Showing 228001 words to 231000 words out of 259716 words
Doc Kamal sumaila vice governor d’in Kano state…sun had’u da shi ne ta sanadiyyar tsay
a musu da ta yi a matsayin mataimakiyar lawyer su na shar’iar da suka yi ta fafatawa yau kusan shekara d’aya kenan akan mulkinsu da aka yi musu almundahna to yanzu dai Alhamdulillah komai ya daidaita sun hau kan mulki wanda sai a lokacin ne ya fito mata da
k’udirinsa!
Ya fi wata d’aya yana binta tana cewa a’a shi ya d’auka ma ko saboda kasancewarsa babban mutum amma bai tab’a aure bane ya sanya tace masa a’a sai da ta fito masa ta basa labarinta tukunna ya fahinceta…cikin ikon Allah shima d’in hakan ce ta
yi ta faruwa da shi dan sau hud’u ana samun matsala da aurensa ana fasawa dan haka yace mata ta yi hak’uri tta daure su bawa relationship d’in chance inshaaAllah wannan karon da ga shi har ita za su dace…
Da kyar da taimakon su Manubiya da ta gayawa suka
dinga bata shawarwari aka samu ta amincewa Alhaji kamal yanzu dai ya zo sau biyu jiya kuma sunzo shi da Abokinsa sun gaida Daddy.
Hatred tsana da takaicin Mommy ne ummul’aba’isin kwanciyar Daddy rashin lafiya ga kuma damuwa daban daban gashi Yashjub
ba ya kusa.
Last week Abhi ya zo ya dubasa sam bai ji dad’in yadda ya ga jikin nasa ba,ba don yana da aiki ba da ba zai koma gida ba.
Hankalinsa duk ba a kwance ba Hakanan ba dan ya so ba ya wuce Uk…tun a jirgi ya kira Yashjub yace”yana son ganinsa a Uk
idan ba damuwa.
Ya san suna waya da video call da Daddyn amma ya kamata ya je ya gansa gaskiya.
Bayan kwana uku da dawowar Abhi su Manubiya suka zo ita da Yashjub d’in…ta yi fari k’all ta yi k’iba ta yi fresh ta k’ara kyau amma babu ciki babu alamun s
a a tare da ita wanda hatta su Hajiya mama sai da suka d’an ji d’arr!!amma kawai sai suka basar suka ci gaba da murnar ganin juna.
Abhi kam ya ma fi su Hajiya mama damuwa,har ga Allah fa wannan yana daga cikin confidential reason d’insa da ya sa ya so a
ce Yashjub yanada mata biyu ne ba wai Kausar ba A’a bayan ya sake ta ya so ya auri wata saboda ba zai yiu ace Yash ya k’are rayuwarsa a haka ba duk wannan uban dukiyar ace shege ne kad’ai zai juyata………
“Abhi Ina wuni!”
D’in da Yash d’in ya ce masa ne ya
katse masa tunani.
Ahankali ya ke kallonsu shi da Manubiyan kafin ya d’an yi murmushi ya amsa gaisuwar tasu tukunna ya d’aura da cewa “duk kun yi k’iba kun yi kyau abunku tubarkallah!”
Sunkuyar da Kai Manu ta yi cikin tsananin jin kunya yayinda Yashju
b ya d’an sosa k’eyarsa yana murmushi….
Ciki su Hajiya Mama suka wuce da Manubiya bayan an gama gaishe gaishe..suna wucewa Abhi ya gyara zama ya kalli Yash yace masa”yaushe za ka je ka dubo mahaifinka??”
Tashi d’aya yanayin fuskar Yash d’in ta chanja
idanunsa suka d’an fara kad’awa.
Sai da Abhi ya sake jeho masa tambayar a karo na biyu tukunna da kyar ya samu yace”ba rana!”
“Saboda me??”
Abhi ya tambayesa cikin tarar numfashinsa.
Wata nannauyar ajiyar zuciya Yash ya sauk’e kafin yace”Abhi pls
dan girman Allah ka bar maganar kawai.”
Jinjina Kai kawai Abhi ya yi kawai daga haka ya d’auki waya ya danna kiran Hajiya mama tana d’auka yace”Mama sai fa kinzo saboda ya k’i gaya mini.”
Runtse idanu Yash ya yi da tafukan hannunsa kafin ya cika ya d
’ago ya kallesa yace”Abhi saboda Kausar ne fa dan Allah kawai ka bar…”
“Kausar dai is one of the reasons Yash!,ko har ka manta message d’in da ka turo mini da hannunka??”
Muryar Hajiya mama ta katse sa tana mai k’arasowa inda suke ta zo ta nemi guri ta
zauna tana mai fuskantar sa tace”Yash an baka space kamar yadda ka buk’ata Kausar is no longer your wife!dan haka menene dalilinka na k’in komawa Nigeria ko kanada waenda suka fi mu ne da ba za ka gaya mana matsalar ka ba sai su?”
Hawayen da ya zubo ma
sa ya sa hannu ya goge kafin yace”barin maganar nan shine mafi alkhairi ga kowa Hajiya mama bana son yinta…”
Sake gyara zama ta yi da zaman gilashin idanunta ta fuskancesa sosai tace”ni kuma yau na nace sai na ji komai,dan haka the sooner you talk the b
etter dan ka san ba zan tab’a hak’ura ba ko?.!”
Jin jina mata Kai ya yi dan haka tace”perfect..muna sauraronka!”
Sai da Yashjub ya d’auki sama da mintuna goma ya yi shiruu kawai,kafin chan ya zaro wayarsa ya kai musu inda videos d’in Yassir suke ya
mik’awa Hajiya mama ya yi sauri ya mik’e ya fita……
….
Sai da hawan jinin Hajiya Mama ya tashi Abhi kansa sai da ya yi Hawaye ba sau d’aya ba….ba su iya b’oyewa Daddy komai ba hakanan suka sanar da shi komai wanda shima sai da suka yi da sun sanin fad’a
masa da suka yi ta waya dan sosai ya gigita ya kad’u matuka da al’amarin da kyar Ummi ta taushe sa aka samu ya sha magani ya yi bacci bayan sallar asubah dan throughout ranar ba su runtsa ba.
Da kyar da mugun kyar suka lallab’a Yashjub ya yarda zai zo d
an ba k’aramin Takaici ya ji ba da ya ji sunce har sun turawa Daddy shi har ga Allah ba haka ya so ba…sai da Hajiya mama ta zaunar da shi ta yi masa fad’a ta nuna masa illar yin shiru da guduwar da ya yi tukunna ya yarda da kyar ya amince ba dan ya gamsu h
undred percent ba.
Sai da suka yi sati d’aya tukunna suka samu zuwa Yashjub Manubiya Abhi da Hajiya mama da Abhi…
Manubiya kanta Hankalinta a masifar tashe yake dan tunda Yash ya sanar da ita komai ta fahimci yau case ne a gidan,shiyasa ta nemi alfar
mar ya bari su Ya Musbah su zo
su d’auketa a airport ta yi missing su Inna dayawa bata samu ta yi musu sallama ba,gashi har gwaggo Suwaiba itama ta zo.
Ya fahimci zillewa take son yi kuma shima baya son a yi a gabanta shiyasa ya amince tun kafin su yi bo
ardn ta sanar da su ai kuwa a airport d’in su suka fara gani shi da Ya Nafi’u kafin su Junior suma su ka k’araso.
……If not because Yassir ba ya gidan ya tafi Abuja ya ce ya je yin business ne to da tuni Daddy ya dad’e da d’aukar mataki a kan sa…da fark
o masifa ya shiga da tashin hankali mai tafe da tausayin Yassir d’in yanzu kuwa haushi da tsanar sa yake ji he don’t think zai ma iya kallon fuskarsa.Ba ya son jin ko da sunan sa ne….
Kaff gidan zuwa yanzu kowa ya san Daddy yana cikin b’acin rai on top
of na farko da kuma rashin lafiyar sa shiyasa kowa ya sha jinin jikinsa harda Mommy wadda ta fara shirye shiryen yi masa bori saboda kwata kwata ya daina raba musu kwana ita da Ummi,dukda ko da chan d’in ma tana zuwa yake korarta amma dai ai ya fi mutunci
da daraja a kan yanzu da ya had’ewa Ummi kwanakin gaba d’aya kaff.
Jirginsu Yashjub ya sauk’a da safe around 6:00am na su Yassir kuma ya sauk’a around 6:40am Shiyasa ya zamana sun shigo cikin gidan kusan a tare dan su Yashjub suna gama shiga shima ya sh
igo.
Side d’insa ya fara nufa ya je ya yi freshening up
Daga haka ya fito a gurguje dan ya yi misssing Kausar over!!
Dukda wajen sabuwar budurwarsa da suka had’u a instagram ya je ya gwangwaje abunsa amma da kewar Kausar yake kwana yake tashi,har ga A
llah shi kansa bai san wanne kalar so yake yiwa Kausar ba.
Ita kuwa Kausar tana chan ta shiga damuwa dan mutanen sun ce mata ba za su tona Yassir ba he kept his promise ya dad’e da taimakawa oganninsu sun gudu.
Ba k’aramin tashin hankali Yassir ya
shiga ba da ya fara jiyo kamar muryar Yash suna magana shi da Ummi a baki bakin k’ofar.
Aikuwa yana shigowa da shi ya fara cin karo ya juya baya yana magana shi da Ummi….
Tashi d’aya hankalinsa ya tashi ransa ya yi masifar b’aci zuciyarsa ta fara tafa
rfasa wani irin sabon haushi tsana da k’iyyayyar Yash d’in suka yi masa k’awanya..
“K’araso ciki Yassir!!”
Muryar Abhi ta katse masa tunani,a dake!.
Kasa juyawa Yashjub yayi sakamokon wani irin yanayin da ya tsinci kansa a ciki.
Yassir d’in kama
r ba zai kula sa ba sai kuma ya d’an matsoshi yace”sauk’ar yaushe?”
Bai jira jin amsar sa ba yace”welcome”
Daga haka ya wuce ciki dan he can’t stand him.
Parlourn taff cike daga Mommy sai Kausar wadda take ta uban bacci ba ma ta san sun dawo bane kawa
i babu.
Shiruu kowa ya yi har su Yadira da basu san me ke faruwa ba!
Yayinda su Daddy suka tsura masa idanu kawai.
Cikin nutsuwa Yassir d’in ya k’araso ya nemi guri ya zauna ya fara kallonsu one by one dan zuwa yanzu kam ya san something is defini
tely wrong.
Gyaran murya Abhi ya yi kafin ya kalli su Yasmeen yace “ku d’an bamu guri”
Girgiza kai Daddy yayi yace”ka barsu Abhi,Ina buk’atar shaidu.”
Bai jira d’aukar lokaci ba ya kallesu one by one yace”ina so duk ku zama shaidata!
Daga yau har g
aban abada babu ni babu Yassir!!!”
Sai kuma ya kalli Yassir d’in yace”mintuna arb’ain na baka ka tartara ya naka ya naka ka bar mini cikin gidana!!!!”.
Da mugun sauri Yashjub ya juya ya fita Yayinda su Yusra suka kaure da kuka suka shiga rok’ar Daddy s
una basa hak’urin ya taimaka ya bar Yassir ko me ya yi bai yi deserving haka ba!….dan Allah ya janye maganarsa.
Daina ji Yassir ya yi na y’an sakanni…
Ya riga ya san duk inda aka je aka dawo su grenade ne Ummul’abaisin wanan mummunan al’amari da ya far
u da shi a yanzu,dama ya san delay d’in da ya yi wajen sakar su dole ya yi facing consequences amma kuma a tunaninsa 3 million d’in da ya bayar ta isa ta yi silencing d’insu.
Innalillahi wa inna ilaihirrajiun ya shiga ambato a cikin ransa dan bai ma san m
ai zai yi ba ya zai yi ba mai zai ce ba!!!!.
Is this really happening to him kokwadai mafarki yake yi….zai iya cewa tunda yake a rayuwar sa bai tab’a zama helpless cikin matsanancin tashin hankali ba irin wannan!!
Na farko ya san tabbas an san me ya yi n
a biyu kuma yanzu shi idan ya fita ta ina zai fara?
Ba shi da halin da zai iya ciyar da rai biyu,besides da ma ya gama tsarawa ita kanta yanzu kam sai dai ta ci gaba da ciyar da kanta dan last kud’in hannun sa ne ya yi amfani da su ya je Abuja ya dawo……
Da farko zuciyarsa tunzurasa ta fara yi akan ya yiwa Daddyn bori yace”babu inda zai je sannan yace sharri aka yi masa amma kuma indai videos da voice d’in da mutanen suka turo masa shi suka turawa su Dad tou tabbas bai Isa ya fara cewa sharri baneba..Ida
n ya yi hakan kamar ya sake tsunduma kansa a wani sabon bala’in ne…so it’ll be better for him ya yi laying low a halin yanzu da halin da yake a ciki.
Cikin fushi Abhi yace”we are morethan disappointed in you Yassir ban tab’a tunanin za a samu b’ata gari
a cikin zuri’ar mu ba!dan haka tun kafin mu fara yi maka baki ka b’ace mana daga gani a yanzu yanzu ba sai anjima ba!.”
Dai dai nan Mommy ta sauk’o k’asan.
Wani Irin rikicewa parlourn ya yi da koke koke hatta Yahanasu sai da ta yi hawaye kafin daga
bisani ta mik’e ta shige d’akinta.
Dai dai nan Mommy kuma tana k’arasowa cikin parlourn ta tsaya a tsakiyarsu ranta a mugun b’ace hankalinta a masifar tashe jikinta yana wani irin karkarwa tace”Ashe dama gulma da munafuci aka shirya shiyasa na ganku gab
a d’aya kun yi family kun zo????”
Bata ga mik’ewar Daddy ba sai k’arasowar da yayi ya d’auketa da wani mahaukacin mari!!
Cikin tsananin fushi hargagi da hargowa yace”dabbancin naki yau har ta kan Mahaifiyata ya biyo Khadija!!!saboda ke mahaukaciya ce w
adda ba ta san wa ya yi mata gata ba shine a gaban idanunmu za ki furta wannan kalmar??
Waye ya ke yi miki munafurcin??”
Ya yi mata tambayar kamar yana shirin rufeta da duka!
Tashi d’aya Mommy ta sha jinin jikinta tashin hankalin da take a ciki ya sake
hauhawa…Tabbas a yadda ta ga Daddy ya fusata d’innan ta san muddin ta biye masa to fa za ta janyowa kanta matsala….
Shiyasa tashi d’aya ita ta sauk’o a take ta fashe da kuka ta durk’ushe a wajen cikin kuka tace”ka yi hak’uri Daddy dan Allah ka yi hak’uri
b’acin rai da tashin hankalin jin abunda kak’e ik’irari ga Yassir ne ya janyo hakan amma ka yi hak’uri da abubuwan da na fad’a ba zan sake ba sannan da n Allah ka yiwa Yassir adalci hak’uri ko me ya aikata a ganina bai chanchanci hakan daga gareka ba!”
Da mugun sauri Yassir ya mik’e ya fice..inshaaAllah tunda har Mommy ta sauk’o ya san za ta san abun yi.
Cikin kuka Ya’isha ta tari numfashin Daddy tace “Daddy ka yi hak’uri akan komai,dan Allah.
Sannan ka duba yadda fa ka ke yiwa Mommy!!!ka sanyata ta
durk’usa haka a gaban kowa!!
a gani na kamar yadda ranka ya b’aci muma namu fa zai b’aci idan ka tab’a mana mahaifiya!”
Cikin tsawa junior yace mata”bar nan kafin na yi ball da ke!!
Manya suna magana kina saka musu baki that too ‘rude tone’!!”
Harara t
a zabga masa wanda hakan ya sanya ya mik’e ya nufota gadan gadan,cikin bashi kwarin guiwa Hajiya mama tace”kana zuwa ka rufeta da duka kar ka raga mata!!”
Ganin yadda ya taho kuma ta san tsaf zai aikata ne ya sanya ta mik’e ta bar wajen da gudu ta haye sa
ma tana sharar hawaye.”
Tsaki Hajiya Mama ta yi tace”marar kunyar banza”
Sai kuma ta kalli ragowar tace”duk wadda na sake jin muryarta a cikin ku za ta sha mamaki.”
Yayinda Daddy ya had’iye wani abu mai d’aci a mak’oshinsa da kyar ya juya kawai ya k’a
rasa ya d’auki wayarsa ya fara k’ok’arin playing video d’in da sauri Abhi yace”ka yi hak’uri ba sai kowa ya ji ya gani ba”
Cikin fushi Daddy yace”tabbas Abhi ya kamata kowa ya ji ya gani sabida idan ba haka ba wannan makirar matar sai ta k’unsa k’iyayyata
a zuk’atan dukkannin jama’ar gidan nan dan cewa za ta yi Yassir bai yi mini komai ba hakanan na koresa,kalli fa kukan kissa da kisisinar da take yi bayan itace silar komai!
Muguwar zuciyar ta da gurb’atacciyar tarbiyyar ta su suka janyo komai dan haka ka
wai ka bari kowa ya ji ya gani.”
Daga haka ya wuce ya k’arasa inda take ya cilla mata wayar yace”bud’e ki kalla ,kalla ki ga abunda rashin tarbiyyar da kika yiwa y’ay’ana ya janyo mana!!ki duba kiga abunda Yassir ya aikata a d’an uwansa…..”
Tarin da ya s
ark’afe sa ne ya sanya ya gagara ci gaba da magana…
Da sauri Abhi da Hajiya mama suka k’arasa inda yake suka ruk’osa suka kaisa kan kujera suka zaunar Junior ya yi saurin matso masa ruwa daga dispenser ya kawo….
Shiruu parlourn ya d’auka in banda sheshsh
ek’ar kukan Mommy da na su Yassira ba ka jin komai!!.
Mommy ce take kallon video d’in amma iyaka voice d’in Yassir da bayanansa sun fahimtar da kowa na wajen abunda ke faruwa!!!
A tare Yasmeen da Yadira suka mik’e suka bar wajen suna wani irin kuka k
amar ransu zai fita dan ba ma su san abun cewa ba.
Da kyar aka samu Daddy ya dawo dai dai,tarin ya d’an lafa…cikin gajiya da komai ya d’ago ya kalli Hajiya mama yace”ki gafarceni Hajiya mama ba zan iya ci gaba da zama da matar nan k’ark’ashin inuwa d’ay
a ba!”
Gaba d’aya a tare Yasira
Yusra da Mommy k’irjinsu ya yi wani irin mahaukacin bugawa..Ummi kuwa ta san me Daddy zai yi dan ya dad’e da gaya mata matsayin Mommy a cikin gidan dan haka ta mik’e da sauri ta wuce sama…..
Har ga Allah Junior ya ji d
ad’in abunda ya faru da Yassir amma kuma sam bai ji dad’in abunda yake da shirin faruwa da Mommy ba shiyasa ya ce”Daddy koma me Mommy ta yi ka yi hak’uri…”
Cikin tarar numfashinsa yace”Junior ba ka san me ta yi ba!!!”
A hankali yace”Daddy ta ci albarkaci
n y’ay’anta!!!”
Girgiza Kai kawai Daddy ya yi yace”not anymore!!!
Daga haka ya kalli Mommy yace”shekaru 32 kina zaluntata Khadija..na san nima wasu lokutan na kan sab’a miki ta hanyar nuna soyayyar wata fiye da taki ko kuma nuna halin ko in kula da nak
e yi a kanki amma Khadija wannan ma duk laifin ki ne!saboda kin san ba na sonki ba na k’aunarki amma haka kika tilasta mini zama da ke…tsakanina da ke wata shari’ar sai a lahira dan wallahi ko da zunubin tarbiyyar Yarana da kika lalata a ka barki ya ishek
i!!
Duk wata cutarwa da kika yi mini da su Ubangiji zai saka mana!!
A alamarin Khadija
Sam ban kama ki da komai ba Tabbas kin yi k’ok’ari wajen kare kanki amma na san komai laifinki ne kuma shima zaki had’u da Ubangiji zai yi mana hisabi mu uku ya bi m
ata hakkinta wanda a ko da yaushe idan na tuna hankalina tashi yake yi matuk’a amma dole na san sai na fuskanci Ubagiji da wannan tarin