Showing 186001 words to 189000 words out of 259716 words
tsananin tausayinta da kunyarta yake ji….
Wayarsa ce ta d’auki k’ara a karo na hud’u dan haka ya d’ago da niyyar kashe
wayar gaba d’aya amma sai yaga ‘Honey’ a kan screen d’in yana yawo….
Wasu zafafan hawaye ne suka shiga bin fuskarsa hannunsa ya fara karkarwa k’irjinsa ya shiga dukan uku uku.
Har ta katse bai d’auka ba haka ta sake kira ta katse daga k’arshe ta turo ma
sa message”Baby Ina wuni hope you are fine..d’azu ka kira Ina barci yanzu na farka..ba ka d’aukan wayar!hope all is well I need you I want to see you plss.”
Yana gama karantawa ya yi jifa da wayar ya mik’e ya fad’a toilet ya sakar wa kansa ruwan sanyi yan
a wani Irin huci kansa yana wani irin juyawa….
Ya fi awa d’aya a cikin band’akin da kyar ya yi wanka ya yi alwallah ya fito yana istighfari….jallabiyarsa ta riga ta jike tana band’akin shiyasa sai da ya jira ya yi order aka kawo masa tukunna ya mik’e ya
tada ik’ama yana ta istighfari dan bai tashi tuna bai yi sallar Magrib da isha ba sai da ya gama wanka ya fara alwallah saboda bai tab’a kaiwa war haka bai yi ba shiyasa ya manta…..
Yana idar da sallar ya tashi ya fara jero nafilfili,ko da ya gama ma k
aratun Al’kur’ani ya zauna yayi sai wajajen 1 na dare tukunna ya d’an samu zuciyarsa ta fara sanyi…
Wayarsa ya d’auka…
Ya danna dial a number Manu ya kashe yafi sau shidda kafin daga baya kawai ya rufe ido ya danna ya runtse idanuwansa zuciyarsa tana w
ani kalar mahaukacin bugawa.
“Assalam alaikom”
Ya jiyo muryarta mai dad’in sauraro da kwantar da hankali.
A hankali ya lumshe idanunsa hawaye suka shiga zirara kafin ya ce”ameen wa alaiki assalam,ba ki yi barci ba har yanzu?”
A hankali
Cikin firg
ice tace”Ya Yash kaima kuka kake yi?har yanzu?
killace kanka da k’aurace mini ba shine zai yi mana maganin damuwar mu ba.
Na kasa nutsuwa hankalina a tashe! ban yi tunanin za ka gujemini a irin wannan lokacin da nake matuk’ar buk’atarka ba Ya Yash.”
Kuka sosai ta ji ya saka ya kashe wayar,yana kashewa ya yi switch off d’inta gaba d’aya.
Ta kira sa ya fi sau ashirin amma switch off dan haka hankali ta ya sake tashi!ta fara wasu Irin hawaye masu zafi…ta shiga tashin hankali da firgici matuk’a a lokacin
da aka ce cikin jikinta ya fita amma dama ita 50%na damuwarta Yashjub ne…da farko ta d’auka fushi ya yi da ita bayan damuwar da yake a ciki shiyasa ya k’i zuwa gareta amma yanzu da suka yi waya tashi d’aya ta fahimci tsananin damuwa da tashin hankali ne s
uka sanya shi ya killace kansa ya k’i zuwa wajenta…ta san Yashjub yana sonta yana son cikin jikinta amma ba ta yi tunanin abun zai kai ga haka don wanda ya basu ya amsa ba.
Bayan ya gama waya da Manubiya da kamar awa d’aya da rabi lokacin ya san ta hak’
ura ta daina gwada layukansa ya kunna d’ayar wayar sa ya kira Yahanasu,bai damu da dare ko kuma kar ya tasheta a barci ba haka nan ya yi ta kira yana sake kira har sai da ta d’auka cikin magagin bacci a d’an rikice tace”Assalam alaikom”
“Yash Ina ka tafi
ne an je har gidanka ba ka nan kuma ba ka d’aukar waya?”
“Yaha ki taimakeni ki yiwa Manubiya bayanin abunda ya faru ba zan iya ba ba kuma zan iya b’oye mata ba..sannan mun riga mun yiwa juna alk’awarin babu b’oye b’oye a tsakaninmu…kuma na san ko yaya
mutum ya kai ga iya b’oye sirri dole sai an samu leakage idan ta ji a wani wajen za ta karaya sannan ba za ta sake yarda da ni ba…ki yi mata bayani ki
Ba ta hak’uri ki fahimtar da ita on my behalf Ina son ganinta amma ba zan iya fuskantar ta ba i’m shy af
raid disturbed and scared………”
A hankali Yaha ta share hawayenta tace”slow down Yash….!”
Kafin ta mik’e ta zauna ta na mai kunna bedside lamp tace”maganar b’oye mata kam dama bai taso ba dan na san ko da gangan sai an samu masu gaya mata!Tunda abu ne wa
nda kowa ya sani…
Ka kwantar da hankalinka InshaaAllah Manubiya za ta fahimceka na ji dad’i matuk’a da ka ce ba za ka b’oye mata ba saboda b’oye b’oye babu abunda yake janyowa sai b’arna sannan mai gaskiya yana tare da Allah ba zai tab’a tab’ewa ba.!
Ins
haaAllah gobe da safen zan shirye in je in sameta,ka kwantar da hankalinka Kausar za ta girbi abunda ta shuka Allah yana tare da kai…”
A hankali yace”inshaaAllah”
yana jin zuciyarsa tana wani irin tafarfasa…
Sai da ta sake kwantar masa da hankali tace”y
a yi ta sallah da nafiloli idan ya kasa bacci komai zai yi daidai inshaaAllah sannan idan ya samu hali gobe da safe ya kira Daddy saboda hankalinsa a mugun tashe yake…….”
Daga haka suka yi sallama yana mai jin sassaucin abunda yake ji kafin su yi magana….
Tabbas Yahanasu is one of the best gift da Ubangiji ya sako cikin rayuwarsa tana tsaya masa a akan komai tana son farincikin sa sannan ta yi trusting d’insa d’ari bisa d’ari!kalli yanzu he don’t even have to explain himself tashi d’aya ta san sharrin Kausa
r ne….Addu’a ya fara yi a cikin ransa Allah Ubangiji ya sa Manubiya ma ta kawar da kishi Yahansu tana yi mata bayani ta aminta da shi ta yafe komai……..
A b’angaren Kausar kuwa har chan cikin dare ba ta farfad’o ba.
Yasmeen ta yi mata duk abunda ya
kamar ta yi dressing mata ciwukan fuskarta amma idan
ka ganta in ba cikakken sani ka yi mata ba tou ba lalle ka shaidata ba dan fuskarta ta kumbura ta yi sutu sutu ga ciwuka ta koina kamar ba ita ba.
In banda zubar hawaye babu abunda Mommy take yi…da
kyar su Yasira suka lallab’ata aka bar Kausar a gida
dan Yasmeen tace musu”she’s fine kuma idan aka kaita asibiti a haka case ne sannan in akayi bincike aka gano Yashjub zai iya shiga matsala.”
Dakyar Mommy ta yadda
amma da cewa ta yi a kaita asibitin
a haka ya shiga matsalar shi ya sani ita ba damuwar ta bace ba.”
Dan ba kad’an ba ta ji mugun mugun zafin halin da Kausar d’in ta ke ciki ba kad’an ba
dukda ta san maybe dagaske Yash d’in yake tricking d’insa Kausar d’in ta yi ya kwanta da ita amma sam
ita ba wannan ne a gabanta ba! Bata ga dalilin da zai sanya ya illata mata Yarinya haka ba wannan ai rashin imani ne!Yarinya y’ar amana!yanzu inda za a tashi uwarta a nuna mata Kausar unconscious da fuskarta haka
ai batasan da wanne ido zata kalletaba r
anar gobe k’iyama.
Da Mommy da Yassir sun fi kowa tashin hankali a cikin d’akin sai Yadira wadda yanayin Kausar d’in ya fara bata tsoro itama ta fashe da kuka junior yake ta faman lallashinta.
Yassir har ya fara shirye shiryen appointment dan yace “
tana bud’e ido za su bar k’asar!”
Saboda tabbas yadda kumatunta da gefen idanunta suka fashe ya san sai an yi wani abun a wajen…dukda ba shi da enough kud’i but zai
ranta a wajen Abokan sa a
je a yi mata aiki kafin ya samu ta warke tukunna ya dawo t
a kan Yash dan bai ma san ta Ina zai fara ba!
ya yi taking nashi by surprise sam bai yi tunanin zai
Illata masa Kausar har haka ba…dukda ya san end d’insa ya zo dan yanzu Manubiya da Daddy za su juya masa baya saboda ya gama shiryawa da kansa zai tura m
ata message ya gaya mata komai!amma dole Yashjub ya yi paying for dukan nan da ya yiwa Kausar wallahi,dole!…
Ummi ce kawai babu a d’akin sai Daddy amma kaff gaba d’ayansu suna d’akin.
Junior kawai kallon Yassir yake yi…a yadda ya d’aga hankalinsa tabb
as ya tonawa kansa asiri ne a idanun Junior saboda bai kamata ace ba ya fushi da Kausar a yanzu ba bayan abunda idanunsa suka gane masa hours before now.
Suna tsattsaye wasun su a zazzaune a kanta ta d’an fara motsi kafin a hankali ta dawo cikin haiyyac
in ta!
Sai dai ba ta bud’e ido ba…
Ta san ta daku dan fuskarta in ba da kyar ba sai ta had’a da plastic surgery
amman kuma ba ta jin akwai ranar da ta tab’a tsintar kanta cikin tsananin farin ciki Irin wagga rana!…dan ta riga ta san nan da 10 days insh
aaAllah burin ta zai cika
ko da balai ko ta wanne Hali!
Batajin alamun ciwo ko wani abun a mararta kuma dama ta san Yashjub bai sameta a wajen ba dan haka tana da yak’inin cikin ta yana nan daram!. Yo ai ko ya fita sai ta sake yin wani ta lik’awa Yash!
yadda aka kamasu d’innan is the most amazing thing da za ta rik’e as weapon ta kowanne fanni.
Ta ji dad’i matuk’a gameda yadda plan d’insu ya tafi daidai babu targard’a.
Sannan bata wani damu da Manubiya ba dan ba Manubiya ba ko auren irinta uku ne da Ya
sh wuyarta ta auresa Wallahi sai ta yi waje da ita!.
Mommy dake daff da kanta ce ta d’an matso tace “Kausar”.
Ahankali ta d’an fara k’ok’arin bud’e idanunta…
Duk matsowa sukayi sai da ta d’an bud’e idon guda d’aya saboda d’ayan ba zai bud’u ba!
Tu
kunna gaba d’ayansu suka ce
“Alhamdulillah”.
Da sauri Yassir ya je ta wajen kanta ya d’ago kanta ya d’aura a kan cinyar sa
Yace “Yasmeen d’an sake duba ta!idan babu emergency
Inaga yanzu za mu fara shirin wucewa kawai!na san dole flight d’inmu ta A
buja zai tashi”sam bai damu da yadda fuskarta ta kumbura kamannin ta suka sauya ba shi dai kawai ya san Kausar d’insa ce dan haka yanason ta a ko wanne irin yanayi.
Ajiyar zuciya Munirat ta sauk’e tanajin yadda zuciyarta take tafarfasa..a hankali
tace
“Allah ya k’ara sauk’i”
Daga haka ta juya ta fita da sauri.
Ba wanda ma ya san ta fita ko ya jita dan tun d’azun ma ba wanda ya kula ta babu wanda
ya damu da existence d’inta a d’akin.
A b’angaren Munirat d’in itama ba wajen su ta zo ba dan in band
a gaba harara da bak’ak’en maganganu babu abunda yake shiga tsakaninta da su Kausar d’in…Yassir ta biyo lokacin da taga sun kinkimo Kausar an kaita d’akinta ya fito ya fad’a d’akinsa shine ta tsaya akan idan ya fito su yi magana amma ko da ya fito sai ya d
’auke kai kawai ya afka side d’in Kausar ya wani tamke fuska dan karma ta kula sa..itan ma ta yi alk’awarin fita daga harkarsa kwanakin baya amma babu yadda ta ita ne saboda yanzu haka maganar da take so su yi d’in is very important shiysa ta tsaya tayi ta
jiran fitowarsa jin shiru shine itama ta shiga side d’in Kausar d’in….
A yadda taga yake d’innan ta san ba zai saurareta ba shine ta hak’ura ta tsara zata nemo numbersa kawai ta tura masa message ta san zai gani….
Sarai ya lura da ita!tana fita ya yi ts
aki ya ci gaba da dudduba Kausar yana tambayarta Ina ne yake yi mata ciwo…
Ba abunda ya fi d’aurewa su Mommy Kai kamar yadda sam Yassir bai wani damu ko ya nuna jin haushi a kan abunda ya faru tsakanin Kausar da Yash ba shi ta lafiyar ta ma yake yi..
K
o da ya yi fushi ya fita d’azun suna zuwa suka tarar da shi a d’akin Kausar d’in yana safa da marwa…sun san dole zai tausaya mata amma
kuma sam babu alamun kishi ko wani jin haushi a tare da shi
ko irin kishin da ya nuna a d’akin Yashjub sam ba su ga a
lamarshi a tare da shi ba…dukda tace masa forcing d’inta Yashjub ya yi but ya kamata ya ci gaba da jin haushi ko da d’an k’ank’ani ne kamar yadda ya nuna a wajen dinner earlier da ta tafi side d’in Yash d’in da k’afarta.
Gyaran murya Mommy ta yi kafin t
ace”Yassir ka bar batun tafiya tukunna yanzu a ji da abunda ya faru..indai ba so kake Daddynku ya fusata da kai ba to ka ja bakinka ka yi shiru ka koma gefe tun kafin a huce a kanka.”
Zai yi magana Junior yace”kana fara batun fita da ita waje ma na san ts
af zai saka question mark akan yadda sam ba ka yi kishin komai ba!”
Ya fad’i hakan idanunwansa cikin na Yassir wanda ya juyo ya zuba masa su shima….lumshe idonta guda d’aya Kausar ta yi dama so take ta yiwa Yassir sign ya gane ya dena abubuwan da yake yi
tun kafin ya tona musu asiri…Aikuwa gashi har an fara magana…
Shima Yassir d’in sai yanzu ya d’au haske dan haka ya ce “okay Mommy”kawai..daga haka ya mik’e sai da ya yiwa junior wani kallo tukunna ya sa kai ya fice saboda ya ji haushi da mamakin yadda d’
an uwa kuma Abokin nasa ya so kunce masa zani a kasuwa! Ya san Junior ya sanshi ciki da waje duk abunda ya yi yana ganewa ya san wannan d’in ka ya gano da gashi har yana shirin yi masa b’aramb’atama a bainar Nasi amma ba komai za su had’u zai yi maganin sa
dan ya lura ya fahimci komai kuma ya san yadda yake ji da yashjub dan haka dole ya yi silencing d’insa da wur wuri tun kafin ya janyo musu ruwa.
Washegari da sassafe Yahanasu ta tashi ta shirya tana shirin tana fargaba…if not Yash ya zab’eta ne kuma
ta ji tausayinsa jiya wallahi da ba ta ga dalilin da zai sanya ta zamo itace wadda za ta gayawa Manubiya wanna mummunan al’amari ba.
Ummi ce ta yi breakfast suka shirya ita da Yahanasu suka nufi asibitin za su chanji Hajiya Mama da Siyama…
A d’akin
suka tarar da Yashjub ga mamakinsu…lokacin Najeeb har ya je ya d’auki Siyama da Hajiya Mama zai maida su gida,ba k’aramin dad’i Hajiya Mama ta ji ba da ta ga Yashjub ya zo haka itama Siyama saboda dama tana ta addu’a Akan Allah ya sa ba fushi ya yi ko ya
k’ullaci Manu ba.Ta san dole da zafi shiyasa ta d’aga masa k’afa ya d’an huce gudun kar ta jagula abun hakanan ta yi ta addu’a gashi kuwa yanzu ya zo…..
Shi ya tarar da su Hajiya Mama su Ummi kuwa ba su same su ba iyaka Yashjub d’in suka tarar.
Suna za
une Manubiya a kan gado shi kuma a gefenta ya rik’e hannunta ya sunkuyar da kansa k’asa ita kuma tana video call da Jiddah wadda Manubiya ta ji matuk’ar dad’in ganin yadda k’anwar tata ta yi k’iba ta yi fresh a cikin kwanaki k’alilan alamun Hankalinta a kw
ance yake.
Yadda su Ummi suka ga walwala da murmushi a kan fuskarta ya sa suka fahimci ba ta ji komai ba.
Gaisawa suka yi da Yash da ga haka ya mik’e ya k’arasa ya shiga had’a mata Breakfast Yayinda ita kuma suka yi sallama daJidda bayan sun gaisa da s
u Yaha ta ajjiye wayar suka shiga gaisawa da su Ummi.
Yana gamawa ya k’arasa ya ajjiye mata,ya fara k’ok’arin bata tace masa”ai Likita yace akwai allurar da zai yi mata kafin ta ci abinci”
“Okay”kawai yace ya d’an yi mata smiling kafin ya mik’e ya fi
ta domin kiran Doctor d’in.
Yana fita yaha ta zauna a wajen da ya tashi tace”MashaaAllah Jidda ta yi fresh abunta,Al’ameen ya iya kiwo”
Dariya duk suka yi har Ummi kafin Manubiya ta kalli Yahanasu tace”Yaha akwai abunda yake damunsa ne bayaga al’amarin
da ya faru da ni? Na ga yanayinsa gaba d’aya ya sauya.”
Shiruu ta yi ta d’an k’ura mata ido kafin tace”za mu yi magana anjima,ki kwantar da hankalinki”
Daga haka ta yi sauri ta mik’e ta fice, ba itace Yashjub ba amma yunk’urin sanar da Manu da ta yi k
ad’ai a yanzu tashi d’aya k’irjinta ya fara dukan uku uku.
Kusan karo suka yi da shi dan tana fita shi kuma yana shirin yin knocking.
“Ina Doctor?”
“Yace yana zuwa”
Ajiyar zuciya Yahanasu ta sauk’e kafin tace”Yash Ina ga gara mu bari ta warke garau kaf
in mu sanar da ita also har ga Allah bana so in yi tarnishin walwalar da na gani a kan fuskarta.”
Jinjina kai ya yi kafin yace”abunda nima nake tunani kenan,da na shigo d’azu she was soo happy to see me ta ma kasa b’oye murnar ta,I don’t think zan iya l
alata farin cikin da nake gani a kan fuskarta ba zan iya fad’a ba Wallahi shiyasa kema dama na shirya akan zan ce miki ki yi shiru to Alhamdulillah tunanin mu ya zo d’aya.Mu bari mu koma gida sai a san abunyi dan tabbas kam ba zan b’oye mata har abada ba.”
Yahanasu ta bud’e baki za ta yi magana kenan suka jiyo k’arar fad’uwa sai kuma salatin Ummi…kafin ta fara cewa”Yashjub Yahanasu kuna Ina Ina likitan!!”dai dai ta bud’e k’ofa za ta fito a gigice suka yi kicib’is da su dan haka ta juya ta koma ita a tuna
ninta ma tare suke da likitan…
A rikice suma duk suka yi kan Manubiya da ta ke zube a k’asa yashe a tsakar d’akin…
Kasa tab’ata Yashjub ya yi tsabar tashin hankalin da tsoro
a mugun rikice ya rarumo gorar ruwa ya shiga yayyafa mata hannunsa yana wani i
rin karkarwa…ganin ta k’i motsi ne ya sa ya mik’e a gigice ya nufi k’ofar da niyyar sake kiran Likita suka yi karo,ba ma ya iya cewa kawai Manu