Showing 72001 words to 75000 words out of 259716 words
k’arasa inda take
ba tare da b’ata lokaci ba ya ware hijabin nata ya nemo
wuyan ya zura mata.
Ai kuwa har ajiyar zuciyar da ta sauk’e sai da ya ji kafin ahankali yaji tace “thankyou”
Murmushi kawai yayi yana kallonta yana mamaki da tunanin ta yadda
zai sa ta d’an saki jiki da shi ta cire wannan tsoron….jin jina mata kai kawai ya d’an yi kafin yace” welcome,mu je ki yi alwallah muyi nafila”
Ji ta yi kamar tace masa’ita bama ta sallar’sai kuma kawai tace “Nayi”
Jinjina kai yayi daga haka ya kama ha
nnunta suka fita waje cikin d’akin.
Akan kafet d’in ya shimfid’a musu darduma ya tada ikama suka gabatar da sallar nafila raka’a biyu….ya jima yana addu’o’i kafin ya juyo gareta
ya d’aura hannunsa a kan goshinta nan ma ya yi addu’a
tukunna ya gyara
zama sosai yana fuskantar yace
Ta mishi karatu yana son jin k’ira’arata….Suratul Mulk ta karanto masa tun daga farko har k’arshe…kamar kuwa kar ta daina haka ya ji,kafin shima yace ta zab’i inda takeso ya karanta mata..ganin ba zata iya magana ba yasa ya
karanto mata Suratul Ibraheem
Shiruu ta yi tana sauraron yadda yake karantun bisa ka’ida kamar wani shahararren malamin ne yake karatu haka ta ji,ita har ga Allah duba da yadda ya girma a Uk sam ba ta yi tunanin yana da ilimi har haka ba.
Tambayoyin da
suka shafi addini ne suka biyo baya,ba kad’an ba shima ya yaba da ilimin addininta dan haka ya sake godiya ga Ubangiji…. ya ji dad’i sosai yadda matarsa ta kasance mace mai ilimin addini saboda hakan yana da fa’idodi da yawa.
Ganin tana hamma ne yasa yac
e “Ta tashi ta shirya ta kwanta dan ya lura a gajiye take”
Yadda ta mik’e zumbur!lokaci guda sai da ta basa dariya.
Yana kallonta ta ta d’auki manyan manyan kayan bacci ta shige closet d’inta…drying kanta ta fara yi da hair dryer da su Aisha suka jera ma
ta tukunna ta saka kaya…har ta
fito bai yunk’ura ba kuma bai ce mata uffan ba instead sai kawai ya girgiza kai yana mamakin kayan baccin da ta saka abun takaicin ma har da hula kuma wai a hakan ma sai wani kakkare jikinta take yi…..yana a nan kan dardum
ar ta zo ta wuce ta haye gado ahankali tace masa”sai da safe”
“Za kiyi bayani ne”
Ya fad’i hakan a cikin ransa
A fili kuma yace”Allah ya bamu
Alkhairi”
Wani sanyi ta ji a ranta ganin bashida niyyar yi mata komai,cikin nutsuwa ta ja quilt d’in dake sh
imfid’e a kan gadon ta lullub’e duk jikinta da shi,har kanta.
Tsorone ya kamata jin ya mik’e ya je ya kashe wuta kuma bai fita ba,tana cikin tunani da zullumin son jin fitartasa ta ji ya yaye fuskar ta dake cikin bargon kafin yace”Kar ki rufe har fuskarki
”
Sai kuma ya durk’usa yayi kissing forehead d’inta yace “good Nyt”
Har da d’an murmushi ta yi mishi wannan karon ahankali tace”nyt”
tana kallonsa ya koma kan dardumar ya ci gaba da karatu.
K’are masa kallo kawai takeyi
tanajin yadda sonsa yake sake
shigar ta…ita ala dole tana b’oyewa ne a bargon kar ya gane kallonshi takeyi
ba ta san gaba d’aya hankalinsa yana a kanta ba
duk abunda tayi yana kallon ta.
Gashi a gabanta tana kallonsa ga sanyin A c ga shauk’i ga kuma farin cikin an rabu da ita ta
huta…sam ba ta san lokacin da barci ya kwasheta ba!ba ita ta tashi farkawa ba sai wajajen k’arfe 3 na dare lokacin da ta ji bak’on al’amari a tare da ita a ranta tace”kenan Yashjub wayo yayi mata sai da ya bari ta sakankance.
Shi kuwa Yash ba zai iya jur
ar ganin kukanta ba kuma tun d’azu a closet ya fahimci kukan zata yi masa muddin yayi yunk’urin yin wani abun.
Kamar kuwa ya san abun da ke ranta kenan.
…Tun tana magiya da lallashi har ta fara kuka hankalinta bai gama tashi ba sai da taji shima ya saka
mata kukan yana lallashinta,ba abunda ya fi bata tsoro irin yadda ta ji yana yamutsa ta kamar ba ya haiyyacinsa kamar wani mahaukaci….da tafiya ta yi tafiya kuwa had’iyar zuciya kawai ya rage ba ta yi ba gashi a yadda ya koma mata ta san ko aljanace ita ba
lalle ta iya kwatar kanta ba,bata tab’a sanin Yashjub mugu bane sai da ta ji yana shirin kasheta…duka cizo yakushi amman duk a banza sam bai ji ko d’aya ba dan a wannan gab’ar inda ace za’a saita masa bindiga to ko sunansa ba lalle ya kawowa ba!….
Tun Ma
nubiya tana tunanin kalar jinyar da zata yi idan Allah ya bata ikon tashi har ta zo ta cire rai ta fara basa wasiyya had’e da shirme da surutai,shi kam ya san dai tana magana amman bai gane ko d’aya ba,yana so ya tausaya mata amman sam ya kasa.Sai da kyar
da mugun kyar tukunna Manubiya ta samu ya sarara mata lokacin har an fara kiran sallah a masallaci…….
Shi kansa ya san yayi laifi amman kuma ba laifin sa bane
kasancewarta macen da tafi ko wacce mace a duniya ne
silar janyo mata wannan b’arna da
aika aika da yayi…..sam bai yi zaton hakan ba dan tabbas komai ya wuce zatonsa an tashi kansa shiyasa ya gagara controlling kansa.
Ahankali yanajin yadda take numfashi da sheshshek’ar kuka da kyar ya samu ya janye daga gareta wanda sai da ta ji kamar ana
zare mata rai ne,cike da kasala yana jin yadda kansa yake wani irin mahaukacin sarawa ya koma gefe ya kwanta cikin lumshe ido da sauk’e numfashi yace”Alhamdulillah”a fili.
Manubiya kuwa da ke kwance a gefensa ji tayi inama ace tanada k’arfi da lafiyar da
za ta samu ta juyo ta rufesa da duka.
…..
Earlier
Tare motar Yahanasu da suke tare da Munirat suka shiga cikin mansion d’in da ta Yassir
lokacin twelve har ta d’an gota
Gidan shiruu baka jin komai sai k’arar mikano.
Ita Yahanasu sai yanzu ma ta tu
na cewa makullin d’akinta yana hannun Yassira!tashi d’aya ta san za su yi case idan ta shiga dan itama yadda take jin zuciyarta a yanzu kam wallahi kaff cikinsu babu wanda zata ragawa.
Tana yin parking Yassir ma yana fitowa daga cikin tasa motar.
Tun d
a suka taho dama
Munirat ta riga ta gama deciding abunda za ta yi a cikin ranta dan haka ta juya ta kalli Yahanasu tace”Bara in karb’i sak’o na sai na shigo”.
Yahanasu ba ta kawo komai a ranta ba tace mata “to”
daga haka ta bud’e musu motar suka fito a
tare ita ta nufi main door Munirat kuma ta bi bayan Yassir wanda ya nufi b’angaren sa….tana ganin Yahanasu ta shige ta k’ara sauri..
Sarai ya ga lokacin da ta biyosa amman ya yi banza da ita yayi wucewarsa kamar bai ganta ba,sai da ya zo shiga har ya za
ro key ya ji tace
“Na san ka lura da ni”
Shiruu yayi kamr mai tunanin wani abun kafin ya zura key d’in ya bud’e k’ofar tukunna ya juyo yace “Munirat a gajiye nake sosai!Make it fast pls..wat do you want?”
Matsowa kusa da shi tayi
tace “har haka muka z
ama?
Make it fast?baka ma da lokacin saurarona?
Okay ba komai shikenan!”
Ta fad’i hakan tana k’ok’arin juyawa,rik’o hannunta ya yi ya janyota garesa har sai da fad’a jikinsa kafin ya tallafe k’ugunta da hannunsa d’aya yace”Ke fa kikayi pushing d’ina a
way,wallahi har gobe Ina sonki Ina k’aunarki
amman no matter what ba zan yi forcing d’inki into a relationship with me ba…..”
Gaba d’aya she’s uncomfortable dan tunda take wani Namiji bai tab’a yi mata irin wannan ruk’on ba idan ba shi d’in ba
amman
kuma so take su shirya,kar ta
turesa ko kuma ta hanashi rik’eta ya zama furious sannan ga maganganunsa
na ‘yana sonta’
Da suka k’ara narkar mata da zuciya shiyasa ta k’i motsi sam
tak’i cewa komai.
Hakan kuwa ba k’aramin dad’i ya yiwa Yassir b
a dan haka ya sake hugging d’inta sosai yaci gaba da gaya mata k’arya da k’arairayi har da cewa”har zazzab’i da rashin lafiya yayi kwanaki duk a ta dalilint,idan ya ganta kamar zai mutu haka yake ji gashi ba ta kulasa shiyaaasa za ta ga kamar gudun ta yake
yi!”..
sannan ya fito k’iri k’iri ya ce mata shi fa ba zai iya yin relationship d’in y’an k’auyen da take so su yi ba in dai har tana sonshi to ta sake da shi after all ai shi za ta aura at the end of the day so ta daina wahalar da kanta tana wahalar da
shi,indai har ta yi trusting d’insa kuma shi takeson aura to a ganinsa ya kamata ta sake jiki da shi.!
Ko da ta yi masa maganar Kausar ma k’iri k’iri ba kunya ba tsoron Allah yace mata “shi ba komai tsakanin sa da Kausar ba sonta yake yi ba kawai
dai su
n shak’u ne tun yarinta”…..Sai da Yassir ya tabbata ya gama zurma ta ta kamu tukunna ya d’aura da cewa”I love you so so much,so very much only you Munirat”
Har cikin zuciya da jininta kuwa ta ji wannan kalmar tana yawo…… sai da ta lumshe ido ta sauk’e aji
yar zuciya tukunna tace”I love you too”ta fad’i hakan tana k’ok’arin zamewa jin yadda ya sake mannata a jikinsa,kallon fuskarta ya yi kamar bai fahimci son zamewa take yi ba yace “mun shirya ko?”
Jin jina masa kai ta yi tana murmushi,ahankali yace”bari i
n yi confirming to”bata ankara ba ta ji ya fara kissing lips d’inta.
Bata biye sa ba saboda shock
tsoro ga kuma bata saba ba.
Ya kai 1 minute tukunna ya rabu da ita yana mayar da numfashi ahankali yace”That’s more like it”
Ya fad’i hakan yana murmushi
yana shafa kumatunta.
Ya lura da yadda jikinta ya d’au karkarwa tun d’azun har yanzu,sannan sam ta k’i magana taki ma ta yarda su yi
eye contact sam.
Ahankali yace
“Munirat,ko na b’ata miki rai ne?”Ya fad’i hakan yana lek’en fuskarta.
Dakyar ta i
ya cewa
“A ‘a”.
Murmushi yayi….he need rest kuma ya lura ba abunda za ta iya yi masa yanzu dan ya ga yadda ta shiga shock daga iya ka kiss
shiyasa cikin son sallamar ta yace
“Muje in raka ki,kema ki samu
ki huta ko?”
Ahankali tace
“Okay”
Gaba
d’aya jikinta a sanyaye…..rik’e hannunta yayi daganan ya d’an janyo k’ofar entrance na side d’innasa
suka fara takawa yana d’an janta da hira amman ita daga ‘um’sai ‘um um’.
Sai da ya kaita kan kwanar da za ta sadata da main door d’insu tukunna ya d
’ago hannunta yayi kissing yace mata”good nyt zan kiraki”
Ahankali ta d’anyi murmushi tace “Sweet dreams”
daga haka ya yi waving d’inta suka rabu.
Sai da ya b’acewa ganinta tukunna ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya….ta san yin hakan is wrong amma
n ba ta jin zata iya hak’ura da Yassir gaskiya!za ta biye masa
kuma inshaaAllah zata nuna masa rashin dacewar hakan along the way,ta san Yassir yana sonta dan haka idan ta sake d’ukar hankalinsa ta samu ya sake dulmiyawa a cikin kogin sonta to ta san za
ta iya hana sa abubuwan da yake yi mata daga nan sai su yi tsaftataccen relationship d’insu su yi aurensu in ya so sai ta sallama masa komai ta kula da shi yadda ya kamata su samu happy ending.A ganinta hakan shine mafita
akan dai ace ta rabu da shi
bay
an suna son juna,ba za ta iya zuba ido Tabbas kallonsa ba dan yadda ta ga ya fara nuna intrest akan Jidda ta san in ta bari aka tafi a haka shikenan sunanta sorry.Ba ta da mai bata shawara su Ummi tun kwanaki da ta ganta da Yassir sam suka daina sake mata
ko hira Ummi da Yayarta sun
daina yi da ita sun nace akan ta fito da miji,ba dan haka ba da ko yayarta ta tuntub’a da maganar amman ta san sam ba za ta fahimceta ba wani sabon case d’in ne ma zai taso,shiyasa ta yanke decision d’in ta da kanta,ta yi abunda
ta ga shine dai dai.
Da wannan tunanin ta k’arasa bakin main door na mansion d’in ta danna,ganin a bud’e ne ma yasa ta tura zundumemiyar bullet proof door d’in ta shiga….
A tsattsaye ta samu kowa
Mommy da Kausar ne kawai babu sai Daddy amman har Umm
i tana k’asan,amsa sallamar ta Ummi tayi kafin tace”Daga ina kike??”
Cikin tarrar numfashin Ummin tace”Waya na tsaya yi ne”
Kallonta Yahanasu tayi ta d’an yi shiru sai kuma tace “Mu je d’akinki,in kwana achan”.
Daga haka ta juya ta kalli Yassira tace
“Ki dafa key d’in ki cinye dan Allah!”
Ta fad’i hakan tana k’ok’arin wuce ta.
Fincikota Yassirar ta yi ta dawo da ita gabanta ta tsayar tukunna tace”Inaga baki fahimceni ba Yahanasu!
bacci ne kwata kwata yau baki Isa yi a cikin gidan nan ba!
dan walla
hi yadda kika shiga tsakanin mu da d’an uwan mu
ki ka d’aga mana hankali kema ba ki isa kin runtsa ba!.
Cikin fushi Ummi tace “baki da hankali ashe Yassira?”
Kafin Yassira wadda ta juyo a fusace ta yi magana tuni Ya’isha ta amshe cikin tsiwa ta far
a cewa”Haba ke kuwa!wai
ashe kwata kwata kwakwalwarki bata d’aukar lissafi ke!.
Magana ake ta y’an uwa!,tun d’azu sai ce miki ake yi ki
wuce ki tafi d’akinki amman
kin nace sai da kika ji komai
kuma hakan ma bai ishe ki ba tsabbar shishigi kin wani
tsomo wa mutane baki,
Ina ce Daddy dakansa yace
‘ki fita harkar kowa kuma in family suna magana ki daina saka baki’.?”
With full confidence Munirat ta taho tace”Ya’isha!tou ai ni a ganina idan aka bar family d’in za su yi b’arna da shirme tunda bas
u san abunda ya dace ba
shiyasa Ummin take saka muku baki dan idan aka barki Allah kad’ai ya san kalar dak’ik’ancin da za ku yi”
Dasauri Ummi ta damk’o hannun Munirat ta tura ta tace “wuce ki tafi d’akinki kafin na makeki”
Dan yadda ta ga Yusra da Ya
’isha sun yo kan Munirat ta san idan bata yi wani abun ba tsaf za su rufeta da duka.
Za ta yi magana Ummin ta daka mata tsawa tace wuce”Nace ki wuce!”
Da sauri Yasmeen tace”ai sai ta wuce d’in mu gani idan saman ubanta ne ya gina!.Kun je kun gama yi
wa mutane shishshigi kun k’ulla k’ullalliya shine yanzu zaku ce za ku
kwana lafiya?ai ba ku taki zaman lafiya ba dan haka bacci bai ganku ba,masifa da tashin hankali ne ya ganku!”
Cikin fushi Munirat tace”Okay!yanzu na gane matsalar ku
ko kuma ince
matsalolinku!
Na farko baku samu yadda kuke so ba
na biyu kuma Ya Yash ya fatatttake ku shine kuka zo zaku d’aga mana hankali zaku hana mutane bacci saboda tsabar bak’in ciki da k’unci kun rasa Ina zaku sa ranku shine kuke so ku huce a kanmu ko?.
Ai b
a mu muka ce ku zama bad people ba,have it been u guys are nice da duk haka bata faru da ku ba.Kuma abunda ban gane ba shin idan mun tsaya d’in mai hakan zai k’are ku da? kawai kar mu yi bacci shine burinku ko me??
kuna jin abunda kukeyi kuwa?
kowa fa ya
na jin hakan ya san kawai kuna neman in da za ku yi venting anger d’inku ne,haba mana!ku gyara abun naku ta hanyar yin something not lame
kmar haka!”
Fincikota Yusra ta yi da dukkan k’arfinta daga gaban Ummi,
Ummi ta yi mamakin yadda Munirat ta zabgaw
a Yusran mari dan ba ta yi tunanin wannan audacity d’in da ga Munirat d’inba…..
A chan sama kuwa,tun d’azu da Baba larai ta cewa Mommy “ba su yi komai a gidan Yash ba suka dawo”shikenan Mommyn ta koma kamar robot,dukda Baba ta kawo sabon plan amman sam
ita gani take tunda basu yi wanchan na farkon ba shikenan ta shiga uku!zuwa yanzu so take ma ta yi kuka amman sam hawaye sun gagara fitowa daga idanunta.Ga kuma yanzu da ta yi wa Kausar bayanin dawowar Manubiya da Yash cikin gidan tukunna a samu a yi komai
….a tunanin Mommy Kausar za ta yi murna da hakan amman sai ta ga sab’anin hakan dan tashi d’aya Kausar d’in ta birkice ta shiga ce mata tace”Ashe ma bata da burin raba auren Yash da Manu tunda har ba zata iya korarta a wanchan gidan ba har sai an kuma d’au
kar lokaci an barta ta dawo nan kafin nan ma maybe ta dawo da ciki shikenan komai ya lalace mata dan ta san indai Manu ta samu ciki to ta gama cin riba a kansu……ita kawai ta lura ja mata rai suke yi suna yi mata wayo dan haka yanzu kawai abunda Mommy za ta
yi mata shine ta kira Yash a yanzu ta ce masa ya saki Manubiya if not sai ta tsine masa,indai har Mommy ta yi hakan to ta yarda ba raina mata hankali suke yi ba,idan kuma bata kira Yash ba wallahi sai ta bar gidan a yau kuma ba zata sake ganinta ba!”
Han
kalin Mommy idan ya yi dubu tou ya tashi,ta san idan ta yi hakan tabbas Yash zai saki Manubiya amman ko hauka takeyi ba za ta tab’a yin abunda hakan ba saboda ta san yin hakan kamar ta kashe relationship d’inta da Yashjub da Daddy ne,dan kowa bak’in ta zai
gani kuma ita kanta Kausar d’in muddin hakan ta faru to Yash ba