Showing 174001 words to 177000 words out of 259716 words

Chapter 59 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

15

Junior ya shigo.

Da sauri Hajiya Ma

ma tace”ya fito da mota ga su nan sauk’owa zai kaisu asibiti.

Munirat da Ummi ne suka sauk’ar da ita suka sakata a mota suna ta faman jera mata sannu,Junior da Hajiya Mama da Manubiya sai Munirat da ta d’aura kan Manu akan cinyar ta,ne suka fara yin ga

ba suka nufi asibitin,Ummi kuma sai da ta koma ta sanarwa su Mommy tukunna ta bi bayansu a motarta,da taimakon kwatancen Munirat da suke waya ta Isa asibitin……

Yashjub yana zaune a office gaba d’aya tunani ya yi masa yawa dan sai yanzu ya ke ganin r

ashin kyautawar sa ga Manu…waya ya d’auko da niyyar kiranta amma sai shigowar Racheal ya katse masa hanzari…..

Cikin takunta ta k’araso tace”Sir,a guy named Abbakar is here to see you!he said he’s a friend of your wife.”

A take k’irjin Yashjub ya buga,

sai da ya d’an d’au lokaci kafin ya samu ya d’ago a hankali ya kalleta yace”send him away”.

Duk wani Abu da zai kawo matsala tsakaninsa da Manu ba ya so,gudan sa yake yi.

Ya san ya tsani Abbakar,yana kishinsa saboda Manubiya shiyasa ya zab’i k’in ganin

sa.

Har ta juya za ta fita sai kuma ta juya tace”Sir he said it’s very important and urgent,he need to see you!..”

Wannan karon cikin d’an fushi yace”Racheal!send him awayyy!!!”

“Ok sir”

Ta ce,daga haka ta juya ta fita.

Dafe kansa wanda zuwa y

anzu ya fara sara masa ya yi…ya d’an jima a zaune kafin ya gama deciding ya mik’e da niyyar zuwa gidan nasu ya samu Manubiya,shiruu da kyaliya bai kamata ace ya fara shiga tsakaninsu tun yanzu ba…abunda ya yi kwata kwata bai kyauta ba….

Yana wannan tu

nanin ya sauk’a ya shiga motarsa yana shirin kunnawa Abbakar ya k’araso wajen…tun da ya fito ya gansa dama dan haka ya sake tamke fuska tamau.

With full confidence Abbakar ya k’araso ya na zuwa ya d’an yi knocking glass d’in motar wajen mai zaman banza

kafin ya bud’e ya shiga ya zauna.

Shiruu Yashjub ya yi sai kuma kawai ya kunna motar ya ja ya fice.

Sai da suka d’an yi nisa tukunna ya faka ya juya ya kallesa yace”I made myself pretty clear kuma na san Racheal ta gaya maka..”

Cikin tarar numfash

insa Abbakar yace”I have to see you,shiysa ka ga na yi hakan..”

Yashjub ji yake kamar ya bud’e motar ya hanakad’a Yaron dan ya yi tunanin idan ya yi masa hakan zai fita amma sam baiga alamun shakka ko shirin fita daga garesa ba ,shi kuma har ga Allah he

can’t stand him.. ko sunan shi ba ya so ya ji an kira wallahi…ga kuma gudun zuciya..

“Am…Yashjub ban yi

Mamakin yadda kake treating d’ina ba, dan na san haushina kake ji kamar yadda nima nake jin haushinka!”

Muryar Abbakar ta katse masa tunani..

Juy

awa kawai ya yi ya zuba masa jajayen idanunsa..wanda hakan ba k’aramin dad’i ya yiwa Abbakar ba dan ya hango trigger…

Cikin sauk’e numfashi yaci gaba da cewa”A da na so in b’oye maka kamar yadda Manu ta buk’ata amma kuma sai na ga rashin dacewar hakan d

an bai kamata mu yi ta b’atawa kanmu lokaci ba shiysa na zab’i in tunkare ka…”

Cikin katsesa da tsananin fushi Yashjub yace”Kaii!dan ubanka na yi maka kama da Yaro???ni za ka zowa da wannan shirmen?fice mini a mota kafin na illataka!!!”

Murmushi ya g

a Abbakar d’in ya yi kafin yace”idan ni ban maida kai Yaro ba ai Manubiya ta maida kai Yaro jariri ma kuwa..gashi kuma ina k’ok’arin wayar maka da kai amma kak’i ka saurare ni!.”

Kama sitiyarin motar Yash ya yi da mahaukacin k’arfi ya d’aura kansa a kai

ya shiga karanto addu’o’i dan ya san tabbas tsaf zai iya kai Abbakar lahira muddin ya ce zai biye sa…

Tsabar b’acin rai zuwa yanzu sama sama yake iya jin Abbakar d’in yana cewa”Tun Yarinta muka taso ni da Manubiya..ba ta yi tunanin Ina sonta ba shiyasa

ta karb’i soyayyarka…yanzu kuma ta fahimci Ina k’aunarta she’s ready to leave you for me Yash!saboda tace ko dan family d’inka ma ba za ta iya rayuwa da kai ba gashi ba ta son ka…kawai matsalar itace tace mini ba ta san ta yaya za ta gaya maka ba!tana jin

kunyarka har gida ka siyawa iyayenta…ganin duk mu uku muna ta b’atawa kanmu lokacine ya sa na yanke shawarar tunkarar ka a yi ta ta k’are.”

A hankali Yashjub ya zare makullin motar ya d’ago kansa ko kallon Abbakar bai yi ba haka ya bud’e ya sa kai ya f

ita,dan tabbas shaid’an ya fara kad’a masa ganga maganganun Abbakar sun fara tasiri a kansa gashi zuciya

In banda tunzuroshi ya rufarwa Abbakar babu abunda yake yi shi kuma ya san muddin ya biye Yaron a halin nan da yake ciki to sai dai wani ba shi ba.

Bai san shima Abbakar d’in ya fito ba sai hannun sa da ya ji ya kamo ya saka masa wayar sa yace”idan baka yarda da ni ba ka duba wannan.”

Duk yadda Yashjub ya so ya yi k’ok’ari kar ya kalli wayar sai da ya kalla…chat d’inta ne da Abbakar har yana ce m

ata shifa yana kishi gaskiya ta daina yarda da yash ita kuma ta yi masa alk’awarin ta daina sannan tace”ba za ta iya haihuwa da shi ba ba za ta iya haifar niece ko nephew d’in su Yasira ba shi kuma ya yi mata recommending magani ya ce ta dinga sha kullum g

uda d’aya a hankali cikin zai zube………

Kafin yashjub ya gama karantawa ya had’a wata uwar zufa fuskarsa ta yi jaa…how dare he! ta yaya ma zai fara mishi wannan shegen zancen on top of that har yana da guts d’in nuna mishi kamar Irin shi ne ya saka Matarsa

ta ke k’aurace masa sannan har yana da bakin yin magana akan cikin jikinta HOW DARE He!!!…..

Cikin son k’aryata zancensa kafin ya ci ubansa ya shiga bincika wa yana dubawa da kyau sai dai kuma duk ta inda ya so ya k’aryata d’in abun ya gagara…..ya duba nu

mber ya fi sau a k’irga amma number Manubiya ne da komai nata…

Gashi kuma tabbas wannan itace number da take ta kiran Manubiya amma ba ta tab’a d’auka a gaban sa ba!dan ya ga number ya haddace tsananta bincike ne ba ya so shiyasa bai tab’a kira ba.

“Inna

lillahi wa inna ilaihirrajiun”

Yashjub ya shiga maimaitawa a cikin zuciyarsa yana jin wani kalar gagarumin tashin hankalin yana yi masa k’awanya.

“Actually wannan sirrin mu ne bai kamata in gaya maka ba but I have no choice..…dalilin da ya sa na nuna

maka na san idan ba gani ka yi ba ba za ka tab’a yarda ba,ni kuma har ga Allah na gaji dan tun kuna Cyprus ake Abu d’aya shiyasa ita kanta Manu d’in ma na shalllake ta na yi gaban kaina gara ka san gaskiya mu daina b’atawa kanmu lokaci.…

Mahaukacin Marin

da Yash ya d’aukesa da shi ne ya saka shi a silent…ba ji ba gani ya rufe sa da duka sai da ya ga ya daina motsi tukunna ya tsallakesa ya shige cikin motarsa yana jin abunda bai ma san me ya ke ji ba!!…..

Tafiyar mintuna uku ya yi ya ja ya faka dan wani

irin duhu duhu yake gani…ji yake kamar ya koma ya cinnawa abbakar wuta ko ya ji sauk’in abunda yake ji a cikin zuciyarsa…he can’t believe guts da audacity na Yaron!d’ayar zuciyarsa kuma tana ta faman tunzurashi da son tabbatar masa da maganganun Abbakar d

’in saboda gashi har gudunsa da take yi Abbakar d’in ne kenan ya hanata ashe,adduarsa d’aya kar maganar zubar da ciki ya zamo gaskiya infact Allah ya sa ma mafarki ne yake yi ya samu ya farka a yanzu ko kuma ya ga wani abun da zai nuna masa wannan al’amari

n k’arya ne…..

Wayar sa ce ta d’auki k’ara a karo na bakwai…. da mugun kyar ya zaro wayar daga aljihu da niyyar kasheta gaba d’aya amma sai ya ga sunan Hajiya Mama yana yawo a kan screen d’in dan haka ya d’auka ya kara a kunnensa ba tare da ya ce koma

i ba.

“Ka zo! Yanzunnan..muna asibiti Manu ba ta da lafiya….”

Daga haka ta gaya masa sunan asibitin da kwatance ta kashe dan suma hankalinsu gaba d’aya a tashe yake ganin yadda jini ya kuncewa Manubiya….

Ikon Allah ne kawai ya kai Yashjub asibit

in dan shi kansa gani kawai ya yi har ya iso amma ya ma manta ta Ina da Ina ya bi.

Yana shiga ya tarar da su carko carko a reception,da sauri Hajiya Mama ta k’araso tana zuwa yace”menene yake damunta??”

Ya yi mata tambayar yana addu’ar ya ji tace zazza

b’i ko wani abun amma sai kunnuwansa suka jiyo masa sautin muryar ta taana cewa”ciwon ciki ne yake damunta…”

A hankali ta sake cewa”yanzu kuma ta fara bleeding!.”

Wani kalar mahaukacin bugawa k’irjin Yash ya shiga yi bai san lokacin da ya durk’ushe a w

ajen ba kamar wani zararre….babban abunda zai tarwatsa shi a halin yanzu ya burkitashi shine idan aka ce cikin nan ya zube! Allah kad’ai ne ya san kalar tsantsar so da k’auna da kuma yadda ya kwallafa rai a cikin nan…..

Dai dai nan Dr ya fito ya kalli H

ajiya Mama yace”pls follow me!”

Daga haka ya wuce ya nufi office d’insa.

Da kyar Hajiya Mama ta iya kamo hannun Yash ta rik’e sa ta mik’ar suka nufi office d’in har da Ummi aka bar Munirat ta shige wajen Manu.

Suna shiga likitan ya kallesu one by on

e kamar ya ce Yash ya fita dan ya san maybe shine Mijin sai kuma kawai ya zab’i ya yi maganar a gabansa dan haka ya kalle su yace”have a seat”

Saida duk suka zazzauna tukunna ya ajjiye takardar da yake rubutu a kai a gefe ya cire glasses d’in idanunsa ya

kalli Hajiya Mama yace”ke grandma d’inta ce?”

A hankali Hajiya mama ta jinjina masa kai alamun”eh”

tsura mata ido ya yi kafin chan ya sauk’e ajiyar zuciya ya fara magana”ya kamata ku da kuke manya ku dinga saka idanu a kan y’ay’ayenku da jikokinku,ku d

inga gaya musu abunda ya dace da wanda bai dace ba..yanzu gashi saboda kyaliyarku da rashin kula Yarinyar nan ta je ta yi ta shan maganin zubar da ciki kuma mai k’arfi,we lost the Baby!!but ni babban tashin hankalina anan shine ba lallai ta k’ara haihuwa

ba saboda maganin da ta dinga sha yana da k’arfi kuma ta sha sa over ne….

A hankali Yash ya tura kujerar sa baya ya mik’e ya juya ya fice….kamar wanda kwai ya fashewa a ciki haka ya fita daga asibitin ya hau titi ya kama tafiya ba tare da ya ma san ind

a zai je ba………….MANNUBIYA

(Book 2)

Page 34

Na

Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Ya yi tafiya mai nisa sosai dan sai da ya kusan k’arasawa gida ma tukunna ya tari Napep ya shiga ganin jiri yana shirin

zubar da shi.

Yana shiga gidan dai dai su kuma su Mommy suna fitowa har da Yassir domin zuwa asibitin.

Ba su kula shi ba shima bai kulasu ba dan sun riga sun fito shi kuma napep Tana ajjiyesa ya afka cikin gidan,yanayin sa ba k’aramin dad’i ya yi musu b

a dan ko ba’a fad’a ba sun san cikin ya zube shiyasa ya zama haka.

Direct side d’insa ya nufa

yana zuwa ya rufe ko’ina ya turawa Siyama message yace ‘Manubiya ba lafiya’daga haka ya kashe wayoyinsa ya rufe ko’ina ya kwanta ya yi shiruu.

Su Yassir

suna fita ya turawa Kausar message kamar haka”Yashjub is home,he looks weak

and terrible,this is the perfect time…get ready.”

Hajiya Mama da Ummi suka tarar a d’akin Manubiya tana kwance tana barci dan tunda aka fito da ita ba ta bud’e ido ba.

H

ajiya Mama ba ma ta san sun shigo ba dan ta yi zurfi a tunani matuk’a,idan a kwai abu guda da za ta iya rantsuwa a kai shine Manubiya ba za ta tab’a shan kwaya domin ta zubar da cikin jikinta ba sannan tunda har Doctor yace magani ta sha cikin ya zube tou

kuwa maganin ta sha ba tare da ita kanta ta san tana sha d’in ba bi ma’ana drugging d’inta aka dinga yi har cikin ya zube!

Daga ita sai Yasira Yusra da Yadira a cikin gidan sai gwaggwo sai Yashjub.”Innalillahi wa inna ilaihirrajiun rajiun” ta shiga maimai

tawa a cikin ranta dan suspects d’inta su Yasira ne!Tabbas Mommy ta cucesu ta cuci jikokinta muddin hakan ta kasance dan ta san ita ce ta koya musu wannan muguwar dab’iar.

“Maama Ina wuni,ya mai jikin?”

Muryar Mommy ta katse mata sak’e sak’enta.

D’agow

a ta yi kawai ta zuba mata idanu wanda hakan ya sanya ta sha jinin jikinta ta hau dibi dibi…kallonta kawai Hajiya Mama ta ke yi tana sakewa a ranta tana mamakin how can someone be this evil!tun tana Uk take mugayen mafarkai akan su Yasira da Manubiya shiya

sa tunda ta zo aka ce mata suna gidan sam hankalinta bai kwanta ba amma kuma dukda haka bata tab’a kawowa za su iya aikaata wannan mugun abu da take zarginsu da shi ba!.

Da kyar ta iya cewa”lafiya Alhamdulillah.Jiki da sauk’i.”

Shiruu duk suka yi sun

a so su tambaya su tabbatar da cikin ya zube ne amma kuma suna shakkar kar Hajiya Mama ta gano wani abun dan iyaka kallon da take yi musu kad’ai sun sha jinin jikinsu,shiyasa suka ja bakunan su suka yi shiru.

Baba Larai ce tace”itakam wannan cikin nata

mai laulayi ne,Allah dai ya raba su lafiya!”.

Sai da Hajiya Mama ta d’an k’ura mata ido kafin tace”Ciki kam wanda ya bayar ya karb’a ,sai dai mu yi addu’ar Allah ya kawo masu albarkaa Allah ya sa wannan d’in mai ceto ne.”

Guntun murmushin da Ya’isha

ta yi da kuma ajiyar zuciyar da Mommy ta sauk’e sai da Hajiya Mama ta gani ta ji dan haka ta sunkuyar da kanta k’asa kawai ta hau salati a cikin ranta kanta yana wani irin juyawa..Tabbas an zo gab’ar da ya zamo mata dole ta shigo

rayuwar cikin gidan Dadd

y ta san abun yi,Mommy rub’abb’en seed ce da ya zamo dole ta b’intike ta tun kafin ta fara kisan gilla,ta riga ta cucesu ta yi poisoning mind d’in su Yasira ta kafa musu muguwar d’abia a ciki amma it’s not too late tana da yak’inin za ta ita gyara jikokin

ta muddin Mommy ta yi nesa da su.

A hankali ta d’ago kanta ta kalli Mommy wadda sai a lokacin tace”To Allah ya kawo masu albarka”

Ita da su Yasira.

Cikin rashin son ganinta tace”ki tafi ki je wajen Yashjub!yana da buk’atar ki,za mu kula da Manubiya.



Babu musu tace”to shikenan Hajiya Mama”dan itama so take ta gudu ta san tshoho duk inda yake ya fika wayo shiyasa take so ya yi nesa da ita gudun kar ta gano wani abun game da su dan wannan kallon da taga tana yi mata ta san ba na lafiya bane ba.

“Alla

h ya k’ara sauk’i.” Tace daga haka tayi musu

sallama suma su Baba larai suka yi musu daga haka duk suka fice zuciyoyinsu fess! kamar an yi musu bushara da gidan Aljannah.

Hatta Ummi sai da ta dasa ayar tambaya a kansu itama ta fara zarginsu dan yadda

suka yi da yadda suka nuna halin ko in kula gameda batun zubewar cikin dole abun ya saka duk wani mai hankali a shakku.

Shiruu d’akin ya d’auka bayan fitarsu,kafin daga baya Ummi ta ce”Bari in je in yi girki kafin ta farka.”

“Sannu Ummi Allah ya yi mik

i albarka”

Hajiya mama tace dan gaba d’aya jikinta ya yi sanyi ta kad’u kwarai.

Jaka Ummi ta d’auka daga haka ta fita itama jiki babu kwari.

Baya ta fara dubawa dan ya ci ace Munirat ta kammala shanyar kayan Manu da suka tafi yi,ga mamakinta sai ta

ganta ta fito daga lab tana tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki,sai da ta zo daff da ita tukunna ma ta lura da ita.Da mamaki ta tsaya take kallon idanunta waenda suka kumbura kamar wadda ta sha kuka..”Ummi za mu wuce ne?”

Ta yi mata tambayar ba tare

da ta had’a idanu da ita ba.

“Kuka ki ka yi?”

Itama ta jeho mata da tata tambayr.

“Cleaner d’ince ta d’an watsa mini hypo a ido garin wanke zanin Manu shine na je lab d’in suka duba mini sun ce ba komai bai ma shiga idon ba.”

Wata bahaguwar ajiyar z

uciya Ummi ta sauk’e saboda da har ta fara tunanin wani abu daban.

Sai da itama ta sake duba mata idon tukunna suka nufi gida.

Ummi tana fita Hajiya Mama ta kira Daddy a waya tace”ya zo yanzunnan tana da buk’atar ganinsa.

Suna gama magana Inna Siy

ama da Muhsin suka shigo,har da Sir Najeeb wanda ya je zance ne ya ji zancen shine ma ya kawosu.

Cike da girmamawa suka gaida Hajiya Mama ta amsa da kulawa kafin suka shiga jaje da tambayar jikin nata.

Cike da alhini Hajiya Mama take sanar dasu ai ciki

n ma ya zube har sun yi mata wankin ciki…gab’a d’aya shiruu aka yi jiki da zuciya duk ba dad’i.

Hawaye kawai suka ga yana bi ta k’uncin Manu wadda shigowar su Inna ne ya farka da ita ba ma su sani ba.

Numfashi Hajiya Mama ta fesar kafin ta tura kujerar

ta dai dai saitin kan Manubiya a hankali ta shiga rarrashinta tare da yi mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login