Showing 156001 words to 159000 words out of 259716 words

Chapter 53 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

32

wutar d’akin da na d’akin Muhsin kuma suka d’auko wasu takardu wai d’akin Muhsin d’in ma rushesa za su yi filin rabi ne na Baba rabi kuma nasu…a ranar babu wanda ya runtsa.Ya Yusuf dai shi yake ta k’ok

’arin hanasu Anty Umma ma har kuka ta yi tana lallab’asu tana so ta ga an rufe case d’in amma sai tujara suke yi kaka mallan yana gefe yana mana gori kala kala..har da cewa ya Musbah ya gudu ya barmu,kema wai an bi kwad’ayi an aura miki mai kud’i gashi ba

ya tsinana mana uwar komai ko kwayar shinkafa bamu da ita rabon da ya ga mun yi girki har ya manta,wai dama shiyasa ya ke so a aurar da ni a Ya Yusuf ya rufa mana asiri ya dinga ciyar da mu amma mu kuma mun k’i yarda.”

Mun d’auka maganar d’akin Muhsin

fad’i kawai suke yi ashe su sun d’auki abun serious dan da muka zo duba ki bricklayers suka nemo wajen mutun shidda suka nuna musu d’akin aka fara rushewa…Baba yana d’aki sai jin rushe rushe ya yi da hayaniya,baya so ya kula su yace tun last two weeks ya l

ura kawai neman masifa suke yi da shi shiyasa ya k’i fitowa ya tsaya a d’aki ya yi ta kiran Ya Musbah shi kuma ya k’i d’auka to inaga bak’in cikin hakan ne ya sa muka shigo muka tarar da shi a sume……

“Innalillahi wa Ina ilaihirrajiun”

Manu ta ke ta mai

maitawa kafin ta share hawayenta ita ta ma rasa bakin magana,chan tace”kuma har yau bai zo ba?”

Jinjina kai Jidda ta yi alamun “eh”kafin tace “inna tace mini d’azu da na fita siyo mana abinci ya kira Baba ya yi masa ya jiki inaga message d’in da na yi mas

a ya gani sannnan ya ce gobe zai zo….”

A hankali Manu tace”da ke da Muhsin mu je gidana mana kafin mu ga yadda hali zai yi su Inna kuma tunda suna nan they are safe dan gaskiya Jidda ba za ku koma gidan nan ba abun ya yi yawa an kai peak!”

Murmushi Jid

da ta yi cikin jin tsananin tausayin kansu tace”Adda Manu kin manta su waye dangin mijin na ki ne?ai kema kin san zamn mu a cikin gidan ki ba abu mai yiwuwa bane ba….”

Shiruu duk suka yi kafin Jidda ta sake cewa”Ya Yusuf dai tunda ya zo ya ke ta bada ha

k’uri kuma ya kawo takardu wai ya siye mana gaba d’aya filin daga wajensu har ya kira an fara gyarawa…..

To dai wannan karon gaskiya Baba ya zuciya dan tunda Ya Yusuf ya zo bai sake da shi ba daga amsa gaisuwa ya ja bakinsa ya yi gum!Inna ce ma ta d’an sa

urare sa kad’an,har da cewa wai ya sayi sabon fili zai yi maaana gini waye waye Baba ya yi hak’uri kar ya damu dan ya Musbah ya daina kula mu inshaaAllah indai yana raye da shi da Inna ba za su yi kukan rashin d’a ba.”

“Wai shi Yusuf yana nufin aikin ba

nkin ne duk ya azurtashi haka??”

“Hmm”Jidda tace kafin ta d’aura da cewa”Siyama ta ce mini idan fa kika shiga side d’in Baba Habu za ki d’auka a hotel kike tsabar yadda ya gyara sa,ya yi interlock a gaba d’aya compound d’in gidan ya sakawa iyayensa sola

r shi kuwa gidan da ya gama ya koma akace har abun tsoro hawa biyu fa,motocin sa fa uku,wayar sa wadda ta fito last month ita yake rik’ewa…y’an unguwa sai magana ake yi amma iyayensa da kaka mallan sunce hassada ce ya ci gaba da business d’insa ya dage da

addu’a kawai ya yi harkar gabansa kar ya kula kowa….”

“Ha’a Manu yaushe kika zo??”

cewar Inna wadda ta fito da niyyar bin bayan Jidda dan ta ji shirun ya yi yawa…a hankali Manu ta tafi jikinta ta rungume ta…cikin rashin jin dad’i inna tace “yanzu Yarin

yar nan sai da kika fito?duba fa hannunki har da cannula!to Allah ya kyauta..””Bismillah”daga haka ta juya ta nufi ciki suka mara mata baya.

A zaune suka tadda Muhsin yana assignment Baba kuma yana zaune a kan gadon jinyarsa yana kallon k’ofar da alamun

shigowar tasu yake jira dan ya ji Inna ta ambaci sunan ‘Manu!’.

A hankali ta k’arasa ta d’an durk’usa ta gaida sa tukunna ta zauna a kujerar mai jinya ta shiga tambayarsa ya jikinsa..

Murmushi ya yi duk da bai so ta fito ba duba da yanayin jikinta amm

a kuma ya yi matuk’ar jin dad’in yadda ta damu ta taho dukda itanma a kwance take…

Cikin fesar da numfashi ya yi ta’auzi ya kawar da shed’an d’in da ya fara comparing masa himmar Manubiya da Ya musbah a kansa,tukunna yace”ya jiikin naki?”

A hankali tace”

Alhamdulillah”

“MashaaAllah Allah ya inganta”ya ce kafin ya d’aura da cewa”ki kira mijinki ku koma Manu dare fa ya yi,ai na warke ma Alhamdulillah”

Murmushi ta yi tace”ya tafi siyo abu sai ya dawo za mu tafi..”

Jin jina kai kawai Baba ya yi daga haka su

ka d’an tattauna Akan batun su Uncle,Manubiya ba ta so ace Yashjub ne ya bawa iyayenta gidan da za su zauna a ciki ba,amma ba ta da choice tashinsu a kusa da su Uncle shine mafita dan abun nasu ya yi yawa..shiyasa har wani sanyi ta ji da ta ji Baba yana ga

ya mata ai Ya Nafi’u ya yi masa batun maganar da suka yi shi da Yashjub shi kuma

ya amince,inshaaAllah yana fita daga asibiti za su tare,dan d’azu ma Yash d’in ya zo ya d’auki ya Nafi’u suka je ya basa gidan tare da makullai da takardun.Da Nafi’un ma ha

r yana cewa zai zo ya kawo yanzu to sai nace ya barshi kawai dare ya yi..ma had’u gobe.A gidan ma har da b’angaren Musbahu Allah ya sa dai Baraka ta yarda ya dawo gidan su zauna….”

Ahankali Manubiya ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace zai dawo inshaaAl

lah Baba,ku dinga yi masa addu’a kar ku bar b’acin ransa a cikin zuciyoyinku fushinku a garesa masifa ne.”

Jin jina kai Baba ya yi kafin yace”ki na da gaskiya kam,Allah ya sa mu dace.”

Knocking suka ji dan haka Muhsin ya mik’e ya je ya bud’e k’ofar….

cikin girmamawa ya gaida Yash ya amsa masa da kulawa tukunna suka k’araso cikin d’akin a tare bayan Muhsin ya maida k’ofar ya rufe.

Sai da Yashjub ya d’an russuna tukunna ya gaida Inna da Baba suka amsa ya tambaya ya k’arfin jikin yace”Alhamdulillah”

Wallahi dama shiyasa d’azu bai shigo ba yanzu ma kawai ya ga dare sosai ne shiyasa ya shigo tafiya da Manubiya kar ya barta tana yawo ita d’aya da dare…Sam ba ya so su Baba su yi masa godiya amma suna gama gaisawa suka hau yi masa godiya har da su Jidda w

adda itama sai yanzun ne ta ji batun daga bakin Baba.

Kamar zai nutse k’asa haka ya ji,hakanan ya sunnar da kai yana ta faman cewa”Ameen Ameen.”

Ba su wane dad’e ba,suka yi azamar tafiya,Saida duk ta yi musu sallama tukunna ta yi hugging Jidda ta b

a ta atm card d’inta da ta d’auko

daga jaka tace gashi,karb’a Jidda ta yi tukunna ta fara shirin rakasu,murmushi Yashjub ya yi ya ce “ta barshi ai su biyu ne.”

Daga haka suka tafi Yashjub yana tunanin

“Ba dan suma a asibiti suke ba da sun tafi da su Ji

dda”.

A mota Manubiya ma ta so yi masa tata godiyar amma ya yi kicin kicin”wai idan ta yi sai sun yi fad’a”

Har wani turo baki wanda hakan ya sa ta fara dariya….

“Shine amma baka gaya mini ba?”

“Na san zugawa za ki yi ai ki hana,shiyasa na zaga

ye ki!”

Ya bata amsar yana mai d’an juyowa ya kalleta.

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace”da Ya Nafi’u kuka yi magana kenan?”

Sai da ya d’an yi shiru tukunna yace”ni ne na tambayesa na nace shi ne ya gaya mini komai”

Cikin mutuwar jiki tace”ba la

lle ai ya Musbahn ya yarda ya tashi daga gidan da yake d’in ba.”

Kamar ba zai ce komai ba sai kuma yace”na sa a nemo mini number landlord d’in nasu,kar ki damu zai tashi.”

Shiruuu ta yi haka shima Yash d’in daga nan har suka k’arasa asibiti.Kowa da t

unanin da ya ke yi,Yashjub gaba d’aya hankalinsa yana a kan wayar Manubiya ne ya lura wayar a silent take kuma sai faman kiranta ake yi tana rejecting shiyasa ya tafi tunanin ko dai wannan wanda ya kira ta ta k’i cewa komai jiya ne?

To kenan ta san waye t

unda har take k’in d’auka…bai yi expecting za ta b’oye masa wani abun ba shiyasa shima ya yanke a kan ba zai tambayeta ba,zai danne kansa ya ga iyakar gudun ruwanta.Amma fa yadda zuciyarsa take yi sakamokon kishin da ya ke tunzurosa hatta jijiyoyin gaban g

oshinsa sai da suka fito rad’au!.

A b’angaren Manubiya kuwa Abbakar ne yake ta nacin kiranta da messages na ban hak’uri wai yana son magana da ita yana neman taimakon ta,ta ji zafin yadda ya banzatar da ita amma kuma babban dalilin ta na ignoring d’insa

Yashjub ne! Ba ta so su samu matsala ita da shi saboda wani Abbakar kuma he made it pretty clear to her cewa ba ya son relationship d’inta da Abbakar d’in kwata kwata ko gaisawa ba ya so su yi!…ta san ba ya son shi saboda yana tunanin kamar son ta yake yi

kuma ta tuna b’acin ran da ta ji a muryar sa ta kuma gani a fuskarsa duk a ta dalilin Abbakar d’in,shiyasa yanzun ta ke jin tsoron gaya masa ‘Abbakar d’in ya na ta kiranta,ya turo mata message yana buk’atar taimakonta.’Ta zab’i kawai ta rabu da shi da zar

ar ta nutsu za ta nemo yadda ake block ta yi blocking d’insa gaba d’aya,ta san Abbakar ya taimaka mata ba adadi ya kamata ace ta taimakesa yanzun itama amma Yashjub comes first a komai na rayuwarta kuma tunda ya nuna ba ya son ko gaisawa ne su yi da shi in

ashaAllah za ta yi masa biyayya…..…..MANNUBIYA

(Book 2)

Page 31

Na

Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Sai dare tukunna Baba larai ta tambayi Mommy ya suka yi da Daddy…duk yadda suka yi ta zaiyyane mat

a,tashi d’aya Baba larai tace mata”bugar cikinta ya yi amma tunda ta ga bai yi mata komai ba yana so ya yi confirming ne dan haka ta nutsu ta sa ido sosai ta yi taka tsantsan.”

Tashin hankalin da Mommy ta shiga ba zai misaltu ba dan sai da Baba larai ta y

i mata bayani dalla dalla tukunna itama ta fahimci tabbas bugar cikin nata yayi..yo Ina zata fahimta?gaba d’aya d’azun duk a rud’e take hankalinta a tashe.

Sai wajajen k’arfe sha biyu na dare tukunna Yassir ya yi sneaking daga d’akin Kausar ya tafi s

ide d’insa a lokacin ya san kowa ya yi bacci babu mai ganinsa….

Ba k’aramin mamakin ganin Munirat a zaune a cikin d’akinsa ya yi ba…shaf ya manta da lokacin da ya bata makullan side d’in nasa shiyasa yace”ta ya kika shigo?”

Murmushi ta yi ta mik’e tace”h

ar ka manta lokacin da ka mallakamin makullan d’akinka har ma da na zuciyar ka kenan??”

Sai kuma ta girgiza kai tace”hmm..of course you do”

Numfashi ya fesar a ransa ya aiyyana”lokaci ya yi da zai yi getting rid of Yarinyar nan fa”

Dan haka ya kalleta

yace”ki je ki yi bacci please,kaina ciwo yake yi..kar ki sa raina ya b’aci”

Wani irin kuka ta fashe da shi tace”you snake!!ashe dama duk yaudara ce Yassir??yau ni ce zan b’ata maka rai?ka manta yadda kake cewa ba ka iya bacci idan ba na kusa da kai,ka ma

nta duk kalolin k’aryayyakin da ka dinga zuba mini Yassir yau ni kake wulak’antawa kake pushing away Ina kiranka ba ka d’auka ba ka replying messages d’ina saboda ka riga ka samu abunda kake so???”

Runtse idanuwa ya yi da k’arfi kafin ya bud’e ya matso

daff da ita tukunna ya ce”ki fad’a ko nawa kike da buk’ata zan biyaki fansar budurcinki”

Wani mahaukacin mari ta zabga masa wanda sai da jinsa ya d’an d’auke na y’an sakanni.

Cikin tsananin b’acin rai ya d’ago ya zuba mata manyan idanuwansa da suka yi ja

zir yace”zan baki mintuna biyu kacal Munirat! ki fice ki bar mini side d’ina if not wallahi zan baki mamaki….aikin banza!!! ba ma ki kai yadda na yi expecting zan same ki ba amma kin bi kin wani d’aga mini hankali sai kace wadda kika ba ni ranki!”

Kallo

nsa kawai take yi jikinta yana wani Irin karkarwa kamar mazari idanuwanta suna zubda ruwa kamar fanfo….maganganun cin mutunci da cin zarafi ya ci gaba da fad’o mata dan haka kawai ta wuce sa ta nufi k’ofa tun kafin ya sa zuciyarta ta buga,har ta fice bai d

aina magana ba sai da ya tabbatar da ta yi nisa tukunna ya yi tsaki ya fad’a bathroom……

Washe gari da sassafe ta rubuto masa doguwar wasik’a da tsinuwa da Allah ya Isa kala kala ta had’o masa da makullayensa da duk wasu gifts da ya tab’a bata ta kai sid

e d’insa ta ajjiye ta.Tabbas Yassir ya koya mata lesson a rayuwa kuma ya cuceta har abada,amma ba komai ya je zai gani……

Da safe Dr ya sallami Manubiya dan jikin nata Alhamdulillah sai d’an abun da ba a rasa ba.

Direct gida Yash ya kaita bayan ya

tsaya ya siya musu abinci a hanya…sai da suka yi wanka suka ci abinci suka huta tukunna ya ce “bara ya je ya d’auko mata Jidda da Muhsin su taya ta zama kafin ya je ya d’auko mata gwaggwo mai aiki.”

A take kuwa farin ciki ya wanzu a fuskarta,murmushi ka

wai ya yi yai kissing forehead d’inta ya fice bayan ya tabbatar ba ta buk’atar komai.

Ko da ya je Inna ta so ta hana su Jiddan zuwa dan ta san halin k’annensa da mahaifiyarsa kar zuwan na su ya zamo case amma sai Baba ya ce”ba komai su je kawai”

Dan a

duniyar nan Baba bai ga alfarmar da Yashjub zai nema a wajensa ya k’i yi masa ba muddin bai fi k’arfin sa ba.

Hadda Siyama aka taho dan a lokacin ita da anty Umma sun je duba Baba Yash d’in ya je

hakanan ita da su Ya Nafi’u waenda suka zo da makullan gi

da suka ta yi masa godiya suma..Anty umma ta na saka masa albarka…..

Sai da ya kai su gida yace”su d’ebi kaya”dan a cewarsa “kwana za su yi”tukunna suka kama hanyar nndc quaters. Ba sa so su yi jayayya da shi,shiyasa kawai suka ce masa to suka d’ebo

kayan amma sun san ko da ace suna son kwanan ma su Inna ba za su bari ba….

Yana hanya Najeeb ya kirasa ya ce masa yana k’ofar gidansa dan haka ya ce”ya basa 5 minutes yanzu zai k’araso shima inshaaAllah”.

Suna isa tsabar sauri Siyama ko gama pa

rking Yash bai yi ba ta fito da sauri ta nufi entrance..ta ci sa’a kuwa dan Manubiya tana k’asa dama tana jiransu…murnar ganinsu da oyoyo d’in da Manubiyan ta tsaya yi ne ya sa ba ta samu ta shige d’aki ba har Najeeb d’in ya shigo shi da Yashjub.Allah ya s

o da ma Manubiya ta hijab d’inta dan ba ta dad’e da idar da sallar azahar ba.

Sama suka nufa Yayinda shi da Najeeb suka zauna a nan k’asan….ba k’aramin tausayi Najeeb ya bawa Yashjub ba dan ya fahimci komai kuma ya lura ko kallonsa Siyama ba ta son yi d

an haka ya gama shirya yadda zai yi ya samu ya ceto rayuwar Abokinsa saboda in banda tsantsar so da k’aunar Siyama ba bu abunda yake hangowa a tartare da shi….

Siyama da Jidda har ma da Manubiyan ne suka sauk’o suka yi musu fried rice da coslo mai d’an

karen dad’i itakam Manubiya kafin a gama ta jigata dan wani irin amai da zazzab’i take ji gashi aman ya k’i fitowa……

Ana gama cin abinci Yashjub ya kira Manubiya yace “ta turo masa Siyama”

Da d’an mamaki Najeeb ya kallesa sai kuma ya yi shiru kawai ya

ci gaba da tunanin da tun d’azu yake ta yi dan ko da suka zauna ma Yash d’in ne yake ta magana.

Cikin nutsuwarta ta k’arasa cikin parlourn inda suke ta sake gaida Yash tukunna ta zauna a kan one seater da ya yi mata nuni yace “ta zauna”

Kamar ba za

ta kula Najeeb ba sai kuma kawai tace”Ina wuni”

Saida ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna yace”Alhamdulillah,kwana biyu…”

Ta san jan magana yake so

,shiyasa kawai ta sharesa.

Shiru parlourn ya d’auka kafin taji muryar Yash ta d’ira a dodon kunnuwant

a kan sa tsaye yana cewa”Siyama mai yasa ba kya kula Abokina?ki ke ta bashi wahala..ko kwata kwata ba kya son shi?”

Nauyi tambayar ta yi mata gashi ba ta yi expecting hakan ba..shiyasa ta sunkuyar da kanta ta yi shiruu ta gagara cewa komai.

Jan numfa

shi Yashjub ya yi,kafin yace”a da ban yi niyyar saka muku Baki ba amma naga abu har wajen 4 months ya k’i gyaruwa sai gara mini Aboki kike yi shi kuma na san ba hak’ura zai yi ba!”

“Na san watak’il a kan Ya’isha ne kuka samu sab’ani da shi…wanda ko baki a

uri Najeeb ba na san ba zai auri Ya’isha ba tunda ba sonta yake yi yanzu ba kinga an yi biyu babu kenan.

Kasancewar ni yaya ne ga Ya’isha ba shi zai sa in k’i bin bayan gaskiya ba,Maganar gaskiya Ya’isha ita ta yi neglecting Najeeb har ya zo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login