Showing 60001 words to 63000 words out of 259716 words
tukunna ya mik’a masa hannu alamun su yi musabaha.
Ba tare da ya kallesa ko hannunsa ba ya cewa Jidda
“Wuce ki shiga gida!”
Kamar jira takey
i
kuwa hakanan ta wuce wuff
har tana d’an tuntub’e.
Bata san ya sukayi ba amman ko da ta je gaff da shiga gidan ta juyo ta tsinci Ya Musbah ne yana magana da Al’ameen d’in kuma daga gani ba maganar dad’i bace dan ran Ya Musbah a mugun b’ace yake yi
masa
maganar har yatsa taga yana nunawa Al’ameen d’in.
Tana shiga d’akin su ta fara nufa,ba kowa daga Inna sai Mama sai wata y’ar tsohuwa(iya ramma).Inna tana had’a y’an ragowar kayayyakin Manubiya da suka yi saura tana hawaye Mama tana zauna a gefe
nta suna rarrashinta ita da iya ramma.
Anan ta zauna ta shiga taya Inna suna yi suna hawaye duk su biyun sun k’i ma su ji rarrrashin da ake ta yi musu.
Jidda ba ta yi mintina uku da zama ba…suna gama zuge akwatin wayar Mama ta hau k’ara,cikin mutuwar j
iki ta k’arasa ta d’auki wayar a hankali ta kara a kunnenta dan duk su Inna sun gama kashe mata jiki…
“Subahanallah”
Suka ji Mama ta ambata kafin tace”ki yi hak’uri ki daina kuka gani nan zuwa.”
Tana ajjiye wayar Inna ta mik’e ta na share hawayenta k
afin ta shiga tambayar ta “mai ya faru?”
A gaggauce tace mata”Ammi ce ta kirani wai in zo mu kai Al’ameen asibiti yanzunna haka kurum yana shiga gida ya yanke jiki ya fad’i…dama ni tun da ya dawo wallahi na lura kamar ba shi da lafiya kullum wani iri n
ake ganin sa.”
Cikin rashin jin dad’i ta k’arasa ta rike hannun Inna kafin tace”ki yi hak’uri inna,na so in zauna na raka Manubiya d’akinta,amman Alhaji baya nan dole suna buk’atata!”
Da sauri Inna tace”kar ki damu ki je ba komai hakan ma wallahi na go
de kwarai Mama,Allah ya basa lafiya”
Ahankali ta jinjina kai tukunnan ta yi musu sallama ta wuce,sai da ta fita tukunna Inna ta lura da yadda Jidda ta cusa kanta a cikin cinyoyinta jikinta har wani irin vibration yake tana wani irin silent kuka kamar ra
nta zai fita,ajiyar zuciya ta sauk’e dan dama sai da ta saka haka a ranta daga jin bayanin Mama….a hankali ta k’arasa kusa da ita ta zauna
tukunna ta sa hannu ta d’ago fuskarta wadda ta yi dagaje dagaje da hawaye da gumi har ma da majina,sai da ta share ma
ta fuskartata tukunna ahankali sosai tace”kin had’u da shi ne yanzu?”
Cikin kuka Jidda take kallonta tana so ta yi magana amman sam sai ta gagara shiyasa kawai sai ta afka jikin Inna ta sake fashewa da wani Irin kuka abun tausayi.
Ajiyar zuciya wanna
n tsohuwar ta sauk’e kafin ta k’araso kusa da su ta ci gaba da lallashinsu dan ita ba ta ji abunda innar ta ce da Jiddan yanzu ba……Sun jima sosai matar tana lallashinsu kafin da kyar aka samu Jidda yi shiru ta shiga sauk’e ajiyar zuciya a jere a jere.
A
haka Siyama ta shigo ta same su itama idanunta sun yi jaa alamun ta taya Manubiya kuka,sai da ta k’arasa kusa da su ta zauna jikinta duk a sanyaye tukunna tace”Umma tace wai ace miki iyayen ango sun zo,a je a ce musu su shigo ne?
Dum!!
Haka duk su b
iyu suka ji k’irjin su ya buga.
A hankali Inna ta kalli Jidda tace mata”su je ita da Siyama su shiga da su parlourn su Siyaman. “
Ba su dad’e da fita ba itama suka fita ita da wannan Iya ramma wadda ta tilasta mata dole suka wuce parlourn su Siyama tare…
..
Su Jidda suna fita da Baba larai suka fara cin karo tsaye
a bakin motar Yassira tana zazzare ido tana k’arewa gidan kallo fuskar nan a yatsine.
“Ya salam”
Jidda ta ambata a cikin zuciyarta kafin ta d’auke kai
ta k’arasa wajen Yahanasu
wad
da ta gani suna fitowa daga mota itada wata,kusa da
motar Yahanasu motar Ummi ce itama su biyu dan haka Jidda ta d’an saki fuskarta….Su Ummi dama tun ranar farko ba su raina gidansu Manubiya ba,to haka yau suma k’awayensu da suka zo tare da su….. talaka
da mai kud’i duk Allah ne yake yinsu,kuma Ubangiji yana iya maida talaka mai kud’i cikin dare d’aya vis versa sannan
kowa da kalar tasa baiwar,kuma babu wanda yafi wani a wajen ubangiji sai wanda yafi bauta masa ya fi tsoronsa,shiyasa su kam basuga kuma
basuji komai ba,all that matters shine Yash yana son Matarshi kuma tana da tarbiyya hankali da nutsuwa.
Sab’anin su Yassira da hankalinsu ya sake tashi
ransu ya sake b’aci….”tabbas
dama a yadda Yash yake nuna halin ko in kula a garesu da Mommy kanta
!ta san cewa yanada matsala kuma bai san ciwon kansa ba amman bata tab’a sanin cewa shi mahaukaci bane sai yau.
Yanzu nan ya zo?ashe dama
akan wadda ta fito a wannan gidan Ya Yash ya ke abubuwan da yake yi da uban rawar k’afar da yake ta faman yi kamar
wanda zai auro y’ar gwal!?.
Sannan su kansu k’annenta ashe daga nan suka fito amman har suke da guts d’in wani ciccin magani a gabansu?ba laifin kowa bane laifin Yash ne da
ya had’asu da su..tabbas Yash ya janyo musu babban insult da abun kunya a rayuwa….
wallahi ko gidan su gwaggwo mai aikin su ya fi wannan kyan gani…….”
Yasira ta zaiyyane hakan a cikin ranta. Same thing suma su Ya’isha duk lissafin da suke yi kenan.
Yasmeen kam ji takeyi kamr ta fashe da kuka dan ba kad’an ba wannan insult ne,ta ya
Y
ash zai had’asu family da Irin waennan mutanen,what has
gotten into him?”cikin bawa kanta amsa tace”tabbas wannan aikin asiri ne babu tantama,amman za ta gane inda ta zo ne!……dan ba ta jin za su iya tolerating Yarinyar nan na 1 month ma wallahi,gwara da
Allah yasa ba su yi gaiyyata ba yau da sun kwashi abun kunya!.
Yassira bata iya fitowa a mota ba sai da ta kira Mommy a video call ta shiga nuna mata gidan.
Mommy ta san Yash ya wulak’antasu kuma ya k’ask’antar da su da shi kansa amman kuma ta d’an
ji dad’i dan a yadda Manubiya take bata da gatan nan tabbas ta tabbata k’aramin alhaki a hannunta,shiyasa har Kausar wadda take ta faman lallashi tun d’azu ta nuna wa video call d’in da Yassira takeyi sannan
ta sake tabbatar mata da cewa’ba su da wata ma
tsala dan Yarinyar da ta fito daga wannan gidan ba za ta zame
musu jidali ba InshaaAllah’.
Har waje Yassira ta fito tana video call d’in tana nunawa Mommy gidan da layin ba tare da damuwa ba wanda hakan ba k’aramin d’aurewa mutanen da suke kai kawo Ka
i ya yi ba,why!?for what reason za ta fito tana yin video d’in da kowa ya fahimci layin da gidan kawai take d’auka dan in da ace videos d’in d’aukar Amarya za ta yi ai kowa ya san
sai an shiga ciki tukunna ake farawa
besides yanayin yadda take yin video
d’in nata kana gani za ka san gidan kawai take d’auka ba komai ba. Waenda
suke kusa da ita sosai ne suka fahimci video call ne ragowar
kuwa sam ba su fahimta ba…..
Girgiza kai kawai Ummi ta yi ta fito da ga motar ta,kafin ta k’arasa inda su Yahana
su suke tsaye ita da su Jidda…
Da farko Siyama da taga abunda Yassira takeyi har za ta kula ta su yi,amman kawai sai ta basar da ita gudun kar su yi creating scene ta jawa Manubiya abun fad’a kuma tana juya wa suka had’a ido da Ya’isha,ta san idan ta biye
su to tsaf za a yi ta ba dad’i dan ta lura kamar yarinyar fad’a take nema da ita dan yanzun ma tana juyawa ta zabga mata harara shiyasa kawai ta rabu da su amman wallahi ba dan
yau ranar Manubiya bace da sai ta koya musu hankali gaba d’ayansu.
Kallo
n duk su biyun Ummi tayi kmr ta san me ke a cikin zuciyarsu tace”ku yi hak’uri,ku yi komai saboda yar uwarku,kar ku bari ayi abun fad’a a ranar aurenta ku danne
zuciyar ku kunji y’an albarka”
Murmushin k’arfin hali Jidda tayi dan ba k’adan ba itama zu
wa yanzu ta hau dan har wata dariya take jiyo su Yusran sunayi
Irin dariyar rainin hankali da k’ask’anci d’innan,a hankali tace”inshaaAllah Ummi”
Daga haka suka sake gaisawa suka gaida k’awayensu kafin su ce musu “bismillah”
Su Jidda a gaba su Ummin k
uka a baya haka suka nufi gidan.Dai dai su Siyama sunzo wucewa kenan Yusra tace”Am Yasmeen ni kam anya ba kejin kaji da tumaki aka mana kwatance ba kuwa?inaga
gara fa mu kira mu sake confirming….”
Wani irin tafarfasa zuciyar Siyama ta shiga yi,inda a
ce iyakar i su iskancin nasu ya tsaya to da dasauk’i amman kejin kaji da tumaki da Yusra ta ambata it means tana referring har da iyayen su kennan,shiyasa duk yadda Siyama ta yi alk’awari ta kuma so ta kyale su sam sai ta kasa,ta san tana juyawa za ta iya
kifa wa Yusra mari shiyasa still sai da ta kuma tausar zuciyarta tukunna ta juyo tace
“Group leader d’in ‘rashin sanin yakamata‘
kuna iya shigowa kuma idan kun so,ku d’auki Amarya
kamar yadda aka umarceku ku yi daga gida”
Tayi maganar tana kallon Baba
larai dan Babba bai fi Babba ba.
Tana gama fad’in haka ta wuce ciki.
Shiruu duk suka yi dan ba su yi
tunanin za ta kulasu ba
saboda sun lura kamar yaran sunada d’an tsoro,amman fa sun ji dad’in kulasun da ta yi hakan ya nuna ta ji zafin maganar ta
su kuma wallahi sai sun nuna mata ba su san ya kamatan ba kuwa!.
Yasmeen ce tace”mu je ciki mu d’auki Amaryar”daga haka duk suka yi ciki suma.
Sam Ummi ba ta so Siyama ta tanka musu ba dan ta san za su yi mata shirme ne a gaban dangi da y’an uwa,kama
r
ta san haka suka shirya d’in kuwa!….
Siyama ta yi zaton za su tanka mata amma sai ta ga ba su ce komai ba,kusan tare ma suka shiga parlourn nasu kafad’a da kafad’a ita da su Ya’isha ba wadda ta kalle ta a cikinsu.
Parlourn cike yake taff da mutan
e…dukda k’amshin turraren wutan da yake tashi tunda ga k’ofar gidan hakan bai hana su yatsine fuska ba
sannan suna tafiya kamr kar su taka k’asa sai kace masu tsallake kwata….Lace ne a jikin Yassira wanda a k’alla ya kai naira dubu d’ari hud’u,haka itam
a Ya’isha dan nata da na Yassira kala ce kawai ta bambanta na Yassira blue na Ya’isha kuma brown,mayafi 3D suka rufa a kansu y’an k’anana suka zagaye wuyan su da shi,
Yassira bubu ne a jikinta
Ya’isha kuwa fitted gown.
Iyaka zobuna da
awarwarayen go
ld d’in dake a hannayensu kad’ai sun isa su gigita mutum.
Su Yasmeen kuma super ce a jikinsu itada Yusra,su kam har d’auri suka yi suka rufa mayafansu a wuya,
amman suma dank’ara dank’aran gold d’in jikinsu hannu wuya kunne da y’an yatsu kad’ai abun ka
llo ne.
Yadira ce kawai mai material
d’inkin fitted gown amma
itama kana gani kasan yadin yaji kud’i,a kunneta kawai ta saka gold sai agogon ta na gold ko zobe ba ta saka ba ita.
Maganar gaskiya
kaff gurin kayansu ne ya haskaka ko Ina dan tun a
waje kafin su shigo babu mai kyallin su!kana shigowa layin in ka kalli kowa zaka ga su ne pronounce,ga wayoyin hannun su irin wadda ake yayi ta shekarar.Shiyasa suka zama abun kallo sannan
behaviour d’insu ya zama
kowa ya gani saboda idanun
kowa a ka
nsu yake….
Suna shiga parlourn wata mata tace”Allahu akbar!ga dangin ango!”
Dakyar Yassira ta d’anyi murmushi tace”na jini ma kuwa”
Ta yi maganar tana kallon Munirat wadda ta fito daga d’akin da Manubiya take ciki d’auke da kaskon turaren wuta a han
nunta”.
Murmushi Munirat d’in ta yi kafin tace mata”ina wuni,har kun iso?”
K’ura mata ido kawai ta d’an yi kafin ta d’auke kai ta maida dubanta ga matan da suke karkad’e kan kujeru duk sun rikice sun ga gwalagwalai da sutura,dan tashin mutane ma akay
i akan kujerun aka shiga karkad’e musu inda za su zauna.
Ba wani datti a wajen
amman dukda haka sai da matar da ta karkad’e wajen tace musu “bismillah” ya fi sau biyar tukunna dakyar Yassira ta d’an zauna ita da Yasmeen da Baba larai,su Yusra kuwa a tsa
ye suka tsaya akan kafet da takalman su!sam ba su damu da yadda suke tattaka abincin
da aka ci aka zuzzubar akan
kafet d’in yana mammannewa ba,wayoyin su kawai suke daddannawa.
Ita Yassira abunda yafi damunta shine kar ta je ta kwashi infection a ji
kin kujerun
dan har wani danshi danshi ta ji da ta d’an d’osana bombom d’inta ta zauna…jin yadda danshin yake sake ratsata ne yasa ta ga inaa!ba za ta iya ba!dan haka tashi d’aya ta mik’e ta zare d’an kwalinta dama a ka ta rufa mayafin shiyasa ta zaro sa
ta shimfid’e
akan kujerar tukunna ta koma ta zauna wanda hakan da ta yi sam bai yiwa rabin matan parlourn da suka san ciwon kansu dad’i ba.
Dariya k’asa k’asa Yasmeen ta yi wanda hakan ya sake k’ular da su Siyama waenda suka dawo daga d’aukowa su Um
mi fararen kujerun zama suka shigo yanzun.
Ba tare da sun kalli su Yasmeen d’in ba suka wuce suka ajjiye wa su Ummi kujerun fuskokinsu tamau.Suna ajjiyewa Ummi tace”Siyama ki barshi ba sai kun yi wahala ba ai,”
Murmushi kawai Siyama ta yi tace”ba koma
i Ummi,bismillah”
Dai dai nan Inna Iya ramma da Maman Siyama suka fito daga d’akin.
Su Inna basu damu ba suka zauna a chan gefen carpet yayinda su Yasira suka hahhatd’e k’afafu akan kujera, su Ummi ma inda su Innar suke suka k’arasa suka zazzauna aka shi
ga gaisawa cikin mutunta juna
ana introduction.
Yahanasu ce ta yi introducing tun daga kan Baba larai har izuwa kan Yadira,su kuma suka nuna Inna farar bafulatana mai k’aramin jiki kkyakkaywar gaske a matsayin mahaifiyar Manubiya
Maman Siyama kuma a ma
tsayin gwaggon ta.
Ummi ce tace musu”Ita Ummin sa ce step mom,Mahifiyarsa tana gida bata samu zuwa ba”.
Kamar jira Yasmeen take ta
tari numfashinta tace “Yeah!tanada allergy duba da yanayin arean nan ne yasa ba ta zo ba”.
Rabin matan ba su gane m
e take nufi bama sai y’an kad’an
ne suka fahimceta.
Shiruu Ummi tayi haka ma kowa kafin Yahanasu ta d’anyi murmushi ta kawo k’arshen shirun ta hanyar cewa”ko za’a
fito mana da Amaryar mu wuce!na ga magariba har ta gabato”
Sai a sannan maman Siyama
tace”da ikon Allah,bari in je in kawo muku ita”
daga haka suke mik’e su biyu ita da Iya ramma
sannan sukace Ummi ta biyo su.
Idan ka kalli Baba larai
kai kanka Babba sai ta baka tsoro,ta had’e rai ta yi tamau da fuska ta kumbura.A nata lissafi
n wai tsabar an rainasu ko including d’insu ma ba a yi itada su Yassira!su Ummi da Yahanasu kawai suke komai sam su ba a d’aukesu da mahimmanci ba,ga kuma takaici da tsanar Manubiya da ahalinta baki d’aya,ga shi ba su samu sunyi abunda suka yi niyya d’azu
za su yi a gidan Amaryar ba..Shiyasa gaba d’aya ranta ya b’aci ta kumbura ta yi suntum!tana mai jin kamar ta d’aura hannu aka ta yi ya zabga uban ihu….
Ba a yi mintuna shida ba suka fito da Manubiya sanye cikin fara k’al d’in alkayabba sai
kyalli da
tashin k’amshi takeyi.
A gefen Ummi suka ajjiyeta,tana zama Ummi ta rungomo ta izuwa jikinta sannan tace”Allah ya yi miki albarka,Allah ya sa ki zame mana sanyin idaniya”
“Ameen” gaba d’aya kowa ya ce ana raha daga nan aka bawa Ummi amanar ta,suka k
arb’a hannu bibbiyu ita da
Yahanasu,aka yi addu’a aka shafa kafin a fara shirin mik’ewa…..Yassira ce tace
“Yauwa Inada magana
saboda akwai al’adar da muka saba da ita mu y’an gidan mu!”
Runtse ido Yahanasu ta yi
kafin ta kalle Yassirar tace
“Yassira inaga gara mu wuce kawai,yamma ta yi”
Murmushin rainin hankali Yasirar ta yi mata kafin tace
“Nop!It won’t take long.”
Sannan ta kalli Inna tace”and first of all inaga ya kamata in d’an yi muku clarifying wani abu”
ta yi maganar idanunta c
ikin idon Inna kafin ta ci gaba da cewa “Ita wannan wadda kika bata amanar y’ar ki!
Matar Baban mu ce,itama
kamar uwa take a wajen mu
amman ba ta san cikakkiyar A’adar gidanmu ba dan ko
shekara d’aya ba ta yi a gidan ba.
Wannan itace yayar mahaifiy
armu wadda aka turo ta wakilceta”ta yi maganar tana nuna Baba larai kafin ta ci gaba da cewa”Actually!,
a al’adar mu!’mu da muka zo d’aukar amarya,to tun daga kan Baba larai har izuwa kan Yadira dole ne sai Manubiya ta bi mu one by one ta durk’usa a gaba
n mu sannan ta gaishe mu a matsayinmu na dangin mijin ta,daga nan ne idan mun ga muna so za mu karb’e ta mu yarda da ita tukunna mu d’auke ta mu tafi da ita’.”
Cikin tarar numfashinta Ummi tace “Yassira wanne irin shirme ne wannan???”
Da d’an murmush
i kwance a kan fuskar Yasmeen tace
‘’Ai gaskiya ce Ummi,kuma
ai ba abun zafi bane
kamar wasa ne hakan game ne
you just watch…it will be fun.”
Ta k’arashe maganar tana