Showing 162001 words to 165000 words out of 259716 words
haka suka tursasa ta gaba d’ayansu abun mamakin har su Ya
sira waenda suka yi musu k’abe k’abe ko motsi suka yi idanunsu a kansu yake ….su dai su Manubiya kawai sun zuba musu ido ne suna kallon ikon Allah da rashin wayonsu dan wannan rashin wayo ne saboda yadda suke yi kowa ya riga ya san they are up to something
shiysa daga Manubiya har Siyama suke ta addu’o’i da neman tsari daga sharrin su…dukda kuwa d’azu Yasira ta bawa Manubiya hak’uri ta ce “ta yi hak’uri akan abubuwan da suka yi mata duk sharrin shaidan ne kuma sun fahimci itace zab’in yayansu ta yi hak’uri
inshaaAllah hakan ba za ta sake faruwa ba they wants to start a fresh with her”amma hakan bai sa Manubiya ta yarda da su ba…kawai dai ta bita da murmushi tace mata “komai ya wuce”
Dukda gwaggwo ta zo hakan bai sa sun yi shirin tafiya ba..shima kuma Yash
jub bai ce musu komai ba ya rabu da su amma dukda haka idanunsa a kansu yake.
Ko da dare ya yi su da kansu suka tsara cewa’Siyama ta kwana a d’akin Manubiya na da,su kuma za su zauna a d’akin da Yadira ta zauna’.Gwaggo kuma dama tana k’asa d’akin bak’i.
Murmushin yak’e Siyama ta yi dan ta yi tunanin a wajen kwanan ma za su nanik’e musu ne…Yasirar ma gudun kar su ga suna ta manne musu ne ya sanya wannan karon tace a yi hakan.
Sun mik’e kenan kowa za ta tafi ta kwanta wayar Manu ta fara haske a karo na
biyar daga zaman su zuwa yanzu,duk tsura mata idanu suka yi sai da ta yi musu murmushi tace”sai da safe”daga haka ta juya ta nufi sama tukunna suma suka wuce d’aki.
Suna shigewa Manubiya ta dawo da sauri ta Isa gaban Siyama wadda ke k’ok’arin shiga d’a
ki itama tace”Siyama dan Allah ya ake yin blocking mutum,na kasa”
Kallonta ta yi kafin tace”ki duba goggle”kamar ba za ta tambaya ba sai kuma tace”wa za ki yi blocking haka jikinki har yana rawa”
“Abbakar”Manubiya ta bata amsa a tak’aice tana mai daddana
wayar hannunta kafin ta d’aura da cewa “ya ishe ni da kira,wai dan Allah yana buk’atar taimakona. Kin san shi kuma Ya Yash ya ce ba ya so ko gaisawa in yi da shi”
Ta faiyyace mata hakan a lokaci guda tana k’ok’arin blocking Abbakar dan har ta gano yadda
za ta yi.
Shiruu Siyama ta yi tana tunanin”ko dai ta gaya mata Mahaifiyarsa ce a kwance a gadon asibiti rai a hannun Allah, ta san shi yasa yake ta kiranta.
Ko kuma kawai ta rabu da ita inyaso ita da Jidda sai su san yadda za su yi su karb’i kud’in a h
annunta su basa dan ta san kud’i yake so.”
“Done!”
D’in da Manubiya tace ne tana haki kamar wadda ta yi y’ar tsere ya katsewa Siyama tunani.Daga haka Manubiyan tace mata sai da safe ta juya ta haye chan sama.
Sai da Yusra ta ji Siyama ta shige ciki
ta rufo k’ofa tukunna ta juya ta nufi su Yasira waenda suka tsura mata ido tana wani irin murmushi….tana zuwa ta zaiyyane musu abunda kunnuwanta suka jiye mata Manubiya da Siyama suna cewa…ji suka yi kamar an yi musu bishara da gidan aljannah!Tabbas Allah
ya na son su,saboda dama neman hanyar da za su bi su nunawa Yash kamar Manu ce ta zubar da cikin da kanta suke yi yanzu kuwa Yasira tana jin wannan batun tashi d’aya ta san abun da ya kamata ta yi dan haka ta cewa su Yusran gobe duk runtsi su yi ta kwak’um
arta har sai sun ga password d’in wayarta daga nan kuma sai su nemi number a wayr tata,saboda ita gobe za ta fita office…Yadira tana da kwakwalwa shiyasa tashi d’aya tace mata d’azu dai da yake ta kira ta ga number 090443 ne farkon number k’arshen kuma ba
ta gani sosai ba
”Ba damuwa,Allah ya sa ba ta yi deleting history d’in ba idan muka d’au wayar time d’in kawai za mu duba na san lokutan da ya kikkirata ai”
Cewar Yasira.
Cikin tarar numfashinta Yusra tace”ko ta goge ma ni na san inda zan shiga in dubo
,Allah ya kaimu goben da rai da lafiya.”
Baba larai suka kira suka sanar mata sannan suka d’aura da cewa”Sun fara zuba abubuwan da ta basu a duk abincin gidan,sannan ba za su samu matsala wajen jefa mata tablet d’in a ruwa ta sha ba saboda lucky for the
m ba ta shan bottle water ko na dispencer iyaka ruwan borehole kawai take iya tara a cup ta sha sakamokon laulayin ciki shiysa easily d’azu tana ajjiye cup d’in kafin ta je ta dawo suka jefe mata kwayar ba tare da sun farga ba daga ita har Siyama,to dai d
a ta dawo ta d’an yi sip biyu daga nan ta ajjiye maybe taste d’in ne ta ji ya chanja mata shiysa suka yanke shawarar raba kwayar gida uku saboda kar ta gane,to dai a halin yanzu sun zuba mata a gorar ruwanta na borehole uku da ta tara ta saka a fridge za t
a dinga sha…”
Murna a wajen Baba larai abun ba a cewa komai..ji take kamar ta zuba ruwa a k’asa ta sha…kafin tace”amma Yasira cctv fa?”
Dariya ta yi tace kar ki damu Baaba ba zai tab’a ganewa ba ta cikin fridge d’in muka saka kuma ba direction d’in cct
vn take kallo ba…murmushi ta yi tace”MashaaAllah Alhamdulillah,Allah ya ci gaba da taimakon mu”
daga haka ta mik’awa Mommy,itama duk da tashin hankali da fargabar Daddy sai da ta yi farin ciki matu’uka ta yi ta sanya musu albarka daga k’arshe suka yi sall
ama suna masu hango silver lining….
A b’angaren Najeeb da Siyama kam a ranar kusan kwana suka yi suna waya…da kyar ta samu ya yi mata sallama suka katse kiran nan da nan bacci ya yi awon gaba da ita yayinda shi kuma ya duk’ufa Nafila…Tabbas ya manta
rabon da ya shiga farin ciki kwatankwacin wannan..shiysa ya kwana sallah yana godewa Ubangiji sannan yana rok’onsa ya tabbatar da aurensa da Siyama!…
Ya Musbah kuwa da ya yi alk’awarin zuwa ko alamar sa babu kuma bai yi waya ba,har cikin dare sai da ya
Nafi’u ya gawada kiransa amma bai d’auka ba saboda ya Nafi’u ya lura har da takaicinsa ne suka tarar wa Baba ya birkice musu lokaci guda haka…shi kam zuwa yanzu ya daina jin haushin Ya Musbah instead tausayinsa yake ji kuma inshaaAllah zai taimakesa ya fit
ar da shi daga kaidin Baraka..shiysa ya shirya zuwa gidan nasa gobe da sassafe dan shi da Yashjub dama sun riga sun san gidan…zai je ya samesa su fara ceto rayuwar Jidda da take shirin fad’awa halaka a gobe daganan zai san abunda zai yi dan abun na Baraka
ya zama abun tsoro.MANNUBIYA
(Book 2)
Page 33
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
A zaune ta same sa yana aiki a computer…zafi sosai take ji sakamokon zazzab’in da ya fara sauka daga jikinta dan hak
a ta nufi bathroom domin ta samu ta sake yin wanka bayan wanda ta yi ba da jimawa ba.
Sai da ta sauya kaya tukunna ta fito…kallon ta yake yi yana mamakin yadda ta shiga ta yi wankan ta fito da wayarta rik’e kyam! a hannunta…da sauri ya kawar da zargi a
cikin ransa ya mik’a mata hannu alamun ta zo garesa..
Sai da gabanta ya yanke ya fad’i!…ta san Yashjub ya yi k’ok’ari sai dai ita kuma laulayin ciki ya zo mata har da k’in son kasancewa da shi dan babu abunda ta ji ta tsana kamar yace zai nemi wani abun d
aga gareta.
Murmushin yak’e ta yi ta nufesa,tana zuwa ya gyara zama ya d’aura ta a kan cinyarsa cikin muryar bege yace”yanzu dai ai jikin da sauk’i ko?”
Sunkuyar da kanta ta d’an yi k’asa kafin ta girgiza kai alamun”a’a”.
Ya ji babu dad’i tabbas dan y
ana lura da yadda ko hannunta ba ta so ya rik’e a cikin kwana biyun nan..amma sai ya dake still,yace”haba mana!a ji da ni gaskiya ko in yi miki kuka..”
Daga haka bai bata ikon yin magana ba ya fara kissing d’inta cike da shauk’i….
Wani irin kuka ya ji ta
fashe masa da shi cikin kukan ta shiga k’ok’arin kwatar kanta.
Dakatawa ya yi ya d’an cikata sannan ya zuba mata rinannun idanunsa yana kallonta kafin da mamaki yace”Abunda na yi yanzun ne ya sanya ki yin kuka har haka?”.
Kasa magana ta yi dan ba ma ta
san me za ta ce ba,kafin ta mik’e ta sauri ta zagaya d’aya b’angaren gadon ta kwanta ta juya masa baya still tana sheshek’ar kuka..
Ya fi minti ashirin a haka ya k’ame kawai a yadda ta barsa ya ma kasa motsi kafin da kyar ya samu ya kwanta rigingine yan
a kalllon sama zuciyarsa tana wani irin tafarfasa ga wani irin ciwon ciki da ya turnik’e sa tashi d’aya.
Tashin hankalin zarginta da yake shirin dasuwa a cikin zuciyarsa sam bai sa ya yi tunanin ‘watak’il cikin jikinta ne ya zo da laulayin hakan’ ba besid
es shi bai ma tab’a sanin masu ciki suna gudun mazajensu ba sai ma son kasancewa a tare da su….shiyasa gaba d’aya zuciyarsa ta jagule ransa ya b’aci matuk’a hankalinsa ya tashi,dan ya lura ba ta fara basa wannan attitude d’in ba sai da aka fara kiranta a w
aya….
Gaba d’aya kwakwalwar sa ta yi zafi haka ma zuciyarsa tunani kala kala yake yi ganin zuciyarsa ta na shirin tarwatsewa ne ya sa kawai ya mik’e ya fad’a bathroom ya kama ruwa ya yo alwallah ya zo ya tada ik’ama…..
Sai da ta ji shigewarsa bathroom
tukunna ta sauk’e ajiyar zuciya ta yi addu’o’i ta shiga karatun Al’Qurani a cikin ranta da haka wani bacci mai d’an karen dad’i ya yi awon gaba da ita…..
Sai da ya tashe ta sallar Asubah tukunna ya juya ya fice ya nufi masallaci…ta lura da yadda ransa
yake a d’an b’ace dan haka ta shirya idan ya dawo za ta yi masa bayani ta basa hak’uri ta san zai fahimceta.
Tana idar da azkar Yahanasu ta kira ta tace”tun jiya cikin dare ta so ta kirata,da kyar ta iya bari asubah ta yi…kamar yadda su Yash suka samu
identity d’in mutum biyu su kuma sun samu na mutum biyar har an fara nemansu maybe Allah bai yi su Yash d’in za su ga wannan footage d’in ba,yanzu tana ganin su gayawa Yash d’in ne su k’ara musu haske su had’a k’arfi da k’arfi ko kuma su yi nasu a daban?”
Ajiyar zuciyaManubiya ta sauk’e ta yi hamdala a fili tana mai jin dad’in good news d’in tukunna tace”Yaha mu yi namu a daban kawai,inaso in taimaka nima,Ina kwad’ayin ganin farin cikin da zai wanzu a fuskar Ya Yash a ranar da muka kama culprit d’in inaga
ya ga muma mun yi participating mun taimaka.
Na ji suma suna maganar da sir Najeeb and a ta b’angaren nasu akwai haske,if to say they are stuck ne to da sai mu k’ara musu haske, dan haka kawai muma mu yi namu idan mun riga su yin nasara Alhamdulillah idan
sun rugamu hakan ma Alhamdulillah kawai ni inaso in taimaka in yi participating ne.”
Murmushi Yahansu ta yi kafin tace”shikenan Manu,duk yadda kika ce”
“Ok akwai kud’in da na ajjiye zan baki na case d’in yaushe za ki karb’a cash ne”
Murmushi Yaha ta yi
tace”ai kawai ki barshi…”
Da sauri Manu tace”Ina so in yi participating ta ko ina ne fa Yaha,pls kar ki ce A’a”
“Ok”kawai Yahansu tace kafin tace”yana Ina?”.
Dai dai nan Yash ya k’araso bakin k’ofar d’akin.
Tarr ya ji muryar Manubiya tana cewa”ya fita
sallah ai,shiyasa ma na samu damar yin wayar,jiya ma na ga misscall na san watak’il a kan maganar ne shiyasa ban d’auka ba saboda muna tare da shi…”
Da sauri ya juya ya bar wajen dan ba ma ya so kunnuwansa su sake jiyo masa wani bala’i da tashin hankalin
..har dishi dishi yake gani da kyar ya k’arasa kan sofa na corridor ya zauna
yana wani irin haki kamar wanda ya yi y’ar tsere…
Manubiya ta san akwai gwaggwo mai aiki kuma har ta fara jiyo k’amshin girki amma hakan bai hanata mik’ewa ta d’an kimtsa do
min ta je ta had’awa Mijinta breakfast ba dukda kuwa morning sickness d’in da ya fara rufar mata mai zafiii.
Tana fitowa ta hangesa zaune a corridor kan sofa ya dafe kai da hannu bibbiyu.K’arasawa ta yi da hanzari da d’an mamaki ta zauna a kusa da shi k
afin tace”Ina kwana”sai kuma ta d’aura hannunta a kan nasa tace”Ya Yash”.
A hankali ya bata iko ta zame hannuwan nasa da yake k’ok’arin yi daga kansa kafin ya juyo ya zuba mata ido kawai ba tare da ya ce komai ba.
Sai da gabanta ya fad’i sakamokon yadda
ta ga idanuwansa sun yi jazir…tashi d’aya tausayinsa ya rufe ta sannan gaba d’aya ta shiga jin babu dad’i dan ta san itace silar wannan yanayin da yake a ciki…ta san ba ya iya d’aukar kwanaki masu tsawo ba tare da ya rab’e ta ba.
Haushin kanta ma ta soma
ji dan haka cikin inda inda tace”Ya Yash dan Allah ka yi hak’uri,ka san ba ni da lafiya shiyasa…”
“It’s fine”d’in da ya ce mata cikin katseta ne ya sa ta yi shiru.
Tashi d’aya ta ga ya mik’e,yace “idan breakfast ya kammalu ki kawo mini,bari in d’an kwant
a kaina yana mini ciwo,idan na tashi zan ci”
Daga haka ya wuce ya shige cikin d’akin.
Sukuku! haka ta had’a masa abinci jikinta da ranta duk babu dad’i ga kuma zazzab’i,babu yadda Yasira da gwaggwo ba su yi da ita a kan ta kawo su taya ta ba amma t
ace musu”ba komai,za ta iya”dan haka Yasira ta yi mata sai anjima ta wuce office Gwaggo kuma ta ci gaba da had’a na su.
Abinci kala uku ta yi
masa da coffee ta d’auka ta nufi saman ta je ta ajjiye a cikin d’akin,ta so ta zauna a tare da shi amma tana z
uwa sai ta ga yana bacci gashi d’azu ta yace mata kansa na ciwo shiyasa ba ta tashe sa ba ta ajjiye a dining table d’in d’akin ta yi wanka a hankali yadda ba zai ji ba ta fito ta rufo masa k’ofar d’akin.
Tana fita ya bud’e ido ya bi k’ofar da kallo…”a yad
da ta ga yanayin sa in da ace ta damu da shi ai da ta tsaya a tare da shi”
Ya aiyyana hakan a cikin ransa.
A d’akin da Siyama take ta tarar da su Yusra suna hira itama Siyaman ta na d’an biyesu ba laifi…
Sai da Manu ta zauna tukunna suka gaida ita k
afin Yadira ta mik’e tace”bari ta je ta d’ebo mata abinci”
Ba yadda ba ta yi da ita akan ta barshi ba amma ta k’i ta fice ta tafi deb’owa.
Tana fita Yusra tace”jiya ma kuwa muna rabuwa Mommy ta kira tana so ta ji ya jikinki ba ta so ta kiraki direct kuma
gudun kar ta tasheki dan ba ta sani ba watak’il ko kun yi bacci,bari in kirata yanzu sai ku yi magana”.
Murmushi Manubiya ta yi kafin tace”barshi ni in kirata da layi na”
Murmushi Yusra itama ta yi tace”anya kuwa kina da sabon layinta?barshi dai in ki
ra”
Daga haka ta kara wayar a kunnenta bayan ta yi dialing…
Bugu biyu a na uku Mommy ta amsa sai da suka gama gaisawa tukunna tace”ga Adda Manu d’in ta sauk’o jikin nata Alhamdulillah amma ga ta dai ki ji muryarta.”
Tashi d’aya Mommy ta fahimci they a
re up to something dan haka ta ce “ok ba ta wayar”
Kawai.
Yusra tana mik’awa Manubiya wayar ta tsink’e.
“Ki yi magana mana kin yi shiru”Yusran tace.
“Ai naga kamar ya tsink’e ne”
Cewar Manubiya.
“Oh God!I forgot fa!wayar tawa ban yi recharging ba
!akwai kud’i a wayar ki?Yadira ta fita kuma ban san password d’inta ba….”
Yusra ta fad’i hakan ta na mai mik’ewa ta k’arasa kan Manubiya ta tsaya tana jira ta bata wayar.
Siyama har za ta ce ga tata nan a kira dan kamar ta fahimci akwai wani abun,sai kum
a ta tuna babu kud’i a wayarta dan haka ta fara k’ok’arin cin bashi da sauri dan a samu a kira Mommyn da wayartata amma sai ta ji Manu tana cewa”Eh akwai gashi”kafin Siyama tace wani abun har ta danna password d’inta ta bud’e ta mik’awa Yusran wayartata it
a kuma ta sa hannu ta karb’a tana cewa”Bara in saka miki sabuwar number tata in yi saving,ai ta dad’e ta daina amfani da wachchar.
Zuciyar Manubiya d’aya dan ba ta yi tunanin akwai abunda Yusran za ta iya yi daga karb’ar wayarta da making call ba..cikin j
injina kai tace”tabbas kam dan ko na kirata wani zubin ta shiga ba ta d’auka ba wani zubin kuma ba ta shiga.
“Yeah a salon aka sace ita kuma ba ta samu ta yi welcome back ba har yanzu”
Ta fad’i hakan tana kwafe number da ta ga anyi ta kiran Manubiyan da
ita a jiya ba ta d’auka ba dan gashi ta ga 090 kamar yadda Yadira ta fad’a dan haka ba ta da tantama itace ta gayen.
Sai da ta gama kwafewa ta adana a wayarta tukunna ta yi copying sabuwar number Mommyn daga wayartata ta loda a wayar Manubiya ta danna
call ta mik’a mata tana murmushi.
“Lucky morning!na ga password na kwafe number.”
Yusra ta fad’i hakan a cikin ranta.Kafin ta juya