Showing 258001 words to 259716 words out of 259716 words
yi wata mummunar gobara
babu dai wanda aka rasa duk an fitar dasu on time ammafa ko cokali basu samu sun d’auka ba komai sai da ya k’one….a lokacin ya Musbah ya fara tashen arzik’insa shi ya kwashessu ya kama musu haya na shekara d’aya…a cikin watanni tara aka gina musu gidaje ma
su bene hawa d’add’aya part uku har da anty umma da babban parlourn kaka mallan….
Sai da su Baba Habu suka yi da gaske tukunna kunya danasani da nauyin Baba suka barsu suka zo gidan suka yi godiya suna kuka sosai suka nemi yafiyar Baba bisa ga abunda suka
dinga yi masa!!….murmushi kawai Baba ya yi ya ce musu komai ya wuce burinsa kawai shi a yanzu a yi zumunci bai rik’e kowa a cikinsu a rai ba!
A rayuwa kowa ya kanyi kuskure the best part shine idan mutum ya gane kuskurensa ya gyara shi kuma wanda aka yi
wa laifi ya yi k’ok’ari ya yi hak’uri kar ya ce zai rama ta hakan ne za a ga dai dai komai ya tafi bisa tsari.”
Ai kuwa Baba ya ga zumunci ganin idanunsa kuma yana kan ganin zumunci saboda a halin da ake ciki Hatta d’inki tare Baba Habu da Uncle suke yi
da shi komai iri d’aya wani zubin har agogo iri d’aya suke sakawa gidansa kuwa suna yawan zuwa kasancewarsa k’aramin cikinsu ya sanya shima yake zuwa nasu gidajen sosai dan ya hutashshesu.
Anty Umma kuwa tun da akayi gobarar da ta dawo gidan Baba har y
au su Inna sun ce kawai ta zauna tare da su…Gwaggo Suwaiba ma tana yawan zuwa Mijinta har yau yana nan amma fa ciwo ya ci ya cinyesa ko tafiya ba ya iya yi haka nan take fama da jinya.
Kaka mallan shima yanzu kam tun shekaru shidda baya ko bakin magana
ma babu yanzu kuwa ba ma ya sanin waye a kansa.ciwo ya ci ya cinyesa sosai.
…….
Hannun Ya Musbah a bud’e yake sosai shiyasa yake dad’a samun bud’i kwata kwata bashi da rowa bashi da kyashi…Ya Nafi’u ma ya samu chanjin aiki yana da rufin asirinsa amma du
k da haka Ya Musbah sai da ya siya masa gida ya chanja masa mota tukunna hankalinsa ya kwanta sannan har gobe kayan abinci kayan sakawa na sa da Yaransa biyu mace da Namiji da na matarsa kullum ya Musbahn ne yake siya k’iri k’iri ya hanasa yin duk wata hi
dima ya d’auke masa komai dan idan duniya da alk’awari ba zai tab’a mantawa da Nafi’u ba.!
Duk wani business da yake yi sai ya san yadda ya yi ya saka Nafi’u a ciki shima ya samu abunda ya samu.
Sosai rayuwa ta chanja tables suka juya Yaransa uku a halin
yanzu duk maza dan Hadiza ta Haifa masa Yashjub da Naf’iu.
Jidda itama suna zauna cikin Jin dad’i dukiya da daula da tsananin k’aunar juna suna son juna ita da Ammi Sosai suke zamansu lafiya….Yaranta uku biyu mata d’aya Namiji ta kammala karatunta a no
rthwest yanzu haka tana businesss.
Siyama ce mai Yaro d’aya saboda sai da ta haihu tukunna ta dumfari karatu shiyasa suka tsayar akan sai ta gama sai ta d’aura daga inda ta tsaya sosai suma suke zaune lafiya dan shima Najeeb mijin marainiya ne ma sha Al
lah.
Yahansu ta auri Kamal wanda a yanzu shine governor na Jahar Kano state dan shekara d’aya asalin governor d’in ya yi ya yi ya rasu shi ya maye gurbinsa aka basa ruk’on kwarya da aka zo zab’e kuma jama a suka sake zabaar sa.
Yasmeen ta yi aure.
Munirat ma ta auri Alhaji bashir (asalin saurinta)matarsa ta rasu ata sanadiyyyar ciwonta da ya motsa mata haka kurum..ta yi jinyar sati biyu Allah ya karb’i ranta. Ko da ya dawo yace zai auri Munirat su Ummi basu b’oye masa komai ba nan yace ya ji ya gan
i ai k’addara tana kan kowa kuma har Yaron zai rik’e..Aikuwa ya rik’e amana dan shekara ta hud’u suke a ciki amma bai tab’a nuna mata rashin mutunci ko
gori ko banbanci a kan d’anta ba sosai ya had’a da Yaronta wanda ta Haifa masa da y’ay’ansa na wajen uw
argidansa marigayiya da d’an gidan Yassir d’in yake kula da su tsakani da Allah itama kuma Munirat ta rik’e masa Yara bilhakk’i da gaskiya….
Ya’isha da Junior sun koma Uk da zama d’ansu d’aya yanzu take da cikin na biyu,suka zamansu Alhamdulillah.
Haj
iya Mama kam k’iri k’iri Ummi da Mama sun yiwa Mom wayo sunce suma ta bari su samu nasu ladan.
Za ku sha mamaki idan na ce muku Abbakar Yusra ya aura.
Wanda itance ta ce ta ji ta gani duk duniya ita shi take so…da farko farko ma b’oyewa tayi sai da ta
ga k’aunarsa ta na shirin yi mata illah tukunna ta fito ta fad’a…da farko su Manu k’in yarda suka yi amma da suka ga k’anwar tasu ta mato da yawa kuma Abbakar ya yi nadama sai kawai suka nemi zab’in Allah ai kuwa tunda aka fara maganar har aka d’aura aure
komai sumul…yanzu haka Shekarar su biyu da aure suna zaune a garin Abuja inda yake aiki d’ansu d’aya mai sunan Daddy.
Muhsin ma yana Abuja yana karanatar English a nile university level 1.
Yasira ce dai Allah ya d’aura mata jinkirin aure dan sai yanz
u tukunna Allah ya fito mata da miji alhaji isma’il matansa biyu itace ta uku…yanzu haka an saka rana wata uku….
An yankewa Mommy hukuncin d’aurin rai da rai….kisan da suka saka aka yiwa mallan lawal..mutuwar Ya’isha da kuma d’an Khadija na farko wand
a ita da Baba Larai suka dinga d’urawa mata magani suka kashe tun a ciki.
Dama tun kafin y’an sanda su tafi da ita ta daina gani…Shekarar ta d’aya a prison mugayen prisoners suka jefa mata bonk gado na k’arfe a k’afafuwanta,ba a bata kulawa da wuri ba
har sai da k’afafun suka rub’e hakanan tana ji tana gani sai yankewa aka yi..kuma har yau an gagara a samu yadda aka yi akai mata transfer zuwa gidan gajiyayyun hakanan take fama a prison ba ido ba k’afa.
Manubiya da Yashjub Yaransu uku..ta farkon
mace takwarar Hajiya Mama ‘Yahanasu’ suna ce mata Noor sai maza biyu masu sunan Baba da Najeeb,
Yaran Masu tsananin shiga rai kamannin Manu duk suke d’aukowa gasu da k’ok’ari da wayo tubarkallah.
Itama ta kammala karatunta ta yi masters yanzu haka PhD ta
keyi kuma tana lecturing a buk…..
A ko da yaushe idan Manubiya ta kalli rayuwarta sai ta yi kwallah….Duniya rawar y’an mata
Kasancewarta y’ar talaka talakan ma maskini hakan bai hana Ubangiji yin ikon sa a kanta ba dan gashi abunda mutane wasu suke gani
impossible ita ya faru a kanta kuma tana rayuwa a cikinsa…ta samu mai masifar sonta wanda sam ba class d’insu d’aya ita da shi ba! ta aura kuma ya sota yana kan sonta tsakaninsa da Allah
Tabbas komai yayi farko zai yi k’arshe farkon rayuwarta da kuma t
sakiyar rayuwarta (lokacin da su mommy suka sakota a gaba kowacce hanya ta kulle) inda ace wani zai ce mata za ta ji wannan dad’in da take ciki a yanzu ta samu wannan kwanciyar hankalin a gaba da ba zata tab’a yarda ba..amma with du’a everything find its p
lace perfectly…tabbas in da Rabbana komai ba wahala.
Mugu ba shi da riba,musamman ma mugun da yake zalinci yake cin riba baya tuba kullum ribar kawai yake gani!Tabbas irin su a rayuwa sun fi kowa wulak’anta daga k’arshe sannan kuma azabar su ta fi tsana
ni ranar gobe k’iyama.
A ko da yaushe idan mutum ya yi hak’uri ya dogara da Allah Tabbas komai mai wucewa ne kuma komai akwai lokacin sa.
A bangaren Yashjub shima babu abunda zai ce sai Alhamdulillah!!ga matarso Allah ya basa ga Yara Alhamdulillah
ga Mahaifiya ta gari ga mahaifi mai k’aunarsa ga y’an uwa masu sonsa ga arzik’i dukiya farin ciki da jin dad’i da tsantsar kwanciyar hankali ya samu yana kan samu ta koina!!tabbas a ko da yaushe bashi da kalmar da ta fi dacewa yacewa Ubangiji sai ‘ALHAMDUL
ILLAH!!!!!.’
Alhamdulillah!Alhamdulillah!!
Na godewa Allah da ya bani ikon kammala littafina mai taken suna’MANNUBIYA’.
Kuskuren da na yi a ciki Allah Ubangiji ka yafe mini,darussan da suke a ciki Ubangiji ka sa mu amfana.
*****************
*****
⬇
**************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************
⬆
**********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Roma
nce, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US
******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 08138873799
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatt
a facebook group dinmu ma za ku samu.
**********************
⬇
**************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
**********************
⬆
**************************
GODIYA TA MUSAMMAN GA
Nazeefa Sabo Nashe.
Da
Maryam Bulama.
Ba zan tab’a mantawa da ku ba,alkhairin Ubangiji ya isar muku a duk inda kuke.
JINJINA da GODIYA mai tarin yawa ga mutanena
Oum Zahra
Maman Aliyu
Fauziyya Gwandu
Hannah OC
Binta Muhammad
Yumin Aliyu
Shamsiyya w
ada
Ummi Muhammad
Indo Aysha
Fati Abbas
Kudra
Maman Hafeez
Zahra Auwal
Iymert
Habiba Idris
Salmerh
Maryam Mustapha
Hannah collection
Mrs MB
Sadiya
Oumhanan
Da duk wani member na group d’in MANNUBIYA group one and two..ba zan tab’a mantawa d
a ku ba,ba ni da bakin gode muku sai addu’a wallahi!na gode na gode sosai Allah ya bar zumunci ya kuma kare mini ku kullum da ko da yaushe!na gode kwarai!!
Ina muku fatan alkhairi.
FATAN ALKHAIRI ga
duk wani member dake Mikiya Writers Association,Rab
bi ya dafa mana ya sake had’a kawunanmu.
Taku har kullum
Humayrah Bulama.