Showing 153001 words to 156000 words out of 259716 words
ba son r
abuwa da babyna nake yi ba hak’uri kawai nakeyi ina biyeka.”
A hankali ta kamo hannunsa ta d’aura a kan cikinta tace
“This is our child,
kasancewarsa jininka ya sa na ji Ina matuk’ar k’aunarsa
saboda tsananin son da nake yi maka ba zan iya rabuwa da
shi ba,wallahi ban tab’a jin so da k’auna bayan wanda nake yi maka ba sai a kan cikin nan!”
Damk’e hannunta ya yi da k’arfi dan ba kad’an ba
maganganunta sun shige sa sun yi tsananin tasiri sun ci galaba a kansa.
Ya jima maganganunta suna ratsa sa k
afin a hankali cikin kwantar da murya yace
“Kausar!!
Daddy will kill me
Mommy ma Allah kad’ai ya san mai za ta ce…me”
Cikin katseshi tace
“Are u just thinking about yourself??”
Da sauri yace
“Of course not!.
Baby I’m also thinking about you
mana
ban san wanne kallo duniya za ta yi miki ba!sannan kema ba wai sauk’i za ki samu daga wajen su Daddy ba.
Kinga dama da ni da ke muna da bak’in jini a wajen Daddy idan ya ji wannan batun ban san mai zai yi mana ba.
Ke da kanki kince 1% kawai gareni
,na tabbatar idan Daddy ya ji wannan batu tou kashina ya bushe
Ni da shi babu taimako babu zaman lafiya daganan har abada
In that case
Yash will remain the king!…
Tayaya kike tunanin zan kula da ke da Baby idan hakan ya faru?
Kausar my company is n
ot that good sannan a wajen Daddy ma 1% gare ni,idan muka haihu
while not yet stable
ya kike so Babyn namu ya rayu??
I love you sannan nima inason Babyn nan amman
we need to make sure munada plan da better future d’in da za mu bashi kafin mu yanke s
hawarar kawosa duniya”.
Shiruu duk sukayi kafin chan Kausar tace”Yassir na san abunda zan yi but har yanzu bani da tabbacin ko ka yarda dani d’ari bisa d’ari…”
Ahankali yace”Kausar mun rufe maganar nan fa!na yarda da ke mana”
“Ka tabbatar?”
“
Na tabbatar“
Ya bata amsar yana kallonta
sannan ya d’aura da cewa
“Na fad’a miki na riga na yarda da ke Kausar,kawai dama inaso in yi confirming ne shiyasa na sake yi miki wachchar tambayr amman tun shigowata cikin d’akin nan da kika fara yi mini mag
anar farko tashi d’aya na yarda dake.Baki ga ban yi miki denying batun estate da cire taya ba?ko so kike in yi miki confessing??”
Ba tare da ya jira jin mai zata ce ba yace ‘’ok I did it’’
“If to say
ban yi trusting d’in ki ba kina tunanin zan fad’a
miki haka ne?”
Ahankali ta sauke ajiyar zuciya tana ji inama ta saita record a lokacin da yake confession d’innan da ta ajjiye as evidence d’in da za ta nuna ta tura sa prison bayan ya gama taimaka mata ta auri Yash…but with time inshaaAllah kafin ya ga
ma taimaka mata amfaninsa ya k’are a wajenta za ta san yadda za ta yi ta sanya shi ya k’ara confessing!”
Ahankali ta gyara zamanta ta fuskancesa sosai
tukunna ta fara magana
“Yassir
Inaso ka cire kishi
da negative thinking ka duba future d’inka
sannan Ina so ka san cewa ko ka yarda da wannan shawarar tawa da zan fad’i maka yanzu ko baka yarda ba ni dai ba zan tab’a zubar da cikin nan ba.
Akwai hanyar da za mu bi
mu haifi Babyn mu ya rayu cikin farin ciki…kuma hanyar ka sani itace silar warwa
rewar duk wani k’uncinka
amma we need to stick together sannan mu yarda da juna kafin komai”.
Jinjina kai yayi
alamun yana jinta kuma yana fahimta.
Ahankali ta sauk’e ajiyar zuciya tace”ka ce Daddy zai ji haushinka zai yi fushi da kai
watak’il f
orever idan har ya ji maganar cikin nan ko??”
Jin jina kai kawai yayi
“Good!
What if Yashjub ne a matsayinka??”
Da k’arfi yace
“What!!how??”
“Relax
I mean what if we frame him!.
Ka ga na farko
Ni kaina Daddy zai ji tausayi na
sannan
zai yi fushi da Yashjub
Above all
zai shirya da kai ya janyoka a jikin sa sanna idan Yashjub yana tunanin wannan Babyn sa ne
tsaf za mu yi amfani da hakan
mu samu abunda mukeso”
Shiruuu kawai Yassir ya yi ya dafe kansa kafin chan ya d’ago ya kal
leta tukunna yace
“Taya za ki yi hakan??
Taya hakan zai faru ??”
“Good
Bari kaji step one”
Ahankali ta matso ta zaiyyane masa komai…
Da farkon murmushi ya fara yi sai kuma ya mik’e tsaye yace
“Inaa! Kai!!!
no ba zai yiu ba.”
Mik’ewa ta yi
ta rik’e hannunsa cikin son fahimtar da shi tace
“Nothing will happen between us”
“Yeah I know,but just the fact that za ki kwanta waje d’aya da shi that too n**kd,inaa Kausar ki kawo wani plan d’in gaskiya banda wannan.”
Murmushi ta yi tace
“Ya
sir a lokacin da abun zai faru fa ba ma ya cikin haiyyacin sa
balle ma ya gane komai.
Kuma that’s the only way da za a kamashi red handed.
Kar ka bari kishi ya rufe maka ido mu kasa cimma burin mu.”
Shiruu ya yi kafin yace
Kausar,ta ya zan bay
ar da d’a na a wani?
Tunda idan fa kika haihu
kowa Yashjub zai ce shine uban Yaron..ta yaya zan yi claiming rights d’ina a matsayin Uba?”
“Yassir ko wanne family suna da nasu secret d’in let’s this be ours(da ni da kai)..
Ka duba ka ga fa sau biyu k
ana attempting kashe Yashjub amma hakan bai yiu ba kuma dukiya har yanzu tana hannunsa,a gani na don ka hak’ura wannan Yaron ya zama nasa na shekara d’aya ko months mun samu da dabara da sharri da abubuwa komai ya dawo hannunka,it’s normal ai…
A da kai ka
d’ai ne ka ke ta had’a plans d’inka kana failing yanzu kuwa zan taimaka maka na san za mu yi winning.
Idan Daddy ya ga Yash ya mutu ga kuma jaririn Yaro mara gado bani da tantamar tashi d’aya Daddy zai tartara komai ya saka a sunan Yaron kar ka manta yadd
a Daddy ya ke ji da Yashjub dan wani abu ya shiga tsakaninsu sun yi fad’a ya daina kulasa ba shi zai sanya ya k’i son d’ansa bayan mutuwar sa ba.
Ka fahimce ni Yassir wins ne da mu ta ko wanne angle a cikin plan d’innan fa…kaga Yaro dai yana hannu na ku
ma kai zan aura at last komai ya zama naka Yashjub ya tafi sannan Yaro kuma ya taso a hannnun iyayensa mu kula da shi mu haifi k’annensa ya taso cikin ahalinsa,mai ya fi wannan riba??”
Shiruu Yassir ya yi kafin yace
“but idan kuma ita wachchar matar ta
sa ta haihu kinga mun yi 2 zero ko?dan kowa d’anta zai kwallafawa rai na san.
Tunda by now he’s supposed to be dead ta yadda zan ga bayan cikin amma ya k’i mutuwa a yadda yake gadinta d’innan ni ko ke bamu isa zuwa ko kusa da ita ba ballantana mu yi wani
abun….
Murmushi Kausar ta yi kafin tace”don’t ask me Y and how,kawai inaso ka cire cikin Manubiya a lissafi dan wallahi ba ta isa ta haihu ba…kawai ka yi trusting d’ina when I say cikin nan ko one month bai isa ya k’ara a jikinta ba….”
Ajiyar zuciya
ya sauk’e kafin yace”I trust you Kausar.”
Murmushi ta yi tace”Thankyou..na san maganin da xa mu yiwa Yash amfani da shi zan rubuta
sunan sai mu je tare da ni da Yasmeen
amman ita kanta ba zan bari ta gane menene ba kawai zan
ce mata wanda ya ke sa
kani bacci ne akai mini recommending sabo.
Za ta nuna id card d’inta mu siyo maganin saboda ba za su
tab’a bani ba ni it’s super strong.”
Kallonta yayi sai kuma yace
“Da wuri haka?”
D’an zaro ido ta yi kafin tace
“Yassir tou sai yaushe?
Ai ba
wai yanzu yanzu ba but inaso komai ya zama ready
ta yadda Ina ganin opportunity komai zai kammala.
Manya manyan jajayen layukan da suka fito B’aro B’aro a kan tsinken
nan ya na nuni da cewa cikin nan ya kwana biyu a jikina
Idan ba da kyar ba ya fi
1 month.
Kuma kaga idan ma zan ce inada ciki sai fa kamar irin 2 weeks haka bayan incidence d’in…
Shiruu yayi kafin chan yace
“Okay kausar
duk yadda kika ce hakan za a yi”.
Murmushi ta yi kafin ta yi hugging d’insa tace “Thankyou Yassir.
T
hanks for trusting and understanding me”
A ranta kuma tace”Ashe ba ka da wayo…wannan plan A ne dole da kai za’ayi plan B kuwa ni kad’ai zan yi abuna dan ana tabbatar da cikin nan aure Yash ba zai zama abu mai wahala a gareni ba sai dai kawai ka ji a sal
ansa…
Ya zama dole nima in nemi farin cikina in tsayawa kaina kuma in yi protecting Yash daga sharrinka…….”
“Tabbas ya fahimci Kausar kuma ya yarda da plan d’in dan akwai nasarori a tattare da plan d’in…..sannan zaifi jin dad’i idan Yash ya mutu da tab
o da mugun suna.”
Yassir ya aiyyana hakan a cikin ransa yana mai sake saka saka ta a cikin jikinsa
Yashjub yana fita,d’akin ya rage daga Manubiya sai Yahanasu….a hankali Yahanasu ta mik’e ta k’araso inda take ta zauna a gefen gadon tukunna tac
e”me zan zuba miki??”
Zama Manu ta gyara ta ruk’o hannun Yahanasu kafin tace”Yaha Ina buk’atar taimakonki”
Shiruu Yahanasu ta yi ta d’an k’ura mata ido dan kamar ta fahimci mai za ta ce,kafin da kyar tace”anything! Manu..”
Ahankali Manubiya ta sauk’e
ajiyar zuciya kafin tace”lokacin da aka kwancewa Ya Yash tayar mota kin san shi da kansa ya san kashesa ake so a yi ko?”
Ba ta jira jin me za ta ce ba ta d’aura da cewa”wannan karon ma kinga abunda ya faru ko? amma na ga kamar ba ya so na sani shiyasa nim
a ban nuna masa na sani d’in ba saboda inaso in taimaka nima kuma na san ba zai barni ba…. Yaha ba zan zauna in zuba ido in nad’e hannu ana wasa da rayuwar Mijina ba….”
Hawayen da suka zobo mata ne ya sa Yahanasu ta matso ta shiga goge mata fuska kafin da
kyar ta samu ta iya cewa”yanzun ma haka kike suspecting ko!nima yanayin yadda na ga abun gaskiya dama na san hakan ne…”
Cikin jan hanci Manubiya ta zaiyyane mata abunda Yasira ta ji mutanen suna fad’a da suka shiga gidan k’awarta.
“Innalilla wa inna ila
ihirrajiun”
Yahanasu take ta maimaitawa,tana jin gabanta yana wani irin bugawa..
Addu’arta d’aya Allah ya sa babu hannun Mommy a lamarin nan dan tabbas itakam za ta taimakawa Manubiya za su tsaya tsayin daka har sai sun gano gaskiyar lamari an kuma hukun
ta mai laifin kashe mutanen nan,justice must be served!.
A nan a take suka fara shirye shirye kuma suka yi alk’awarin ba za su bari Yash ya sani ba dan sun san zai yi yunk’urin ya hana su especially ma ita Manu da a yanzu ba shi da wani burin da ya wu
ce ta yi ta hutawa kawai.
Dama Yahanasu tana da connections kasancewar lawyer dan haka tun a lokacin ta shiga making phone calls aka fara shirye shiryen first step……
Yashjub ma sai chan dare ya samu ya dawo….Yahanasu ta wuce gida shi kuma ya nema waj
e ya zauna ya ruk’o hannun Manubiya….bai so Manubiya ta sani ba gudun kar ya d’aga mata hankali amma kuma ya yiwa kansa alk’awarin ba zai sake b’oye mata komai ba tun lokacin da su Yasira suka kusan had’a masa bomb da zancen Kausar,dan haka ya shiga zayyan
e mata yadda duk abunda ya faru da binciken da suka fara tun a yau…successfully cctv ta yi capturing incidence d’in tun shigowar y’an ta’addan har fitarsu kuma mutane biyu ogannnin cikinsu babu mask a fuskokinsu sannan an shaida guda d’aya dama ana neman s
an dead or alive…dan haka yanzu step d’in da suka d’auka shine na kama wannan mutumin ta wajen sa ne kawai za a gane waye ya turosu a ji komai dan muddin suka kamasa kalar interrogation d’in da za su yi masa dole ma ya fad’i gaskiya…….
Shiruuu Manubiya
ta yi jikinta duk babu dad’i,kusan step d’in da ita da Yahanasu suka d’auka shi su Yash d’in suma suka d’auka amma su sun yi nisa dan su ko binciken cctv d’in ma ba su yi ba….kamar yadda ya ce ba ya so ya b’oye mata komai shiyasa itama ta fara k’ok’arin ga
ya masa shirinsu ita da Yahanasu amma sai ta ji yana cewa”dan Allah dan annabi ki kwantar da hankalinki,ba na son ki yi komai..if not because ba na son b’oye b’oye a tsakanin mu da ba zan gaya miki ba,dan haka dan Allah ki kwantar da hankalinki ki kular mu
n da ku..inshaaAllah all will be fine,ok?”
Ajiyar zuciya ta sauk’e,a take ta fasa gaya masa saboda har ga Allah tana son ta taimaka dan haka kawai ta jini jina kai a hankali ta yi huggin d’insa…
Ba dan Yash ne da kansa ba da babu abunda zai sa Doct
or ya bar Manubiya ta fita ba tare da ya sallameta ba…sai da ya sake dubata tukunna suka tafi dubo
Baba ita da Yashjub…
Had’add’en private hospital mai kyau da tsada Yash ya kai sa dan har ya ma fi na family Doctor d’insu da Manubiyan take kwance.
A harabar asibitin suka tarar da Jidda a tsaye ta kauda kai gefe da wani,sai da suka k’arasa tukunna suka fahimci ashe Ya Yusuf ne…
Da mutuntawa suka gaisa shi da Yash kafin ya kalli Manu itama ya gaida ita daga haka ya yi musu sallama ya tafi…
Yashjub n
e ya iya amsashi dan daga Manubiya har Jiddan babu wanda ya tanka masa, ita Jidda haushi da tsanar sa ne yasa tunda suka fito ba ta ce komai ba Manubiya kuwa tsantsar mamaki ne ya hanata yin magana dan ba ta yi expecting ganin Yusuf da Jidda a tare ba.
S
ai da Yashjub ya rakasu bakin k’ofar d’akin tukunna ya juya bayan yace “su shiga zai je ya d’an siyo abu idan ya dawo sai ya ga jikin Baban su wuce..”
Da “to”suka amsa shi daga haka ya wuce…ko gama fita daga corridor d’in bai yi ba Manubiya tace”Jidda me
kike yi da Yusuf a waje???”
Numfashi Jidda ta fesar kafin tace”Baba ne ya ce in rako sa…”
Kukan da ya taho mata ne ya sa ta yi shiru ta fara kokawar danne wa..cikin rashin jin dad’i da rashin fahimta Manubiya tace “Jidda ai da sai ku tsaya a nan da kika
fito ya wuce ke kuna ki juya meye naki na yi masa rakiya har chan waje?? Jidda Yusuf ne fa!!!”
Cikin sauk’e ajiyar zuciya tace”da ya zo ya gama dubiyar ya tashi tafiya shine ya kalle ni yace wai ‘ba rakiya!’
‘In zo in rakasa’! a gaban Baba da Inna tsab
ar ba shi da tarbiyya.Sai da ya fad’a sau uku tukunna Baba ya kalle ni yace”mu raka sa da ni da Muhsin amma muna fitowa ya cewa Muhsin d’in ya koma ni kuma ya kamo hannu na ya jani kamar wata kayan wanki saboda ya ga Ina shirin komawar,ko da muka fita da n
a fara k’ok’arin juyawa gani na yi yana shirin runguma ta shiyasa na tsaya kawai.
Tsabar rashin sanin darajar manya saboda Allah adda Manu ta ya Baba zai ce mu rakosa amma ya kora Muhsin.”
Cikin rashin Jin dad’i Manubiya tace”kuma wai a haka ace Baba b
a ya ganin laifin Yusuf??”
Ajiyar zuciya Jidda ta sauk’e kafin tace”yana gani fa! kawai kawar da kai yake yi wasu lokutan saboda gudun magana amma ni na san yana gani…ba ki da lafiya ne shiysa ban gaya miki abunda ya faru ba….kin san tunda ya yi kud’i b
a shi da Aboki sama da Kaka mallan to shekaran jiya Kaka mallan d’in ya nemi ganin ya Nafi’u da ya musbah,Ya musbah bai je ba sai ya Nafi’u,shine fa tsabar rainin wayo kaka mallan d’in yake ce masa wai ya fad’i ko nawa yake so su basa ya saka baki a yi au
rena da Ya Yusuf,wai duba da abunda yake ta faruwa a tsakanin Baba da su Baba habu ya san Baba maybe ya chanza ra’ayi dan haka Ya Nafi’u ya yi naming price ko nawa su bashi ya yi convincing Baba. Shi kuma kaka mallan zai tsayawa Ya Yusuf ko su Uncle ba su
yarda ba a d’aura.”
Cikin takaici Manubiya tace”kutt me ya ce masa shi kuma?”
“Kema kin san ai ya Nafi’u ba zai yarda ba…wane tudu wane gangare suka bi daga haka dai hayaniya ta fara tashi,shine fa akayi fad’a da ya Nafi’u da kaka mallan har da Uncle
a case d’in wanda da ga jin hayaniya ya afka parlourn ya yi ruwa ya yi tsaki.To dai daga k’arshe Baba ne ya je ya raba da kyar ta hanyar janye ya Nafi’un …shine fa cikin dare wajajen k’arfe d’aya kamar waenda aljanunsu suka tashi haka kurum Uncle ya zo ya
shigo har cikin d’aki wai Baba ya zab’a ko su ko ya Nafi’u,saboda ba zai you Yaro ya yi musu rashin mutunci ba kuma ya ci gaba da huld’a da shi yana shigo musu cikin gidan ba. Haka nan dai suka yi ta hayaniya wallahi kamar mata daga k’arshe Baba ya ja bar
go ya kwanta kawai ya rabu da su,shine suka yanke mana