Showing 78001 words to 81000 words out of 259716 words
da tashin hankali idan t
a samu rest ta d’an nutsu za ta dawo daidai,ko sun je asibitin ma abunda za’a ce musu kenan.!”
A d’akin Kausar d’in suka ya da zango tukunna Yasmeen ta fita ta je ta had’o allura mai mugun nauyi su Mommy suka danne ta aka yi mata aikuwa ko gama tsiyaya ru
wan allurar Yasmeen ba ta yi ba Kausar ta fara lumlumshe ido nan da nan kuwa ta yi bacci.Sai a sannan tukunna suka samu kunnuwansu suka huta dan kuka sosai Kausar d’in take yi tana cewa”ita fa ba zata kwana a cikin gidan nan ba,ba ta da k’arfi a jikinta da
n Allah Yassira ta taimaka mata ta fitar da ita daga cikin gidan nan,a nemo mata Manubiya yau sai ta kasheta……”waye waye..harda shirme hakanan ta dinga had’awa tana yi kafin aka samu ruwan allura ya saka ta a silent.
Su Mommy kuwa a tsaye suka kwana dan
tashi d’aya bacci ya k’auracewa idanunsu tsabar tashin hankalin da suke a ciki.
Yadira ce kawai ta d’an runtsa
Mommy kuwa ko zama bata iya yi ba dan abu biyu ne suka had’ar mata,na farko ba wai iya Kausar bace take cikin tashin hankali a wannan rana har
ita dan wallahi babban
abunda zai k’arasa kasheta bai
wuce ace Manubiya ta samu ciki ba,dukda Baba larai tace mata “ta kwantar da hankalinta za ta kunce mata jini har zuwa lokacin da za su dawo cikin gida kusa da su da zama a san abunyi”amman sam hanka
linta ya gagara kwanciya .
Abu na biyu kuma ‘Ummi da Daddy’!dan tun d’azu take safa da marwa a bakin stairs d’in Daddy amma ba ta ga sauk’k’owar Ummi ba.Tana ganin Daddyn ya zo ya wuce lokacin da suka dawo daga asibiti,a tunaninta magana kawai za su yi d
a Ummin da saukk’o amman har yanzu an fi awa uku da hawan sa babu Ummi babu motsinta.
……
A kwance cikin sofa Daddy ya sami Ummi a cikin d’akin nasa har ta d’an fara bacci saboda sun d’an dad’e a asibiti tukunna suka dawo,a kusa da ita ya nemi waje ya zau
na ya d’an ruk’o hannunta ya na kallon saman goshinta inda Yasira ta daketa wajen har ya d’an yi jaa….farkawarta kenan ta ji ya mik’e dan haka ta shiga bud’e idanunta dai dai ta ga ya nufi fridge da towel a hannunsa yana zuwa ya bud’e ya d’auko ice ya saka
a cikin towel d’in ya juyo ya nufota,mik’ewa ta yi ta zauna dai dai ya k’araso tace”ya jikin Yaha?”a hankali ya ce”Alhamdulillah,she’s fine tana d’akinta”tukunna cikin kulawa ya zauna kusa da ita sosai ya fara daddana mata k’ank’arar a inda ya yi jaa yan
a mai jera mata sannu a d’an rikice….Ummi ba ta san lokacin da ta saki wani sassanyan murmushi ba wanda hakan ya sanya ya tsayar da abunda yakeyi ya shiga kallonta,ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya sunkuyar da kansa k’asa yana tunano ire iren abubuwan da
aka yi mata a cikin gidan amman ta yi hak’uri ta zauna,bada hak’uri baya daga cikin tsarinsa amman tashi d’aya a yanzu ya yanke shawarar chanja tsari dan tabbas Ummi ta chanchanci ya bata
hak’uri ya jinjina mata…a hankali ya d’auke hannunsa daga kan goshin
nata ya runtse k’ank’arar dake a cikin towel d’in a hannunsa duk biyu kafin ya kalleta cikin rashin sanin ta Ina ma zai fara yace”am..Ummi,ki yi hak’u!”
Da sauri ta sa hannunta ta toshe masa baki ta shiga girgiza masa kai alamun kar ya bata hak’uri sannan
tace”ba komai,ka d’auka a ranka kamar baka tab’a yi min komai ba kamar su Yasira ma ba su tab’a yi min komaiba…”cikin tarar numfashinta yace “taya zan iya?”
Yanzun ma katsesa ta kuma yi tace”dan Allah dan Annabi komai ya wuce,pls ka manta da komai let’s
start a fresh.”Ta fad’i hakan tana murmushi sannan ta sake cewa”plssssss”ta had’e hannuwanta waje guda.
Kallonta kawai ya tsaya ya na yi yana mamakin kyakkyawar zuciya irin tata…yana mai jin k’aunarta tana sake shigarsa. A hankali ya ajjiye k’ank’arar a
gefe ya sa hannuwansa duk biyu ya rungumota izuwa jikinsa daidai saitin kunnenta yace”thankyou Saddik’a!you are right!let’s just start a fresh ta yadda zan nuna miki da gaske i’m sorryy and I love you so much!”
Murmushi tayi itama tace”i love you”tana mai
jin son mijinta yana sake shigarta.
……
Sai da gari ya fara haske tukunna Yashjub ya farka daga wahalallen baccin da ya yi awon gaba da shi sakamokon zazzab’in da ya rufar masa lokaci guda!
Juya wa ya yi ya kalli Manu wadda ke kwance lamoo a gefensa ida
nunta a lumshe,wani kalar farin ciki da annashuwa ne suka lulub’esa yana kallonta yana jin kamar kamar ya had’iye ta gaba d’aya ya huta watak’il zai samu sauk’in abunda yake ji game da ita.Yadda fuskarta ta kumbura saman idanunta sukayi luhu luhu ne ya sa
nya ya d’an ji wani iri dan ya san ya yi laifi!sam baya so ya zama silar kukanta amman kuma wani ikon Allah ji yake kamar ya k’ara!wallahi he can’t get enough of her..Manubiya ita ce mace ta farko kuma inshaaAllah ta k’arshe da ya fara sani amman tabbas ya
san she’s different ba lalle a kuma samun irinta a cikin mata ba idan kuma an samu to ba su fi 1%out of hundred ba wallahi..shi kad’ai ya san me ya ji. Ahankali ya matsa gareta yana mai jin yadda gaba d’aya gab’ob’in jikinsa sukeyi masa ciwo, sosai ya shi
ge jikinta yana addu’ar Allah ya basa ikon lallashintan da yake da niyyar yi ba tare da ya sake yin wani laifin ba,wani sassanyen murmushi ne ya sub’uce masa wanda har sai da sautin murmushin ya fito fili kafin a hankali ya sa hannu ya yi hugging nata ya l
umshe idanunsa yana mai sauk’e wata nutsatsiyar ajiyar zuciya tashi d’aya ya shiga koro kirari ma Ubangiji a cikin zuciyarsa kafin ya d’aura da addua da sanya albarka a Manubiya
matarsa farin cikin sa cikar
burinsa…. bud’e idanunsa yayi ya na mai kallo
n fuskarta yace”Baby!”a hankali.
Tun d’azu idanunta biyu dan bacci ba nata baneba,sai dai kuma ba ta jin za ta iya bud’e daidai da kwayar idanunta a halin yanzu…Sau uku yana cewa “baby”jin shiru ya sa ya sake zubawa fuskarta idanu sosai k’irjinsa yana du
kan uku uku,ganin tana d’an motsi ne yasanya sa fesar da numfashi a hankali yace
“Alhamdulillah”.
Sai kuma ya sake hugging d’inta ya ruk’umk’umeta kamar wanda akace za’a kwace masa ita……da godiya ya fara kafin
ya d’aura da sanya albarka
sai kuma alk
’awarurruka iri iri,har da hawaye sai da Yashjub ya yi yana mai yi mata godiya cike da shauk’i da k’auna bayan wanda ya yi jiya.
Itakam wasu ta fahimta wasu kuma bata fahimta ba tsabar azabar da take a ciki….ta san ruwan zafi zai taimaka mata shiyasa ba
ta da burin da ya wuci da ta jita a cikin ruwan zafin a halin yanzu,dukda ta san za ta sha sabuwar azaba amman ta san hakan kad’ai ne zai taimake ta.
Kamar ya ji abunda yake a ranta kuwa dan shima tashi d’aya tunanin had’a mata ruwan zafi ya zo masa….anan
kuwa ake yinta!dan duk k’okarin sa sam sai ya ji ya kasa matsawa daga gareta,yadda ya yi hugging d’inta ya sanya ya sake jinsa a sama ya ji bashi da wani burin daya wuce ya ji sa a duniyar da ya tsinci kansa a ciki jiya,tsabar fitina shi kansa gab’ob’insa
da cinyoyinsa ciwo suke yi ga kuma zazzab’in da ya rufar masa amman a haka ya fara k’ok’arin maida su ruwa….Manubiya ba ta san tanada ragowar k’arfin da har sautin muryar ta zai fito ba sai da ta ji ta rushe masa da wani irin gigitaccen kuka mai k’ara!.
Shiruu ya yi yana maida numfashi kafin ya samu da kyar ya cika ta ya mik’e ya nufi bathroom ya na tangad’i dan ya san idan ba tashi ya yi ba bazata tab’a daina yi masa kukan nan da yake jinsa har cikin ransa ba.
Sai da ya shiga bathroom d’in tukunna ya ne
mi towel ya d’aura sannnan ya soma had’a mata ruwa a makeken bathtub d’in.
Ko da ya fito a yadda ya barta a haka ya sameta sai dai ta d’an sassauta sautin kukan nata,ko bargon da ya sauk’a ya bar mata a iya guiwar ta saboda saurin ganin ya bar cikin d’aki
n ba ta samu ikon ja ta rufe jikinta da shi ba.
Tsayawa kawai yayi yana kallonta a ransa yace”Allah mai halitta!how can some one be this beautiful!and this perfect!!so awesome.”
Ta san yana kanta a tsaye kuma yana k’are mata kallo gashi ta kasa motsi s
hiyasa kawai ta k’ara sautin kukan na ta.Shi kam yana chan zuwa yanzu idanunsa sun sauk’a akan d’an jinin da ya biyo ta gefen cinyoyinta d’an kad’an ba mai yawa ba,dama ko bai ga hakan ba ya riga ya sani amman ganin da ya yi sai ya sake sanya shi cikin wan
i irin farin ciki yana mai jin sa a saman gajimare yana yawo ga kuma tsananin nutsuwa da nishad’in da ya samu shiyasa kawai ya fara jinsa kamar wani
sabuwar halitta!.Ya ma rasa wanne irin gift zai bawa Manubiya as token of appreciation dan tabbas bai isa
ya ce zai bata gift dai dai da abunda ta basa ba…. ba kad’an ba ganinta a hakan ya sauya shi amman sai ya daure yana jin tausayi da begenta suna ratsashi,ahankali ya lumshe idanunsa da suka d’an fara chanja launi ya bud’e su kafin ya k’arasa inda take ya
d’urkusa ya shiga share mata hawayenta yana cewa”ni kaina haushin kaina nakeji,kar ki damu anjima zan baki bulala ki zaneni!”yana gama fad’in haka ya d’auketa suka nufi bathroom d’in bai ajjiyeta a koina ba sai cikin ruwan d’umin da ya gama had’a mata.
Ita kanta batasan ta na da raki ba sai yau amman kuma ba za ta kira hakan da raki ba dan wallahi ko macen soja ce ta ji kalar azabar da take kwasa yau ta tabbata itama sai ta koka. Da kyar ta tsaya ya yi
mata ruwa biyu ya ta ya ta tai wankan tsarki yai m
ata wankan sabulu daga haka ya sake sakar mata warm water ya juya ya fita
don ya samu ya chanja zanin gado.
Yaye mara kyan ya yi ya shimfid’a sabo tukunna ya d’auki mara kyan ya nufi toilet d’in da shi ya je ya saka a washing machine ya d’auraye ya bu
sar ya saka a closet d’in dan ya d’an sha iska tukunna ya koma cikin bathroom d’in wajenta.
A kwance cikin ruwan ya sameta kamar d’azu ta lumshe idanunta,ita kanta tana jin dad’in yadda ruwan zafin yayi mata tana jin yadda jikinta yake d’an sakewa ciwon
yana raguwa….kamar d’azu yanzun ma d’aukarta ya yi bayan ya d’aura mata towel sai faman shagwab’a takeyi shi kam kamar ya maida ita ciki haka yake ji sai wani lallab’a ta yake kamar ya samu kwai,a haka suka fito ya sanya mata babban hijabi ya kwantar da i
ta a kan gadon tukunna ya koma ciki dan
shima ya samu ya yi nasa wankan bayan ya ce mata “ta yi sallah anan inda take babu
damuwa.”
Sai da ta d’an zauna da kyar tukunna ta samu ta yi sallar,ta na idarwa ta kwanta
atake bacci mai masifar nauyi ya y
i awon gaba da ita….ko da ya fito ya ga tana baccin bai tasheta ba,Sallah shima yayi
daganan ya je ya soyo musu omelet ya had’o da ruwan zafi da kayan shayi da dambun nama ya zo ya ajjiye a d’akin tukunna ya wuce sama d’akin shi ya shirya tsaf cikin wata
dakakkiyar sky blue d’in shadda da farar hula!ya yi kyau matuk’a kyawunsa ya sake fitowa gashi har wani glowing yakeyi ya fito ango abunsa ras…idan ka gansa dole ka sake waigawa ka kalla.
Tana cikin baccin ta ji ana shafa fuskarta,turo baki ta yi
kad
’an kafin ta d’an bud’e idanunta….kyakkaywar fuskarsa ce ta fara yi mata sallama yana kallonta yana murmushi,a hankali ta mayar ta rufe idanunta ta d’an kauda kai gefe.Murmushi ya yi ya kama kunnensa kafin yace”sorry!”
Ganin ta k’i ta bud’e idanun nata ne
ya sanya ya d’an rissina dai dai saitin kunneta ya shiga rad’a mata wasu kalamai da suka sanya ta ta fara k’ok’arin tashi a gigice amman kuma ta gagara tashin,ganin k’iri k’iri ta kasa tashin ne yasanya kawai ta fashe da kuka….Cikin rashin jin dad’i yace”
Wasa fa nake yi miki…so kike hawayenki su k’afe a yau ne??”
Ya fad’i hakan yana mai taimaka mata ta zauna kafin a
hankali ya sakata a jikinsa ya shiga lallashinta har sai da ya ga ta yi shiru tukunna ya mik’e ya k’arasa gaban dressing mirrow ya d’auko
abinci ya kawo.Kamar jiya yau ma shi ya bata a baki yana ci yana bata tana ci yana gaya mata cewa”likita za ta zo ta yi mata allura ta bata magani”
Tana gama cin abincin kuwa lokacin dai dai 8:00am ko gama saka kaya da shiryawa ba ta yi ba wayarsa ta ha
u k’ara dan haka ya fita ya sauk’a cikin mintunan da ba su gaza biyu ba ya dawo d’akin ya kama hannunta suka fita wajen Dr d’in…….sosai ta ji dad’in allura da maganin ga wani bacci mai d’an karen dad’i da yake ta faman fusgar ta.
Akwai abubuwan tafiyar
su da zai karb’a sannan ya kamata ya je ya ga su Mommy dan
haka yace mata ta basa 30 minutes inshaaAllah zai je ya dawo yanzu…
Sai da ya rufe koina ya tabbatar bata buk’atar komai
tukunna ya fita bayan ya ga
bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ita…
..shi kad’ai sai faman murmushi yake ta zubawa….ya san dama zai iya yin komai akan Manubiya amman yanzu ya sake tabbatar da hakan!Mata rahama ne,shi a
lokacin da bai fara soyayya ba
mamaki yake idan ya ga wasu mazan suna nan nan da matan su da kuma mut
anen da idan suka fara zina ba sa iya dainawa sai waenda Allah ya kubutar…sai yanzu ya fahimci bayan zazzafan so da k’auna ashe wannan rahamar ce dalili….
Yana wannan tunanin ya tsaya ya karb’i sak’on nasu daga nan ya wuce gida.
Ba kowa shiruu parlourn
dama ba ya son hayaniya balle a rik’esa. Zai samu lokacin su Yassira amman ba yau ba dan a halin yanzu fuskar Manubiya kawai yake son gani
Allah Allah yake ya koma gidan
besides ba zai tab’a yarda ya yi ma kansa ruing wannan momment d’in na genuine ha
ppiness da yake a ciki ba ta hanyar tunkurar su Yasira….tbh
wallahi jikinsar har ya fara karkarwa ya san za su fafata
shi kansa bai yi expecting haka ba amman he can’t help it.
D’akin Mommy ya shiga ga mamakinsa ba ta nan dan
haka ya d’auki waya y
a kirata….har lokacin suna d’akin Kausar ta samu wani bacci mai dad’i ya kwasheta
anan kan sofa wayarta ta fara ringing….Baba larai ta kalla bayan ta kalli screen d’in kafin tace “Yashjub!”
Da sauri Baba larai ta matso tace”Ki d’auka duk yadda na gaya m
iki ki yi dan Allah ki yi
k’ok’ari ki danne zuciyarki.
Sai da ta tsinke ya sake kira tukunna Mommy ta iya d’auka dakyar ahankali tace”Yashjub!”
Numfashi ya fesar kafin yace
“Na zo bakya nan”
“Ganinan zuwa”tace
daga haka ta kashe wayar ta rik’e a h
annunta tana huci.
Ba k’aramar lecture Baba larai ta yi mata ba itada Yassira wadda karatun Baba larai ya shiga kunnenta ya samu mazauni a kanta,kafin ta mik’e ta nufi side d’in nata fuskarta a murtuke,sai da ta yi da gaske kafin ta samu fuskar nan ta d
’an sake dan ba kad’an ba hankalinta ya ke a tashe ji take kamar ta yi hauka! abubuwa sun yi mata yawa jiya haka ta dinga zirya har asuba tana lek’e ko za da ga sauk’k’owar Ummi daga side d’in Daddy amma shiru babu Ummi babu alamarta kuma har bacci ya d’au
keta lokacin 8:49 ba ta ji ta sauk’o ba shiyasa ta kuma shiga cikin tashin hankali tana mai jin kamar ta je ta barbard’a musu fetur ta kyasta ashana!tsabar rashin mutunci ko sallar asubah ba ta ga Daddyn ya fito yi ba…..
Ko da ta zo shiga side d’in nata
ma sai da ta yi da gaske tukunna ta samu ta tura k’ofar ta shiga dan wallahi sam ba ta k’aunar ganin fuskar Yashjub!.
A parlournta ta samesa yana ta faman safa da marwa dan ya k’agu ta zo su gaisa ya biya ya gaida Daddy ya wuce.
Sai da gabanta ya yanke
ya fad’i sakamokon fresh d’in da ta ga ya yi.Su na had’a ido yad’an daidai ta kansa kafin ya taka zuwa inda take ya d’an rissina yana
kallon k’asa yace”Mommy Ina kwana!”ya fad’i hakan yana sosa k’eya.
Murmushi ta yi kafin tace”Da ikon Allah yau kunyata
Yashjub yake ji.Ina ita surukar tawa?
ya ba ku zo tare ba??”.
Yanzun ma sosa k’eya yayi kafin yace”Am..tana bacci
sai zuwa jibi InshaaAllah za mu zo tare” .
Dum!!!
Haka k’irjin Mommy ya buga,da kyar ta lalumo nutsuwa ta sakawa kanta
kafin ta yi yak
’e cikin son fahimtar wani abun tace”Ai dama da gajiya!”
Cikin son b’oye sirrinsu da kuma kar ya bawa kansa kunya Yash d’in yace”Ni kaina kam gajiyar bikin nan tambaya ta take yi,balle ita da ta ke mace”
Ajiyar zuciyar da Mommy ta sauk’e sai da Yashjub y
a ji ya d’an kalleta.
Da sauri tace”Inata fama da Kausar ma shiyasa ban yi muku ko breakfast ba,ku yi
hak’uri!”
Tashi d’aya Mommy ta lura