Showing 135001 words to 138000 words out of 259716 words

Chapter 46 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

37

yadda y’an uwan Baba suka sako sh

i a gaba..ba su ajjiye wayar ba sai da suka yi wa tufkar hanci daganan suka yiwa juna sallama bayan ya Nafi’u ya yi wa Yashjub alk’awarin zai sanya Baki ya lallab’a su Baba su yarda su k’arbi gidan da Yashjub d’in ya basu su koma..

Ba k’aramin lallash

i likitan ya yiwa Yashjub ba da ya ji batun Manu har ta suma amma ba su sani ba,ya san ba laifin sa bane ko na nurses tunda sun gama yi mata allurai kuma ita da Mijinta suka barsu a d’akin sannan da aka zo fita ba a kira kowa ba amma hakanan ya yi ta bawa

Yash d’in hak’uri dan ya lura ran sa a b’ace yake.

Dama ba so yake yi ta fita d’in ba aikuwa likitan yana zuwa da ya duba ta yace”ba zai yiu ta fita yau ba gaskiya jikin ta ba kwari”…

Hakanan da kyar ya samu ya sake lallab’ata ta hak’ura dan jikinta

duk ya yi sanyi daga wayar data gama yi da Jidda yanzu

Dan Jiddan ta gaya mata komai itama…….

Yahanasu Yash ya kira ta zo

ta zauna da Manubiya yayinda shi kuma ya nufi estate d’innasa….

Sai da ya je Estate d’in nasa tukunna ya ga abunda ya faru

da b’arnar da aka yi,tashi d’aya zuciyarsa ta aminta da zargin da yake ta yi tun d’azu ‘tabbas kashesa ake so a yi’ shi aka so a akashe da basaja sai Ubangiji ya kub’utar da shi kuma wannan aikin na jikin sa ne yake yi,da kunce masa tayar mota da aka yi da

incidence d’in dole sai na jikinsa wanda kuma ya san shige da ficen sa ne zai iya yi,but who could it be???dan zuwa yanzu ya fahimci ba Kausar bace ba,wannan aikin sai dai aikin gayya ko kuma kwararren tantiri tunda har da y’an fashi a lamarin…gabansa ne

ya yanke ya fad’i a tashi d’aya ya yi istighfari da ta’auzi dan kamar yadda d’azu kwakwalwarsa ta basa ‘Mommy ce ta turo Yasmeen ta yiwa Manubiya allura,’hakanan yanzu ma lissafinsa ya basa’ita da Kausar maybe da ko Yasira ne suka yi wannan aika aikar dan

aikin ya wuce b’arnar mace d’aya’

Cikin runtse idanunsa ya shiga kokawa da zuciya da kwakwalwarsa dan sam bai ga ta inda mutuwarsa za ta zamo riba wa Mommy ba….ta ya ma zai yi tunanin hakan ita fa ta haifesa.

Still shi da kansa a cikin zuciyarsa yace”am

ma fa some facts cannot be denied,a iyaka d’azu kad’ai ya fahimci kamar ba ta tab’a shiga fushi irin na yau ba,ta ya za ace d’anki ya kusan mutuwa amma da kika gansa ya dawo safe and unharmed kwata kwata ba ki yi

farinciki ba instead sai fushi da bak’in c

iki…kamar tana fushin ganin plan d’insu bai ci bane shiysa ta fusata ta kasa controlling kanta…..but y?me yasa suke son kashe sa me za su yi achieving?

A take zuciyarsa ta shiga aiyyana masa tana yi masa flashing yadda ba sa son Manubiya! kenan za su kas

he sa saboda sun kasa raba sa da Manubiya kenan? Da sauri ya bawa kansa amsa ta hanyar cewa”noo it doesn’t make any sense!.”

Bai san lokacin da hawaye suka shiga ziraro masa ba yana mai jin wani irin yanayi na tashin hankai da bak’in ciki da rud’ani a ran

sa ya ce”Mommy ba za ta iya kashe ni ba but duk wata alama tana mini nuni ne da tsaf za ta iya aikata hakan….tun ba yau ba ya san ba ta sonshi sannan tunda ya d’auko maganar aure abubuwa suka sake tab’arb’arewa,ga kuma abunda ta yi yau.”

Rud’ani rikici da

kuma rashin sanin gaskiyar lamari ne suka sanya ya runtse idanuwansa da mugun k’arfi still a cikin ransa yace “i’m definitely missing something here…akwai abunda ban gani ba kuma ban sani ba!what is it????”.

Ya yiwa kansa tambayar ba tare da ya san mai b

asa amsar ba!.

Ajiyar zuciya Najeeb ya sauk’e ya dafa sa ganin yana hawaye sannan ya runtse idanuwa yace”Yash sai hak’uri fa!na san me kake tunani amma ka kwantar da hankalinka ka ci gaba da addu’a bawa bai Isa ya yiwa bawa abunda Ubangijinsa bai yi ba”

A hankali ya bud’e idanunsa da suka koma kamar garwashin wuta ya zuba su a kan Najeeb

Jin jina kai Najeeb ya yi yace”yeah tun Akan incidence na accident d’inka na fahimci akwai wanda yake harin rayuwarka kawai na yi shiru ne saboda na ga kaima ka sa

ni amma ba ka son tada maganar,yanzu kuma duba da yadda motarka tana shigowa suma suka baiyyana suka rufe gate suka fara kashe mutumin suka kunna wuta,ya sanya na sake tabbatarwa…amma kar ka damu a hankali zan taimaka maka za mu yi bincike ko dan rayuwakan

mutane kusan d’ari da aka b’atar inshaaAllah za a kama whosoever is behind it…..

“A hankali jikin Yashjub ya fara kararwa duk yadda ya so hana kansa yin kuka sai da hawaye suka balle masa sosai..yanzu a ta dalilin sa aka kashe duk waennan mutanen….how

can he ever forgive himself??

Ga kuma zargin Mommy da yake yi wanda ya sake hautsina sa…MANNUBIYA

(Book 2)

Page 30

Na

Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Duk yadda Yassir ya so ya jira ya d’an saisait

a kansa kafin ya fuskanci Kausar kasawa ya yi…ba ya so ya tunkare ta yanzu dan tabbas zai iya illatata amma kuma zuciya da bak’in cikin rashin samun nasarar kashe Yashjub da kuma kishi ne suka k’i su barshi ya jira d’in dan haka kawai ya nufi gida gadan ga

dan.

A b’angaren Kausar kuwa

A rikice ta shiga gidan itama

sakamokon wani amai mai k’arfi da ya hanata sukuni yake ta faman yunk’uro mata…ta na shiga d’akin ta kuwa ya taho da mugun k’arfi..

Da gudu ta nufi toilet amman tun kafin ta k’arasa ta far

a sakinshi.

Ta jima tana yi kafin ta samu ya d’an sarara mata ta shiga mayarda numfashi…Yanayin k’arnin aman ne ya firgitata ya tsoratata,haki ta shiga yi tana addu’a a lokaci guda ta shiga hargitsa toilet d’in tana neman pts.

Da ikon Allah kuwa ta sa

mu

dan haka ba ta yi wata wata ba ta auna kanta.Bata iya ajjiyewa lokaci ya cika ba hakanan ta shiga safa da marwa a cikin band’akin da abun a hannunta idanunta kyam a kai,gaba d’aya ta hargitse ta ma rasa tunanin me za ta yi…tun da take ba ta tab’a

jin tsoron shigar ciki da fargaba da tashin hankali kamar na yau ba!.

Aikuwa tashi d’aya ta fara ganin alamun positive…kafin ma ya gama tabbatar mata da hakan ta fashe da wani irin kuka ta durk’ushe a wajen tana kallon yadda abun yake yi mata nuni da tana

d’auke da ciki ne.

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”

ta shiga maimaitawa a cikin zuciyarta tana wani irin kuka kamar ranta zai fita…..

Ganin kuka ba zai fishsheta ba ne ya sanya ta share hawayenta ta mik’e jikinta yana wani irin karkarwa ta ajjiy

e abun ta shiga lissafin neman mafita.

Tashi d’aya kwakwalwarta ta d’auki chaji dan haka ta fito ta nufi side d’in Mommy jikinta har yana wani Irin karkarwa.

Su Mommy suna isa gida ta wuce sama d’akinta,Baba larai tana ganin haka ta bita da sauri…

Sai da ta kai k’ofar d’akinta tukunna ta lura da Baba larai dan haka tace”larai ki je kawai ina buk’atar space..”

Daga haka ta bud’e ta shiga tana k’ok’arin rufowa Baba larai ta sa hannu ta tare k’ofar ta shiga ta rufo,Mommyn tana shirin yin magana ta ji

Baba larai tana cewa”Khadija zama na a cikin gidan na ya k’are dan haka na zo ne in yi miki sallama sannan in gaya miki abunda ya faru da kuma taimakon da na yi miki d’azu wanda ya taso na gaggawa.Daga nan ni kam yanzu ba sai anjima ba zan tafi!”.

Runtse

idanuwa Mommy ta yi kafin ta bud’e tace”dan Allah Larai ki barni in huta tukunna we’ll talk anjima..”

Cikin tarar numfashinta tace “Au wai a tunaninki barazana ce nake yi?…wallahi wallahi na gama sakawa a raina Khadija barin gidan nan zan yi! Dan ba zan

zauna rashin hak’uri da rashin lissafinki ya kaini prison ba!.Bari ki ji abunda ba ki sani ba d’azu kuna fita na ji Daddy yana waya,ko kin san wanene ya kirasa?”

Kallonta Mommy ta yi tukunna tace”A’a”

Sai da Baba larai ta sake ce mata “kin san wa ya kira

sa?”Mommyn tace “a’a”

suka yi haka sau uku tukunna Baba larai tace”Mallan lawal!”

Wani kalar mahaukacin bugawa k’irjin Mommy ya yi kafin cikin in Ina tace”mme yya ce mmasaa??”.

“Cewa ya yi yana son magana da shi inaga,dan ji na yi yana cewa”mallan la

wal dama kana raye Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” sai kuma ya fara basa hak’uri kafin na ji ya yi shiru yana sauraronsa sai

kuma yace na godewa Allah nauyi d’aya ya sauk’a a kaina mallan lawal amma ba za ka iya gaya mini ta waya ba dole sai na zo??”

Daganan na ga ya fice compound ya nufi parking lot, to inaga case d’in Yashjub ne ya tsayar da shi ba dan haka ba da tuni yanzu yana garin Garin Mallan……

Cikin takaici Baba larai ta d’aura da cewa“wallahi Khadija in da ace ba ki tsaya dawo mana da aiki

baya ba da tuni ba mu zo nan ba!,na gaya miki Yarinyar nan barinta tare da Yashjub masifa ne a gareki amma kin k’i ki bada goyon baya a samu a fitar da ita daga rayuwar tasa cikin sauk’i yanzu ga irinta nan! Idan kika ga yadda hankalin Daddy ya tashi ya r

ud’e za ki yi mamaki lokacin da ya ji mallan lawal yana a raye…kin san yanzu zai fara wasu wasin mutuwar Khadijah ko?”

A mugun rikice Mommy tace”larai shiyasa tun a lokacin na ce a kashe su kika ce A’a za ki san yadda za ki yi dasu yanzu ga irinta nan ai”

sai kuma ta fashe da kuka cikin gunjin kuka tace”wannan duk ba laifin kowa bane laifin Manubiya ne ita ce wallahi tun da ta zo ta lalatamin komai larai na gaji kashe Yarinyar nan zan yi wallahi kuma ba ki isa ki hanani ba…”

Ajiyar zuciya Baba larai ta s

auk’e kafin tace”ba za a yi haka da ni ba,in da ace zan barki ki kashe rai da tuni mun yi tun a kan Khadija..hak’uri za ki yi ki kwantar da hankalinki ki danne zuciyarki tukunna ki ci riba ba zan tab’a gajiya da gaya muku da ke da su Yassira ba saboda haka

n ne kad’ai mafita”.

Cikin wani irin kuka Mommy tace,Baba larai yanzu to

ba Manubiyan ba,shi mallan lawal d’in Baba larai mun bashi second chance amma kinga yanaso ya tona mana asiri na rok’e ki da giraman Allah ki taimaka mini ki rufa mana asiri a kaw

o k’arshen sa dan wallahi na san gaskiyar lamari zai fad’awa Daddy idan har suka had’u if not menene zai sa yace yana son ganinsa?…”

Numfashi Baba larai ta fesar kafin tace”kar ki damu..Daddy yana fita na kira mutumin da muka ce ya saka mana ido a kans

a,ashe ciwon hanta ne ya ke damunsa likita yace ba shi da sauran lokaci shiyasa yake neman Daddyn ya samu ya gaya masa gaskiya.”

Numfashi ta fesar kafin ta ci gaba da cewa”tunda dama mutuwa zai yi shiyasa kawai na cewa mutumin ya k’ara masa gudu zamu bash

i naira miliyan d’aya,to dai a halin yanzu Ina tabbatar miki mallan lawal ya tafi kai balance dan mutumin a lokacin ce mini ya yi a take zai aiwatar da aikin dan gidan dama ba kowa shi mallan lawal d’in ne kawai da shi da jikarsa ita take jinyar sa to alok

acin ya ga ta tafi kasuwa……yanzu miliyan d’ayan za a tura masa dan naga ya kirani d’azu Ina asibiti shiyasa ban d’auka ba.!Muna tura masa ni kuma zan kama gabana dan ba zan zauna ki ci gaba da lalata m….”

Cikin Jin dad’in maganganunta Mommy ta rungume Bab

a larai wanda hakan ne ya sa ta kasa k’arasa abunda take cewa,wani kuka Mommy ta fashe dashi tana cewa”na gode Larai na gode sosai ki bani accnt number miliyan biyu ma zan bashi wallahi….sannan zan gyara wallahi zan yi yadda kike so dan Allah kar ki sake c

ewa za ki tafi.”

Da kyar Mommy ta lallab’a Baba larai ta hak’ura da tafiya,daganan suka kira mutumin ya shaida musu cewa”Mallan lawal yana ma shirin shiga k’asa a halin yanzu dan wanka ma ake yi masa.”

Naira miliyan biyu Mommy ta tura masa a take daga

nan ta nutsu tana sauraron hud’ubar Baba larai.

Da sallama Yasira ta turo k’ofar d’akin ta shigo,kafin ta k’araso ta zo ta tsaya a gabansu.

Kallonta kawai Baba larai ta yi ta maida hankalinta ga Mommy kafin tace”a baya da kika iya kwantar da Kai wac

ce kalar riba ce ba ki ci ba?yanzu kuwa kinga ai komai lalace miki yake yi saboda rashin tunani da lissafin da kika bawa ragamar rayuwarki,kuma bari ki ji ba ni da tantama a yau Yash ya dasa ayar tambaya a kanki wallahi saboda abunda kika yiwa Manubiya a g

aban kowa ya na nuni ne da kin tsaneta dama tun asalin farko wanda hakan zai sanya ya fahimci dama chan pretending kike yi kuma bakin ku d’aya ke da su Yasira duk ba son matarsa kuke yi ba!dan haka yanzu ko ciwon yatsa Manubiya ta yi Ina mai baki tabbacin

Yashjub ke zai zarga tunda dama ba wata shak’uwa ce a tsakaninku ba balle ya ki zarginku,kuma ko su Yasira sun je gidan ido zai sanya musu ya dinga d’arr d’arr da su ta yadda ba su isa yin komai ba shikenan kina ji kina gani Manubiya zama daram!

Hakanan a

bubuwa za su yi ta faruwa da mu,tunda kink’i ki bada goyon baya mu samu a yi abunda za ta tafi.

Shiysa na yanke shawarar in tartara ya nawa ya nawa in kama gabana tun kafin bomaboman da za su iya hallaka ni su fara fashewa.”

Ajiyar zuciya Yasira ta sau

k’e kafin tace”Mommy nima gaskiya abunda kika yi yau ban ji dad’in sa ba….”

Cikin tarar numfashinta Baba larai tace”Yasira yo

ai har da ku!”

Jin jina kai Yasira ta yi kafin tace”ni kam zuwa yanzu Baba larai duk yadda kika ce inshaaAllah hakan za ‘a yi,s

aboda hakan ne kawai mafita,gara in yi tolerating d’inta in nuna ina sonta in ja ta a jiki na wata d’aya ko biyu akan mu rayu da ita har abada muna fama da ita tana janyo mana masifu kala kala,na tabbatar kashe Ya Yash da aka so yi a yau shima duk a cikin

masifun da take tafe da su ne!.”

Cikin sauk’e ajiyar zuciya ta kamo hannun Baba larai ta ci gaba da cewa”dama ai ya san za mu je mu tayata gyaran gidan ko?”ba ta jira jin mai Baba laran za ta ce ba ta d’aura da cewa”zan yiwa su Yasmeen magana da su Yusra

na yi miki alk’awarin inshaaAllah daga yau mun chanza zani,amma Ya’isha ba za ta bimu ba dan na san za ta iya b’ata mana komai…ki had’a duk wasu abubuwa da ya kamata inshaaAllah this time around ba za mu baki kunya ba ,za ki sha mamaki…”

“Allah ya yi

miki albarka Yasira,zuwa dare zan ganku ke da su Yasmeen d’in kafin ku tafi”

Jin jina kai Yasira ta yi kafin ta kalli Mommy tace mata”Daddy yana son ganinki…”

Daga haka ta juya ta fita ta rufo musu k’ofar….

Tana fita Baba larai ta saki murmushi dan

tabbas ta hango jajircewa a idanun Yasira,ta san kuma su Yasmeen ma za su yi mata biyayya inshaaAllah wannan karon akwai nasara….cikin jikin Manubiya za su fara farma a yadda Yash yake ji da cikin nan ta san easily za su samu matsala da shi da ita idan har

suka nuna masa kamar Manubiyan ce ta zubar,but tayaya za su nuna masa hakan??dole su nemo reason da zai yarda da shi……

Tana wannan tunanin ta ji Mommy tace”bari in je…”

Kallonta Baba larai ta yi kafin tace”Juyin duniya!Khadija kar ki kuskura ki bari ya

fahimci kin san wani abun”

Jinjina kai Mommy ta yi gabanta yana dukan uku uku ta juya za ta fita…cikin son kwantar mata da hankali Baba larai ta ruk’o hannunta tace”ki kwantar da hankalinki…”

Hawayen da suka b’allewa Mommy ne suka sanya ta kasa ci gaba d

a magana,a hankali ta rungumota ta shiga lalllashinta..fashewa Mommy ta yi da kuka cikin kukan tace “dan Allah dan annabi larai kar ki sake cewa za ki tafi,a wannan worst situation d’in larai idan kika tafi kika barni Ina makomata??…”

Ajiyar zuciya Baba

larai ta sauk’e ta cikata tace”ba bu inda zan je amma Khadija kema sai kin chanja zani!kamar yadda su ka yi alk’awari dan Allah kema ki gyara…mu samu Yarinyar nan ta tafi daganan mu aura masa Kausar bayan shekara d’aya ko biyu idan ta haihu muka samu abun

da muka so sai mu k’arasa shirin mu a samu a rufe chapter nan wallahi na gaji,sai abu d’aya ake yi yau kusan shekara nawa amma ba riba!”

Ajiyar zuciya Mommy ta fesar kafin tace”Larai I can’t trust Kausar with Yashjub anymore,a da na d’auka soyayyar da t

ake yi masa mai sauk’i ce ko kuma lust ko wani abu makamancin haka shiyasa na yi tunanin idan suka yi shekara d’aya ko biyu ta samu abunda takeso ta haihu ta d’an zauna da shi ya fara fita a ranta to za ta iya yi mana abunda mukeso dan na san tunda ba ya s

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login