin ta yana sake hauhawa sakamokon yadda ta ga fuskokinsu
sharkaff da hawaye dagaje dagaje kowa ta yi tagumi Yassir da Yassira kuma basa nan.
A d’an rikice ta tashi ta zauna ta kallesu tace “Ya’isha mai kuma ya faru??”
Sai a lokacin ma suka lura ashe ta farka dan haka daga Ya’ishan har Yusra haka nan suka nu
feta da sauri suka fad’a jikinta suka fashe da wani irin kuka.
Zuwa yanzu jikin Mommy har wani irin karkarwa yake yi!
A hankali ta zaro su daga jikinta k’irjinta yana dukan tara tara tace”ku fad’a mini menene kafin zuciyata ta buga”
Sai da ta sake tam
bayar su!ta maimaita!!ta daka musu tsawa a karo na uku tukunna da kyar Yusra ta bud’e wayarta ta kai mata hoton ta mik’a mata tana wani irin kuka.
A hankali jiki na karkarwa Mommy ta saka hannu ta karb’a hoton…………..Babu idanuwa sannan an yanke nonuwa da p
rivate part da y’an yatsun k’afa da hannu amma hakan bai hanata gane Larai tashi d’aya ba.
Jifa ta yi da wayar a mugun tsorace sai kuma ta turesu ta mik’e ta d’aura Hannu a ka ta fasa wata razananniyar k’ara.
Dai dai nan Yassir da Yasira suka shigo da
sauri suka k’araso suka rik’eta Yasira itama cikin kuka tace”addu’a za ki yi mata Mommy dan Allah ki yi salati ki daina ihu…”
Sai a lokacin Mommy ta shiga ambaton innalillahi wa inna ilaihirrajiun ba k’akk’autawa a gigice tana wani irin kuka jikinta yana
karkarwa.
Shiruu duk suka yi suna kuka kafin Ya’isha tace”an baku ita?”
Jinjina kai Yassir ya yi yace”Tana mortuary sun yi saurin saka ta a k’ank’arar saboda ta kumbura gawar ta fara wari!zuwa gobe da safe inshaaAllah sai a yi mata wanka a binne ta!”
Wani irin kuka mai k’arfin gaske Mommy ta fashe da shi
Haka suma su Ya’isha,babu mai rararahin wani kowa kawai kuka yake yi gaba d’aya d’akin ya birkice dan ko kusa da d’akin ka zo a wannan dare sai ka fahimci an yi musu rasuwa.
A tsaye ranar suka kw
ana babu wanda ya runtsa.
Washegari da sassafe suka nemi sallama aka sallami Mommyn daga nan suka d’auki Larai suka wuce da ita gida domin su yi mata wanka a mik’ata gidanta na gaskiya!!!.
Kamar yadda su Yasira suka ci karo da labarin gidan tsafin da
jami’an tsaro suka binciko a garin kano tare da hotunan victims d’in ta watsapp hakanan yau suma su Daddy suka gani har da Kausar…Hankalinsu ba k’aramin tashi ya yi ba..Yashjub ma yana idar da sallar asubah ya gani..
Daddy ya so ya hanashi zuwa inda suk
e amma kawai sai ya rabu da shi ya tafi Hajiya Mama kuma ta kira Yusra da Yasira ta yi musu gaisuwa tace ta mik’a gaisuwarta zuwa ga su Ya’isha.
Motocin su Yasira suna gama yinparking a k’ofar gidan Momy wanda ke a tudun yola dai dai nan Yash ma yana k’
arasowa kamar had’in baki, da ma ya san nan d’in suka nufa.
Mommy tana hangosa ta fito a fusace ko ya kan su Yasira da suke ce mata “ta tsaya su shiga ciki tukunna sai a yi” ba ta bi ba hakanan ta nufi Yashjub tana zuwa ba ta yi wata wata ba ta zabga ma
sa wani Irin rikitaccen mari……….
Da mamaki ya dafe wajen yana kallonta kawai ya ma kasa magana.
Ita kanta sai da ta mareshin ta d’an ji sanyi a cikin ranta tukunna ta ta yi tunanin considering the fact that Yassir fa da kashe sa ya so yi bai kamata ace
ta maresa ba,dan haka tace”tsabar kai dak’ik’i ne Yashjub ace a had’a video da voice d’in d’an uwanka amma ka gagara gane k’arya ne aka shirga?ina karatunkka da ilimin ka suke?sannan ka tartaro mini su Hajiya mama ka sako su cikin case d’in nan saboda bak
a san ciwon kanka ba?”
Ba ta jira jin ta bakinsa ba ta d’aura da cewa
“To bari ka ji ba ni ka wulak’antaba wallahi kanka ka wulak’anta kuma inaso ka sani wallahi tallahi muddin baka je ka wanke d’an uwanka ka shiryasa da mahaifinka ka gyara abunda ka la
lata ba ni da kai har abada!!
Ka b’ace mini daga gani duk ranar daka gyara b’arnar da ka yi sai ka zo gareni!”
Tana gama fad’in haka ta juya fuuu ta wuce ciki ta shiga ta gate d’in da su Yasira suka bud’e suke ta k’ok’arin shiga da motocin.
Har suka g
ama shigewa Yash yana nan yadda yake ya ma kasa motsi..”shin da gaske Mommy ta yi believing sharri aka yiwa Yassir kokodai