Showing 123001 words to 126000 words out of 259716 words

Chapter 42 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

81

maybe su Mommy ne”

Ai kuwa tana bud’ewa suka yi

Ido biyu da Yasira

Yasmeen da Ya’isha.Ba musu ta matsa musu suka shigo..sai da suka fara yi wa Manubiya ya jiki tukunna Yasmeen tace “Mommy ce tace ta zo ta duba ta”

Cikin tarar numfashinta Yahanasu tace

“Ai Likita yana hanya”

Murmushi Yasira ta yi ta matsa kusa da Yas

hjub da Mannubiya da suke zaune a bakin gadon tace’’Manu ya akayi kika bari ya kira Dr bayan gamu da soon to be consultant a gida?Yasmeen matso ki duba ta Mommy tana jira,ta ce in ta kama sai a wuce asibiti.

Gaba d’aya hankalinta har mu duk a tashe yake…a

man da ta yi ai dole a dubata da wurwuri in ma k’arin ruwa ne a yi mata dan na san she’s weak’’.

Shiruu Yashjub ya yi kafin chan ya d’ago ya cewa Yasmeen d’in “matso mana mai kike jira?”

Sai kuma ya kalli Ya’isha yace

‘’ki je ki cewa Mommy jikin nata

fa da sauk’i ta kwantar da hankalinta”.

Murmushi duk suka yi banda Yahanasu da gaba d’aya hankalin ta yake a tashe

Har ga Allah ta gama shiryawa akan ko da ace cikin ne to za ta san yadda za ta yi ta lallab’a Yashjub su b’oye har sai ya d’an yi kwari

tukunna a fad’a

amma gashi yanzu su ne ma za su fara sani

Sannan yadda suka dad’e a saman nan ba su sauk’k’o ba bata da tantama plan suka gama had’awa….

Tana wannan tunanin ta ga Yasmeen ta matsa kusa da su ta shiga duba Mannubiya dama har da abun au

na hawan jinin ta ta taho da ragowar abubuwa.

Duk wani gwajin da ya kamata sai da Yasmeen ta yi mata.

….Tun a kan pulse d’in Mannubiya Yasmeen ta jiyo alamun ciki ga kuma ragowar gwaje gwajen da ta yi mata waenda suma suke nuni da hakan

shiyasa tashi d’

aya gaban ta ya yanke ya shiga fad’uwa dan ba ta san ya za ta yi ba sannan ba ta san ma ta Ina za ta fara ba…

Cike da murmushi da tsantsar farin cikin da ya baiyyana a iyaka kan fuskar ta Yasira ta matso ta ce ‘’good news ko?pls tell me I’m about to bec

ome an aunt.’’

Ta k’arashe maganar tata da y’ar guntuwar dariya kwance a kan fuskarta.

Murmushi Yashjub ma ya yi yana jira kawai ya ji ance masa Mannubiya na d’auke da ciki ne amma instead sai kunnuwansa suka jiyo masa muryar Yasmeen d’in tana cewa’’A’

a gaskiya ba ciki bane ba, dan in da ace shine da zan ji yanayin pulse d’in ta ya d’an chanja sannan ragowar gwaje gwajen da na yi mata suma duk ba su yi detecting pregnancy ba,inaga gajiya ne da fever…

But first bari in fara yi mata allurar tsaida aman n

an dan da na duba idonta gaskiya she’s very weak sannan ba ruwa a jikin nata zata iya fainting anytime from now.!”

Gaba d’ayan su jikinsu sanyi ya yi especially ma Yashjub wanda ya gama kwallafa rai ya gama yarda akan kawai cikin ne, ganin yadda Mannubi

yan ta yi ne ya sa cikin son bata kwarin guiwa ya samu dakyar ya aro jarumta yace’’ok,dama nima na yi tunanin gajiyar ce, a ina za’a siyo allurar?

A samu a yi mata da wuri a samu ta d’an ci wani abun ta kwanta ko?”

Cikin tarar numfashinsa Yahanasu tace

‘’Ina ga gara dai a jira Doctor d’in ya zo shima ya dubata tun da kaga shi Babba ne!

sai a san da me da me ya kamata a bata.”

Da sauri Yasira tace ‘’ba ki ji abuna itama Yasmeen d’in tace ba?

Iyaka allurar tsaida amai za ta yi mata saboda itace emerge

ncy ana buk’atar a tsayar da gaggawa.’’

Cikin katseta Yahanasu tace’’Yasira allurar tsaida amai fa tanada k’arfi sosai! ki bari a yi kwak’kwaran bincike kafin a fara d’irka mata abubuwa’’

Murmushi Yasmeen ta yi sannan tace”Na yi duk gwaje gwaje fa

In da ace akwai ciki ko na sati d’aya ne to da zan gani zan kuma fahimta, kar ki manta Gynea na yi specializing a.

Also allurar da zan yi mata yanzu ba ta da wani k’arfi iyaka tsayar da aman za ta yi.’’

Zuwa yanzu ran Yahanasu ya b’aci kuma ta sake tab

batarwa akwai abunda suka shirya dan haka tace

‘’Ai nima ba cewa na yi ciki ba cewa na yi ki tsaya dai a yi kwakkwaran bincike dan wannan gwajin da kika yi bai kai ace ya yi detecting komai b..’’

A hankali cikin katseta Yashjub yace

‘’Yaha Mommy ce t

a aiko su kar k….’’

Juyawa kawai ya ga Yahanasun ta yi ta fice daga d’akin da alamun ranta ya b’aci.

Shiruu kawai Yashjub ya yi,

sam bai ji dad’in abun da ya yi mata ba amma kuma ba ya so Mommy ta yi fushi..

Shiyasa ya bari akan idan su

Yasmeen d’in

sun gama zai je ya bata hak’uri,gara ace ita ta yi fushi ta bar case d’in akan su Yasmeen su je su gayawa Mommy ta ga kamar ya sace mata guiwa ne daganan ta yi fushi.

Tunda sun ce ita ta turo su kuma ta na chan hankalinta a tashe ya san idan ya hana su b

azata ji dad’i ba…

Gara Yahanasu ya san ita za ta fahimcesa idan ya je ya bata hak’uri zuwa anjima…

As far as he knows,su Yasmeen ba za su tab’a yi masa k’arya ba kuma ba za su cutar da shi ko Mannubiya ba…dan ko kwanaki da aka yi ta case yanzu ya fahi

mci saboda Kausar suka yi ta abubuwa amma yanzu gashi da ya dage da addu’a ai sun shiryu sun dawo saiti dan yadda suke yiwa Manubiya tun zuwansu har kawo yanzu ya ji dad’i kwarai ya fahimci suna sonta yanzu….shiyasa har ga Allah tunda suka ce ‘babu ciki’ya

yarda kuma ba ya so ma wani likitan ya zo ya kuma duba ta ya ce ‘babu cikin’ saboda shi kad’ai ya san kalar disappointment d’in da ya ji a lokacin da Yasmeen tace ‘babu cikin’….

ya san kuma a b’angaren Manubiya itama haka ne…..

Da waya Yasmeen ta kira

Yusra tace ‘’dan Allah ta duba cikin bed side d’inta na left akwai wata green Leda ta d’auko ta kawo mata

Allurar tsayar da amai ne a ciki da su paracetamol”.

…Already dama sun riga sun gama had’a plan d’insu shiyasa suna gama wayar su Baba larai suk

a yi sauri suka bawa Yusran ledar allurorin da su Yasira suka je suka siyo,ta karb’a ta sauk’o ta nufi d’akin Yahanasu da shi….

Ita dai Mannubiya ta yi shiruuu tana ta istighfari a cikin ranta dan lokacin da Yasmeen tace ‘bata da ciki!’ kad’an ya rage b

a ta yi sab’o ba….haka shima Yashjub ya yi shiruuu ran sa a mugun dagule….yayinda Yasmeen take jin inama akwai wani waje da za ta gudu ta b’uya dan wallahi har ga Allah ba ta son yin allurar! ba ta son ta kashewa Yashjub Baby!,she can’t believe wai yau ita

ce take shirin yin kisan kai,that too Babyn yayanta.!

Suna a haka Yusra ta yi sallama ta shigo ta mik’awa Yasmeen laidar allurorin.MANNUBIYA

(Book 2)

Page 28

Na

Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Y

ahanasu tana fita ta nufi sama side d’in Daddy…dan wallahi sai dai fa a yi ta! a cikin gidan nan amma ba za ta bari Yasmeen ta d’irkawa Mannubiya allura ba tare da an tsaya likitan kwarai ya zo ya dubata ba

Ya za’ayi mace tana irin wannan aman ga jiri ga

fever sannan kuma amarya amma tace wani ‘ba ta da ciki!’

Ta san ba ta yi aure ba kuma bata da experience amma tanada shekaru da hankalin da zata iya banbance mace mai ciki da mara ciki.

In banda tsabar rainin wayo a ta ina aka tab’a tabbatr da ciki da r

ashin sa ba tare da an yi test na jini ko na fitsari ba!…

Ba b’oye b’oye tana zuwa ta cewa Daddy “ga Yasmeen chan za ta yiwa Mannubiya allurar tsaida amai ba tare da ta duba ta ko ta bari Likitan da aka kira ya zo ya dubata ba.”

“Kuma allurar tana da k

’arfi sosai!ba a cika son yin ta anyhow ba”.

Shiruu Daddy ya yi kafin ya mik’e ya ce “mu je wajen nasu.”

Kusan a tare Daddy suka k’arasa bakin k’ofar shi da Mommy wadda duk yadda ta so yin fushi ta bar Yasira ta yi dealing da Yasmeen sam ta kasa hak

’ura sai da ta sak’k’o a yi komai a gaban idanunta.

Tun ba ma da Yasmeen d’in ta kira Yusra tana cewa ta kawo mata ledar ba dan a lokacin sai da Mommyn tasa Yusra ta tambayeta tace “akwai?”

Ita kuma tace mata ‘yh’kawai ba tare da ta bari su Yashjub d’in

sun gane ba.

Shiyasa sam ta gagara sukuni ta sake burkicewa ta sauk’o ta nufi d’akin Yahansun a gigice a hakan ma wai Baaba larai ta ce mata ta nutsu ta yi controlling kanta…

Su Daddy suna shiga itama ta shige

dai dai Yasmeen tana shirin zurmuk’awa

Manubiya allura a cinyar hannu.

D’an dakatawa ta yi ta tsaya kawai tana kallon su

Suna had’a ido da Daddy yace

‘’Yasmeen an yi duk wasu gwaje gwaje da suka kamata ne???ku je asibiti a yi test har na jini mana’’

Wani kalar kallo Yassira ta shiga jif

an Yahanasu da shi dan ta san ita ta je ta kirawo Daddy.

Mommy kuwa ta fi jin haushin Yasmeen! ji takeyi kamar ta je ta rufe ta da mahaukacin duka dan in da ba ta tsaya delay ba da tuni komai ya kammala.

Sannan yanzu da ta ga sun shigo tun da har ta riga

ta kai allurar kan cinyar hannun Manubiyan meye nata na wani tsayawa ta d’ago instead of kawai ta soka ta juye mata ruwan allurar..dama chan ba ta son yi ai shiyasa ta lalata musu komai!…

Har wani duhu duhu take gani tsabar tashin hankali,ganin bakin Yas

ira take yi yana motsi alamar tana yiwa Daddy magana amman ba ta san ma mai take fad’a ba dan ba ta jin komai tsabar masifar da ta shiga.

Tana k’ok’arin ta bud’e Baki ta san dabarar da za ta yi su samu Daddy ya bari su yi allurar cikin sauk’i ta ji muryar

Yash yana cewa

‘’Ok,d’an bani 2 minutes,’’ sai da ta kalle sa tukunna ta fahimci waya yake yi,sai da ya ajjiye wayar tukunna ya kalli Daddy yace‘’Am Daddy family Dr ya zo

Ince ya bari shikenan tun da kace asibiti za’aje ko?’’

‘’No,bar shi ya shigo

d’in kawai tun da ya riga ya zo.Ya’isha je ki shigo da shi

Idan ya tafi sai a wuce asibitin,ba dad’i ka kirawo babban mutum ya baro aiki ya zo kuma a ce ya koma.’’

Wata kalar zufar da ta ketowa Mommy sai da Yahanasu ta ganta b’aro b’aro a kan goshinta

tsabar yawan ta.

Cikin in ina da rashin sanin tudun dafawa Mommyn tace

‘’Daddy nake ganin gara a ce ya tafi

Namiji ne bai kamata ya tab’a matar aureba….”

“Ya’isha je ki shigo da shi mana!’’

Daddy ya fad’a da d’an k’arfi kamar ma bai san Mommyn t

ana magana ba dan ya fara k’ulewa da ita

Ya ga alama tana neman zarce gona da iri tun lokacin da ya goya mata baya a kan case d’in Yashjub da su Yasira ya bata goyon baya ita da su Yasira,ya ga alamar kamar so take ya dinga biyeta akan komai….bayan shi b

a wai bayan ta ya bi ba ko a wannan lokacin yana da nasa dalilin shiyasa….

Ganin har ya na shirin fita amma su basu da niyyar fita ne ya sa cikin kakkausar murya ya kalle su yace

“A bar Yahanasu Manubiya Yashjub da Yasmeen a d’akin kowa ya fito….jikin

Mommy har karkarwa yake yi zuwa yanzu..

ta riga ta san one more move daga gare ta to tsaf Daddy zai b’aro jirginta shiyasa kawai ta hak’ura ta yi kalmar shahada ta fice ta wuce sama d’akin ta direct.

Ita dai Mannubiya ba da ban Daddy ne da kan sa yac

e ‘a duba ta’ ba to da babu abun da zai sa ta kuma tsayawa a duba ta dan ba ta son ta sake ganin wani disappoint d’in a idananun Yashjub…



Su Daddy suna tsaye a parlourn Ya’isha ta shigo da Doctor,suna gama gaisawa da Daddy ta wuce da Doctor d’in ta ka

i sa har d’akin ta fito, itama ta nemi guri ta zauna hankalinta chaaa a tashe.

A Chan d’akin kuwa Dr yana shiga suka hau gaisawa da Yashjub sai da ya kuma yi masa Allah ya sanya alkhairi tukunna cikin zolaya yace

‘’Ai ba wani abun tada hankali bane

amai is a normal thing a pregnancy but bara dai in duba .”

Shiruu duk suka yi kafin ya fara dubata sai da ya kuma tambayar abubuwan da suke damunta da date na last period d’inta ya ji tukunna ya matsa kusa da ita

Kamar yadda Yasmeen ta ga alamun cikin

a tattare da ita hakanan shima amma bai fad’a musu ba

Instead sai ya zaro pt a cikin box d’insa ya basu yace “gashi ta je ta gwada”

Cikin son fahimtar da shi Yashjub yace “Yasmeen fa ta duba ta yanzu ba ciki ba ne”

Da d’an mamaki Dr d’in ya juya y

a kalli Yasmeen kafin yace “da me kika duba ta??”

Dibi dibi ta hau yi kafin tace ‘’ban ji a pulse d’inta ba sannan na ga bp d’inta bai yi kamar na masu ciki ba”

ta fad’i hakan tana addu’ar Allah ya sa kar ya haddasa mata case.

Sai da ya k’ura mata ido

sosai

kafin cikin d’an b’acin rai yace ‘’Doctor Yasmeen kin san abun da kike yi kuwa??a bp da pulse dama ake ganin ciki???

What else ki ka yi bayan BP d’in da kika gwada??”.

Cikin nemawa kanta mafita tace

‘’Duk na gigice ne na ga tanata amai I wasn’

t myself shiyasa..gaba d’aya duk ta bani tausayi…”

Cikin fushi yace

‘’Really??!,yanzu idan aka kawo miki family member d’in ki in a critical condition Ashe ba za ki iya yin abun da ya kamata ba?are u really this weak!!!”

Ahankali Manubiya ta d’an d

afe kanta sakamokon sarawar da yake yi mata tace “wash!!!”

Sai da ya gama watsawa Yasmeen kallo tukunna ya juya ga su Yashjub ya shiga yi musu bayanin yadda za su yi amfani da pt d’in.

Suna wucewa cikin toilet d’in ya juya ga Yasmeen ya shiga yi mata fad

’a had’e da yi mata nuni da abubuwan da ya kamata ta fara yi next time idan an kawo mata patient a irin wannan condition d’in Sannan yace ta cire fargaba ta daina saurin giigicewe dan za ta jawa kanta problem dan ko shi tbh yau kam he is very disappointed

in her!”

Su Yashjub suna shiga toilet d’in Manubiya ta kalle sa tace

‘’Ko dai za mu ce masa mun yi kawai?

Ba na son gwadawa ni kam har ga Allah.’’

Ta fad’i hakan tana hard’e hannuwanta a k’irji.

A hankali Yashjub wanda ya samu hope da kwarin guiw

a daga jin yadda Doctor d’in yace “Yasmeen ba ta gwada yadda ya kamata ba”ya matso kusa da ita yace

“Ki taimaka ki gwada! pls…for me?’’

Shiruu ta yi ta d’an sunkuyar da kanta k’asa tace “to ka fita”

Wata dariya yayi yace “Yarinya ba ki da wayo ashe

….”

…Daki daki yadda aka nuna musu haka suka yi.

Dayake doctor d’in ya ce “idan sun gwada su ajjiye for five minutes saboda result d’in ya fito sosai”

Ya sa Yashjub ya karb’a ya ce bari ya kai kan window su jira time…..

Daga ita har shi gabansu fad’u

wa yake yi

Haka ya nufi window da tsinken da niyyar ajjiyewa idanunsa a kai

Kawai ya ga layi na biyu ya fara kamawa

Wani irin mahaukacin bugawa k’irjin sa yayi

Da wani irin sauri ya juyo ya koma gareta ya tsaya a gabanta ya ma kasa magana kawai ya k

afe abun yana ganin yadda layi na biyun yake kuma fitowa yana turuwa yana dad’a baiyyana.

Ganin yadda ya kad’u sannan ya mayar da kafatarin hankalinsa ga tsinken ne ya sa Manubiya matsowa tace ‘’mai kake kallo?’’k’irjinta yana d’an bugawa.

Ahankali ya d’

ago lumsassun idanuwansa da suka cika taf da kwallah ya kafe ta da su kafin ya juyar da fuskar tsinken gareta wanda a yanzu jajayen layuka biyu suka fito rad’au!Hannun ya na rawa ya saita mata shi a dai dai saitin fuskarta a lokaci guda kuma hawayen da s

uka tarar masa a idanu suka samu damar b’alle masa,a take yayi mata wata mahaukaciyar runguma ya fashe da wani irin kuka…..

Ita kanta Manubiya hawaye ne suka b’alle mata.

A take wani sanyin farin ciki da annashuwa mara misaltuwa ya mamaye masoyan…lamoo t

a yi a jikin sa tana hawaye tana jin yadda yake kuka bilhakki da gaskiya jikinsa har karkarwa yake yi sannan zuciyarsa tana wani irin bugu..

Sun jima a haka kafin Manubiya ta d’an fara k’ok’arin zamewa a hankali tace

‘’Godiya za mu yi wa Ubangiji….’’

Ahankali ya sake matseta a jikinsa yace

“Tun d’azu nake godiya,Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah ya rabbi…bayan fatar baki da zuciya ina so in yi godiya ga Ubangijina…..’’

Murmushi ta yi a hankali tace ‘ka yi ta sadaka’’

Sai da ya sauk’e wa

ta k’ak’k’arfar ajiyar zuciya ya tsaida kuka da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login