Showing 216001 words to 219000 words out of 259716 words

Chapter 73 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

62

gaskiyar lamari da kuma duk wasu abubuwan da ta aikata a b’oye su samu evidence a kanta ta yadda za su fi hukunta da hujja, dan tabbas ta san Mommy ta dad’e tana cutarsu ba tare da sun sani ba..to shi kuma Daddy gashi yanzu ya sa

ke k’ak’abawa Yashjub Kausar.

Ta san ba laifin su bane ba amma she can’t help it dole ta fusata saboda abun ya tab’ata sosai.Dan Auren Kausar da Yashjub kamar an sake kafe Mommy a cikin zuriarta ne….

Sallamar Junior ce ta katsewa Hajiya Mama tunan

in da take yi,

A hankali ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya ta kallesa tace”ba sa gidan ko?”

Jinjina kai ya yi yace”driver d’insa na samu yana tartare kayansa yace mini wai an sallameshi ne saboda Yash d’in yace masa “sun tashi daga gida”

Yau da asub

ah wai ya kaisu hotel d’azu kuma ya je ya d’aukesu ya kaisu airport,yace bai san jirgin Ina suka bi ba.

Ajiyar zuciya ta sauk’e tace masa”ba ni wayata”kawai.

Yana mik’a mata ta nemo number Daddy ta danna call ta kara a kunnenta.

Ko gaisuwarsa ba ta am

sa ba tace

“Yashjub ya tafi ba ya nan,ya turo mini message ya gaya mini abunda Khadija ta je gidansa ta yi Jiya,yace min dan Allah kar a nemesa.

Dan haka Ina mai baku umarnin kar wanda ya bibiyesa kamar yadda ya buk’ata,

ku bar shi ya huta da bala’in K

hadija da y’ay’anta.

Ka ja mata kunne ka jawa su Yasira kunne sannan ka gaya wa d’an uwanka shima ya sani.”

Tana gama fad’in haka ta kashe wayar ta ajjiye a gefe zuciyarta tana wani irin tafarfasa.

Daga wajen Hajiya mama direct gida Yahanasu ta nufa

dan tana son magana da Mommy yau kam ba za ta yi shiru ba!abun ya yi yawa.MANNUBIYA

(Book 2)

Page 40

Na

Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

A d’akin su Yadira ta same ta ita da su suna hira…

Tana shigo

wa duk suka d’ago suka kalleta sai kuma suka d’auke Kai babu wanda yace mata ci kanki hakanan suka ci gaba da hirar su,Mommy tana shirin yi mata magana ita Yahanasun ta riga ta ta hanyar cewa”Ina so za mu yi magana!”

Sai da gaban Baba larai ya yanke ya fa

d’i dan in ba da kyar ba a yadda ta ga Yahanasu yau kam tabbas za ta iya fasa mata kwai a wajen Mommy kuma ta san Mommyn za ta ji haushinta.

Kallon Yahanasu Mommy ta yi kafin ta d’an kalli Baba larai sai kuma ta mik’e ta nufi Yahanasu n ba tare da ta saur

ari

Yusra wadda take cewa”eh lallai rainin hankali ma kenan.”ba.

Duk idanu suka zuba musu Baki sake har suka fice daga d’akin.

Side d’in Mommy suka nufa suna shiga Mommyn ta kalleta tace”ya aka yi ??Yahanasu”.

Har ga Allah ta san bai kamata ta di

nga jin haka game da uwar da ta kawota duniya ba amma she can’t help it!

Wani Irin haushi da takaicin Mommy take ji,ba ma ta jin za ta iya tsayuwa su yi wata doguwar magana dan haka cikin k’aguwa da son barin inda take ta d’an matso kusa da ita tana kallo

n cikin idanunta tace”ki cewa Yashjub kin janye maganar tsinuwa sannan ki daina treatning d’insa da tsinuwa idan ba haka ba wallahi tallahi sai na gaya masa cewa ‘ba ke ce kika haife sa ba’!”.

Wani irin zabura Mommy ta yi jikinta ya d’au karkarwa gaba d

’aya ta fice a haiyyacinta tashi d’aya fuskarta tayi jazur.

D’an k’ura mata ido Yahanasu ta yi kafin tace”as I suspected..ba ki san na sani ba ko?to kuwa wannan karon Baba larai ta munafurce ki.”

Hawayen da suka zubo mata ne suka sanya ta yin shiru it

ama Mommyn hawaye ta ke yi sosai zuwa yanzu.

Da kyar Yahanasu ta tsayar da hawayenta ta goge fuskarta ta ce”A ranar da kuka dawo daga makarantar mu!a ranar da kuka je kuka had’a guiwa da principal d’inmu kuka saka ta shirgawa Mama k’arya kuka ce Daddy ne

ya fad’a!to a ranar ne na ji komai.

….” Tun lokacin da Mama ta fara zuwa wajena a makaranta na so in fad’a muku ke da Daddy amma sai ta ce mini ba ta so ku sani wanda a da laifinta na gani da ta nemi in b’oye muku amma da na ji abunda kuka yi kuka saka a

ka ce mata Daddyn yace! ne ya sanya na fahimci dalilinta na cewa in b’oye muku.

Tana zuwa wajena a kai a kai har ta fara yi mini maganar tana so za ta d’auke ni in zauna a wajenta zan bita?!’ni kuma na ce mata ‘eh’. A wannan lokacin shekaruna ba su haura

takwas a duniya ba amma sai na yi lissafin cewa idan na b’oye muku wannan al’amari to

kamar na munafurceku ne,dan haka na yanke shawarar gaya muku ke da Daddy saboda daga ke har shi kuna nuna min tsananin soyayya shiysa na ga rashin dacewar b’oye muku zan

cen.

Ina zuwa dai dai k’ofar d’akin ki na ji muyarki cikin fushi kina cewa”Larai!!wannan yana d’aya daga cikin dalilan da suka sanya na ce miki kar mu fitar da Khadijah har ma da mallan lawal d’in amma kika k’i yarda kika ce ba za ki iya bari su mutu ba!

Yanzu ai ga irinta nan inda ace Daddy ne ya fara jin labarin zuwan da Khadija take yi wajen Yahanasu ya san cewa ta na raye har yanzu ai da mun shiga uku!!!kuma dan mun ce wa principal ta ce mata ga abunda Daddyn yace ke kina tunanin za ta hak’ura ta dai

na bibiyar y’arta ne?dan kawai ance za a tona mata asiri?ina ce farrak’u kika ce kin yi mata da duk ahalin gidan nan sannan kin kafeta a duk inda take?to ya akayi ta fito?”

Kai na ne ya d’aure dan ban gama fahimtar me kike nufi ba sai da na ji batun Ba

ba larai tukunna na fahimta,ta inda take cewa”Kar ki damu akasi aka samu amma zan gyara sannan saboda Allah Mommu yanzu ace duk Irin taimakon da lawal ya yi mana sai mu barshi ya mutu??ba dan shi ba ai da tuni Khadija har yanzu tana tare da Imam…”

A lok

acin I was 8 amma tashi d’aya na fahimci abunda kuka yi na fahimci komai saboda a ko da yaushe cewa ake yi gobara ne ya kashe mahaifiyata kuma na tuna yadda ko shekara ba a yi ba Daddy yace mana kar wanda ya sake kiran ko da sunanta kuma akwai ranar da na

ji yana kuka yana cewa Hajiya mama da ya sani ya tsananta bincike da ya sani bai kunna musu wuta ba.

Shiyasa na fahimci komai na fahimci tabbas duk shirin ku ne ke da Baba larai.

So na yi in tuna muku asiri amma sai na ji kina cewa”shikenan na yarda da

ke amma gaskiya ya kamata ki yi Abu mai k’arfi wannan karon a kansu ki sake kafe ta a duk inda take inda Hali ko makwabta kar ta samu jin dad’in shiga saboda wallahi na tsorata matuk’a sannan inaga larai gara kawai in fito in gayawa Yahanasu gaskiya ta san

cewa ni ce na haifeta na san za ta fahimceni!kalli fa yadda Khadija take zuwa wajenta a b’oye a matsayin Mahaifiyarta itama kuma ta b’oye mana!

A gaskiya abun ya fara damuna kuma Ina tsoron kar ta girma abun nan da na yi kuma na yi shiru ya yi affecting

relationship d’ina da ita”

Ban yarda da abunda kunnuwana suka jiye mini ba sai da na ji Baba larai ta katse ki itama tana cewa”Khadija ki rufa mana asiri kar ki ja mana,kar ki je garin soyayya da k’ulaficin y’ar ki ki je ki tarwatsamu!!Wallahi ko da wa

sa idan aka san Yahanasu ce y’arki ba Yashjub ba to komai ya lalace mana kenan..kar ki yi tunanin idan kika gaya mata maganar za ta b’uya ni na san dole za ta fito dan haka ki ja bakinki ki yi shiru mu samu mu cimma burinmu tukunna sai mu san abunyi!as far

as I know Yahanasu tana gabanki za ki kula da abarki sannan babu wanda zai cutar miki da ita dan haka idan har zan baki shawara ki d’auka to ki ja bakinki ki yi shiru.

And again!yadda kike yi a gaban Daddy ki d’an rage har ma su Yasirar suma ki rage..jiy

a bakiga shock da mamakin da Daddy ya shiga ba da akace masa kin daki Yasira saboda Yahanasu kuma itama Yasira suna cin abinci ina jinta tana cewa Mommy ta fi son Yaha a kansu!!dan haka ki ja bakinki ki

Iya takunki tun kafin ki tonawa kanki asiri.”

…….

Hawayen da suke zubo mata sharkaff ta sa hannu ta goge kafin ta ci gaba da cewa”Ina jinta tana ce miki kar ki damu ko nan da shekara nawa ne indai kika gaya mini ke ce mahaifiyata ta asali ba zan guje ki ba kuma ba zan ji haushin ki ba,za ta yi mini kata

nga da mutane saboda gudun kar in yi k’awaye a gaba in fahimci duniya su zuga ni idanuna su waye in fahimci kin zalinci ni.

Sannan za ta rufe mini Baki saboda kar in gaya wa kowa na ga Mama sannan za ta rabani da Mama ba zan nemeta ba ta inda za ta yi min

i abunda ba iyaka maman kad’ai ba ban Isa in sake shiga jikin wani har mu yi sirri da su in kasa fad’a miki ba,nan k’arshen kuma tace”za ta yi abunda ke kad’ai za ta bari a jikina bayan ke babu wanda ya Isa ya shiga jikina ya san cikina komai kawai kika c

e zan bi ki in karb’a hannu bibbiyu ba zan yi jayayya ba.!

Saboda har abada ba za ki gaya wa Daddy gaskiyar tsakanina da ke ba gudun matsala,so idan kika yi mini haka za ki gaya min ke mahaifiyata ce zan amince in karb’eki

Hannu biyu kuma ba zan gaya wa

kowa ba ba zan kuma ji haushi ba!.

Da farko ce mata kika yi a’a amma da ta ci gaba da tsara ki Mommy saboda tsabar son kai da son zuciya tashi d’aya kika amince a yi mini duk wa’ennan abubuwan duk dan kar in tona miki asiri kuma kar in k’i amincewa da k

e as mahaifiyata a lokacin da kika gama tsara plan d’inki kika shirya karb’ata kika shirya gaya mini ni y’arki ce.”

Cikin kukan Yahansu ta ci gaba da cewa”sam ba ki yi tunanin hakan da kika yi mini zai iya shiga tsakani na da aure ba!.”ta k’arashe maganar

tata cikin tsananin fashewa da kuka kafin ta ci gaba da cewa

“Ina tsaye a wajen Ina kuka har Baba larai ta fito daga d’akin naki ta ganni, na san ta san idan kika ganni a haka kika fahimci na ji komai to za ki karaya ne kuma ta san akwai matsala,shiyasa

a wannan lokacin ta toshe mini Baki ta ja ni d’akin ta ta zaunar da ni.

Ita kanta na san a wannan lokacin ta sha mamaki na dan bata yi tunanin na yi wayo har haka ba saboda duk yadda ta so yi mini wayo ni kuma na k’i Bata k’ofa kuma ta fahimci na san kom

ai na kuma gane komai inaga shiyasa ta je ta yi tsafe tsafenta ba tare da ta sanar da ke cewa na ji komai ba.

Na san da ke da ita duk kun d’auka asirinku ne ya yi tasiri a kaina na daina shiga jama’a kamar yadda kuka tsara amma asalin gaskiya Mommy tsana

r ki bak’in cikinki da haushinki ne suka maidani na zama abunda na zama har kawo yanzu.

Sai yanzu Mommy ta iya tsayar da kukanta da kyar tace”Yahanasu dan Allah kar ki ce kin tsane ni! Komai da kika ga na yi wallahi duk na yi ne saboda ku!”

Cikin d’an

d’aga murya Yahanasu tace”saboda ke dai Mommy!duk abunda kika yi saboda kanki kika yi!!!.

Mommy kina kallo fa tun Ina y’ar k’arama ko jama a idan na gani kuka nake yi hakanan na tsani komai na tsani kowa nima mutane suka tsane ni,

Kina gani yadda aka din

ga yawo da ni k’asashen waje dan a gano matsalata na dinga shan wahala daga k’arshe aka ce depression gareni lokacin ko shekaru sha biyu nan Kai ba amma mommy ba ki yi motsin komai ba.

Sau nawa ana fasa d’aurin aurena kin san bani da kowa ba ni da komai a

mma Mommy haka kike murzawa idanunki toka ba kya zuwa ki dad’e da ni ki ji ainihin matsalata saboda kar a zargeki kar asirinki ya tonu,

a gaban idanunki su Yasira suke yi mini duk wani kalar cin kashi amma sai dai ki zuba ido kawai idan anyi sa’a shine za

ki ce musu su daina amma ba ki tab’a tsawatar musu ko kuma ki tsayamini ba.!

Ta ina hakan ya zama ba selfishnesse ba???ta ina hakan ya zamo duk a ta dalilin neman farin cikina ne????”

Yahanasu ta yi mata tambayar cikin d’aga murya.”

Cikin share hawaye

ta sake cewa”kuma ko tsafin ma da kuke tunanin shine ya yi tasiri a kaina ba ki tab’a yunk’urin gyarawa ba despite duk wannan wahalwahalun da na sha a rayuwa amma a haka kike tunanin idan kika ce mini ke mahaifiyata ce a gaba zan karb’eki in yafe miki sabo

da kina tunk’aho kin yi mini asiri ko?”.

Ba ta jira Mommyn ta bata amsa ba tace”Never!!!”

Sannan ta d’aura da cewa”Mama Khadija itace mahaifiyata har gaban abada shiyasa kika ga kawai na zuba miki idanu ban tab’a tunkarar ki da komai ba saboda ban d’auke

ki uwa ba!

kamar yadda ba ki damu da ni ba nima haka ban damu da ke ba, na san a baya a lokacin da na ji maganganunku na shiga tashin hankali ga k’arancin shekaru ga kuma no one to talk to amma believe u me wallahi wallahi Mommy yanzu abun ba ya gabana.

Alhamdulillah I ‘ve move on Ubangijina ya yaye mini damuwa.”

Cikin sake matsowa daff da ita tana kallon yadda take kuka billhakki da gaskiya tace”Dan haka Ina mai sake gaya miki ki janye maganar tsinuwa sannan ki kirawo Yashjub ya dawo gida cikin family d

’insa if not tabbas Mommy za ki yi mamaki na saboda a yadda na ke jin haushi da takaicinki tona miki asiri its the least I can do a halin yanzu.”

Dai dai nan Baba Larai ta turo k’ofar ta shigo a d’an hargitse!

Kallonsu ta yi kamar yadda suma suke kal

lonta,ta riga ta san Yahanasu ta gama fasa kwai duba da yadda Mommy take kuka kamar ranta zai fita amma ba ta wannan ta ke ba tukunna dan haka ta kalli Yahanasu tace”D’an bamu guri!”

Daga haka ta ja hannun Mommy suka nufi bedroom d’inta.

Had’e rai Mo

mmy ta yi kamar ta turje ta k’i binta sai kuma kawai ta rabu da ita ta yi mata shiru dan tsabar mugun mugun takaici da haushin Baba larai d’in ma ya sanyata ta kasa cewa komai.

Suna shiga Baba larai ta turo k’ofa ba tare da ta damu da yanayin Mommyn ba ta

ce”an yanka ta tashi fa!babu aure tsakanin Kausar da Yashjub!..”

Ba ta jira Mommyn ta tambayeta k’arin bayani ba ta d’aura da cewa”kin san ai kawar musu da lissafin duk wani abun da zai sanya a fasa auren nan muka yi dama,shiyasa kwata kwata ba su yi tuna

nin ‘ba fa a d’aura aure da ciki ‘ ba.

Ni kaina ban sani ba sai yanzu da na fito zan zo nan na ji suna maganar Abhi da Daddy..wai har wani babban malami suka tambaya ya tabbatar musu da cewa ‘ba a aure da ciki!’

Ban ji bayanin nasu sosai ba dan k’us k’us

suke yi a chan corridor na babban balcony kamar harda Hajiya mama suke maganar ta waya,shiyas….”

Cikin katseta Mommy tace”Larai me yasa kika b’oye

mini batun Yahanasu???”

Cikin rashin jin dad’i Baba Larai tace”kash!!!

Ki bar wannan maganar za mu yi

ta amma ba yanzu ba yanzu mu ji da wannan ba mu san wani step su Daddy za su d’auka next ba ya kamata mu yi musu shigar sauri!”.

Cikin daka mata tsawa Mommy tace”ni kuma wannan maganar nake so mu yi dan haka ki amsa ni idan na ce miki me yasa kika b’oye

min batun Yahanasu sannan me da me kika yi mata? Har ma da ni kaina tabbas kin yi mini abu dan haka ina son jin komai a yau a yanzu ba sai anjima ba idan ba haka ba wallahi za ki sha mamaki na!!”

Numfashi Baba larai ta fesar kafin tace”shikenan tunda k

in dage sai kin ji!

Duk abunda na lissafa miki nace ce za mu yi mata shi na yi…”

Cikin tarar numfashinta Mommy tace”Sannan nima kika d’auke hankalina daga kanta ko?saboda akwai abubuwan da kika saka ni na yi kika kuma bani na ci duk sai yanzu kwakwalwata

take fassaramin ma’anar su sannnan tun da na yi har yau ban k’ara tunanin fad’awa Yahanasu gaskiya ba!

Dan haka ba na son k’arya da b’oye b’oye larai!! Inaso ki gaya mini gaskiya tun rai na bai gama b’aci da ke ba!!!”.

Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk

’e kafin tace”Mommy gani na yi kina shirin tona mana asiri ni da ke kina shirin kaimu prison saboda muddin Daddy ya aan mun musanya Yara to

duk wani Abu da muka yi sai ya bnciko ya fito kowa ya gani a hankali a hankali k…”

Marin da Mommy ta d’auke ta da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login