Showing 129001 words to 132000 words out of 259716 words
kamar dalma…..
Sam ba haka Mommy ta so ba so ta yi ace Manubiya ko k’anwarta ko Innar tasu wani ya biy
ewa Ya’isha daga nan ayi kacha kacha su yi zuciya su tafi da y’ar su ta yadda za ta raba auren ta kuma ga bayan cikin ta kowacce hanya hankali kwance…..
Yanzu haka ji take yi kamar zuciyar ta za ta kama da wuta ita kad’ai ta san halin da take a ciki tsaka
nin jiya da yau..shiyasa ko Baba larai ba ta gayawa ba ta taho asibitin dama opportunity irin wannan kawai take nema ta samu a yi ta ta k’are dan ta riga ta kai peak.Sai dai
Kash!Inna ta lalata mata komai…
Su Inna suna fita Yasira ta yi tsaki ta juya
itama ta fita Daddy da Yassir ta fara kira suka yi magana tukunna ta kira wata k’awar ta wadda bata dad’e da yin aureba a nan estate d’in Yashjub d’in suke haya,dan haka ta kira ta ji ya abun yake sun samu sun fita safe ko?.
Ta ji matuk’ar mamakin yad
da k’awar tata ta amsa wayar hankali kwance har da y’ar tsokana a ranta tace”to ko dai ta fita ba ta gidan ne dan haka a hankali a fili tace mata “kina ina?”
Sai da gaban Yasira ya yanke ya fad’i da ta ji k’awartata ta ce mata”Ina gida mana za ki zo ne?”
Zaro wayar ta yi ta kalla ta tabbatar da k’awar tata ta kira tukunna ta mayar kunnenta kanta tsaye tace’’ji na yi ance gobara fa ya tashi a estate d’innaku!yanzunnan aka kira Yash aka ce masa ga wuta yanata ci an gagara kashewa”
A rikice matar ta raf
ka salati kafin tace “to inaga gaskiya mak’iya ne, wani ne yake so ya yi luring nashi out a samu ya fita a kama shi ko dai wani Abu makamancin haka dan mu kam nan ko k’aurin wuta babu a nan gaskiya ki yi maza ki kirasa kice ya juya…..”
ai tun kafin ta ru
fe bakin ta Yasira ta yi maza ta kashe wayar a gigice ta shiga kiran Yashjub…ta jera masa miss calls sun fi takwas amma bai d’auka ba shiyasa hankalinta ya sake tashi dan zuwa yanzu tabbas ta gama gasgata maganar wannan k’awa tata,
tashi d’aya ta fashe da
wani Irin kuka a ranta ta gama sakawa ‘shikenan an kashe Yashjub’……..
**********************
⬇
**************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************
⬆
**********************
DOWNLOAD More complete Hausa
Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko tu
ro mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 08138873799
Haka kuma domin s
higa kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
**********************
⬇
**************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
******************
****
⬆
**************************
MANNUBIYA
(Book 2)
Page 29
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
..Ko kuma an yi kidnapping d’in sa!.
A rikice ta afka d’akin,suna nan a yadda ta bar su su uku Man
ubiya a gefe tana ta faman hawaye.
Cikin rikice Yasira ta k’arasa gaban Mommy tukunna tace
‘’Mommy Ina ga magauta ne suka kira Ya Yash!dan yanzunnan na kira frnd d’ita ta estate d’innasa,tace “babu wani gobara,shi kuma yanzu haka inata kiran sa a waya ba
ya d’auka!inaga sun sace shi ko sun yi masa wani abun….’’
Ta k’arashe maganar tana mai sake fashe wa da wani irin kuka.
Manubiya kawai tsintar kanta ta yi a gaban Yasira a rikice tace
‘’Ki sake gwada kira InshaaAllah babu abunda ya same sa bara nima
in kirasa idan bai d’auka ba mu yi message,na san in ya gani zai ki kiramu” ta fad’i hakan tana mai juyawa ta nufi wayarta.
Sai a sannan tukunna Mommy ta tashi ta tsaya a d’an rikice tace ‘’ikon Allah to Allah dai ya sa lafiya…babu komai ma ki kautata
zato….”
Kafin minti sha biyar gaba d’aya hankalinsu ya sake tashi
dan babu kalar kira da sak’onnin da ba’a yi an tura masa ba amman sam ba ya d’aukar waya kuma bai yi responding messages d’in ba.
Banda kuka babu abunda Manubiya take yi tana kuka
tana aikin kiran waya ba’a amsawa abun tausayi…
Suna a haka Daddy ma ya kira wayar Yasira yace “da shi da Yassir sunata kiran sa suma amma baya d’agawa but ga su yanzu suke barin gida za su je su duba estate d’in na sa..”
Yassira ce ta yanke shawarar
ta sake kiran friend d’in tata inyaso ko mai gadin su ne ta sanya ya tayasu ya bincika ko Yashjub d’in ya k’arasa chan…gaba d’aya ta gigice haka ta shiga kiran k’awar tata.
Matar tana d’auka tace ‘’ya ake ciki Yasira?kun yi magana da shi?”
A tare da
matar da Yasira suka fara jiyo hayaniya da ife ife…ta cikin background d’in Yasira take jiyo k’ara ta ban mamaki kamar ana fasa abubuwa da kuma na bindigu da ihun bayin Allah suna neman ceto….
A hankali jikinta yana wani irin karkarwa ta ji matar tace”I
nnalillahiwa innalaihirrajiun,Yasira kina jin abunda nake ji?bara in duba…”
Sai kuma a rikice taji tace”y’an bindiga ne suka shigo mana sun fi mutum d’ari…..”
K’arar harbin da Yasira ta ji ne ya tabbatar mata da k’awartata aka kashe dan a tare ta ji k’ar
ar wani abu ya fashe kamar k’ofar aka fasa da kuma harbin….
K’amewa ta yi ta kasa cewa komai,tana sauraron yadda mutanen suke magana suna cewa”a sake duba gidan sosai idan babu kowa su yi sauri su kunnawa wannan ma wuta su tafi next house they don’t have
much time…su yi su yi su tafi,yanzu Grenade ya yi masa waya yace su yi retrieving sun riga sun kashe gayen sun k’ona motarsa tun a bakin gate….“
K’afafuwan Yasira ne suka shiga kakarwa tashi d’aya ta gagara ci gaba da tsayuwa dan haka ta durk’ushe a waj
en ta fashe da wani irin kuka.
Daidai nan Manubiya ta matsa kusa da ita kusan a tare ita da Ya’isha suka ce mata “m-m mai ya f fa rru!??’’
Suka yi mata tambayar a tsorace dan yanayin ta ya yi matuk’ar sake firgita su.
Da kyar ta iya d’agowa ta kalli Ya
’isha ta yi mata bayanin abunda ta jiya faru sannan ta d’aura da cewa”na ji yana cewa gurnade ya ce sun kashe sa sun k’ona motarsa tun a gate,Ya’isha Ya Yash suke nufi shi ake so a kashe dama shiyasa aka yi k’arya da gobara aka ja sa wajen saboda su b’adda
track d’insu kar a gane manufarsu.Ba y’an fashin gaske bane Ya Yash d’inmu aka shirya kashewa dama Wallahi…”
‘Sululululu’ haka Manubiya ta tafi ta fad’i a wajen sumammiya…
Mommy ce ta kira Daddy
a rikice ta ji muryarsa yana cewa“gasu nan sun zo sh
iga layin motocin sojoji suka taresu wai y’an fashi sun kaiwa estate d’in hari an hana su shiga sun ma rufe gate d’in layin gaba d’aya but gasu nan dai ana ta k’ok’arin shiga motocin sojoji biyu sun kutsa kai yanzunnan…”
Yadda su Yasira suka ji muryar Dad
dy yana yiwa Mommy bayani ta wayar yana kuka ne yasanya suma suka fashe da wani irin kuka.
Sun san Daddy ba lalle ya so su je wajen ba shiyasa ba su ce masa za su je d’in ba instead suna gama wayar da shi suma suka fice dan hankalinsu gaba d’aya ya yi w
ajen….a nan suka fice suka bar Manubiya a yashe a k’asa suka nufi estate d’in suna kuka gaba d’aya su ukun..
A Chan suka tarar da Daddy da Yassir suma duk hankali a tashe lokacin har an bud’e gate d’in layin wajen taff cike da sojoji da y’an kwana kwana
dan kusan kaff gidajen sai da suka cinna musu wuta tukunna suka gudu ba a kama ko d’aya ba.! Yadda estate d’in ya k’one ya koma wani abu daban dole ya bawa mutum al’ajabi sannan ya sanya ka sake ka’daita Allah ka kuma tabbatar da cewa abun duniya da duniy
ar kanta ba a bakin komai suke ba.Su Yasira suna hango su Daddy suka k’arasa wajen su suna kuka shima Daddyn hawaye yake yi cikin sharar hawaye yace “akwai hope! ga dai motarsa chan a k’one da mutum a ciki amma gaskiya ba shi bane inaga kamar driver d’insa
ne kuma shi har yanzu wayarsa tana shiga,amma wayar mutumin ciki ta k’one da na duba ba ta aiki.
Sannan munata dubawa har ciki amma kamar ma shi d’in bai zo nan ba kwata kwata.
Cikin jinjina kai Yasira ma tace “Nima Inada hope Daddy
dan yanzu ma na
kirasa wayar tasa tana shiga,Allah dai ya sa ba wani abun ne ya same sa ba
dan gaskiya bai zo nan ba.”
Daddy ne ya kira asibiti
dama ga polisawa da sojoji a wajen dan haka ambulance suna zuwa aka fara fitar da deceased da injured abun ba dad’in gan
i dan mutane sunfi talatin waenda suka mutu
injured kuma wajen mutum goma……
Bayan kamar awa d’aya wajen ya cika taff da jama’a dan har su Baba larai duk sun k’araso suma kowa in ka kalla hankalin sa a tashe.
Dukda cewa zuwa wannan lokacin sun ta
bbatr da cewa Yashjub ba ya wajen dan kaff jama’ar dake yashe a harabar wajen da gefen gefen titin a lokacin da abun ya faru an shaida identity d’insu amman kuma rashin amsa wayar ta sa ne ya fi komai d’aga musu hankali a halin yanzu.
Dan haka Daddy ya ka
lli Yasir wanda duk hankalin sa ya gama tashi da rashin ganin gawar Yashjub…cikin dafa kafad’arsa yace ‘’ka kwantar da hankalin ka Yassir inshaaAllah babu abunda ya samu d’an uwanka,ka nutsu ka yi addu’a ka ji ko? dan ni kam zuwa yanzu inda hope ‘’
Ahanka
li Yassir ya had’iye wani k’ululun tashin hankalin da ya toshe masa mak’ogwaro kafin yace ‘’To Daddy’’.
Cikin fesar da huci Daddy yace ‘’d’an sake gwada kiran sa mu gani”
Still yanzu ma a hankali ya sake cewa “to Daddy”
Daganan ya matsa gefe k’irjinsa y
ana dukan uku uku dan baya k’aunar ya kira a yi rashin sa’a ya ji muryar Yashjub safe and sound!..Hatta seconds da komai sai da aka k’irga from inda yake to the estate sannan ya bada numbobin motocinsa duka incase ma
Idan ya chanja mota,kuma sai da suka y
i waya da mutanen suka ce masa gashinan ya shiga estate d’in yanzu tukunna suka fara aikin amma bai ga alamun sa a wajen ba!sai driver d’insa wada yanada tabbacin bai cika yawo da shi ba,mai ya faru???where is he????adduarsa d’aya Allah ya sa a wani wajen
suka danna gawarsa shiyasa ba a gani da wuri ba!…Allah ya sa a nemota yanzunnan a duk inda take a cikin estate d’in a fito da ita dan tabbas zuciyarsa za ta iya tarwatsewa idan akace Yashjub ya yi getting out of this one alive and safe…
Da kyar ya samu ya
d’an nutsu tukunna ya zaro wayarsa daga aljihu,hannunsa har karkarwa yake yi haka ya danna kiran Yashjub..bugu biyu a na uku ya d’auka yace ‘’Yassir! kuna Ina??’’
A hankali Yasir ya lumshe idanuwansa wasu zafafan hawayen bak’in ciki da na tashin hankali
suka shiga silalo masa…
Sai da Yashjub ya sake cewa ‘’Yassir ba ka jina ne?kuna Ina??”
tukunna da kyar da mugun kyar ya samu ya iya had’a kalmar ‘’ga mu nan duk a estate d’in ka’’
‘’Okay gani nan zuwa but bawa Manubiya wayar first Inata kiran ta ba ta d
’auka!is she fine??”
Shiruu ya yi ya d’an kalli Daddy wanda ganin kamar waya yake yi ya sa ya tunkaro sa
Cikin tsananin rikici Daddyn ya ce “shine??ya amsa?”Sai kuma ya sa hannu ya karb’i wayar.
A take ya lumshe idanuwa wasu hawayen farin ciki suka z
ubo masa jin muryar Yashjub safe and sound yana cewa ‘’Yassir,ka yi magana mana!Ina Manubiya take?ka bata wayar”
Dai dai nan su Mommy ma suka k’araso wajen,suna masu tambayr su “shi ne?ya d’auka?”.
Sai da Daddy ya jin jina musu kai yace ‘’eh’’ tukunna ya
maida hankalinsa ga Yashjub wanda ya rikice ta waya yana tambayar ‘Ina Manubiya?’ya ce
‘’Yash Manubiya ba tana asibiti ba? ka nutsu mana she’s fine ai ko?….”
‘’Daddy tare na barsu ita da su Mommy na fita,and she was very worried a time d’in,sannan yanz
u na ji Yassir yace duk kuna estate meaning har da su Mommy kenan kuma ita ban ji ta ba sannan Ina ta kiran wayar ta bata d’agawa..”
Yashjub ya zaiyyane masa hakan a rikice.
‘’Slow down Yashjub” Daddy ya ce kafin ya d’aura da cewa ‘’relax!!ok..”tukunna y
a juya ga Mommy yace ‘’Ina Manubiya??”
‘’Tana asibiti”kawai tace da alama ran ta a b’ace yake kafin ta d’aura da cewa
“Duk ya bi ya d’agawa mutane hankali kalle mu gabad’ayan mu a rikice shine tsabar rashin sanin ciwon Kai zai ishemu da Manubiya!Manu
biya!!,
Mannubiyan baby ce?goyota yake so mu yi mu taho da ita crime scene irin haka salon shima idan mun yi hakan yace za ‘a cutar da ita??”
Numfashi Daddy ya fesar kafin yace”yanzu fa lokacin murna da farin cikin kasancewarsa safe and unharmed ne god
iya ya kamata mu yi wa Allah,ba wai haushi ya kamata ki ji ba‘’sai kuma ya maida hankalin sa ga wayar da yake yi yace ‘’Yashjub Manubiya tana asibiti mu kuma muna estate d’in ka”.
Without thinking twice yace ‘’okay bara in je asibitin’’ daga haka ya kashe
wayar kitt!!!.
Shiruuu Daddy ya yi ya kusa minti d’aya da wayar a kunnen sa…kafin da kyar ya zaro ta ya mik’awa Yassir jikinsa a matuk’ar sanyaye….ya rasa dalilin da ya sanya no matter how ya kauce ya goce duk dan a zauna lafiya dole shi kuma Yashjub s
ai ya fito fili ya nuna masa Manubiya ta fi su matsayi a wajensa itace za ta zo first a sama da kowa da komai na rayuwarsa..he can’t help it but to think anya idan ya yi sake ganin Yashjub d’in ma ba zai gagaresa ba kuwa wata rana?!….
Yahansu ce ta ce
“
Daddy mu je asibitin,chan ya nufa ko?”
Saida ya juyo ya kalle ta tukunna ya d’aga mata Kai alamar ‘eh’ da ‘to’ daga haka ya wuce cikin tsananin mutuwar jiki.
Yana wucewa Ummi ta bi bayansa bayan ta bawa Munirat makullin motarta ta ce ta taho a ciki d
an tanaso ta d’an fahimtar da shi dalilin da ya sa Yashjub d’in ya yi haka saboda ta fahimci ya ji haushi.
Tana wucewa suma suka fara shigewa motocin su suna bin bayansu.
Wajen ya rage daga Yasira sai Yassir da Mommy da Baba larai
Mommy tsananin mamaki
n yanayin Yassir da kuma b’acin ran Yashjub ne suka hanata motsi har sai da Baba larai ta tab’o ta tace “mu je ko?”
tukunna ta samu ta d’auke kan ta daga kan Yassir da kyar
suka nufi motar Yasira.
Suna zuwa ta bawa Yassir key amman sai ya zauna a wajen
mai zaman banza yace “ta ja su kawai”
dan shi kam ba ya jin hannun sa zai iya d’aukar makullin ma ballantaana aje ga jan motar.
A rikice Yashjub ya k’arasa cikin asibitin ko parkin mai kyau da ma’ana bai yi ba hakanan ya fito ya rufe motar ya afk
a ciki dan tun d’azu dama ya tsinci kanshi da fara jin tsananin fad’uwar gaba yanzu kuwa da yake ta kiranta bata d’auka kuma ya ji bata tare da su Mommy he can’t help but ya yi tunanin wani abun ne ya sameta
Yana dialing number yana wani irin gudu gudu s
auri sauri haka ya afka cikin d’akin.
Sai da numfashinsa ya kusan d’aukewa da ya shiga ya ganta yashe a k’asa wan war kamar matacciya,k’amewa kawai ya yi ya tsaya ya kasa gaba ya kasa baya.
Kafin da kyar da taimakon addu’o’in da yake ta jerowa ya samu
k’afafuwansa suka basa had’in kai wajen k’arasawa inda take a rikice ya durk’usa,hannu sa yana wani irin karkarwa haka ya kamo hannunta ya d’aura a ta wajen pulse d’inta
A take ya saki wata k’akk’arfar ajiyar zuciya sai kuma ya rarumo gorar ruwa ya b’int
ike kan ya shiga shafa mata
yana d’an tapping fuskarta still hankalinsa a mugun tashe.
Wani nannauyan numfashi ta ja ta fesar idanunta a rufe ta shiga magana a rikice a tsorace ‘’Mijina!dan Allah Mommy ku ce ya dawo,mu je mu nemosa,babu abunda zai same s
hi, Ya Yash d’ina idan ya bar ni wallahi mutuwa zan yi”
Kallon fuskarta kawai yake yi yana jin wani kalar tausayi da tsantsar k’aunar ta tana dad’a ratsa shi, a hankali wata kwalla ta ziraro ta biyo ta sauka a kan fuskarsa..cike da taka tsantsan ya d’ag
ota ya saka ta a jikinsa wanda jin k’amshin turarensa da kuma jinta a jikin Mijinta ya sanya ta dawo haiyyacinta ta yi sauri ta bud’e idanuwanta domin ta tabbatr wa kanta da shi d’in ne?
A hanakali ya d’ago fuskarta yana kallon cikin idanunta yace ‘’babu
inda zan tafi in barki, inshaaAllah muna tare har gaban abada.”
A hanakali ta lumshe idanunta tana hawaye tana jin wani sanyi yana ratsa ta..
…Da farko gefen kumatunta ya fara murzawa kafin daga baya ya matso da fuskarta sosai garesa