Showing 189001 words to 192000 words out of 259716 words
yake nunawa Doctor d’in hankali a mugun tashe…da hanzari shima Doctor d’in ya k’arasa da taimakon Yahanasu suka
kinkimeta suka d’aurata a kan gadon ya shiga bata taimakon gaggawa Yashjub kam ya ma kasa motsi ko magana hawayen ma sun k’afe in banda karkarwa babu abunda ilahirin jikinsa yake yi especially k’afafuwansa
dan har yanzun ba ta farfad’oba!luu haka ya tafi
zai fad’i da kyar ya rik’e kansa ya samu ya zauna a kan kujerar bayansa yana ganin bibbiyu.
An kai ruwa rana kafin da kyar aka samu ta farfad’o….ruwa Dr ya sake jona mata ya fita ya je ya kwaso wasu allurai ya yi mata har da ta barci…Sai da bacci ya yi
awon gaba da ita tukunna ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya ya juyo ya kallesu yace da Ummi”jiya jiya na gama ja muku kunne akan d’aga mata hankali ko?za fa ku ja wa yarinyar nan stroke da k’arancin shekarunta idan ba ku yi wasa ba!,jininta maimaikon ya
sauk’a hawa yake kuma yi ku kiyaye fa!.”
Cikin d’aurewar kai Ummi tace”lafiya fa muke zaune da ita muna magana,na ga ta fara duba wayarta sai kuma na ga ta mik’e daga haka ta tafi ta fad’i a k’asa.”
Numfashi ya fesar kafin yace idan ta farka ku kira
ni Allah ya rufa asiri”kawai.
Daga haka ya sa kai ya fice.
Shiruu duk suka yi suka zubawa Manubiya ido kafin Yash ya mik’e da kyar ya k’arasa ya d’auki wayarta a k’asan gado inda ya ga ta fad’a ,matsawa Yahanasu ta yi saboda itaama wayar tata take shiri
n dubawa….
Yana bud’ewa ya ci karo da sms daga bak’uwar number ta inda aka sanarwa Manubiya abunda ya faru jiya tsakaninsa da Kausar tiryan tiryan tun daga farko har k’arshe….
Jifa ya yi da wayar cikin fushi yace”enough is enough!!!”
Sannan ya fara k’ok
’arin fita.
Da sauri Ummi da Yahansu suka tare sa dukda Ummi ba ta ga message d’inba itama zuwa yanzu kwakwalwarta ta bata me ya gani.
Sai da suka yi da gaske tukunna suka iya tsayar da shi dan ya zuciya matuk’a ransa ya b’aci….
Cikin muryar fushi yace”
Ummi ki barni in je in same su komai ma ya ishe ni,Wallahi sai na sauya musu kamanni tunda basu san dai dai ba!”
Cikin rarrashi tace”Yash wa za ka tunkara? Me za ka yi musu?”
Ba tare da sanin inda ya dosa ba ma yace”na san a tsakanin su Yadira so
ju
st let me…..”
Hawayen da suka shiga zubo masa ne ya sanya shi kasa ci gaba da magana sai kuma ya nemi guri ya zauna ya dafe kansa”me na yi musu da zafi haka?me yasa y’an uwana suka tsaneni suka tsani farin ciki na?”
Sai da Ummi ta share hawayen da suka z
ubo mata tukunna ta k’arasa gefensa kan sofar ta zauna cikin sanyin murya tace”kar ka ce haka Yashjub,ba ka ta tabbaci…”
Cikin katseta yace”Ummi su ne!idan ba su ba wa ya san maganar in ba y’an gidan mu ba?yaushe aka haifi Yaran nan da za su zama mugaye m
akirai kamar haka?me na tab’a yi musu da za su yi mini haka?”
Shiruu Ummi ta yi dan ta ma rasa bakin magana.Ahankali Yahansu ta matso tace”Kamar yadda Ummi ta fad’a Yash ba lallai su bane ba,ka bi komai a hankali kamar yadda na gaya maka jiya…”ta san ko
da ace su d’in ne Mommy ce ta zuga su suka aikata kamar kullum amma kuma ba ta jin a tsakaninsu ta fi tunanin Mommyn ce da kanta ya aikata wannan d’anyen aikin.
Itama cikin katseta ya mik’e yace”Yaha to
waye idan ba su ba?Daddy wanda ya haifeni?ko kece?
ko Ummi?ko kuma Mommy?….”
Shiruuu ya yi kafin a hankali ya sunkuyar da kansa k’asa yace”damn it!!”
Sai kuma ya koma ya zauna ya yi shiruuu.
Kasa ci gaba da zama a d’akin Ummi ta yi dan ba ta san ta Ina za ta fara ba..ba ta so tana shigar musu Irin wan
nan case d’in.
Shiyasa ta kalli Yahanasu ta ce”bari in je Allah ya rufa asiri,Yash k’addara kowa da kalar tasa ka yi k’ok’ari ka cinye jarabawarka.”
Daga haka ta d’au Jakarta ta fice…ba ta da tantama wannan aikin Mommy ne.
Tana fita yace”ki je kema,id
an ta tashi zan ji da ita,I can face her…”
Cikin tausayawa tace”Yash ka yi hak’uri”
Wani kalar murmushin da ya fi kuka ciwo ya yi kafin yace”Yaha hak’urin nake yi a ko da yaushe amma wani abun dole aga weakness d’ina!…tunda nake a rayuwata ban tab’a
jin labarin uwa irin Mommy ba,I’m not sure yet Akan abubuwan da ta yi mini sannan ta saka su Yasira suka yi mini amma Yahansu tashin hankalin da nake a ciki ba kad’an bane ba saboda Ina jin tsoron ranar da zargina zai tabbata Yaha ban san ya zan yi ba.
In
a jin tsoro in ji sunada hannu a case d’in estate d’ina!
Ina jin tsoro in ji sune suka yi chatting da Abbakar suka bawa Manubiya magani….shiysa nake ta k’ok’arin gocewa amma message d’in nan da aka turo tabbas na san su ne wannan kam ba ni da tantama kum
a hakan ya sanya na sake yarda sune suke yi mini abubuwan da na kasa fahimtar ribar su idan sun tarwatsa ni!”
Ya fad’i hakan yana mai sakin kukan da yake ta k’ok’arin dannewa,rungumesa Yahanasu ta yi itama a take wani irin kuka ya kufce mata…Tabbas ta san
zafin da Yashjub ya ke ji a yanzu da ya fahimci Mahaifiyarsa ba ta son sa sannan ba ta damu da shi ba ba ta damu da farin cikin sa ba saboda she went through the same thing kuma har gobe tana rayuwa ne a cikin pain d’in….
Sun jima suna kuka babu mai rarr
ashin wani kafin da kyar Yaha tashiga lallashinsa tana basa baki…cikin sheshek’ar kuka tace”Yash har gara kai!
InshaaAllah na san akwai ranar da za ta zo maka wadda za ka fahimci Mahaifiyarka ta na son ka ba son kashe ka take yi ba tana son dukkanin abund
a kake so infact tana son ka fiye da komai da kowa a duniyar nan!
Unlike me! da zan rayu and have to live with the fact that mahaifiya ta ba ta sona ba ta k’aunata ba ta damu da ni ba ta yi using d’ina to get what she wan…”
Cikin katseta Yashjub yace”Yah
anasu ki daina cewa haka!babu kyau kin san fa ta rasu kar ki k’ara mata nauyi…kwakwalwata ba za ta iya tuno mini ita ba amma a ko da yaushe hajiya mama tana sanar da ni ita d’in mutumiyar kirki ce,kar ki ce za ki shiga abunda ya faru tsakaninta da Daddy ha
r ta kaisa ga cewa TV ‘kar mu sake ko da ambatar sunanta ne!’ wannan tsakaninsu ne kuma kinga har yau ba mu san menene ba balle mu shiga!
kawai ke dai har ma da ni kamata ya yi mu bi ta da addu’a da fatan samun aljannah…dan Allah Yaha kar in sake ji kin
yi wannan furucin game da mahaifiyar ki!.Mommy kuma tunda Allah ki ka ce nasan gagara misali ne….dan haka nima zan yi addu’ar abunda kika fad’a d’in ya tabbata zan yi addu’ar Allah ya sa duk zargi ne kawai muke yi ba gaskiya ba.”
Kallonsa take yi tashi
d’aya wani Irin yanayi na tausayi k’unci da rashin jin dad’i suka lullub’eta.Ba ta san lokacin da ta afka jikinsa ta fashe da wani sabon kuka ba.!
Sun jima a haka kafin da kyar suka samu suka lallashi junansu ta sake jaddada masa”ya bi komai a hankali k
amar yadda suka gaya masa kar ya d’au mataki a kan kowa ba tare da kwakkwaran shaida ba.”
Awannnin Manubiya biyu tana barci kafin suka ga ta fara motsi…duk su biyun tashi d’aya k’irjinsu ya buga kafin Yash ya dake ya mik’e ya k’arasa ya zauna a setin
kanta bakin gadon yacewa Yahansu ta je ta kira Likitan.
Tana gama bud’e idanunta Doctor ya shigo…yana nan inda yake aka gama dubata Dr d’in ya fita.
Yana fita tun kafin su yi magana ta kalli Yahanasu tace”d’azu kin ce za mu yi magana.Dan Allah Yahan
asu kar ki ce mini akan maganar message d’in da aka turo mini ne dan Allah Yaha ku ce abunda aka rubuta a jiki k’arya ne.”
Yahanasu tana shirin yin magana Yash ya ce “gaskiya ne.”
A hankali ta saki wani irin kuka mai cin rai….mik’ewa Yahanasu ta yi ta
fice zuciyarta sam babu dad’i.
Sai da Yash ya sauk’e wata nannauyar ajiyar xuciya ya had’iye wani abu mai d’aci da ya mak’ale masa a mak’oshi tukunna tiryan tiryan ya fara zaiyyano duk wani abu da zai iya tunawa wanda ya faru a jiyan bai b’oye mata komai
ba…
D’ari bisa d’ari ta yarda da shi sai dai kishi takaici da bak’in cikin da suka tarar mata ne suka sanya take jin zuciyarta kamar za ta hantsilo ta fito waje har wani Jan numfashi take yi yana kufce mata.
Dai dai nan Mommy ta ja ta tsaya a bakin
k’ofar ita da Ya’isha waenda zuwansu kenan.
Kamar zai fashe da kuka yace”mun so mu d’an jinkirta saboda yanayin jikinki daga baya sai mu gaya miki amma kuma sai aka turo miki message.Ga gaskiya nan na faiyyace miki ita Baby da message d’in nan da aka tu
ro miki da kuma abunda ya faru da ni ya kamata ace kin fahimci so ake yi a raba mu dan Allah dan Allah Annabi kar ki bada k’ofa ki yarda da ni plss dan Allah….”
Tabbas wannan abu ne mai nauyi na tashin hankali da ya sameta dan za ta iya cewa bata tab’
a shiga rikici da k’unci kamar yau ba amma kuma ya zama dole ta bawa mijinta support sannan kamar yadda ya fad’a tabbas so ake yi a raba su,dan haka ita kuma duk rintsi duk wuya ba za ta bud’e k’ofa a shiga a raba su ba…..da izinin Allah.
Wani irin zafi d
a rikitaccen tashin hankali ta ke jinta a ciki amma ya zame mata dole ta danne kanta ta taushi zuciyarta ta tsaya musu…dan haka cikin sharar hawaye ta sa hannu ta rungumo sa itama kamar yadda ya yi mata tace”I trust you! kuma babu wanda ya Isa ya rabamu ba
zan bada k’ofa ba…duk runsti duk wuya ba za mu karaya ba.Abunda ya faru jiya babban al’amari ne amma na dad’e Ina neman tukuicin da zan k’ara maka na k’aunarka tsakaninka da Allah a gareni ban samu ba..
Ya Yash a matsayina na matarka Ina so ka saka a ran
ka kamar babu abunda ya faru tsakaninka da Kausar ka goge hakan a kwakwalwar ka nima na goge!ina so mu manta da duk wani takaici da bak’in ciki na daren jiya….indai saboda ni ne kake damuwa da fargabar mai zan yi tunani ko mai zan ce a kan case d’in to ina
so ka san cewa Manubiya ta goge komai ba ta rik’e a rai ba bata saka a gaba ba babu komai a gabanta sai burin farantawa mijinta dan haka ka cire damuwa ka cire bak’in ciki mu ci gaba da rayuwar mu cikin farin ciki…inshaaAllah da ni da kai har abada ba za a
ji kanmu ba.”
Kuka sosai Yash ya ke yi ya k’ank’ameta a jikinsa yana godewa Ubangiji da ya basa mar’atussaliha….ya ma rasa bakin magana in banda sake ruk’umk’umeta babu abunda ya ke yi yana ji kamar ya maida ita cikin cikinsa.
Shiruu Mommy ta yi har
sai da Ya’isha tace”hmmm..mu shiga Mommy za ta ci ubanta ne!.”
Tukunna suka d’an gyara daga tsayuwar lab’en da suka yi suka fara knocking.
Gaba d’aya Mommy kanta ya d’au zafi tabbas Manubiya fa sai sun sake tsayuwa a kanta sun k’ara k’arfi fiye da tun
ani dan tabbas Yarinyar nan ba ta wuce tunani su gashi shegen naci gareta…ita da ta zo ta d’anyi b’arin zance akan case d’in a samu ta ji ta yadda za ta d’aga hankali har sai ta ji komai daga nan su yi baram baram da Yashjub ta tafi sai gashi an samu wani
d’an albarka ya tura mana message ma gaba d’aya amma dukda haka ji abunda take cewa!..tana da tabbacin Kausar ce ta turo message d’in! tabbas dama tundaga jiya ta fahimci Kausar is up to something,ta d’an ji zafin yadda ta tsame su daga plans d’inta ta fa
ra yin gaban kanta ita kad’ai amma kuma da wata wainar gara wata!da Manubiya gara ta bi bayan Kausar sau million ma dan haka a nan za ta tsaya!a yadda ta ji furucin Manu na yanzu ta riga ta gama deciding abunda za ta yi….ba dare ba rana ita da Baba larai z
a su duk’ufa daga yau! Wallahi indai ta haifu cikin uwarta da ubanta sai ta juyawa Daddy lissafi ya aura wa Kausar Yashjub daga nan sai ta ga k’arshen soyayya sai ta ga k’arshen naci za ta ga yadda Manu za ta yi idan Yash ya k’ara aure za ta ga k’arshen ma
ratussalaha da Manubiya ta ke playing….
Yadda yashjub ya karb’esu ita da Ya’isha sai da suka sha jinin jikinsu…ga Daddy ya juya musu baya yanzu kuma Yashjub tabbas Manubiya ta tabbata mugun tsuro a cikin family d’insu amma ba komai inshaaAllah komai
ya kusan zuwa k’arshe.
An riga an yi abunda suka zo yi
shiyasa kawai suka yi musu sallama suka fito jiki duk ba kwari ba kad’an ba attitude d’in Yash ya tab’asu Mommy ta d’an tsorata akan kar fa kwab’arta ta yi ruwa dan muddin Yash da Daddy suka zarge
su suka juya musu baya suka fara gano su to fa akwai Babbar matsala dan haka dole ta tashi ta tsaya tun wuri ta gyara abunda ya fara lalacewa a tsakaninta da su Yashjub ,Yashjub ya auri Kausar Manubiya kuma ta kama gabanta…..
Gashi ta nemi fad’a kacha kac
ha da Daddy amma ba komai za ta gyara inshaaAllah….
Bayan sati biyu….
Babban abunda ya fi d’agawa Ummi har ma da su Yahansu hankali shine guduwar da Munirat ta yi…haka kurum kwanaki tara da suka wuce ta rubuta wasik’a akan ‘kar a nemeta ta tafi ba za
ta dawo ba’ har yau babu inda ba a duba ba babu Munirat babu mai kama da ita,Ummi sai da ta yi sati d’aya a asibiti tukunna aka sallamota tsabar masifa…su Yasira kuwa an samu abunda ake so k’iri k’iri a gabanta suke yi mata dariyar mugunta suke cewa karuw
anci Munirat ta tafi…
Mommy ta so su shirya da Daddy amma abunda ya yi mata sai da ya sakata a al’ajabi dan korar kare ya yi mata da ta je d’akinsa kuma har yau ko kallo ba ya shiga tsakaninsu in kuwa ya kalleta to harara ce! ko abinci ya daina ci a din
ing d’in k’asa duk dan saboda ita.Wannan al’amari ba k’aramin d’aga mata hankali ya yi ba har y’ar rama sai da ta yi gashi Yash da Manu shiruu ba a jin kansu su da suka zubar da cikin suka k’ulla sharri saboda ya koreta amma sai take gani kamar hakan ma sa
ke had’a kansu waje guda ya yi! su Yasira kuwa ana sallamar ta a asibiti Hajiya Mama ta ce su dawo gidan Ubansu shiyasa gaba d’aya ta sake burkicewa gashi ta ga hajiya mama ba ta da ranar tafiya dan da farko sunyi tunanin rako Junior ta yi ta d’anyi sati d
’aya ta koma…Kwanciyar Hankalinta d’aya zuwa biyu a yanzu na farko ta riga ta san Manu babu ita babu haihuwa,sannan al’amarin Kausar da Yashjub akwai haske dan aiki tuk’uru suke yi babu dare babu rana dukda ita da Kausar d’in ba su fahimci juna ba har yanz
u saboda ta yi tambayar duniya ammawkullum amsa d’aya Kausar d’in take Bata itace”Yashjub raping d’inta ya yi”tsabar ta raina wa Mommyn hankali,shiyasa ita kuma ta rabu da ita ta d’au fushi da ita ko taimakon nan ma da suke yi mata ba ta sani ba.
Su Yas
ira ma sun d’an ji haushin abunda Kausar ta yiwa Yashjub gashi suma da suka tambayeta amsa d’aya ta basu irin wadda ta bawa Mommy shiyasa suka daina kulata suka yi fushi da ita…ita kam ko a jikinta dan idanunta sun rufe ba ta damu da kowa da komai ba babba
n burin ta a halin yanzu shine ta ga ta auri Yash daganan kowa ya yi ta kansa.
Abhi ma ya zo dan Daddy da kansa ya kirasa da ya ji labarin yana Niger sun je wani aiki yace dan Allah idan sun gama ya biyo Nigeria,Dan kwana biyu gaba d’aya Daddyn a hargit
se yake ya rasa me yake yi nasa dad’i kansa ya d’au zafi shiyasa ya hana Hajiya Mama tafiya yake kuma buk’atar Abhi d’in shima a kusa da shi.
Junior da Ya’isha ma an saka musu rana nan da wata uku su Siyama ma jiya aka je aka yi tambaya aka bayar aka sa
ka ranar auren wata uku suma……
Ko da Junior ya tunkari Yassir game da zancen Yash tashi d’aya Yassir ya faiyyace masa komai bai b’oye ba!saboda ya San ya riga ya fahimta.
Cikin tsananin b’acin rai Junior ya hau zaginsa yace bai yi expecting zai iya yiw
a Yashjub haka ba ya yi sauri ya gyara mistake d’insa wallahi ko ya tona masa asiri.!
…..A lokacin da suke makaranta akwai wani video da Yassir d’in ya tab’a yiwa Junior shi da wata Yarinya da yake so ta k’i sauraronsa…sai da suka bata abu ta sha ta bugu
tukunna aka yi video d’in na rashin d’a a!Yarinyar naked abun dai babu kyan gani..y’ar Nigeria ce y’ar manyan mutane gidansu babban gida shiyasa a wannan lokacin suka dinga blackmailling d’inta da wannan video d’in ko me suka ce suna so ta yi musu sai ta y
i idan suka kirata dole ta je..ba kalar tujarar da Yarinyar nan ba