Showing 219001 words to 222000 words out of 259716 words

Chapter 74 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

8

/>
shi ne ya sanya ta yin shiru ta zuba mata jajayen idanuwanta cike da mamaki da shock.

Cikin fushi bak’in ciki da b’acin rai Mommy ta fara magana”a duk tsawon tarayyata da ke ban tab’a ce miki ki je ki yi gaban kanki ki yi kutse cikin rayuwata ki yanke

hukuncin da kika ga ya dace miki ba! A tunani na shelter abinci da gatan da na yi miki ya ishi ace kin yi hankalin respecting d’ina da decision d’ina ba tare da kin yi mini shishshigi ba.!”

Cikin fushi sosai itama Baba larai d’in tace”Khadija ni kuma a

tunani na na wuce wacce za ki ajjiye hakanan a cikin gidan ki tana yi miki duk abunda kike so kawai kamar wata y’ar aikinki,a tunani na ni yayarki ce shiysa har na yi miki shishshigin da kike magana a kai na yanke hukuncin da na tabbatar it’s for your own

best!

Amma tunda duk irin rufin asiri da abubuwan da na yi miki tsawon shekaru sama da talatin duk ba ki gani ba yau ta kai har kin d’aga hannu kin Mareni shikenan!!!ba komai Allah ya had’a fuskokinmu da alkhairi..

Daga haka ta juya ta nufi k’ofa taana t

sammanin Mommy za ta tsaida ita amma har ta fice daga d’akin Mommy ko tari ba ta yi ba.

Za ta nemo ta amma bayan ta tafi su daidaita su shirya dan tabbas

Yau kam ba za ta tsayar da Larai ba wallahi,sai ta nuna mata abunda ta yi ba ta kyauta mata ba ta

yadda gobe ba za ta k’ara ba,kalli yadda ta saka k’iyayyarta a cikin zuciyar Yahanasu ta dalilin makircinta sannan gashi kwata kwata Yahansun ma ba ta k’aunarta sab’anin yadda Baba larai d’in tace Yahanasu ba za ta iya ko jayayya da ita ba! A tunanin ta

aikinsu ne yake ci da ta ga Yahanasun shiru shiru ashe tsana da haushinta ne ya cika mata zuciya shiyasa ta ke yawan yin shiru ba ta kulasu.

Sai da ta tabbata Baba larai ta fice da ga side d’inta gaba d’aya tukunna ta fito daga bedroom d’in nata!kamar y

adda ta yi zato ba ta tarar da Yahanasu ba dan haka ta zauna ta yi shiruu ta shiga lissafin ta hanyar da za ta bi ta daidaita tsakaninta da Yahanasu.

Ta fi minti ashirin a zaune su Yasira suka shigo a mugun hargitse suna cewa”ta zo

ta hana Baba Larai taf

iya,ga ta chan ta had’a kayayyakin ta tsaff!tun d’azu suke lallashinta amma ta kafe Akan Itafa sai ta tafi kuma sai kuka take yi dan Allah ta zo ta tsayar da ita ta lallasheta maybe Daddy ko Hajiya mama ne suka yi mata wani abun.

Mik’ewa kawai Mommy ta yi

ta fad’a cikin bedroom d’inta ta kullo k’ofar wanda hakan ya sanya suka

fahimci matsalar daga wajenta ta taso kenan dan haka kawai suka sauk’a da niyyar su je su ji da Baba larai first tukunna su dawo wajen Mommy su ji dalilin fad’an nasu sai dai suna sa

uk’a suka tarar da su Yasmeen suna shigowa cikin parlourn suka ce ta riga ta tafi jaka d’aya ma ta samu ta tafi da ita dan sun rik’e ragowar sun hanata ita kuma ta tafi kawai ta bar musu.Sun so su bita amma ba wani Napep d’in nata kuma a baki baki ta zauna

ta k’i basu access har aka ja aka yi gaba,kuma kafin su shigo su d’au mota sunsan sun riga sun b’acewa ganinsu……

Duk wannan dramar da ake yi su Daddy suna jin su suka manna musu hauka daga k’arshema garden suka fice suka ci gaba da tattaunawarsu….Daddy

ji yake kamar ya fi kowa farin ciki a ransa kuwa addu’a yake yi in shaa Allah Baba larai ta tafi ta bar gidansa kenan har abada next kuma Mommy ce!….Hajiya Mama ta ji dad’i da suka kirata suka gaya mata,tana fushi da su shiyasa yanzu ma kamar d’azu da suk

a kirata suka gaya mata zancen aure ba ta biye musu ba kawai dai tace”a ci gaba da addu’a”

daga haka ta kashe wayar tana jin sanyi a ranta,in shaa Allah k’arshen Mommy ya zo

kenan sannu a hankali za ta gani ne.

Har yanzu mamakinsu take yi tana mamakin y

adda ita kanta su Mommy suka goge mata hadda!!amma ba komai ai gashi nan sun fara gani tun yanzu,kad’an ma suka gani in shaa Allah.

A daren ranar Hajiya Mama ta bi jirgin k’arfe hud’u ta nufi Uk,duk da yadda abubuwa da suka wakana suka yi mata dad’i amm

a

tana so ta tafi…fushin da ta yi ta ga positive effects d’insa sosai a kan Daddy dan haka ta yanke a kan za ta tafi ta je ta yi ta yi musu addu’a Allah ya sa a dace in shaa Allah Mommy ta kusa ganin k’arshen ta kuma duk wasu abubuwa da ta rufe sai sun ba

nkad’a a idanun kowa ya gani.

Ya’isha tafi kowa gigita da lamarin tafiyar Baba larai dan ta san Baba larai itace gatan su saboda yanzu haka aiki take yi mata a kan Siyama da Najeeb!!shikenan ta san ta shiga ukun ta itakam yanzu..Yasira ma ta gigita sosa

i dan itama ta san Baba larai d’in dai itace gatan su dan haka da daddare bayan ta bari Mommy ta d’an huce ta je ta sameta cikin son fahimtar da ita ta fara yi mata bayanin illar tafiyar Baba larai a garesu kuma ko ba komai bai kamata ace sun yiwa Baba la

rai haka ba!ko me kuwa ta yi musu ba ta yi deserving haka daga garesu ba.”

Cikin nuna halin ko in kula Mommy tace”Yasira ba fa ni na cewa Larai ta tafi ba ita da kanta ta yi zuciya ta ce za ta tafi shiyasa ni kuma ban hana ta ba besides abunda ta yi mini

ma ya sanya dole in hukuntata in nuna mata iyakar ta dan haka indai na Isa in fad’a miki ki ji to ki tsame hannunki ki gaywa su Yusra ma duk su tsame hannayensu a lamuranta ko waya bana so ku yi mata,Allah na tuba idan banda failure me muke fuskanta aikin

nata yanzu duk ya daina ci!”

Cikin mamaki da tsanannin rashin jin dad’in abunda Momyn ta yi ta kuma fad’a yanzu Yasirar tace”idan na fahimceki Mommy a yanzu dai Baba larai ba ta da wani amfani a gareki shiyasa kika b’ige da cewa kinaso ki hukuntata ne sa

boda na san inda ace a lokacin da Baba larai take ganiyar taimaka miki komai yake tafiya daidai ne to da ko me ta aikata a gareki ba za ki tab’a barinta ta tafi ba,me ye ma ta aikata miki yanzun da ya yi zafi har haka???”

Yasira ta yi mata tambayar cikin

b’acin rai.

Mik’ewa tsaye Mommy ta yi ta nuna mata k’ofa tace”get out Yasira tun kafin ran ki ya b’aci!!!

Za ta yi magana ta kuma daka mata tsawa tace “get out nace!!!”

Juyawa kawai Yasira ta yi ta fita ranta a b’ace da takaicin Mommy dan ita a rayuwa

rta ba ta son mutum mai use and dump kawai idan ana tare to a kasance tare har abada through thick and thin kuma a taimaki juna amma ita Mommy bayaga use and dump d’inma da ta yiwa Baba larai,

tun ba yau ba ta lura da Mommy she’s just looking out for her

self kawai using d’insu take yi…..

Sai bayan kwana d’aya tukunna Mommy ta je d’akin Yahanasu dan ta san zuwa lokacinta d’an huce.

A zaune ta sameta suna waya da Yashjub tana ganin ta shigo ta yi sauri ta kashe ta ajjiye wayar ba tare da ta kalletaba ta

ce”bacci zan yi”

A hankali Mommy ta sauk’e ajiyar zuciya ta nemi guri ta zauna a kusa da ita ta kamo hannuwanta.

Kawar da kai Yahanasu ta yi,tsabar takaici da bak’in ciki ba ta san lokacin da hawaye suka shiga sintiri a kan fuskarta ba.

A hankali tac

e”na san na yi miki laifi Yaha amma ba laifi na bane ba completely.

Na shirya gaya miki komai in gyara tsakanina da ke amma da Larai ta fahimci hakan gudun kar asirinmu ya tonu sai ta je ta yi abunda ta yi ta kawar da tunanin ki daga gabana if not because

of that Yaha da ba zan tab’a bari mu kawo war haka a hakan ba!

Amma yanzu komai zai gyaru Yaha saboda ke da kuma na fahimci Larai ta saka na cuce ki yanzu haka ba ta cikin gidan nan tun jiya saboda ke y’ata.

Na san this is a lot to ask for amma dan Al

lah ki dubi uwar da aka shiga tsakaninki da ita ba tare da saninta ba ki yi mini adalci ki bani chance Yahanasu….

Mik’ewa da sauri Yahanasu ta yi tace”dan girman Allah ki fita!ba na buk’atar gyaruwar komai a tsakanina da ke Mommy kawai ki bari mu k’aras

he rayuwarmu a haka

Me ye ne ma ya rage??

You’ve missed out all the important stages na rayuwata da na fi buk’atar ki dan haka yanzu ban ga amfani idan kin gyara komai ba wallahi,I don’t need you in my life na riga na san ba kya so na ba kya k’aunata ki

n yi amfani da ni saboda ki samu abunda kikeso which u do dan haka na rok’eki da girman Allah kar ki nemi ki ja ni a jiki saboda ba zan janyu zuwa jikinki ba.

Dan haka kawai ki yi harkar ki nima in yi tawa harkar ba zan tona miki asiriba saboda unlike you

idan na yi Abu yana damuna na san kuma duk lalacewa ke mahaifiyata ce dan haka muddin na bada gudummawar na zamo silar tafiyar ki prison to abun sai ya dameni har k’arshen rayuwata shiyasa kawai na zuba miki ido na ke jira Ubangiji ya yi ikonsa a kanki am

ma fa muddin ba ki daina treatning Yash da tsinuwa ba Wallahi kamar yadda na gaya miki shekaran jiya tabbas zan fad’a masa ba ke ce kika haifesa ba!

Saboda kamar yadda na san guilty conscious zai addabeni idan na fad’i abubuwan da kika yi aka hukuntaki ha

ka zalika guilty conscious zai addabeni idan na bari bak’in cikin ki ya kashe Yashjub dan haka ki daina threatening d’insa!!!

daga nan ni da ke mu ci gaba da treating juna just like before iyakacin abunda nake buk’ata kenan daga gareki ba wai sulhu da fah

imtar juna ba!

Kin riga kin cuceni wata shari’ar sai a lahira,Mommy ba wai iyaka hakki na ba wallahi ko da Hakkin Mama khadija kad’ai aka barki ke da Mallan lawal da Baba larai ya isheku…..”

Shiruuu Mommy ta yi haka itama Yahanasu…tun shekaran jiya d

a Yahanasu ta je d’akin ta ta yi threatening d’inta ta san tsaff za ta iya yin abunda ta fad’a shiyasa ta ke so ta lallab’ata..tana son y’arta kuma ta na so su fahimci juna Sannan da gaske ne Baba larai asiri ta yi mata ta kawar da Yahanasun daga ranta gab

a d’aya amma ita Mommy a halin yanzu Babban tashin hankalinta shine kar Yahanasu ta tona mata asiri

Ta ji haushin Baba Larai kuma ta na so ta san ta yi mata laifi ta yadda ba za ta sake yunk’urin yin wani ba shiysa ta barta ta tafi kuma ta hana a nemota

amma fa Yahanasu tana daga cikin dalilin da ya sanya ta yiwa Baba larai abunda ta yi saboda tana so Yahanasu ta gani ta san ta yi abu Babba haka duk dan ita sai dai kuma ta lura hakan ko a kwalar rigar Yahanasu gashi a iyaka maganganunta na yanzu ma ta lur

a Yahanasu fa ta san har case d’in abunda ta aikatawa Khadija….dan haka dole ta d’auki risk ta aikata dukkan abunda za ta iya ta samu ta yi manipulating Yahanasu ta shawo kanta su fahimci juna tun kafin ta b’allo mata ruwa.

A hankali ta ce mata ki zauna m

u yi magana Yaha zan fad’a miki duk abunda na yi tare da alk’awarin ba zan sake ba..kuma na san idan kika ji bayani na za ki yi mini adalci idan kika fahimci dukkan nin abubuwan da na yi na aikata su ne saboda ku y’ay’ana.

Yahanasu ba ta zauna ba ganin

ba ta da niyyar zaman ne ya sanya Mommy ta fara magana.

“Kamar yadda na fad’a ba zan b’oye miki komai ba saboda Ina so ki yarda da ni mu fahimci juna.

……….Idan ana maganar rashin jituwa da rashin zaman lafiya da rashin so da k’auna to shine asalin zamana

da mahaifinku tun lokacin da muka yi aure…ko

Irin soyayyar na ta amarci bai nuna mini ba, k’arshen rashin mutunci da kyara shi Imam ya dinga nuna mini,tunda muka yi aure sam ba ya ja na a jikinsa ba ya nuna mini kulawa.

Ban rufe watanni biyu a gidan

Imam ba ya tubure ya dage ya d’agawa kowa hankali shi fa sai ya k’ara aure…sai ya auri budurwarsa wadda na san yana masifar so kamar ransa dan k’iri k’iri ya kan ce mini saboda suna na ya zo d’aya da ita ne dalilin da ya sanya yake d’an kulani.

Babu kalar

masifar da ban yi ba amma sai da aka d’aura auren nan lokacin ma da aka d’aura ba na nan ya kaini gidanmu yace a yi mini fad’a Abban mu kuma ya goyi bayansa aka mini horo mai tsanani ta inda aka ce ba zan koma gidan ba Ina ji Ina gani aka yi auren Khadija

ta tare suka gwangwaje amarcinsu ni Ina gidanmu hankalina a tashe.

Yadda na fita daga haiyyacina sai da ya bawa mahaifiyata da Hajiya Mama tsoro amma mazajensu suka tsawatar musu aka ce a rabu da ni hakanan sai da na gama shan wahala imam ya gama cin a

marcinsa tukunna Abban mu ya ce in koma tare da zazzafan warning d’in idan har ya ji case ya taso daga waje na to na bar Imam kenan har abada ba zai bari in koma gidansa ba.

Ina mutuwar son Mijina ba zan tab’a iya rayuwa babu shi ba gashi ba zan iya zama

da kishiya ba shiyasa na shiga tsaka mai wuya na rasa abunyi na rasa tudun dafawa

A wannan lokacin ne larai ta dawo hannun Mahaifiyata da zama (matsayinta na y’ar uwar mahaifiyarta)saboda an samu matsala da ita a k’auyen su an d’aura mata sharrin maita.

Itama tana da damuwa nima Inada damuwa shiyasa muke zama muke tattaunawa…Larai ta tausaya mini sosai haka kurum da na zo komawa tace Tana so za ta biyo ni.

A wannan lokacin da kyar su Abba suka amince saboda Larai a k’alla ta bani shekaru sha biyar kuma

suna so in je in zauna lafiya ni kad’ai in yi hankali kar mu je da larai in ga mu biyu ne in yi rashin mugunci..amma sai mahaifiyata tace ba komai mu je kawai saboda ta ga mun shak’u muna d’ebewa juna kewa sannan tunda Larai ta zo ba mu sameta da wata mugu

war d’abi’a ba in banda addini da sanin ya kamata da muka santa da shi.

Haka nan aka tambayi Imam ya amince muka tafi gidana tare da Baba larai.

A ranar da na koma ma Imam ba a d’akina ya kwana ba,ko kallona ba ya son yi sai bayan kwana hud’u ya kiramu y

a raba mana kwana Akan za mu dinga yin kwana uku uku ni da Abokiyar zama na.

Sai da girki na ya zagayo sau hud’u tukunna ya fara kwana a cikin d’akina saboda da a parlour yake kwana,ko da ya fara kwana d’akin nawa shima kuma babu abunda yake shiga tsakani

na da shi sai dare wajajen 12 zai shigo Idan aka kira assalatu kuma ya fita da ga nan ba zan sake saka shi a idanuna ba sai wani daren a cewarsa aiki ya yi masa yawa!

Da gaske na san ba ya gidan tun safe har dare amma kuma sai ranar girkina ne ya ke yin s

carce dan duk ranar da aka ce miki yau girkin Khadija ne to tun kafin Magrib yake shigewa d’akinta ba abunda yake fito da su sai sallah da cin abincin dare da ake yi tare daga sun yi isha ya kira ta ba kuma zan sake ganinsu ba sai washegari,haka nan zan yi

ta jin hirarsu yana dariya yana raha.

Abun ya ishe ni gashi ban Isa yin rigima ba na san tsaf su Abba za su raba auren ni kuma ba zan iya rayuwa babu shi ba shiyasa na yanke shawarar kashe kaina kawai!!!!…

ranar da zznyi abun Allah ya taimakeni na d’aga

kwalbar fiya fiya kenan zan sha Larai ta shigo ganin yadda na firgita ta fahimci ba ni da gaskiya aikuwa tun kafin ta gama dubawa ta gane menene a ciki.

Hankalinta ba k’aramin tashi ya yi ba dan haka ta fito min a mutun k’iri k’iri tace min Itafa ta

biyo ni ne saboda tana so za da taimaka mini..

Ba ta b’oye mini komai ba tace a kwai wani boka a k’auyensu mutumin tun yana zuwa mata a mafarki har ta gano location d’insa a wata bukka chan a cikin daji ta je..nan yake sanar mata tun ranar da aka haifeta

ya san dama itace za ta gaje sa…

Tun bata d’auki abun serious ba har ta d’auka!!!

bata da uwa sai matar uba dan haka bata yi shawara da kowa ba ta biye masa! ba a yi wata d’aya ba ta koyi kusan komai ya kokkoya mata abubuwa yace ta rik’e da kyau hannunta

yana da zafi fiye da zaton mai zato

Akan wata k’awar su da suka yi fad’a ta fara gwadawa matar har yau tana nan a k’auyen su ba ta gani,daga nan sai ta gayawa babbar k’awarta…tun daga ranar duk wani abu da k’awar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login