Showing 180001 words to 183000 words out of 259716 words

Chapter 61 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

60

a kan kujerar yana jin kansa yana wani irin juyawa,dan Yahansu tana fara maganar ya ji komai ya dawo masa sabo ciwon da zafin da zuciya da kwakwalwarsa suk

eyi sun sake hauhawa.

Cikin rashin jin dad’i sannan a hankali Najeeb yace”and you believed him?”

Ya yi maganar yana kallon Yashjub.

Cikin tarar numfashinsa Yash ya kallesa yace”Nima ban sani ba!iyaka abunda zan iya fad’a kenan ‘nima ban sani ba’!”

“Ka yarda kenan!ka yarda mana idan ba haka ba da baza ka shiga wannan halin ba!da ba za ka k’i zuwa inda take ba Yash wallahi ka bani mamaki.”

Cewar Yaha.

Kallonta ya yi zuciyarsa tana wani Irin tafarfasa yace”kin san me na gani?kin san me na ji?”

“Sai ka fad’a!”

Ta bashi amsa cikin takaici…

Tiryan tiryan ya shiga zaiyyano musu yadda suka yi da Abbakar a yau kafin ya je asibiti…..

Cizan labb’a Najeeb ya yi bai jira ya kai aya ba ya katsesa ta hanyar cewa”Tabbas Yash ba don na san gigin giyar

kishi ce take d’awainiya da kai ba wallahi da sai na rufe ka da duka!

Bari ka ji abunda ba ka sani a kan Abbakar ba…za ka iya tuna ranar da ka zo ka same ni akan mu je gidan su Manu kanason magana da ita urgent muka kira Abbakar ya yi mana kwatance,bayan

y’an mintuna ya kira yace sun tafi k’auye?”

Bai jira jira jin me zai ce ba yace”to k’arya yake yi dan a ranar ma sai da Manubiya ta yi exams kuma ai kaga abunda ya faru next na case d’in black snake wanda hakan yake sake nuni da bbu inda taje tana cikin g

arin amma ya yi mana k’arya saboda son ta yake yi mata sam ba ya so ka rab’eta!.

A ranar da na bashi katin ka na yi masa bayani nace ya bata tun daga ranar na fahimci son ta yake yi ban gaya maka ba saboda gudun irin wannan abun da ka aikata da zargi a ts

akaninku Ashe na yi ta banza tunda gashi Yaro k’arami ya juya maka lissafi!

Saboda ita fa ya nemi transfer dan tunda aka fara maganar aurenku ya gudu aashe kwanciyar kura yayi ya je ya yi sabon shiri ya dawo da niyyar tarwatsa ku!.

A gaskiya Yash ka bani

kunya dan ban yi tunanin za ka yarda da …..”

Cikin tarar numfashinsa Yashjub yace”Najeeb I saw there chat!”

Kamar Yahanasu za ta rufe sa da duka tace”kuma sai ka yarda ita ta yi?”

“To wa ya yi? Wayarta ce kuma number ta na gani da dp da komai nata

ga chats nan na gani waye ya yi idan ba ita ba?besides not just chats,na ji ta tana waya da shi tana cewa,sai da na fita tukunna ta samu damar yin wayar….da asubah! Sannan kusan kullum yana kiranta ina gani ba ta d’auka a gabana…”

A hankali Najeeb yace”

me ka gani a chats d’in?”

Sai da ya share hawaye tukunna yace”Najeeb shiyasa tun farko da ka tambayeni na ce muku ban yarda ba!saboda i can’t believe wai Manubiya zata yarda ta yi maganata da shi sannan har ya yi mata prescribing maganin da za ta sha ya

zubar mata da ciki na da ke a jikinta.”

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”

Najeeb da Yahansu suka ce a tare kafin Yahanasu ta matso ta zauna a gefen sa ta kamo hannayensa tace”Yash look at me!”

Sai da ya juyo ya kalleta tukunna tace” da ka ji Manu

tana waya da asubah ba da kowa take waya ba da ni ce!”

Da mamaki ya kalleta wanda hakan ya sa ta jinjina masa kai tace “tabbas…na yi wa Manubiya alk’awarin ba zan fad’a maka ba amma yanzu kam ya zama dole in fad’a maka….”

Tiryan tiryan ta zaiyyano musu

komai game da yadda Manu tace mata ta taimaka mata suma su yi participating a case d’in estate d’insa,ba za ta nad’e hannu ta zuba ido ana wasa da rayuwar mijinta ba! Da binciken da suke yi akan case d’in da kud’ad’en da Manu ta bayar duk dan a yi bincike

duk sai da ta gaya musu komai ba ta b’oye ba tukunna ta d’aura da cewa”wallahi ka godewa Allah Yash dan samun mata irin Manu ba kowa ba Manu mace ce tam kar dubu!Allah ya zab’e ka kar ka yi masa butulci.

Maganar chats da shan magani kuma ni na san aikin

su waye amma ba zan fad’a maka ba saboda wani dalilinawa kawai Ina so ka tsananta bincike a kai ka duba cctv ai akwai a gidan ka ka yi bincike sosai ta nan ne za ka gano waye ya d’auki wayarta,waye yake saka magani a abunshanta ko cin ta duk za ka gani.”

Ahankali Najeeb ma ya zauna a gefe suka saka shi a tsakiya yace”Yash shaid’an ya tsani ya ga ana zaman lafiya an yi aure ana soyayya tsakani da Allah,nan za ka ga ya fara saka zargi da abubuwa a zuk’atan maaurata,bayan Abbakar da sharrin zubar da ciki da

chats Yash akwai shed’an dan Allah ka daure ka yi trusting matar ka duk rintsi! ba fa a aure da zargi babu kyau ka daina dan Allah kar ka sake wannan tab’argazar shi kuma Abbakar ka bar ni da shi sai na ci uwarsa wallahi zai san Ina ya zo”.

“I don’t thi

nk he’s still alive dan dukan da ni yi masa ba lalle ya rayu ba”

Ajiyar zuciya Najeeb ya sauk’e kafin yace”mu yi addu’ar ya rayun dai”

“InshaaAllah ya mutu”

Yash ya fad’a cikin d’aci yana jin tsanar Abbakar tana sake taso masa.

A hankali Yahanasu tac

e”ai yanada magoya baya shi kad’ai ba zai iya aikata wannan b’arnar ba…..”

Shiruu duk suka yi Hatta Najeeb shima zuciyarsa sisters d’in Yash d’in ta zarga tunda it’s obvious ba sa sonta,amma kuwa da sun cika dabbobi dan in har za su iya kashe d’an wansu

to kuwa abun nasu Azimun ne!ya godewa Allah da ya rabu da Ya’isha bai aureta ba…….

A b’abgaren Yash ma yadda Yahanasu ta yi masa bayani da komai ba bu wasu waenda suka zo kansa sai su Yasira tunda tare suke da su a cikin gidan,sai dai kuma no matter wh

at so yake ya maida zarginsa akan gwaggwo saboda yanzu haka a cikin tashin hankalin binciken estate d’insa yake yana jin tsoron sakamokon shiyasa yake addu’a Allah yasa idan ya yi binciken ya gano gwaggwo ce kawai ba y’an uwansa uwa d’aya uba d’aya ba.!…

Yahansu ce ta ce”Manu da sunan ka ta yi barci a bakinta…ka tashi ka j….”

Tun kafin ta rufe bakinta yace”Bara in je in ganta…..”

Murmushi duk suka yi cikin tsananin jin dad’i suka mik’e Najeeb yace”na san ba zaka fad’awa kowa ba but pls Yash misundersta

nding d’innan da kuka samu da abunda Doctor yace inaso ya tsaya a iyaka mu uku!sannu kamar yadda yaha tace ka yi bincike,Allah ya sa mu dace.”

Jinjina kai Yashjub ya yi yana jin wani sanyi yana lullub’esa kafin yace musu”thanks,alot”a hankali.

Murmushi

duk sukayi suka ce ya dage da addu’a ya cire komai a ransa daga haka suka wuce shi kuma ya hau sama domin ya d’auko makullin motarsa……

Har wannan lokacin Ya’isha tana tsaye tana jiran Najeeb.

Sallama ya yi da Yahanasu ta wuce shi kuma ya d’auke kai ya

yi kamar bai ganta ba ya had’e rai ya nufi motarsa da sauri wanda hakan ya sanya itama ta nufosa da sauri amma kafin ta k’arasa tuni ya shige ya bata wuta ya yi reverse an wangale masa gate ya fice da mugun gudu.

K’amewa kawai ta yi a wajen ta kasa mots

i kafin da kyar ta ja k’afafuwanta ta wuce garden tun kafin ta gama shiga ta fashe da wani irin kuka.

Junior kam yau ya samu fuska a wajen Yadira ba laifi dan suna shiga Yusra ta wuce sama su kuma suka zauna a main parlourn…gaba d’aya jikinta ya yi sany

i shiysa ya sameta yau ta d’an sake da shi wanda murna da farin cikin sa sam suka gagara b’oyuwa.A rayuwarsa yana mutuwar son Yadira so ba na wasa ba,Allah ya jarabcesa da masifaffiyar k’aunarta.

Ummi tana zuwa za ta d’aura girki ta tarar gwaggwo har ta

kusan kammalawa dan haka ta sa hannu ita da Munirat suka yi na duka gidan suka gama daga haka suka wuce asibiti suka je suka kai musu bayan ta had’a na Yash a daban daban ta ajjiye.

Babu yadda ba ta yi da Hajiya Mama ta hak’ura ta koma gida ba tunda ga

Siyama amma tace”ba komai za ta kwana da Manubiya da safe sa chanjeta.”

Yashjub yana hawa sama aka fara kiran sallar Magrib,dan haka ya ce bari ya kama ruwa ya yi alwallah kafin ya wuce.Zuciyarsa ta yi sanyi zuwa yanzu amma ciwon da kansa yake yi ba k

ad’an bane ba,yana buk’atar ya sha magaani

Amma a yadda yake jiri a yanzun ya san idan ya sha babu komai a cikinsa wahala zai sha gashi a side d’in babu cima tunda ba zama ake yi a ciki ba kuma ba zai iya tsayawa cin abinci ba ya san zai d’auki lokaci, da

n haka ya kira gwaggwo a waya yace”ta had’o masa coffe dan Allah yanzu da sauri zai sha ya sha magani da shi kafin ya wuce sallah.”

Lokacin da ya kira ta tana shirin kawo masa abunci dan haka ta ce “to shikenan”.

Daga haka ta katse ta ajjiye basket d’in

ta shiga had’a masa coffee d’in.

Kausar tana kitchen d’in a wannan lokacin dama tana tunanin ta yadda za ta aiki gwaggo ta samu ta ajjiye basket d’in Yash ta juye abinda ta k’unso a cikin abuncin nasa a kai ta ji ya kira ta.Ba k’aramin dad’i ta ji ba da t

a ga gwaggo ta fara had’a coffe saboda dama ta riga ta yi

diluting abun kuma ta san idan ta zuba akan farar shinkafa ko miyar agusin da suka yi zai gane,coffee d’in will be perfect wajen yi mata sauk’in juyewa……

Yana fitowa daga band’akin ya chan

za kaya zuwa jallabiya ya d’auki wayoyinsa ya kunna,sai da ya gwada layin Manu akace masa tana barci tukunna ya zuba a aljihu ya d’au makullin mota ya nufi k’asa dai dai gwaggo tana shigowa da basket.

“Yauwa sannu gwaggo iyaka coffee d’in kawai za ki zuba

mini,ya fad’i hakan yana mai sauk’owa daga stairs d’in a gurguje.”

Itama da hanzari ta shiga zuba masa kafin ya k’araso cikin parlourn har ta gama zubawa.

Sai da ya nemi guri ya zauna tukunna ya karb’a yace “sannu gwaggo”

Daganan ya fara k’ok’arin ka

iwa Baki.

Gani yayi ta tsaya tana kallonsa dan haka ya ajjiye cup d’in ya zuba mata dogayen idanuwansa kafin yace

“Lafiya dai ko gwaggwo?

Akwai matsala ne!?”

Da sauri ta yi firgigit kafin tace”laa a’a ba komai”sai kuma ta juya ta fice ranta duk ba

dad’i…ba ta so ta taso da case kuma a zo a yi bincike

aga ba komai ta shiga masifa

amman haka kawai

ta ji ba ta yadda da Kausar ba!

Ta gama had’a coffee d’in kenan Kausar d’in ta ce mata”ta je sama ta d’auko mata wayarta a sama a parlournta”

Ta

so ta lab’e amma sai ta yi gaba kawai but da ta dawo

tabbas taga kmr an tab’a flas d’in

Although ba ta ga Kausar ta zuba wani abun ba cake ma ta tarar da ita tana ci dan lokacin da ta dawo sai da ta d’an lab’e,amma kwata kwata

ita dai bata yarda da co

ffee d’inba kuma abunda ya sake saka mata zargin Kausar d’in yadda ta dinga cewa ta d’auka “ta kai masa” “ta d’auka ta kai masa”bayan ta dawo d’in.

Gashi ta ga ta ci uban kwalliya

dukda doguwar rigar abaya mai bottons ce a jikinta amma ta fahimci kamar

k’ananan kaya ne ata ciki saboda har cinyarta sai da ta hango a waje

d’azun data zauna tana cin cake sannan ta gyara gashinta

ta sha jambaki

ga uban k’amshi………

Sannan har waje ta biyota

sai da ta ga ta shigo nan tukunna ta tsaya a wajen ta

fara

wasa da flowers tana sinsinawa kmr irin dama abunda ta fito yi kenan……..

Yadda Yashjub ya ga gwaggon ta yi ne yasa yad’anji a jikinshi watak’il akwai abunda take so ya gaya masa amma tana jin tsoro…tashi d’aya lissafinsa ya basa ko dai akan case d

’in Manu ne tunda ai tare suke a gidan har da ita shi fita yake yi dan haka dole ita ta ga wani abun…..ko kuma maybe taana so ta yi masa basaja ta kare kanta ne.!

Yana wannan tunanin yana sipping coffee d’in ahankali ahankali kafin ya d’auki maganin ciwon

kai daga aljihun sa ya b’alle ya sha ya d’an had’a da cake kad’an daga haka yayi gyatsa yai hamdala ya fara k’ok’arin mik’ewa dan ya ji har an shiga sallah.

Yana mikewa ya ji kansa ya wani irin sarawa wanda har sai da hakan ya kaishi ga kaiwa k’asa ya

durk’usa a nan bakin kujerar.

Jiri ya farayi had’e da wani yanayi na daban da ya shiga tashi d’aya abun har abun tsoro!

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”ya shiga maimaitawa dan tashi d’aya gaban sa ya fara fad’uwa saboda zai iya cewa bai tab’a tsintar

kansa a irin haka tashi d’aya ba!

“Ya subahanaAllah

Ya furta a fili… ga Manu a asibiti a ransa yace”da na sani ban sha ruwan zafin nan ba na san duk shine sila

amman kuma tou jirin na menene??”

Ya yiwa kansa tambayar ba tare da ya san me bashi ams

a ba.

Ganin abun fa gaba yakeyi

yasanya yayi sauri ya lalubo makullin motarsa….ya san Manubiya ba ta da lafiya but yana buk’atar kasancewa tare da ita ta hakan ne kad’ai zai iya tseratar da kansa daga fad’awa halaka….saboda this thing da ya ke ji is d

angerous.

Dukda bayajin zai iya yin tuk’i

a halin da yake ciki ga kuma

jiri amma gara ya gwada…kar ya je ya yi abunda zai binne kan shi da ransa.

Da k’arfi ya mik’e tsaye…dan zuwa yanzu ya fara ganin dishi dishi.

Yana mik’ewa ya ji an fara knoc

king…Addua ya fara yi akan Allah ya sa ba gwaggwo bace ta dawo dan ba gwaggwo ba ko Iya ce

Indai mace ce to fa akwai matsala muddin suka kasance waje d’aya a tashin hankalin nan da bala’in da yake a ciki.

Jin bai yi magana ba ya sa Kausar ta shigo a h

ankali ta mayar da k’ofar ta d’an tura ta

barta a bude ba tare da ta saka key ba.

Da farko dishi dishi ya fara ganinta sai da ta matso daff da shi tukunna ya fahimci ashe Kausar ce….tunda yake a rayuwarsa Kausar bata tab’a burgesa irin na yau ba…san

ye

take da wata arniyar gown ta roba iya guiwa

Fitted

Red

ga stones a jiki sai walwali sukeyi,ta rambad’a jan jambaki

tasha kwalli!gashi ta gyara gashinta ta yi parking ta yi styling gaban da jel jelar

kuma tana reto a tsakiyar bayanta ga wani

uban k’amshi da take zubawa.

Dakyar ya iya cewa”Kausar.”

Lumsassun idanunsa suna sake lumshewa.

Wata sabuwar k’aunarsa ce ta lullub’e Kausar a take a hankali ta matso ta sa hannunta a daidai saitin zuciyarsa tana shafawa kafin tace”Dukda kai da Daddy

kunce a baka space amma na kasa yin hakan Ya Yash,i‘ve to come see you!(check on you),situation d’in da na ganka ya kasa barin brain d’ina.”

Ta k’arashe maganar cikin wata shuumar murya

sannan cikin shagwab’a da turo Baki kafin a hankali ta d’an matso j

ikinsa.

Karkarwa jikinsa ya fara yi dan haka ya tureta da dukkannin ragowar k’arfin da yake a jikin sa,cikin fushi yace mata

“Stay away!!!”

Ya daka mata tsawa.

Daga nan ya fara takawa

da niyyar fita amma sai k’ofofin suka juye masa,parlourn ma g

aba d’aya

ya fara juyawa a kwakwalwarsa…ya ma kasa gane wacce ce k’ofar fita!.

Dasauri ta sake zagayowa

ta tsaya a gabansa tace”me ya sameka?In kira doctor ne?”

Tunani yayi tabbas idan doctor ya zo maybe ya bashi magani

dan zuwa yanzu ya san ba

zai iya driving zuwa inda Manubiya take ba dan haka da sauri yace

“Yes pls ki kira harda Yasmeen”.ya fad’i hakan a hankali.

Dan sake matsowa jikinsa ta yi tace”Okay mu je in kaika

Bedroom sai in kirasa”

Daga haka ta matso sosai

batayi wata wata

ba ta yi hugging d’insa.

Wasu tagwayen ajiyar zuciya ta ji yana sauk’ewa a jere jere kafin ya d’ago hannuwansa

gaba d’aya biyun ya rungume ta da dukkannin ragowar k’arfin sa.

Wani farin ciki ne ya lullub’e Kausar tashi d’aya hawaye suka fara ambal

iya a fuskarta

tsabar farin ciki…a hankali ba don ta na so ba tace”Let me go

In kira doctor pls Ya Yashhh”

Ta fad’i maganar cikin sigar da ta sanya Yash ya sake rungumeta tsam a jikinsa…..

Shi dai daganan jin sa ganinsa da komai nasa suka d’auke

D’iff!!!

Ba shi ya farkaba sai……

Daddy ya yi tunanin zai ga Yashjub a masallaci amman shiru..

Dukdda ya san yana cikin damuwa amma ya kamata ace ya je Masjid ai….

Akwai maganganun da yake so su yi ya d’an kwantar masa da hankali tun d’azun amma

sai ya hak’ura ya bari akan idan sun had’u a dinner sai su yi dan ya san maybe sai ya huta ya yi dinner tukunna zai wuce asibitin.

Shiruuu nan ma har aka fara dinner babu Yash babu alamun shi kuma wani abun mamakin babu Kausar.

Tunani ya yi ko dai ya

wuce gidansa sai kuma ya tuna ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login