Showing 171001 words to 174000 words out of 259716 words
yi ya kalli Baban Al’ameen wanda ya k’araso yanzun yace”za a yi d’aurin aure yanzu amma ba da wanchan Angon ba,an chanja sabon Ango.”
Jinjina kai Baba ya yi yana jin wani n
auyi yana sauk’a daga k’irjinsa dan har ga Allah da ya d’aura auren nan yau da bai san ta ya zai kalli Jidda ba,cike da kwarin guiwa ya kalli Limamin yace”sunan sabon Angon Muhammad Al’ameen Muhammad.”
Murmushi mahaifin Al’Ameen ya yi a fili yace “Alham
dulillah”
Daga haka suka d’unguma izuwa masallacin.
Jidda ne kawai da Siyama sai Muhsin wanda shima ya yi jigumm a cikin d’akin….
Kamar a mafarki ta ji ana sanarwa a loudspeaker”An d’aura auren Muhammad Al’ameen Muhammad da Maijidda Musa akan sadaki n
aira dubu d’ari biyu lakadan ba ajalan ba….
Wani irin bahagon numfashi ta fesar ta sake kwantar da kanta a kan cinyar Siyama wasu zafafan hawaye suka shiga gangaro mata a ranta tace”shikenan na zauce!!gashi dai k’iri k’iri da Yusuf aka d’aura auren nan na
riga na sani amma sunan Al’Ameen nake ji…..”
“Jidda kin ji abunda kunnuwa na suka ji kuwa???”
Shiruu ta yi kafin ta tashi a mugun zabure ta mik’e ta zauna sakamokon abunda ita da Siyama da Muhsin suka ji an sake fad’a ana kuma maimaitawa a loudspeaker
dai dai nan su Anty Umma suka shigo Anty Umma tana shigowa ta rungume ta haka ma Aisha wadda take waya da Nafi’u domin ta tabbatar….
Sai da ta yanke wayar tukunna ta sanar da su komai abunda ya faru…
Nan waje ya kaure da murna Jidda kuma ta fashe da kuk
an da kowa ya san na farin ciki ne…
Har cikin d’akin Ammi ta shigo ta rumgume Jidda ta sake neman yafiyarta tukunna tace”Bari ta tafi ta fara shirye shiryen tarbar amarya…”
Tare suka tafi ita da Mama domin su je su d’anyi shirye shirye….Zuwa yanzu Mama t
a tabbatar Yashjub dai d’an gidan Imam Manubiya ta aura dan tana ganin su Yusra ta ga kamanni,ta dad’e da yiwa kanta alk’awarin fita daga harkar Imam da zuri’arsa amma kuma tana so ta ji ya Yahanasun take,dan haka ta tsara a kan za ta ke tambayar Manubiya
halin da y’ar tata take ciki ba tare da ta bari ita kanta Manubiyan ta fahimci wani abu ba….
Akwai tafiyar da Al’ameen zaiyi zuwa Dubai nan da sati d’aya shiyasa ana gama d’aurin auren Mahaifinsa ya cewa Baba”sai nan da sati d’aya tukunna za su d’au a
marya inshaaAllah daganan direct sai a wuce da ita airport”kamar ya sani sai ya d’aura da cewa”amma dai za su fara magana da Angon yanzun duk yadda suka tsayar zai kira sa.”
Aikuwa albishir yana zuwar ma Al’ameen bayan ya gama kukan farin ciki ba kunya ba
tsoron Allah ya ce shifa kawai a kawo masa matarsa yau su zauna a nan kafin su wuce”
Dariya su Ammi suka yi suka kira su Inna suka sanar musu….k’arfe takwas dai dai aka kawo amarya Jidda side d’in Al’ameen da ke cikin gidan.
Sai da kowa ya watse tukunna
ya shigo…farin ciki da tsantsar nishad’i masoyan suka tsinci kansu a ciki mara musaltuwa….tunda ya shigo ya yi hugging d’inta suka yi shiruu da kyar ya cikata suka yi nafila suka d’anci abinci daga haka ya ja ta ya sakata a jikinsa yana sauk’e ajiyar zuci
ya yana hamdala suka kwanta…..Jidda har ta fara fargaba..ganin awa d’aya awa biyu bai yi yunk’urin yi mata komai ba ya sa ta kwantar da hankalinta tana mai sauraron yadda k’irjinsa yake bugawa da k’arfi har zuwa yanzun,a haka suka kwana ranar in ka gansu k
amar wanda aka cewa wani zai kwace masa ita ne,ita kam Jidda jikinta har ya fara tsami tsabar yadda ya ruk’umk’umeta…..
Tun a wajen kai amarya Yusra ta kira Ya’isha tace”to fa babu abunda aikin Baba larai ya yi dan ga Najeeb da Siyama nan kamar za s
u cinye juna!”
Dabass!!!haka Ya’isha ta zauna a kan kujerar parlourn Mommy sai kuma hawaye suka fara bin fuskarta…
Da mamaki Mommy da Baba larai waenda suke cikin tsananin farin ciki suka shiga kallonta don yanzunna ta dawo daga ganin Abbakar take ce mus
u”Da farko ya d’an so ya yi zurfin ciki amma daga baya ya amince d’ari bisa d’ari it’s like ya ma fi su son mutuwar auren Manu da Yash d’in,kuma yace’ba ya buk’atar sisin kobo kawai su kular masa da mahaifiyarsa su biya duk wasu kud’ad’en asibin ta.”
Haka
nan suna ta murna ita da su to kuma me ya saka ta kuka tashi d’aya haka…
Mik’ewa Mommy ta yi ta k’arasa inda take ta shiga tambayarta,da kyar ta iya ce mata”ai Najeeb da Siyama aka
gani tare har yanzu suna tare ba su rabu ba….”
Sai kuma ta mik’e ta fic
e da sauri tana kuka.
Shiruu Mommy ta yi ta fad’a duniyar tunani,har ga Allah tana mutuwar son Najeeb ya auri Ya’isha gashi abun na Y’an matan nata xuwa yanzu ya fara damunta..Jiya ta ga d’aurin auren d’an k’awarta wanda suka shirya ita da k’awar tata a k
an za a had’asa shi da Yasira,tsabar abun da munafurci ko gaiyyatar ta bikin ma ba a yi ba sai kawai d’aurin aure ta gani….
“Ki kwantar da hankalinki,inshaaAllah duk za su yi aure,Najeeb kuma shima ki barni da shi bari mu fara gamawa da Manubiya tukunna”
Muryar Baba ta katse mata tunaninta.
A hankali tace”Baba larai idan kuma ya kai kud’i kafin a gama da Manubiyan fa?”
“Kar ki damu ba zai kai ba,ai ita Manubiya inaga ba lalle ta k’ara sati biyu a cikin gidan nan ba!komai a shirye yake kuma yana tafiya a
kan tsari ga kuma wanchan Yaro d’an albaraka Abbakar shima yana side d’in mu,dan haka kawai ki kwantar da hankalinki a kan komai…kar ki damu Najeeb will come around sannan shima wanchan na Yasirar ko a ta biyu ne za ta shiga inshaaAllah……”
“Allah yasa”
Kawai Mommy tace,daga haka ta yi shiruu haka itama Baba larai.
Bayan sati biyu!.
Satin su Jidda d’aya a Nigeria suka wuce Dubai ita da Al’Ameen dan cikin sauk’i ta samu visiting visa.
Najeeb da Siyama abu ya yi k’arfi da shi da Yashjub har sun j
e sun nemi izinin zuwa zance a wajen su Baba Habu wanda hakan idear Baba ce,yanzu haka kuma maganar kawo
Kud’i da saka rana ake yi…..
Yusuf kuwa babu shi babu labarinsa an hana ma ganinsa,sai dai hakan kms ya sake ruru wutar bala’i tsakanin Baba da y’a
n Uwansa a cewarsu”tsabar mugunta a gabansa shi da Yashjub aka tafi da Yusuf amma ba su yi komai ba instead ma su d’aurin aure suka ci gaba da yi.”
Ya’isha Yassira da Yusra kuma suna gidan Manu har yanzu sun kafa sun tsare,da farko ba sa samun damar y
in chatting da Abbakar ta wayar Manu kamar yadda suka tsara sai da aka yi sati d’aya suka samu Siyama ta tafi tukunna….sai sun daidaici ta tada sallah za su d’auki wayartata su yi abunda suka ga dama su goge su ajjiye mata wayar kafin ta idar dama shima Ab
bakar ya san time d’in da suke samun chance shiyasa he’is always available……Ana gamawa za su goge gudun kar ta gani shi kuma Abbakar yana chan yana tarawa a tasa wayar.
A b’angaren Baraka da Ya Musbah kuwa,tunda ta ji labarin tashi tashin ma zama gida
d’aya da su Inna tace ba ta san zance ba,gashi kuma tun a ranar aka basu notice akace su tashi daga wannan gidan da suke a ciki in one week time mai gidan ya siyarwa wani…
Sai da aka yi fad’a da ita a k’ofar gida tace”ai ba a tab’a bada notice d’in da ba
na shekara d’aya ba dan haka ko ubanwa ya siyarwa gidan wannan tsakaninsu shi da sabon mai Gida ita kam ba za ta tashi ba sai ta cinye shekara d’ayar ta sannan ba za ta karb’i refund ba,da kyar aka rabata da mutumin dan shima d’an a yi ne,sai da ta koma c
iki tukunna mutumin ya bawa ya Musbah kud’in hayar sa ya sake bashi hak’uri yace”ya taimaka su nemi gida su tashi ga kud’insa nan complete ma ya bayar”
Ya Musbah dama yana so ya ci gaba da makarantar da ya soma kuma har ga Allah zuwa yanzu yana son zama
a kusa da su Baba shiyasa shi abun ma dad’i ya yi masa dan haka ya karb’a yace”ba komai za su tashi in one week time d’in inshaaAllah”
Yana shiga gidan da ya so ya yi mata bayani ta k’i fahimta sam ta rufesa da fad’a a ranar dai ba su yi bacci ba,kwana
ta yi tana bala’i kuma ta tabbbatar masa da babu inda za ta je…..
Shi dai ya Musbah a hankali a hankali ya dinga kwasar kayansa da shi da mai sunan Baba suna kaiwa sabon Gida sannan ya je ya biya kud’in registration d’insa ya ci gaba da zuwa makaranta ra
nar da sati d’aya ya cika ya zo ya yi mata sallama yace”za su tafi shi da mai sunan Baba”
Da kyar Baraka ta fita daga shock d’in Musbahu wanda tana tunanin ta riga ta saka a kwalba bai Isa ya yi mata haka ba,ta fahimci akwai matsala shiysa ta danne zuc
iyarta kawai dan ta san dole sai ta sake sabon shiri kuma a yadda ya botsare mata idan tace za ta yi turjiya kanta za ta jawa shiyasa kawai ta ce “ba komai ya jira ta ita ma za ta bishi…..”
Sai washegari aka gama kwashe kaya….a plan d’in Baraka idan ta je
sai ta yi abunda shi da kansa zai ce su bar gidan kuma sai ta had’a sa da su Inna wannan karon ta kissa asiri da komai za ta had’a…sai dai kuma tun da ta je ta ga d’ankareran gida ta ce ba ta ga ta tashi ba,ta san kuma fitar da su Inna a gidan aiki ne ko
da zai yiu to ba yanzu ba….gashi ya Musbah gaba d’aya ya juya mata baya aikin ma ya daina tasiri a kansa Kwata Kwata ba ya sauraronta ba ya jin maganarta,dan yanzu ma k’iri k’iri so take ya d’aga katanga tsakaninsu da su Inna ya fitar musu da gate d’insu a
daban tama ce ita da kanta za ta bayarda kud’in amma yace”ba ta Isa ba!”
“Idan kuma ta sake yi mishi wannan maganar shirmen wallahi sai ranta ya yi masifar b’aci”
Shiyasa gaba d’aya hankalinta yake a masifar tashe,ta sake dagewa gidan kullum idan ka shi
go banda k’aurin hayaki mara dad’i babu yake yi dan haka suma su Inna suka sake dagewa da rok’on Allah.
Jiya da daddare Hajiya Mama da Junior suka zo….Shiyasa yau da safe su Manu suke ta shiri akan za su je.
Kana ganinta ka san ta ci kuka dan fuskarta
duk ta kumbura shiysa tunda su Yusra suka ganta a haka farin cikin su ya nunku ya gagara b’oyuwa har sai da ta d’an lura..a b’angarenta kuwa fad’a suka yi ita da Yash jiya abunda bai tab’a shiga tsakaninsu ba kenan!
Tun bayan sati biyu da ya nemeta ta k’i
bashi had’in kai ta fara kuka shikenan bai sake neman wani abu a wajen ta ba,abun ya yi mata matuk’ar ciwo dan a tunaninta sun wuce haka ita da shi ba ta tab’a expecting zai yi irin wannan fushin da ita ba mutumin da a ko da yaushe ya ke cewa”Manubiya ba
ta laifi a wajen Yash,he loves her morethan life itself”amma shine wai zai yi irin wannan fushin da ita!
Ba wai fushi na k’in magana ba dan suna wasa suna dariya yana kula da ita yadda ya kamata kawai dai ko hannunta ya daina rik’ewa…..
Dama da haushin h
akan a ranta yau kuma k’iri k’iri da ta yi masa maganar makaranta ba kunya ba tsoron Allah yace”ba za ta ci gaba ba!”
Daga haka ya shige toilet ya barta a tsaye kuma ko da ya fito ya ga tana kuka bai tsaya ya rarrasheta ba instead shima sai ya had’e fuska
tamau ya ci gaba da shirinsa ko a jikinsa…hakanan yana ganinta har ta gama kukan ta ta sauk’a k’asa had’a breakfast bai ce mata komai ba.
A b’angaren Yash kuwa..dalilin da ya sa ya d’aga mata k’afa kwana biyu ba ya so ya cika nagging ne ya je garin hak
a ya fara fita a ranta shiysa ya hak’ura akan har sai yaga she’s ready tukunna…..sannan yana so ya yi k’ok’ari ya ga ya kawar da duk wani abun da zai sa ya yi zarginta ko ya ji haushinta.
A yadda ya ji tana waya dole ko ma waye ya dasa mata ayar tambaya
amma shi kuma k’ok’ari yake yi ya goge zargi ya bawa hakan kyakkyawar manufa…
Ya san dole idan ta koma makaranta he’ll be restless tunda ga issue a tsakaninsu dana ba su gama sorting out ba!sannan ga ciki a jikinta da ake buk’atar ace ta huta,shiysa ya
nzu da ta yi masa maganar yace mata”A’a”kuma ya had’e rai.
Sannan har ga Allah ya na kishi shiyasa ya ga dacewar gara kawai ta yi online…
Kukan ta ya tab’a sa sosai amma ya san idan ba hakan ya yi mata ba,ba za ta hak’ura ba!.
Har ta kai masa breakfas
t ya ci ya fita,sam fuskarsa babu walwala.
Sai wajajen 11 bayan sun gama girki Yasira ta ja su ta kai su gidan ita kuma ta wuce office da so ta yi yau ta zauna amma sai Daddy ya kirata.
Shiruuu gidan ba kowa dan haka Manubiya suka ajjiye flask d’in gir
kin da suka yo suka nufi sama side d’in Mommy,kamar ko da yaushe ita da Baba larai sai Ya’isha suka tadda a parlourn nata..zuwan Hajiya Mama ba notice ya d’aga musu hankali matuk’a ga kuma Daddy wanda yake bin diddigin Mommy kamar ba gobe…
Ba yabo ba fal
lasa suka gaisa kafin Mommy ta kalli Yadira tace”ta raka Manubiya wajen Hajiya Mama su gaisa.”
Suna fita ko tambayar ta su Mommyn ba su yi ba Yusra tace”yanzu haka ma cikinta ciwo yake yi,ba ta dai fad’a ba amma tun safe take rik’e ciki idan ya murd’a ha
r sai ta durk’usa”
“MashaaAllah,Alhamdulillah!!”
Baba larai tace cike da farin ciki,kafin ta d’aura da cewa”tunda na ga matar nan da safe hankalina ya tashi dan na san tsaf za ta iya cewa ku dawo gida..”
With full confidence Yusra tace”ai aikin gama ya
riga ya gama yanzu kam..dan duk wani ruwa nata muna sakawa a ciki ita kuma tass take shanyewa.. yau sati biyu ta shanye sachet biyu fa!.
Ragowar abubuwan ne dai da na toilet da na d’aki duk ba mu samu damar yi ba ai dama na gaya miki..saboda ya Yash ko k’
afar benen sa bai bamu fuskar mu tab’a ba k’iri k’iri ma yace mana “ko ba ya nan kar mu shigar musu d’aki. Na abinci ita kuma ba ta yarda da mu ba! dan ko girkin mu ba ta ci kuma tana yawan addu’o’i so na san turaren shima ko ta shak’a ba lalle ace ya yi w
ani tasiri ba dukda dai na lura kwana biyu rikici suke yi but gaskiya ba lalle abubuwan namu bane dan ba ta cin duk wani abu da muka bata…maybe wata rigimar tasu ce daban.”
Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk’e kafin tace”Allah ya shige mana gaba,tunda har
suka fara rikici su kad’ai ai sun sauk’ak’a mana kinga….sannan ba komai dan ba ku samu kun yi waenchan d’in ba indai komai ya tafi yadda muke so,maganin da kuka saka da chatting d’in sun ishi komai.Yanzu Ya’isha ki kirawo Abbakar kice masa zai iya tunkarar
Yashjub a yau!”
Shiruu Ya’isha ta yi kafin tace”amma bai yi wuri ba?”
Murmushi Baba larai ta yi tukunna tace”kina ji fa Yusra tace ta fara ciwon ciki!ai this is the perfect time,dan tunda ta fara ciwon cikin nan ba za ta kai jibi da shi a jikinta ba.”
“Tam shikenan,bari in kirasa…”
Daga haka ta d’au waya ta kirasa….a gaban su suka tattauna kafin daga baya suka yi sallama,zuciyar kowa fesss!!!.
Sosai Manubiya ta ji dad’in ganin Hajiya Mama haka itama Hajiya Maman…bayan gaishe gaishe Hajiya Mama
ta bata tsarabar da ta yo musu ita da Yash ta karb’a tana ta murna da godiya.
Dai dai nan Ummi ta shigo dan haka suka zauna su uku gwanjn ban sha’awa bayan Ummi da Manubiya sun gaisa.
Hirarsu suke sosai,dukda Manu murmushi da eh ko a’a take ta cewa amma
hirar tana yi mata dad’i.
A bakin Hajiya Maman take jin maganar Yadira da Junior ta inda take cewa”ta cewa Daddy kawai ya tsayar da date dan al’amarin Yaran gidan ya fara bata tsoro dan haka tunda har Junior ya nuna Yadira yake so gara kawai a saka rana
a yi aure ragowar suma za ta bincika musu Miji a cikin jikikon k’awayenta na nan Nigeria da suke in contact with!ya zama dole a tashi a tsaya a kansu sun rik’a dayawa.”
Ita dai Manubiya murmushi ta yi tace”Allah ya tabbatar da alkhairi”
Dan zuwa yanzu ci
won cikin da ya addabeta sama sama tun d’azu ya k’ara k’arfi!
Tana ji Ummi tana cewa”ta ji suna cewa Yadiran fa ba ta son Junior d’in…!”
Ita kuma Hajiya Maman tace”Wallahi ko za ta mutu sai ta auresa!,Junior ba shi da wani mugun Hali dan haka dole da aur
e sa.”
“Washh!”
Manu tace sakamokon wani mahaukacin murd’awa da cikinta ya yi.
Da sauri duk suka kalleta sai kuma suka rufar mata sakamokon yadda suka ga ta rik’e ciki ta runtse idanuwa da mugun k’arfi.
Sannu suka shiga jera mata bayan Ummi ta rik’
eta Hajiya Mama kuma ta fara k’ok’arin kiran Yashjub.
Yadda Manubiya ta fashe da wani irin kuka ta shiga kiran sunayen Allah ne ya sa Hajiya Mama ta ajjiye wayar ita da Ummi suka fara k’ok’arin kinkimarta dai dai nan