Showing 204001 words to 207000 words out of 259716 words
tsarawa a gaban Hjiya mama dan t
a san idan sama da k’asa za su had’e ba za ta tab’a yarda ba
Shiysa ta yi godiya ga Allah da ta ga tunda ta shiga ciki bata sake ko lek’owa ba.
Daddy Abhi sai Yashjub wanda Abhi ya k’arasa ya ja hannnunsa ne suka nufi saman,dan haka da sauri jikinta h
ar yana rawa ta bi bayansu.
Suna shiga parlourn Daddy itama ta kutso
Kai bakinta d’auke da sallama.
A fusace Daddy ya juyo yace”the last time da kika hawo mini side d’ina me na ce miki???”
Cikin in Ina tace”Haba Daddy meeting fa za a yi wanda ya
shafi rayuwar d’aana dole ka ganni a nan mana sabo…”
Cikin katseta da b’acin rai sosai yace”za ki b’ace mini daga gani ko sai na yi ball da ke??”
Hawaye ne suka b’alle mata kamar an kunna famfo..
Cikin son tura mata wani bak’in cikin ya matso kusa da it
a yace”da ke da frame ba ku da maraba a cikin gidan nan bi ma’ana sai dai a kalle ki ki kalli mutum shi kenan amfanin ki!.
Daga yau! ko da wasa na ganki a wajen da ake serious maganar da ta shafi ni ko y’ay’ana Wallahi ranki sai ya yi masifar b’aci bana
buk’atar ki a cikin komai nawa! ko yunk’uri kika yi na son shiga cikin maganata ko ta yarana wallahi bak’anta mini rai kike yi.!
Tsabar tsaurin ido ko Ummi wadda na damu da ita ba ki ganta a nan ba amma ke k’ok’ari kike yi ki shigo!….”
Da mugun sauri
Mommy ta juya tana hawaye kamar ruwan fanfo,bibbiyu haka ta sauk’a daga stairs d’in ta nufi side d’inta inda ta bar Baba Larai tana mai had’a hanya….
Tana shiga ta tarar da su ita da su Yasira…
Ganin yanayinta ne ya sake d’aga musu hankali dan haka su
ka rufar mata da tambayar “mai ya faru?”.MANNUBIYA
(Book 2)
Page 38
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
Tana shiga ta tarar da su ita da su Yasira…
Ganin yanayinta ne ya sake d’aga musu hankali dan
haka suka rufar mata da tambayar “mai ya faru?”.
Ba ta b’oye musu ba dan zuwa yanzu tana so ta gogawa Daddyn bak’in jini a idanun y’ay’an nasa ta yadda za su tsaya mata su bi bayanta a kan komai.
Komi ta kwashe ta sanar da su tana kuka abun tausayi wan
da hakan ya sa Yadira da Yusra fashewa da kuka suma…
Yasmeen kam ta d’an ji babu dad’i tunda uwa uwace sai dai kuma har ga Allah ita ba ta ji haushin Daddy ba,Yasira da Ya’isha ne suka fi kowa fusata Ya’isha har da cewa “ai da ba ta fito ba!”da ya ce ta f
ito d’in.
Sosai suka rarrashi mahaifiyar ta su wadda hakan da suka yi ya sa ta d’an ji sanyi,daga nan ta kalli Baba larai tace mata “suna sama suna meeting Larai kin san me ya kamata ki yi a halin yanzu ko?”
“Dalla dalla ma kuwa!”
Baba Larai tace,da
ga haka ta mik’e ta fice Ya’isha da Yasira suka bi ta Yusra da Yadira suka zauna suka ci gaba da rarrashin Mommy yayinda Yasmeen ta fice ta basu guri,dan tunda Mommy ta fara magana da Baba Larai ta fahimci what they are up to…ba ta against wai Kausar ta au
ri Yash kawai ita Asiri ta tsafin nan na su ne ba ta so sannan makircin su har ga Allah ya yi yawa,gashi ba ta Isa ta ce komai ba.
Mommy tana fita Yassir ya shigo…kwata kwata ya kasa
gane kan dalilin wannan dramar da Kausar ta gabatar,zai je ya sa
meta su keb’e su yi magana ya tambayeta dalili amma for now tun kafin iyayen sa su yanke wata muguwar shawarar da zata tarwatsa shi gara ya zo ya fito kawai ya gaya musu zai aureta…a yanzu babu lokacin pretending ko actin domin a yadda abubuwa suka gudana
da abunda tayi ya san tsaf su Daddy za su ce Yashjub ya d’auki responsibility d’in cikin da ya yi wa Kausar ko dan kar sunan family ya lalace.
Ba su kaiga fara magana ba shima Junior wanda sai yanzu ya dawo daga had’o results ya hawo saman ya shigo cik
in parlourn.
Ganin kowa jigum ya sa shima ya nemi waje ya zauna ya yi
shiru….sam ya k’i yarda ya kalli inda Yassir yake ma sakamokon wani haushi da takaicinsa da yake ji.
Numfashi Daddy ya fesar kafin ya kalli Junior yace”ya bayanin
result d’in??
?”
Mik’ewa Junior ya yi ya kai masa takardun da ya shigo da su na results d’in a envelope tukunna ya koma ya je ya zauna sannan yace” irin na d’azu ne cikin exactly 12 days ne..na yi kwakwaran bincike yadda ya kamata,sai da na je ma na sake d’aukar jinin
nata na yi binciken komai kamar yadda ka ce ga kuma scanning d’in shima.”
Dubawa Daddy ya yi ya bawa Abhi shima ya duba.
Shiruuu parlourn ya kasance daga nan kafin Yassir yayi gyaran murya
yace”Daddy idan ba damuwa ni na yarda zan auri Kausar!!!
Aka
n dai ta fita ta tonawa family d’innan asiri on top
of that ta d’auki d’an d’anuwana ta tafi dashi tayi masa raino da tarbiyyar single parent
Ni Naji na gani zan aureta
tunda dama ina sonta.”
Cikin katseshi Daddy yace
“Yassir I’m sorry kawai ka bar
maganar nan,ka san cewa Kausar ba za ta yarda ta aureka ba,tunda har mahaifiyarka ta fad’amawa watak’il ba ka sani ba ne amma ta nuna ta kuma ce ba za ta tab’a aurenka ba don ba ta sonka…k’iri k’iri ta bijirewa auren ku kwanakin baya so inaga yanzu is not
the right time ace za ayiwa Kausar dole
she’s stubborn
I think she’s capable of anything za ta iya tafiya d’in kamar yadda ta fad’a kuma na tabbatar sai ta yi using wannan Yaron against Yashjub besides bai kamata mu bari ta tafi da Yaro ya rayu kamar
yadda ka fad’a ba.
Also akwai abunda ta shirya tunda har ta fara maganar tafiya dan Kausar d’in da na sani ba za ta yi abunda ta yi yau ba tare da ta tanadi kwakkwaran plan ba….ai ta ga ta samu ciki so tanada weapon dan haka ya zama dole mu yi mata shiga
r sauri kafin ta yi b’arna.
Sannan Yassir ko an yi aurenka da Kausar ba za ku zauna lafiya ba ta dinga taso da fitintunu dan zatace an yi mata dole ne,again kamar yadda ka
fad’a kana sonta so za ta ke juyaka ne kawai!
In zan baka shawara ka d’auka dan
Allah ka hak’ura da Yarinyar nan har abada.
Cikin d’an uwanka ke a jikinta
haba mana kwab’ar kar ta yi yawa.
Sannan ba zan ji dad’i ba
Ni kaina idan aka ce ka d’auki
responsibility d’in abunda ba laifin ka bane ba.”
Da k’arfi gaban Yashjub
ya yanke ya fad’i dan a kaff cikin maganganun Daddy tun kafin ya fito ya fad’i abunda yake ransa ainun ya fahimci inda zancen zai dira dan haka ya runtse idaunsa da mugun k’arfi yana sauraron Daddy da ya ci gaba da cewa”some facts cannot be denied!!kasanc
ewar ba na son Kausar ba shi zai sa in rufe ido in k’i gaskiya ba!sannan ko babu komai nima y’ay’a mata ne guda shidda a gabana,idan wani ya yi musu haka ba zan ji dad’i ba!
A al’amarin nan Abu na farko da zan so ka saka a kanka Yashjub shine ba zan bada
goyon baya a zubar da ciki ba saboda haramun ne.
Sannan ka yi hak’uri Yashjub kaima na san ba laifin ka bane ba amma itama ba laifinta bane ba saboda kamar yadda ta fad’a da gaske ne maganar da Likita ya yi akan mahaifarta lokacin na ji zancen dan haka
ka ga ba za ta so ciki da gangan ba tunda ba zata yarda ta yi abortion ba kuma ba za ta so ta haihu babu ciki ba.Ta yiu tricking d’inka ta yi da gaske amma tabbas na san ba ta yi tunanin za ta samu ciki ba.
Abunda nake so ku fahimta a nan shine k’addara
ce ta fad’o mana…. idan muka ce Kausar ta zubar da cikin nan considering health condition d’inta to mun zalunceta kuma ba zan ma bari a zubar da cikin ba,idan kuma aka ce ta haihu babu Miji shima mun zalinceta kuma na san ma ba za ta yarda ta zauna da mu b
a….kuma duk daren dad’ewa kowa ya san Yaro na Yashjub ne dan gaskiya ba ta b’uya.”
Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e kafin ya kallesu one by one tukunna yace”which is Y na yanke shawarar abunda ya kamata a yi a rufawa kowa asiri.Yashjub k’addara ta riga fata
kuma an zo wajen da dole sai ka yi hak’uri ka danne zuciyarka an rufawa juna asiri..ni Mahifinka ne har abada ba zan yi abunda zai cutar da kai ba sai dai in yi wanda ba zai cutar da kai ba wanda zai rufa maka asiri. Ka dai ji dalilan da na bayar kuma na s
an ka fahimta…dan haka ka auri Kausar!
A samu ta haihu lafiya daganan duk decision d’in da ka yanke ba zan ce komai ba!
Ko wanne family suna da nasu secret d’in cikin jikinta it’s just two weeks idan aka yi aure za ta haihu ne on time asirin kowa a rufe
duniya ba ta sani ba.Yaro kuma kai ka san yadda zaka yi a gaba ka fitar masa da hakkinsa ba tare da an kwaresa ba.
Ka yi hak’uri ka d’auki responsibility d’inka,na san ba laifinka bane ba amma duba da yadda Yaron nan zai zo duniya a ganina idan aka barsa
da ga shi sai Kausar a inda ba mu sani ba to gaskiya ba mu yi masa adalciba kuma kai ka san wacece Kausar! ba ta nustu ba ma ballantana ta yiwa wani tarbiyyar da ta kamata.”
Ajiyar zuciya Abhi ya sauk’e kafin yace”Daddy abunda ka fad’a gaskiya ne! san
nan its the only easy option we’ve got dan duk wani ba shi ba to
akwai consequences”
Mik’ewa tsaye kawai suka ga Yashjub ya yi….yana jin kanshi yana wani irin juyawa yace”Daddy idan na auri Kausar zan iya mutuwa amma kamar yadda ka fad’a k’addara kow
a da kalar tasa…zan je in samu Manubiya in gaya mata komai duk abunda tace a yi shi za a yi
Wannan rayuwar mu ce
Na ci amanar ta
A ganina this should be her decision to make.
Dukda cewa idan na auri Kausar zan iya mutuwa amma idan har ta bi bayan
abunda kuka hango kuka fad’a shikenan na yarda zan aureta d’in har zuwa lokacin da za ta haihu!.
Idan kuma ba ta yarda ba i’m sorry to say this amma Kausar is free to do whatever the hell she’s planning on doing,ban damu ba!”
Yana gama fad’in haka
ya j
uya ya fita ko bi ta kan Daddy da yake cewa “yanzu zama za mu yi mu jiraku kenan kake nufi?”bai yi ba.
Sai a lokacin Yassir ya d’an samu nutsuwa…
Sosai Daddy ya ji haushi ya fusata…tayaya Yash zai ce sai abunda ta yanke tukunna shi za su yi??a tak’ai
ce dai Yashjub ba shi da choice sai na Manu su kuma suna zaune suna jira har sai ya je ya tambayota ta fad’a tukunna a zo ya gaya musu su yi.!
Ya san dole abun zai tab’ata tunda abune wanda ya shafi Mijinta da wata mace amma power d’in da Yashjub ya baw
a Manubiya is too much…this is not the right time da ya kamata ya ji haushin Manubiya a kan wannan maganar dan tunda cikin jikinta ya zube shi tausayinta ma yake ji over amma tashi d’aya a yanzu sai ya ji takaicinta ya rufe sa….ba zai tsaya a mayar masa da
d’a boyi boyi ba.
Wato ko abu zai kashe shi kmr yadda ya fad’a in ta na so
zai yi kenan! matar da ya kamata ace she’s even greatful da Yash ya aureta aka kawota cikin family d’in su shine amma ta kafa ta tsare ta ke juya musu d’a suma take so ta juya su
.
Lissafin da Daddy yakeyi haka nan shima Abhi yake irinshi
Exactly.
Dama shi Abhi tun farko da su ka je kai kud’i sai da ya saka hakan a ranshi amma daga baya sai ya janye yanzu kuwa power d’in Manu ya yi yawa gaskiya dole a ja mata layi.
Dan wanna
n Yarinyar idan ba su yi da gaske ba har Hajiya mama sai ta juya.
Numfashi Daddy ya fesar kafin ya kalli Abhi yace”yanzu me ye abunyi?ni dai ba zan jira sai Yarinya ta yanke decision tukunna mu maza za mu yi ba.”
Jinjina kai Abhi ya yi yana d’an lis
safi kafin yace”Daddy a yiwa kowa adalci sannan a duba Yaron da bai ma riga ya zo duniya ba…kamar yadda ka fad’a duba da yanayin hanyar da akabi aka sameshi ya kamata ace mun tsaya tsayin
daka mun yi sacrifing komai wajen ganin mun inganta rayuwa da tarbi
yyar sa…”
Da sauri Yassir yace”Abhi ni k’anin Yashjub ne inason Kausar me yasa ba za ku aura mini ita ba ni???
Wallahi idan kuka had’a Kausar da Yashjub to
kun had’a fitina ne saboda ba sa so…..”
Cikin fushi Daddy ya katse sa yace”One more word fr
om you Yassir Allah sai ka fita a parlourn nan!!!
Mahaukacin banza kawai mara zuciya…
Anya Yassir ka san ciwon kan ka kuwa??”
“Hmmm”kawai Junior yace
Wanda hakan ya sa duk sai da suka d’an kalleshi.
Atake jikin Yasssir ya d’anyi sanyi dan sai
yanzu ya fara tunanin kar fa ya kwafsa..to amma shi yanzu ya zaiyi???….ga duka ga hana kuka!inaa!!!ba zai bari auren nan ya d’auru ba.
Sai da su Abhi suka sake yin d’an k’us k’us d’insu tukunna Daddyn ya d’auki waya ya kira Ummi daganan ya kira manya
n drivers d’in gidan da aka dad’e da su yace “su zo!”
…Manubiya abar tausayice duba da zargin zubar matar da ciki da suke yi sannan Yarinyar ba ta matsala ga kuma tarbiyya da hankali above all d’an su yana sonta he’s happy with her!amma kuma Tabbas ya k
amata a yi limiting d’inta dan ba zai you su je garin tausayin su kunnawa wani haske su kuma su k’ona kansu ba…soyayyar Yashjub a gareta ta yi yawa ba su damu idan ya so ta da yawa ba kawai su problem d’insu importance da power da ya Bata wadda take k’ok’a
rin danne su da k’imar su a idanun Yashjub ne matsalarsu sannan ba a yiwa mace haka!idan su ka zuba ido a gaba za su matsala.
Tun da akayi auren yake haka inda gigin amarci ne da tuni ya daina amma abun nasa k’ara gaba yake yi.son da Yashjub ya ke yi mata
ya yi yawa…ba sa jin haushinta infact su tausayi ma take basu ammafa fa hakan ba shi zai sanya su zuba ido Yashjub ya zama boyi boyi ba.
Sun san idan ya riga ya auri Kausar ya saba da mata biyu ko ya rabu da ita bayan ta haihu kamar yadda aka shirya ba l
alle ya iya zama da mace d’aya ba…Idan aka barwa Manubiya Yash ita kad’ai akwai gagarumar matsala….
Dan haka suka ga dacewar su jefi tsuntsu biyu da dutse d’aya……
Yana gama waya da su Ummi ya sauk’e ajiyar zuciya ya yi shiruuu yana mai jin kamar ya d’a
ura Hannu a ka! ya kurma uban ihu…wai yau shine da kansa zai aurawa Kausar Yashjub!
Tabbas shiyasa ba a son mutum ya tsananta tsana!saboda ba ka san inda rana za ta fad’i ba.
….
Sai da aka kusan yin fad’a da Daddy da Ummi da ta ji wai aure za a d’aurawa
Kausar da Yashjub…so ta yi ta fita ta kira shi ta sanar da shi amma Daddyn ya ce ta zauna Abhi kuma ya shiga bata Baki,ga drivers d’in gidan a zaune sun yi jigum suma kawunansu a k’asa,shiyasa Abhi ya dage ya lallab’ata ba dan ta so ba ta hak’ura ta zaune
ta na mai jin kamar zuciyarta za ta fito babu yadda ta iya haka aka d’aura auren Kausar da Yashjub akan sadaki naira dubu d’ari Abhi ya yiwa Yashjub wakili Daddy kuma ya yiwa Kausar.
Ba abunda ya fi d’aurewa Junior Kai kamar rikicewar da Yassir ya yi,D
an ba da shi ma aka d’aura auren ba korarsa su Abhi suka yi ganin yana shirin yi musu hauka da kyar kuwa ya fita yana huci ya nufi side d’in Kausar amma sama ko k’asa ba ta nan kuma wayoyinta duk gasunan a zube a kan gado.
Ita kuwa Kausar b’uya ta yi a bo
x room d’in saman saboda shi tana kallonshi ya sauk’o a rikice ya nufi side d’in nata sai da ya fito ya sauk’a k’asa tukunna ta fito ta shige dan ba ta shirya fuskantar sa ba Bata gama had’a wayon da za ta yi masa ba wannan karon.
Dukda tana zullumin son
jin dalilin yanayin da ta gansa a ciki amma za ta bari ta ji zuwa gobe.
A b’angaren Mommy kuwa ta fito kenan za ta tafi wajen Baba larai ta ji ya ake ciki ta ga Yassir ya sauk’o kamar ma yana kuka shiyasa ta kasa hak’ura ta haye saman ai
kuwa tun kafin
ta k’arasa jikin k’ofar sosai ta fahimci d’aurin aurene ake yi….
Hamdala da sujjada ta yi sai da ta ji an ida d’aurin auren tukunna ta juya ta nufi