Showing 66001 words to 69000 words out of 259716 words
mata ne yasa ta had’iye maganar ta ta kasa ci gaba da cewa komai.
Aha
nkali Mommy tace
“Dan girman Allah ki yi min uzuri akan case d’in Yahansu Larai,ko me za ta yi kiyi min alk’awarin za ki tsaya akai mu gyara b’arnar da ta yi kawai
dan abunda kike tunani bazan iya sake bada goyon baya akai ba…na ga illar hakan!.
A gani
na Yahanasu k’aramin alhaki ce a halin yanzu da ke kanki kin san idan ba mu tsayawa kanmu ba komai mai iya faruwa ne,dan haka mu ajjiye batun Yahanasu a gefe mu yi focusing akan abunda yake most important.”
Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk’e kafin ta mi
ke tsaye
tukunna ahankali tace “inshaaAllah,as u say…sai da safe.”………
…..
Motar Najeeb ce ta k’arshe
shiyasa basu samu damar yin parking a cikin gidan ba,sai
a waje a bakin titi.
Yana sane ya k’i bud’e side d’in Siyama,ita kanta ta fahimci shine
ya k’i bud’e mata dan tare suka fara kokawar bud’ewa ita da su Jidda
amman duk na su ya bud’u nata kuma shiru.
Ganin tana ta bawa kanta wahala ne ya sa ta hak’ura
da niyyar Jidda na fita itama za ta bi bayanta ta fice.
Munira ce ta fara fita
Tace”
mun gode”
Da murmushi ya amsata dan ba k’aramin farin ciki yake ciki ba dramar Siyama burgesa takeyi yadda ta had’e rai ta chuno baki abun ba k’aramin dad’i yake yi masa ba.
Jidda tana da sauk’e k’afafunta k’asa ta juyo ahankali cikin nutsuwar ta tace
masa”Mun gode”daga haka ta sauk’a a motar.Ganin Siyama har ta matso tsakiya yasa ya yi
sauri ya juya ya sa hannun sa ya janyo murfin motar yana me cewa “Ba komai Jidda”
Yana dariya k’asa k’asa yana kallon Siyaman,bayan ya tabbatar ya sake saka lock a
duk k’ofofin.
B’ata rai ta yi sosai kafin tace”
Zan fita”.
Murmushi ya yi tukunna yace
“Ashe Inada aiki a gabana sosai ni ban saniba,dan handling mace mai kishi
Is not an easy task!”.
Da sauri ta d’ago ta kallesa
sai kuma ta kau da kanta kawai
.
Ganin tak’i cewa komai ne yasa yace “Amman naki yayi tsauri sosai,ya yi yawa pls a d’an rage,atleast a bani chance inyi explaining kaina”.
Cikin tarar numfashinsa tace
“Ni fa ba kishi nake yi ba besides i just knew you,yau kad’ai fa na sanka ta ya za
n yi
kishi??infact ba wani abu a tsakanin mu!,kuma na riga na sani
Ya’isha girlfrnd d’inka ce
Ita zaka aura kowa ya sani…bai
shafe ni ba sannan It’s fine
dan kayi hugging d’inta saboda ba hurumina bane
tsakanin ku ne ku da ubangijinnku,so pls d
an Allah ka daina cewa ina kishi saboda babu komai tsakanina da kai sai mutuncin da muka yi a iyaka yau!
Ba ruwana da relationship d’inka Kai da Ya’isha!
Bud’e min k’ofa in fita
Pls.”
Ta fad’i hakan tana mai sake matsawa kusa da jikin k’ofar dan ta s
amu ya d’auke hannunsa yanzu.
Ya d’an ji zafin yadda ta ce”ba ta kishinsa amman sai ya kawar yace
“Okay!In yi miki tambaya guda d’aya zaki amsamin?”
Kamar ba za ta ce wani abun ba sai kuma ta d’aga masa kanta alamun ‘yes’
ba tare da ta kalleshi ba.
Sai da ya sake juyowa ya fuskanceta sosai kafin yace
“D’azu,you were nice to me,amman tunda kika ganni da Ya isha ki kalleni ma aiki ne a wajenki kuma it’s obvious haushina kike ji,ta ya zaki yi min explaining hakan ba a matsayin kishi ba?.”
This t
ime around murmushi ya ga ta d’an yi…tabbas idan ba ta yi da gaske ba to mutumin nan ba barinta zai yi ba and there is something about him wanda ta san idan har ba ta yak’i ta fatattaki tunanin sa da shi kansa daga rayuwarta ba
tou tabbas akwai matsala…
kar ta je ta jangwalowa kanta abunda ba za ta iya ba dan haka ta d’ago ta kallesa kafin tace”Bana kishinka!like I just said ban ma sanka ba ballantana har in shak’u da kai
wanda shak’uwa ce za ta janyo abunda zai sanya in yi kishin naka,kawai dalilin da y
a sanya ka ga Ina avoiding d’inka shine har ga Allah I’m sorry to say sam ba na shiri da Abota ko kirki ba na yadda in yi da Namiji irinka.”
Shiruu ya d’an yi kafin yace “Namiji irina?,menene ni d’in??”.
Itan ma sai da ta d’an yi shiru tukunna tace”Mas
u double dating!waenda a fuskar duniya ake yi musu kallon mayaudara!”.
Kamar zai fashe da kuka yace
“Siyama ni ba mayaudari bane ba,can you pls allow me to explain myself…”
Cikin katsesa kanta tsaye tace”a yadda ka karb’i number na da kuma yadda ka
ke treating d’ina throughout today,da ni da kai duk munsan inda zancenka zai sauk’a,bayan kuma ka riga ka san kana da wadda za ka aura
wadda kake so itama take sonka.Menene hakan kake shirin yi min idan ba yaudara ba?
Ko mata biyu zaka aura a lokaci
daya?besides na san ma itan zaka aura tunda itace type d’inka ni kawai a side kake da shirin ajjiyeni ka b’ata min lokaci”
Da sauri ya ce “in dan za a bani zab’i ke zan zab’a ke kad’ai!”
Da sauri ta d’aga masa hannu tace “Plss…dan Allah,banaso in ci g
aba da gaya maka maganganu masu zafi
saboda despite abunda kayi
min still Ina respecting d’inka,na cire kunya na cire komai na gaya maka abunda yake raina da abunda na fahimta a kanka
which is the thruth
therefore dan Allah inaso ka fita hanya ta kw
ata kwata.
Bana son case da su Ya’isha
bawai tsoron ta nakeji ba amman duk inda nakai ga iya fad’a bazan iya had’a kaina fad’a da mutanen da basusan darajar d’an Adam daidai da kwayar zarra ba.
So pls
For the last time
Ka fita a hanya ta
sannan
ka bud’e min k’ofa in fita.”
Shiruu kawai ya yi ya tsura mata ido…bai ma san me zai ce ba bai san ta Ina zai fara fita a hanyar tata ba,shi da yake son shiga cikin rayuwarta tashi d’aya tace masa ya fita a harkarta ma gaba d’aya which is the last thing
da zai iya yi arayuwarsa,dan shi kansa ya san ba zai iya rabuwa da ita ba he’s sure of that,ba ta san yadda ya dinga fama da soyayyar ta sama da wata uku ba,ba zai iya yi mata alk’awarin fita a harkarta ko rabuwa da ita ba dan ya san ko ya yi alk’awarin to
ba za ya cika ba.
Ahankali cikin son ta fahimce sa yace “Siyama ba zan iya rabuwa da ke ba,ki yi hak’uri ki fahimce ni ki bani chance ba zan tab’a yaudararki ko in cutar da ke ta ko wacce hanya ba,I promise!”
Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace “me y
e tsakanin ka da ita
Ya’isha?just the truth!
dan Allah”
Sai da ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna yace
“She s my girlfriend”.
Yadda kalmar
‘She’s my girlfriend’
ta daki k’irjin ta
Ita kanta sai da ta yi mamaki.
Da kyar ta iya cewa “kuma h
ar yanzu kuna tare ko?”
Still sai da ya d’an runtse idanunsa na y’an sakanni
tukunna ya bud’e yace
“Yea!but Siyama wallahi ke
nakeso kuma ba wai double dating zan yi ba,soon zan yi mata bayani ta yadda za ta fahimce ni cikin sauk’i zan yi setting
nata free InshaaAllah
Ni da ke
we are meant to be,ki d’an ba ni time I’ll explain things to her….”
Da mamaki Siyama ta tsaya kawai tana kallonsa kafin da kyar tace”Are you listening to yourself??”
Bata jira ta ji abunda zai ce ba ta d’aura da cewa”
za ka rabu da ita saboda ni??”
Da sauri yace”Yeah” sai kuma ya sake cewa”tun ba yau ba Ina…”
Girgiza kai kawai ta yi cikin katse sa tace”pls………”sai kuma ta runtse idanunta kafin ta kama handle d’in k’ofar tace “zan fita!”
Da sauri yace “You ask for
the truth …”
Bud’e idanunta ta yi kamar zata fashe da kuka tace
“Ka bud’e min k’ofa in fita!wai ta ya kake expecting in yi trusting d’inka?ka bar wata saboda ni!ka ga kenan in ka had’u da wata in the future nima ka yi dumping d’ina ban Isa in ce zan
ji haushi ba!”
“Ba haka bane abun namu it’s complicated,ki fahimceni dan Allah”
Cikin takaici ta kallesa sosai tace
“Complicated how???”
Tashi d’aya zuwa yanzu Najeeb ya fahimci ya riga da ya jagula komai da hannunsa,ga shi ya lura Siyaman ta zu
ciya sosai dan idanunta da kan hancinta ya d’an yi jaa!,shiyasa kawai ahankali ya sa hannu a gefen seat d’inshi ya bud’e mata motar,yana shirin
ce mata’ya bud’e’
ya ga ta bud’e ta fice da sauri dan yana dannawa ta gane ya bud’e ne.
A ranta tace baka da
abun fad’a ai dole ka bud’e min
Mayaudari kawai…….
Juyawa kawai ya yi ya jingina a jikin kujerar da yake zaune a kai ya yi shiruuu….One thing is for sure ba zai tab’a iya hak’ura da Siyama ba,ko menene zai faru sai dai ya faru amman Siyama belongs to
him da izinin
Allah. Kawai dai kmr yadda ta fad’a anya ba zai zalinci Ya’isha ba idan ya yi hakan?ga shi shi harga Allah
ba zai tab’a iya auren mata biyu ba tsarinsa na mace d’aya tun farko bayaga haka a yadda yakejin soyayya da k’aunar Siyama 99%da kum
a yadda yakejin na Ya’isha da bai wuce 5% ba ya san idan ya had’asu su biyu a matsayin matansa to tabbas akwai matsala dan ya san ba zai tab’a kwatanta adalci ba.
Ko a lokacin da yake tare da Ya’isha shi dai ya san yana sonta amman bai san zafin so
da a
salin mene shi so d’in ba
sai a kan Siyama…..
Kaff y’an kawo amarya ba bu wanda bai shiga shock ba dan tun daga gate da compound suka fara ganin ikon Allah….an san dama Mijin yana da kud’i duba da yanayin kud’in
da aka bayar lokacin da aka zo saka
rana da kuma lefe
amman sam ba su yi expecting haka ba,dan a kaff cikin su 5% ne kawai suka tab’a sanin akwai Irin gine ginen nan ma a Nigeria,ga furnitures kamar ba za a mutu ba!Tabbas Manubiya ta dandalo arzik’in
dan a kaff area d’in su ba y’ar da t
a tab’a dandalowa….Ah lalle kam dole dangin miji suce da durk’usa uwarta kuma ta amince yo idan sune ko kwanciya akace y’ar su ta yi ai sai ta yi wallahi,Irin wannan aljannar duniya haka gida kamar ba a Africa ba…..
Haka nan dai suka dinga mamaki da zance
n zuci
waenda ba za su iya dannewa ba kuma suka koma gefe aka shiga tattaunawa.
Tun case d’in Baraka da ya Musbah su Maman Abbakar ba kula su Manubiya sukeyi ba
sai yau!yadda Maman Baraka ta ga Manubiya ta samu duniya ya sa hankalinta ya sake tashi
ta kuma bada goyon baya akan y’arta ta koma gidan ya Musbah dan ko banza yanzu kam Musbahu ba shi da nauyi a kansa dan ta san duk Manubiya za ta d’ebe maybe suma su samu su dandala……
Ba a fara barin gidan Manubiya ba sai wajajen 11
na dare…shima kuma
sai da
Yash ya kira Najeeb yace
“Idan bai zo sun fara kwasar jama a suna maidawa gida ba wallahi zai shiga gidan da kansa ya ce musu dare yayi”
Tsaff Najeeb ya san Yash zai aikata shiyasa ya mik’e ya dauk’i makullin motarsa ya fice
gaba d’aya gab’o
b’in jikinsa na masa ciwo,ga tension da tunanin ta Ina zai fara da Siyama da Ya’isha dan gaba d’aya kansa ya d’aure….
….
Zuwa yanzu gidan ba kowa daga Manubiya Jidda sai Yahanasu da Aisha da Siyama da Munirat….Su Najeeb sun tafi kai wasu a cikin mutanen
su dawo.
A tunanin su su za su d’auki su Siyama ma su maida su gida nan kuwa ba su san already
sun cewa su ya Nafi’u in sun gama za su yi musu magana.
Suna zaune gaba d’ayansu
sukaji kmr an shigo parlourn bedroom d’inta,dan haka da sauri Yahanasu t
a lek’a,dariya tayi kafin tace”Au Yassir!ashe kai ne ai na yi tunani angon ne”
Bai damu da yadda ta tsaya ta tare k’ofar d’akin ba haka ya kutsa ya fara k’ok’arin shigewa,ganin kmr zai shige jikinta ne yasa ta d’an matsa tana cewa”babu kyau fa shiga d’a
kin Amarya”.
Sai da idanunsa suka sauk’a akan Jidda da yake ta faman nema tun d’azu ya samu ya d’an nutsu tukunna ya juyo ya d’anyi mata murmushi
kafin yace”Really
Inji wa?”
Ya fad’i hakan yana me maida kwayar idanunsa ga Jidda wadda ta had’e rai
ta tamke fuska amman fa a chan k’asan ranta tsorone ya lullub’eta…dan tun d’azu ita kuma take ta k’ok’arin b’uya gudun kar su had’u,yanzu kam tana ganinsa gaba d’aya hankalinta ya tashi!
Sam bata son Yassir,dan idan akwai mutanen da bataso ta gani yanzu
Yassir ne Sai su Yassira.
Muryarshi ta tsinkaya kawai yana cewa”Jidda muje
Ko”
Ya fad’i hakan yana kallonta.
‘Dum!!!’
Haka k’irjinta ya bada kafin
a ranta tace
“Lalle wannan mutumin bashi da hankali…yanzu shi har yana tunanin zata iya tsay
uwa a k’ark’ashin inuwa d’aya dashi bayan abunda yayi mata talkless of har ta bisa…ta bisa ya k’arasa rungumar da d’azu bai samu access ba kenan…
Yahanasu ce tace”Ai sun kira brother d’insu zai zo ya d’auke su”
Sai da ya d’anyi shiruu kafin
yace”Am..
siyan baki za su yi,
Yash yana k’asa,a yadda
na gansa d’innan na san idan ba su yi sauri sun sauk’o k’asa ba to za su yi loosing kud’in siyan bakin…da kyar muka
tsaida shi da ni da Najeeb
kema ku yi sauri ku wuce
ku basa space dan na lura a mats
e yake..”
Da sauri Yahanasu tace
“A’uzubillahi”
Sai kuma ta kai masa duka.
Kaucewa yayi yana dariya
Idanunsa suna akan Jidda wadda ta runtse idonta
da k’arfi tana mamakin rashin kunya da tsaurin ido irin
na wannan bawan Allah.
Ahankali Muni
rat ta sunkuyar da kanta k’asa…a ranta tana aiyyana shin decision d’in da ta yanke anya kuwa ta yiwa kanta da rayuwarta adalci kuwa.So take yi kawai wani ya bata go ahead yace ta yiwa Yassir duk
abunda yakeso amman daga Ummi har sister d’inta sun kora mata
zazzafan warning akan Yassir sun ce ta rabu da shi,sun k’i ma su tsaya su saurareta kuma tun ganinsu tare da Ummi ta yi gaba d’aya sun k’i su sake da ita balle su ji cikinta sosai ta yadda za su fahimce ta…ita kuma gaskiya ba za ta iya rayuwa babu Yassir
ba,ga shi ta lura ko ta kanta ma ya daina bi ta san kuma yana samun guri a wajen Jidda shikenan ta ta ta zo k’arshee….
Ba ta Ankara ba ta ji hawaye ya zubo mata da sauri ta yi firgigit ta sake yin k’asa da kanta tukunna ta sa hannun ta goge,sai a sannan t
a ji muryar
Yahanasu tana cewa”Munirat ko bacci kika fara ne daga sunkuyar da kan da kika yi yanzun nan?”
Sai da ta d’an gyara fuskarta
da style tukunna ta d’ago tana murmushi tace
“A’a”
Daga haka ta mik’e tsaye tana gyara mayafinta.
Shi Yassir ha
rga Allah sai yanzu ma ya ganeta,shi fa idan ba ganinta ya yi ba wallahi mantawa yakeyi da ita.
Ya san sun had’a ido da ya shigo amman sam hankalinsa ba ya wajen shiyasa ma bai wani fahimci ita d’in ce ba.
Aisha cewa ta yi ba zata je ba haka ma Yahanas
u,sai da Yahanasun ta saka baki tukunna da kyar Jidda ta mik’e ta yarda za ta je,ba kad’an ba k’irjin Munirat ya dinga bugawa dan ba ita kad’ai ba Hatta su Aisha sai da suka lura da yadda Yasir ya ke bin Jidda da ido…..babu yadda bai yi a barsa ya ga fuska
r amarya ba a cewarsa “ai shima zai iya yaye lullub’in tunda k’anin ango ai ango ne”amman k’iri k’iri Yahanasu ta hanasa….haka nan yana ji yana gani ya hak’ura suka fita,ya so ya ga fuskarta sosai wallahi dama yanzu ne chance d’insa na yau dan ya san Yash
ba zai tab’a yarda ya rakosa ba.
Yassir ya so ya d’an wanke kansa a wajen Jidda amma sam ta k’i ta basa chance d’in ya yi mata magana haka ta mak’ale a tsakiyar su Siyama har suka sauk’a.
A k’ofar parlourn chan k’asa dama Najeeb ya tsayar da Yashju
b k’iri
k’iri ya hanasa shigowa ko cikin parlourn yace“wallahi yau sai yayi al’ada,gashi ya tusa shi a gaba da tsiya da zolaya…tun Yashjub yana fushi wai ko Najeeb d’in zai hak’ura har ya hak’ura ya d’an fara dariya kad’an kad’an.
A haka su Siyama suka
sauk’o suka samesu,sai da ya hangesu tukunna ya bar Yashjub ya shigo ya zauna…
Shiruuu parlourn ya d’auka bayan duk sun zauna, su
Siyama basu tab’a sanin ma yadda ake siyan baki ba,
Munirat kuma tana d’an shakkar Yashjub sannann ga tunanin Yassir
shiyasa ta yi shiru.
Tashi d’aya suka fahimci bama su iya siyan bakin ba shiyasa kawia Yassir ya fara dariya k’asa k’asa
Ganin za a rainasu ya sa Siyama ta yi k’arfin halin cewa
“Siyan baki za mu yi”
Murmushi duk sukayi kafin
Najeeb yace “Ai b
a ku za ku yi siyan bakin ba mu ne za mu yi,ko??”