Showing 15001 words to 18000 words out of 259716 words

Chapter 6 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

42

Na

Humayrah Bulama

Mikiy

a Writers Association.

Kamar zata fashe da kuka ta d’aura da cewa ‘’Mommy kinga yadda yarinyar take kallon mutane kuwa’akan hanci’mun had’a ido da ita amma ko gaishe ni bata yi ba,k’annenta ne kawai suka gaishe ni amman ita d’auke kai ta yi ta sake tamk

e fuska’’

Yusra da suke tunanin yarinya ce itanma yau kam ta bi bayansu dan a lokacin da Yasmeen ta shigo tana d’akin Mommyn a tare ta gansu tana taya ta gyaran wardrobe,sosai itama Yusra ta taya Yasmeen zuga Mommy,dama chan ba son auren suke yi ba,yanz

u kuwa ganin Manubiya da kuma abunda Yasmeen d’in take ik’irarin an yi mata shi ya sake tunzura su Yasmeen d’in,a cewarsu ’’sam ba zai yiu su bari Yash ya auro wata chan daban ba gashi tun yanzu k’annenta sun fi su daraja da mutunci a idanun Yash ba ma it

a ba,dama irin abunda suke gujewa kenan ga shi an fara tun yanzu in ba haka ba ta ya zai shanya

Yasmeen a waje ya hanata shiga sannan ya dinga wani ririta k’annen so called fiancé d’in sa

Sam bai ma nuna musu wacece Yasmeen d’in ba

ballantana su girm

amata.

A gaskiya ba zai yiu su bari Manubiya ta rayu da Yash ba

tunda ya fara haka to akwai babbar matsala a gaba gara kawai a tarwatsa wannan auren a had’a shi da Kausar tunda itace tasu,ta haka ne kuma za su zama d’aya kansu ya had’u da d’an uwansu.’’

Ita Yasmeen wani sabon abunda ya sake d’aga mata

hankalin ma shine ‘yarinyar y’ar gidan talakawa ce’

Saboda yanayin abayoyin Jidda da Siyama da hijabin jikin Manubiyan kad’ai ya isa ya sanya mutum ya fahimci talakawa ne,shikenan ta san akanta zai

k’are ita da dangin ta dan yadda yake uban rawar k’afar nan ta san bud’e musu bakin aljihu zai yi ya yi ta b’arin kud’i su tatike komai komai ya koma wajenta,ita kuma ita da su Mommy a ajjiyesu a gefe dan ta lura yarinyar batada kunya sam kuma bata da mutu

nci tashi d’aya zata raba shi da su.

Haka nan dai kamar za su ari harshe suka yi ta mita su biyu

dan sam Mommy ta ma kasa magana saboda ita duk ba wannan ne abunda ya fi d’aga mata hankalinba dan ta san ta riga ta gama tsarawa indai ta haifu cikin uwart

a da ubanta

to Manubiya ba ta isa ta auri Yash ta shigo cikin family d’in ta ba wallahi dan ko hauka take yi ba zata tab’a bari Yash ya auri yarinyar da take tafe da downfall d’in ta ba dan Baba Larai tace ‘’indai har Manubiya ta kasance a tare da Yash t

o duk wasu sirrinkanta na sama da shekaru talatin da y’an kai sai sun bankad’a a fili kowa ya ji ya gani kuma sai ta shiga masifar da bata tab’a tunani ba’’,sannan bayaga haka indai tana raye to Yashjub bai Isa ya auri wata mace idan ba Kausar ba saboda ta

san duk fad’in duniyar nan Kausar d’in ce kawai za ta iya yi mata yadda take so.

Shiyasa ta tsaya tsayin daka ko menene ya kamata to zata yi muddin za ta samu ta hana auren Yash da Yarinyar nan dan ba ta da guri a family d’inta,sai dai kuma idanunta da

suka rufe akan raba aure kawai ya kaita ga kasa yin tunani mai zurfi dan kamata ya yi ace ta raba sa da ita har abada tun a karon farko ba wai iyaka aure ba tunda ko babu aure indai suna tare to akwai matsala gashi kuma yanzu Yasmeen ta zo mata da wani za

ncen na sabon tashin hankali dan ba k’aramin tashi Hankalinta ya yi ba da ta ji

Yasmeen tace’’Yash ya shanyata a waje for more than 30 minutes tana ta knocking sunk’i su bud’e mata da shi da Yarinyar’’

A yadda Yash yake da kud’in nan ta san ba ko wacc

e irin mace ba ce zai nuna yana buk’ata ta k’i amincewa da shi,ballantana Yarinyar da ta riga ta san ita zai aura nan da kwanakin da basufi goma ba.

Karfa ta je tanata k’ok’arin hana d’aurin Aure aje Yarinya

ta samu ciki kafin ma ta shigo gidan,dan i

ndai ta riga ta samu ciki to komai ya zo musu k’arshe,dan ta zame wa Yash k’arfen k’afa kenan.

‘’Mommy!’’d’in da Yasmeen tace mata ne ya katse mata tunani,firgigit ta yi ta kallesu gaba d’aya su biyun ransu a b’ace hankalinsu a tashe

Yasmeen ta bud’e

baki za ta yi magana kenan Mommy ta katseta ta hanyar ce mata ‘’Tashi ki je ki kiramin Baaba Larai,Yusra kema bita ku

turomin ita’’

Wani sanyi Yasmeen ta ji a ranta dan haka ta mik’e ta fice da sauri Yusra ma ta bi bayanta,kamar bayan mintuna

biyar

da fitar su Yasmeen Baaba Larai ta shigo,a yadda

su Yasmeen suka fita suka barta a haka ta shigo ta sameta.

Kusa da ita ta nemi waje ta zauna kafin ta ce’’yi hkr,sun sameni ina girki ne,Ummi na tarar za ta yi masa girki wai an sallameshi Yassir ya tafi

d’auko shi shine na samu na k’arba da kyar kuwa ta barmun kinsan halinta’’.

Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin tace ‘’Kin kammala abunda kika fara ne?’’

‘’Eh!ai shiyasa ma na karb’i girkin’’

Baba Larai ta bata amsa a cikin ranta tana addu’ar ‘’Alla

h ya taimakesu su samu nasara a kan Yashjub dan abun nasa kamar gado ya yi ko me aka yi masa ko anci sa’a ya kamasa to fa ba ya tasiri kuma baya dad’ewa yake karyewa.’’

Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin tace ‘’Sannu y’ar uwata’’

Sai da Baaba Larai

ta gama nazartarta tukunna tace’’mai ya faru kuma?’’

Ta yi mata tambayar tana gyara zama

Sai da Mommy ta sake sauk’e ajiyar zuciya tukunna tace’’Gobe za’a kai kaya ayi tambaya a yi komai Daddy sai shirye shirye yake har yanzu banga alamun fasawa ba,

anya Baaba ana yin komai yadda ya kamata kuwa?naga kamar rura wutar ma ake yi.’’

Ahankali Baaba Larai tace’’da izinin Allah za mu yi nasara,inshaaAllah ba za’a d’aura ba,ke dai kawai ki zuba min ido kamar yadda na gaya miki’’

Numfashi Mommy ta fesar

kafin tace‘’sai maganata ta biyu,mun yi tunanin yara fa Baaba,mun gaza mu yi lissafi mai kyau,ba mu auna cewa tsaf shaid’an zai iya tunzura Yashjub aje Yarinyar ta samu ciki ba ko da kuwa ba ayi auren ba

kinga kuwa in akwai ciki bamu isa hana aure ba ko

da ace ma mun hana d’in to munyi ta banza ne.Na san Yashjub ba shi da neman mata amma akwai shed’an ita kuma yarinyar a nata b’angaren na san a yadda Yashjub yake da kud’i kyau da kwarjini ba ko wacce mace bace za ta k’i amincewa da shi dan in akayi rashin

sa’a akaje ba nutsatstsiya bace sannan gashi tana ganin an kusan auren su kinga ai komai mai iya wakana ne,yanzun fa Yasmeen

ce min ta yi ta fi minti talatin a bakin k’ofar d’akin da yake d’azu tana knocking amman basu bud’e mata ba

Me kike tunani???

Ina amfanin tarwatsa aure in ta riga ta samu ciki?? Dan na san kafin mu samu mu raba su ko mu san abunyi akan cikin asiri na ya gama tonuwa…..’’

‘’Tabbas ba mu yi wannan tunanin ba’’

Baaba Larai ta fad’a tana mai sake gyara zaman ta kafin ta d’aura

da cewa ‘’zan san abunyi,matsalar shine sunan yarinyar da har yanzu bamu gama sani ba,Yassira tace kamar Manubiya ko Maryam ta ji Yahanasu tace ko?’’,sai kuma ta yi shiru kamar mai tunani kafin ta fesar da iska tukunna ta ce’’inshaaAllah komai zai yi dai

dai’’.

Ruk’o hannunta Mommy ta yi kafin tace ‘’Baaba na gaji

zuciyata ba za ta iya sake nad’ar wani sabon bak’in cikin ba..’’

Cikin son kwantar mata da hankali Baaba Larai tace’’kar ki damu,komai zai tafi cikin tsari

InshaaAllah ba zan zuba ido I

na ganinki cikin damuwa ba…’’

Daga haka ta shiga lallab’ata tana bata baki tare da bata assurance tukunna da kyar Mommy ta samu ta d’an nutsu dan ba kad’an ba ta tsorata matuk’a kuma hankalinta ya tashi kwarai.

A bakin k’ofar shiga side d’in Yash

jub Yassir yayi parking

shi da kanshi ya taya sa shigar da jakar computersa da kayan dubiyar da aka kawo mishi

tukunna yayi mishi sallama ya tafi.

Gwaggo da Ummi ne suka kai mishi abinci daganan suka tambayeshi ko akwai abunda yake buk’ata yace ‘’ba

komai’’

dan haka suka mishi Allah ya kare gaba ya k’ara sauk’i suka tafi domin ya samu ya huta,ai kuwa bai huta d’in ba dan duk sai yau masu gadi suka samu zuwa dubiya saboda ta’aziyya da suka tafi na driver kuma

dama shima ya ce kar a gayawa kowa as

ibitin da ya ke.

Wannan ya shigo wannan ya fita haka masu gadi da drebobi har da mak’ofta aka dinga sintiri har dare dan haka ciwon kai ya sake turnik’e shi.

Ya na sane da su Mommy

Yadira ce kawai ta shigo ta duba shi itanma ya lura kmr fushi take d

ashi amman kana ganinta ka san ta damu sosai

dayake yarinyace ita shiyasa ya yi saurin b’aro jirginta.

Hakanan ta yi mishi ya jiki

harda d’an dessert d’inta ta had’o ta kawo masa.

Sam fuskarshi babu annuri haka ta yi ta tafi dukda kuwa ya ji dad’

in zuwan da tayi amma ya kamata ya koya wa yaran nan hankali shiyasa d’azu yak’i sakarwa Yasmeen!ba zai yiu su yi fushi da shi a sanda sukaso ba tare da wani kwakkwaran daliliba sannan in sunga dama su kulashi a lokacin da suke so.Sam ba zai d’auki wannan

iskancin ba,in the first place ma ba su Isa yin fushi da shi ba ko ma me ya yi ai shine Babba shine a matsayin ubansu ko da ace

shine bashi da gaskiya ba zai basu damar yi mishi wannan rashin ‘da’ar ba ballantana kuma shike da gaskiya,wannan tunanin ne y

a sanya ciwon kan sa ya sake hauhauwa dan abun ya b’ata masa rai sosai especially ta b’angaren Mommy ya ji zafi kwarai a ganinsa bai kamata ta biyewa yara ta k’i zuwa duba sa ba,ya riga ya san halinta da

mugun tirjiya shiyasa kawai ya share ya yi k’ok’a

ri ya lallashi kansa da niyyar zuwa wajen ta anjima inshaaAllah ya bata hak’uri.

Daddy ya yi masa magana haka ma Manubiya sannan shima a karan kansa baya son irin zaman da suke yi da ita har cikin zuciyar sa amma ita take janyo komai,Mommy tanada wani h

ali sai wanda ya zauna da ita ne kad’ai zai iya sani

tanada shiru shiru tanada hak’uri amman kuma ba ta da dad’in zama kwata kwata

shiyasa duk wanda yaga irin zaman da sukeyi ita da shi sai ake ganin kmr shi ne ba ya kyauta mata bayan ita take tab’o sa

.

Ahankali ya fesar da iska ya lumshe idanuwansa tashi d’aya tunanin dayake ta yi da rashin sanin abun da ya kamata ya yi game da rasuwar sa ya taso masa dan haka ya d’au waya ya kira Manubiya akaro na uku daga dawowarshi zuwa yanzu,dan tabbas yana buk

’atar advice.

Bayan sun gaisa ne ya nemi ta bashi shawara akan ya yi bincike akan rasuwar driver d’insa ko kuma ya barshi,saboda ya san ba accident bane,dukda ya yi

alk’awarin d’aukar d’awainiyar family d’in mutumin daga nan har abada inshaaAllah to am

ma kuma yana gani kamar bai kyauta ba idan ya bari mutuwar sa ta tafi a banza saboda ya yi protecting kanshi

daga outcome d’in da binciken zai bayar wanda ka iya tarwatsa shi gaba d’aya.

Cikin son fahimtar da shi Manubiya ta yi masa nuni da yadda idan

ya yi binciken kuma ya je outcome d’in ya yi destroying d’inshi to wa zai ci gaba da kula da family d’in mutumin??.the best thing da zai yi wa mutumin shine ya kular masa da family d’insa,shari’ah kuma su barwa Allah subahanahu wata’ala shi zai bi masa hak

kinsa.

Ya ji dad’i kwarai kuma ya samu relief dan dama so yake a hanashi yin binciken.Sun d’an tab’a hira yau yaji dad’i dan babu mita babu complain haka suka sha soyayyarsu kafin su yi sallama ya katse kiran suna ji kamar kar su kashe wayar.

Suna ga

ma waya ya mik’e ya nufi cikin gida.

Yana shiga side d’in Daddy ya wuce suka hau shirye shiryen gobe,ya dad’e sosai a wajen Daddy kafin su yi

sallama ya tafi,ba k’aramin dad’i Daddy yaji ba da ya ga hatta cokali Yashjub ya riga yayi order ya sayi komai

kuma gidan ma ya tsara komai

ya had’a komai ga lefe ma Yahanasu tana kan had’awa

ya san inda Yassir ne da zuba ido zai yi a yi masa komai….

Yashjub yana fita side d’in Mommy ya wuce sai dai yana zuwa k’ofar d’akinta ya ji a rufe ya so su tattauna

ya bata hak’uri su fahimci juna amman yadda ya yi ta faman bugu ya ji shiru ne ya tabbatr masa da ta yi bacci,haka nan

ba dan ya so ba ya juya ya tafi ya barwa gobe.

A b’angaren Mommy kuwa a

lokacin da ya zo tana parlournta ta fara jiyo muryarshi ya

na magana da Yadira wadda take masa sai da safe

dan haka ta yi sauri ta afka d’akinta ta rufe da wuri dan ba za ta iya facing Yashjub a halin da take ciki ba ta san tsaf zata iya shak’e sa…tashi d’aya Yaro ya tsund’umata a cikin bal’ai da tashin hankali

rabonta da ta yi bacci fiye da na awa biyu har ta manta,haka kurum yaje ya d’auko musu mayya!yo mayya mana idan ba mayya ba wacce irin yarinyace haka da za’a yi ta yin aiki a kanta amman a banza?.

Ba abun da yafi sake d’aga mata hankali kamar d’azu da ta

lab’e ta ji Daddy yana waya da Abhi wai yana hanya ya taho,ta tabbata kenan gobe za

a kai kaya a saka rana,dukda Baaba Larai ta ce ‘’ta jira taga goben tukunna in an kai shine sun yi failing’’

Amman ita a a yadda ta ga anata shirye shirye gadan gadan ta

san an riga an kai ma an gama saidai su nema wani alternative d’in…and again ga maganar da Yasmeen ta gaya mata d’azu shiyasa duk take a gigice ta rasa inda za ta tsoma kanta ta d’an ji sa’ida.

Tun lokacin da Manubiya ta gama waya da Yash hankalinta

yake a tashe bata nuna masa bane dan bata so ta sake assassa masa abun amma ba k’aramin firgita ta yi ba da ta ji yace’’ba accident bane wani ne ya so kashesa‘’.

Ganin ta a zaune tanata tunani ne yasanya Jidda matsowa ta shiga tambayarta….ai kuwa ita ka

nta Jiddan ba k’aramin firgita ta yi daga jin zancen ba amman sai ta da daure itama ta shiga kwantar wa da Manubiya hankali sannan ta d’aura da cewa’’kawai ta dage masa da addu’a Allah ya kare sa daga sharrin masharranta dama mutum kamar Yashjub dole yan

ada mak’iya.’’

Suna zaune suna d’an tattaunawa Baba ya shigo dan yau ya shiga busy shi da su Ya Musbah so suke su samu su gama shirye shiryen tarbar su Daddy da za su yi a gobe in Allah ya kaimu.

Sai da ya ci abinci ya d’an huta tukunna ya kira Manub

iya ya zaunar da ita….nutsatstsiyar nasiha mai ratsa jiki ya yi mata,wanda sai da ta kai Manubiya ga yin kuka.

Murmushi kawai ya yi ya dafa kanta yace ‘’Allah ya miki albarka da ke da y’an uwanki Allah ya sa ki shiga gidan aurenki a sa’a.’’

Ahankali duk

suka ce‘’Ameen.’’

Daganan Baba ya mik’e ya sake fita dan ba su gama ba ya shigo.

Murna a wajen su Jidda abun ba’a cewa komai dan yanzun kam maganar biki ta kankama tunda har suka ga Baba ya fara yiwa Manubiya nasiha .

Shiyasa suka yi ta murna sun

a cewa Allah ya sanya alkhairi’’kamar daga sama suka ji muryar inna tace’’Ameen’’cikin muryarta da suka jima suna mararin jin.Aikuwa duk d’insu rufar mata suka yi saida ta sake maimaitawa suka tabbatar tukunna Muhsin ya fita da gudu yaje ya kira su Baba a

masallaci inda suke ta shirye shirye…..

A ranar murna wajen Manubiya da ahalinta ba’a magana dan har kuka sai da Baba yayi kukan farinciki da yaji muryar inna a zahiri,haka suma su Manu suka dinga kuka suna godewa ubangiji subahanahu wa ta ala.

Sun j

ima suna murna suna godewa ubangiji har da ya Nafi’u kafin su Baba suka fita domin zuwa su sanar da su kaka mallan maganar kawo kud’i da saka ranar Manubiya wanda za’ayi a gobe idan Allah ya kaimu……MANNUBIYA

(Book 2)

Page 07

Na

Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Su Baba suna fita daga d’akin ba da dad’ewa ba,su Jidda har ma da Manubiyan duk sai suka kaure da hawaye dan tashi d’aya suka tuno nan da kwana goma fa Manubiya za ta tafi gidanta ta barsu.

Da

kyar ta samu ta share nata hawayen kafin ta samu ta shiga lallashinsu,tukunna suma suka yi shiru Muhsin ya yi bacci ita

da Jidda kuma suka cigaba da tattaunawa…y’ar uwar inna d’aya ce tak a duniya kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login