Showing 234001 words to 237000 words out of 259716 words
son Yassir ne ya sanya ta yi masa wannan borin??”
Ya yiwa kansa tambayar a cikin ransa, Saboda ya tabbatar ko k’aramin Yaro idan ya
ga video d’innan da voice da shaidu ya san ba had’awa aka yi ba.
Juyawa kawai ya yi ya shige cikin motarsa ya kunna ya wuce,yana tafiya ya turawa Yasira mesaage ya yi mata gaisuwar rashin da suka yi,dan Mommy tana shiga ya ga ta fito za ta zo wajensa sh
i kuma ba zai iya sake ci gaba da tsayuwa a k’ofar gidan ba zuciyar sa za ta iya tarwatsewa
..Tabbas Mommy ta tsaneshi!!!
Sai da Yasira ta bari Yassir da su Yusra sun shige ciki tukunna ta yi saurin ruk’o hannun Mommy k’asa k’asa tace”Mommy videos
d’innan da gaske ne fa!!Yassir da kansa jiya ya yi mini confessing…….da kin sani ba ki yiwa Ya Yash haka ba gaskiya,jiya dai na ji haushinsa da bai zo ya ganki ba amma yau ai da mun tsaya mun sauraresa tunda ya zo.”
Shiruuuu ta ga Mommyn ta yi..ba ta da
wani choice da ya wuce ta tubure kawai tace sharri aka yiwa Yassir dan haka ta cewa Yasirar ‘
rikicewa Yassir ya yi jiya shiyasa yace mata shine amma tabbas sharri aka yi masa……’
Rabuwa da ita kawai Yasira ta yi ta bari akan sai an kai Baba Larai zafin
mutuwar da komai ma ya fara raguwa r mata tukunna sai su yi magana da ita ta fahimtar juna.
….
Gaba d’ayansu kashe wayoyinsu suka yi saboda Mommy tace ba ta son y’an gaisuwa su san tana nan bama ta buk’atar ganin kowa a halin yanzu…da kyar da mugun kyar
suka samo matan da suka yarda suka yiwa Baba larai wanka dan a k’ank’arar da aka sakata jiya ya sanya yanzu kuma duk sai ta lagwab’e da k’ank’arar ta narke dan ko jikin nata kana tab’awa sai ka ji kamar zai biyoka ga uban wari!
Suma Matan dai daga k’arsh
en wankan kawai ruwa suka yayyafa mata aka yi mata sutura.
Sai la’asar tukunna suka samu aka sallaci Baba Larai aka kaita makwancinta…
Ana dawowa daga kaita
Mommy ta cewa Kausar ta tafi,ita tsoranta d’aya kar itama Kausar d’in Daddy ya koreta dan t
abbas suna da buk’atar ta a gidan…tare suka tafi ita da Junior Yasmeen da Yadira…..
Suna tafiya Yassir shima yace musu”zai wuce za su ci gaba da zama da wani Abokinsa kafin komai ya yi settling”
Mommy ta so ta tsayar da shi gudun kar wani abun ya same sa
amma da ta fahimci video d’in a iyaka family ne ya yi circulating hukuma ba su riga sun gani ba sai kawai ta rabu da shi ya tafi….ba ta kuma yi masa maganar ba saboda ta lura kamar ba ya son zancen!
Har ga Allah ita she’s proud of Yassir saboda ya yi yun
k’urin kawar mata da matsalar ta
(Dama ita tun a wajen da abun ya faru ta so ta fahimci shine ta kuma fusata da Yash d’in bai mutu da gaske ba)
dan haka ta bisa da kyawawan addu’o’i da fatan alkhairi su Yasira kuma ta ci gaba da yi musu borin ai sharrin
aka yiwa Yassir d’in.
Sai da Yash ya je ya ga Manu tukunna ya wuce gida saboda dama tun jiya take rok’ansa ya barta ta yi kwana uku tunda gida ma za su chanja ai kuwa da ya barta ta ji dad’i kwarai amma kuma tana ganin yanayinsa ta fahimci akwai mats
ala dannhaka ta hau tambayarsa bai b’oye mata ba ya gaya mata cewa”Daddy ya kori Yassir kuma k’arshen abun bai yi dad’i ba dan har da Mommy itama sai da ta bar gidan”
,sosai Manu ta tab’u daga jin zancen da kyar ta taushi kanta sannan ta yi namijin k’ok’a
ri wajen kwantar wa da Mijin nata hankali tukunna suka rabu ya wuce gidan Daddy shi da Najeeb dan yana gidan suka zo shi da Siyama.
Ita Manubiya ba ma ta yi tunanin da Siyaman aka zo ba dan basu dad’e da yin waya ba bata gaya mata ba sai da su Yash d’in
suka wuce tana shiga parlourn nasu daga parlourn Baba ta ganta a zaune ai kuwa nan suka hau murna har da hawayen farin ciki.
Sai da su Yash suka kama hanya tukunna ya tuna bai sanarwa su Manubiya rasuwar Baba Larai ba,dan haka ya bari a kan sai zuwa an
jima sai ya gayamata ya san dole za ta kirasu ko ma ta je addu’arsa d’aya Allah ya sa kar Mommy ta yi mata abunda ta yi masa itama da ma gashi ba ta sonta.
A b’angaren Kausar kuwa zuwa yanzu ta gama sanin abun yi dan haka jimamin Baba Larai yana d’an s
akinta ta kira Ya’isha tace”tana so ta had’ata da Abbakar akwai abunda zai yi mata”
Da kyar Ya’ishan ta had’ata da shi kuwa
Saboda last time Abbakar d’in ce mata ya yi “kowa kawai ya yi ta kansa daga yanzu!
dan plan d’in da suka had’a last time bai yi
masa ba gashi ba su yi winning ba gashi kuma sai da yayi watanni uku a asibiti…”
Hakanan dai ita Kausar ta nace sai da aka had’ata da shi saboda shi ne kawai ta ga intention d’insu ya zo d’aya tunda yana son Manu itakuma tana son Yash dan haka za su taima
ki juna,ta zauna ta yi tunani sam ba za ta wani biyewa Mommy ba wallahi!
Ba za ta iya hak’ura da Yashjub ba…kowa kawai ya yi ta kansa……….
Ita dai Yasira tana jinsu suna wayar da Ya’isha har aka tura number tana mamakinsu a ranta tace”wato dai wanda ya
mutu ya riga ya tafi!duniya kuma kowa sai ya ci gaba da abunda ya saka a gaba.
Kalli yadda suka ci gaba da k’ulle k’ullensu kamar ba yanzunnan aka dawo daga kai Baba Larai kabari ba.”
Ita ma Yusra lissafin da take yi kenan.
Ita sam ba ta yi tunanin Ka
usar d’in ta san da issue d’in Abbakar d’in ba ma maybe Ya’ishan ce ta fad’a mata.
Su Yassir suna gama tafiya Mommy ta cewa su Yasira su zo su raka ta…su sun yi tunanin ma kayan abinci da abubuwan buk’ata za su sissiyo sai da suka ga ta d’auki hanyar in
da za su je tukunna suka fahimci inda suka nufa…
Aikuwa suna isa suka shaida wajen…
Mutumin tsoho tukuff idan ka gansa ba za ka yi tunanin yana gani ba ma tsabar tsufa..hakanan ya k’araso inda suke dan suna yin parking suka ga ya fito yana zuwa yace”lale
marhaba Khadija yau kuma ina Larai??”
Sunkuyar da kai Mommy ta yi ta girgiza kanta a hankali wasu siraran hawaye suka zubo mata….
Shiruu ya yi ya d’an k’ura mata idanu kafin yace”Allahu Akbar amma an yi babban rashi..Allah ya ji k’anta!mu je daga ciki
”
Daga haka suka nufi ciki.
Shi wannan tsohon!wanchan bokan na k’auyen su Baba larai shi ne ya had’ashi da ita tun asalin farko kafin ya rasu kafin ta baro ma k’auyensu ta da who nan Kano inda yake…..idan abubuwa suka shige masa duhu ya kan tambayeta i
tama haka,har nan suna zuwa ita da Mommy idan aikin da suke son yi ya had’a da wanda mace ba zata iya yi ba sai su kawo shi ya yi musu.
….
Sai da ya sake yi mata gaisuwa ta amsa tukunna ba tare da b’ata lokaci ba tace masa”Yashjub ya yi aure ba ta samu a
bunda take so ba har yau kuma Yarinyar ta zo da farar k’afa mutuwar Baba larai na daga cikin masifun da Manubiya ta zo mata da shi saboda dama Baba larai tace
muddin aka aurota to fa an yi ta ganin bala’i kala kala.Yanzu haka ma ba ta gidan Daddy jiya ya
yi musu korar kare ita da Yassir….”
Salati tsohon ya yi kafin ya janyo wata tukunya fall ruwa yana duba cikinta yana jimami….
Sun fi minti ashirin a haka kafin chan ya d’ago ya kalleta yace”ai kin yi kuskure!irinsu waennan ba a barinsu a doran k’asa!
ai idan aka yi aiki ya k’i ci ya k’i cinyewa rabasu da duniyar ake yi tunda sun fi k’arfinka to ta ya zaka tsaya fafatawa da su ai ba zai you ba!”
Ajiyar zuciya Mommy ta sau’ke dan ba k’aramin dad’i ta ji da jin wannan batun ba saboda dama ita takanas a
bunda ya kawota kenan!!a yi ta ta k’are kawai.
Cikin k’aguwa tace”aikin gaggawa nakeso ka yi mana,ba na so Larai ta kwana uku a kabari ba tare da Yarinyar nan ta bi ta ba!”
Cikin tarar numfashinta Yasira tace”Mommy wai kisan Kai kike nufi??”
Murmushi
tsohon ya yi kafin yace”to ai hakan kawai ce mafita!saboda Wallahi Allah muddin Yarinyar nan tana raye tou fa bala’i da masifu yanzu kuka fara gani!!!”.
K’ura masa ido Yasira ta yi kafin chan ta d’auke kanta ta mayar ga Mommy tace”Mommy mu je gida ma yi
magana Plss dan Allah ki bar maganar nan!”.
Girgiza Kai kawai Mommy ta yi kafin ta ce”Yasira har yanzu ke Yarinyace..dan gashi duk abubuwan da suke faruwa a gaban idanunki ba kya gani!inaga sai na mutu kin binne ni tukunna za ki fahimci abunda muke nuf
i!!!”
Da d’an zafi Yasira tace”Mommy Manubiya b….”
Cikin katseta da tsawa sosai Mommy tace”za ki yi mini shiru ko kuma in kora ki waje????”
alamun ta yi shiru su Ya’isha suka yi mata dan haka kawai ta yi shiru ba dan ta so ba kuma wallahi wannan tab
’argazar ba da ita ba ba za ma ta bari a yi ba…
Sai da Mommy ta yi kusan minti d’aya tana hararar Yasirar tukunna ta mayar da kanta ga tsohon wanda shima yake cewa Yasirar “ki tsaya ayi abu a nema muku mafita hatta rashin aurenku duk itace gashi nan na
gani a nan!ko ba kwanan nan wanda za ki aura ya yi aure ba???”
Ita dai Yasira banza ta yi da shi Yayinda Mommy da Ya’isha suka aminta da maganar ta shi d’ari bisa d’ari…
Murmushi kawai ya yi ya mayar da dubansa ga Mommy yace”kar ki damu komai ya zo
k’arshe inshaaAllah!”
Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin tace”yanzu nake so a yi aikin..saboda na gaji na tsani…”
Cikin tarar nunfashin ta yace”sai dai a yi aikin a yau da daddare gobe a tashi babu ita!!”
Jin jina kai ta yi tace”hakan ma ya yi”
“To Alhamdulillah” yace kafin ya d’aura da cewa”yanzu akwai yadda za a yi in samu hularta???”
Kallon juna suka yi ita da Ya’isha suka yi shiruu kafin chan Ya’ishan tace”eh!!
Da me kuma??”
“Iyaka hula,kawai!
Ki tabbatr tana cirewa daga kanta kin k
awo mini kai tsaye ba tare da kowa ya saka ba!
Shikenan abunda na ke buk’ata.”
Cikin yin serious da fuska sosai,ya ture tukunyar gabansa ya mayar gefe ya kallesu sosai yace”da farko dai inaso ku fahimci cewa shi RAI!!
Bayar da shi da karb’arsa wannan Ub
angiji ne kad’ai ya isa bi’ma’ana Ubangiji ne kad’ai yake bayar da Haihuwa yake kashewa bayan shi babu wanda ya isa,duk bala’in mutum bai Isa ya kashe ko ya raya ba…”
Jimm Mommy ta yi tana jin wani sabon tashin hankali yana rifeta, kar dai mutumin nan yac
e ba zai iya yi mata komai ba kuma!!!
Tana wannan tunanin ta ji ya ci gaba da cewa”Abunda mukeyi idan matsala irin taki ta taso shine wannan aikin da zan yi muku a yanzu ammafa yanada matuk’ar hatsari kuma yana buk’atar taka tsantsan!”
Sai da ya sauk’e n
umfashi tukunna ya d’aura da cewa”ita wannan hula da za’a kawo itace nake so a kiyaye kar a samu matsala wani ya saka bayan ita Yarinyar saboda idan aka samu matsala to fa shi wanda ya saka bayan itan da wanda ya kawo duk su biyun aikin zai fad’awa kuma id
an aka yi ba’a janyewa bima’ana idan aka yi an riga an yi ba a tab’a iya karyawa!!!”
Jinjina kai Mommy ta yi tace”na ji na fahimta inshaaAllah za a ayi taka tsantsan..ya aikin yake?”
Ta yi masa tambayar tana kallonsa.
Murmushi ya yi kafin yace”rik’e m
ata numfashi zan yi!…idan kaff likitocin duniya ne za ace su zo su taru a kanta babu wanda ya isa yace tana da rai saboda komai tsayawa zai yi.
Daganan Idan aka yi mata wanka akai mata sutura aka kai ta kabari aka binne muka tabbatar an kai ta ni kuma sai
in saki numfashin ya dawo..kinga dai ai bata isa ta fito ba ko?sai dai ta k’arasa a chan!!”
Ya k’arashe maganar tasa yana sakin dariya…
Da sauri Yasira ta mik’e ta fita hankali a tashe ranta a masifar b’ace..Tabbas bayin Allah marasa Imani suna da yawa
a duniya..ta ya mutum zai iya aikata haka a d’an Adam musulmi d’an uwansa?.
Wani sanyi da nutsuwa Mommy ta ji daga jin bayaninsa dan bata tab’a jin hukunci mafi dacewa daya dace ace ta yankewa su Manubiya ba kamar wannan!!!
Har za ta yi magana sai ku
ma ta tuna da su Yusra dan haka ta kallesu tace”ku d’an bamu guri!”
Sai da ta tabbatar sun fice daga cikin gidan gaba d’aya tukunna ta kallesa tace”Ana iya yiwa Namiji ma ko?”
Dariya sosai ya yi kafin yace”Yashjub ko?
Tsaff za ki yi masa shima amma
shi gashin kansa za ki kawo.”
“……….Samun gashin kan Yashjub zai d’an yi wuya amma hular Manubiya yanzunnan ka jira a daren nan za ka samu,za ‘a iya kawo ribbom ma?”
Jinjina kai yayi yace”indai ya tab’a gashin kanta ku kawo!!”
Wani irin farin ciki ne
ya lullub’e Mommy gudun ma kar su ci gaba da b’ata lokaci ya sanya ta mik’e da sauri tace masa ya bata awa d’aya da rabi daga haka sukayi sallama ta fita jikinta har yana b’ari ranta fess.
A mota duk ta samesu a zaune Yasira ta had’e rai kamar ba ta t
ab’a dariya ba!!
Ta san idan ta biye mata b’ata mata lokaci za ta yi dan haka ta sa hannu ta d’auki Jakarta ta kalli Ya’isha tace mata “zo”
Su kuma su Yasira tace”ku wuce gida.”
Yasira za ta yi magana tace”na rantse da girman Allah Yasira zan yi miki Ba
ki!!idan kuma kema Yasmeen da Yadira za ki zama bismillah ki tattara ki koma gidan ubanki kar ki damu da damuwata!Allah zai yi mini gata!”
Sai kuma tafashe da kuka tace”Larai ce fa ta rasu amma kalli Yadira da Yasmeen ko yunk’urin zama inda nake basuyi ba
ballanata su taushe ni,tunda Manubiya ta zo cikin rayuwarmu komai ya hargitse ku kanku ya’yana an juya muku lissafi kalli abunda kuke yi mini sannan ki ce wani in hak’ura?”
Cikin zubar hawaye Yasira tace”gaskiya fa nake gaya miki Mommy kuma son da nake
yi miki ne ya sanya nake k’ok’arin kub’utar da ke daga hanyar tsira!
Saboda Allah ta Ina kashe Manubiya ya zamto hanyar warwarewar waennan abubuwan da kika lissafa Ina riba a kashe rai??….kece fa baki tsaya kin nutsu kin fuskancemu ba shiyasa kike ganin
kamar mun juya miki baya,Yadira fa ciki ne da ita amma baki ma lura ba kina ta abubuwan gabanki tunda ta yi aure ba ki damu ki duba ya take ba!ko d’azun ma amai ta yi shiyasa junior d’in yace su wuce asibiti kuma na san za ta dawo ba wai k’in zama ta yi a
wajenki ba,kawai bamuga kin nustu bane balle ki bamu listening ear shiyasa kika ga bama…”
Cikin katseta tace”to duk ba uban ku bane ya rikitani kwana biyun nan!wai Yasira “
Itama cikin katseta tace”Mommy babu laifin kowa ba….”
Marin da ta d’auke ta da
shi ne ya sanya ta yin shiru…cikin fushi tace”ku wuce gida!!!”
daga haka ta ja hannun Ya’isha suka wuce suka tari napep….
Sun dai san gandu ne Gidan amma sai da Ya’isha ta kira Yadira ta yi mata kwatance tukunna suka d’au hanya….k’asa k’asa gudun ka
r mai napep d’in ya ji Mommy tace”kina da idear yadda za a yi a samo??”
Jinjina kai Ya’isha ta yi itama k’asa k’asa tace”zuwa zan yi kawai in gaya mata abunda ya faru da Yassir da ke in ce mata nazo ne akan in rok’eta ta yiwa Yash da Hajiya mama magana a
samu ku dawo!
Durk’usawa wada ba gajiya bane ba mu dai kawai mu samu abunda muke so…
A ganina hakan shine kad’ai option d’inmu idan ba hakan ba kin san halinsu da rashin yarda na san ba lalle ta sake da ni mu keb’ance in samu in d’auki abunda nake so d’i
nba.”
Jin jina kai Mommy ta yi tace to ni kenan ba sai na je ba ko?tunda ban jiyo ni a cikin plan d’in naki ba!”
“Eh kawai ku juya idan na gama zan same ku a gidan mutumin ai na gane ba wani nisa ma.”
“To shikenan” Mommy tace daga haka ba ta sake
cewa komai ba har suka kaita ta shige ita kuma ta juya……..
A gate ta same su ita da Siyama, ta rakosu har da Najeeb suna ta hira suna dariya….da kyar da mugun kyar Ya’isha ta hana kanta kuka saboda ko waye ya kalli Najeeb da Siyama ya san hankalinsu a k
wance yake kuma suna matuk’ar k’aunar juna!
Sunyi wani irin kyau sun yi k’iba sun yi fresh har wani glowing suke yi especially ma Siyaman dan in ba kwakkwaran sani ka yi mata ba ba lalle ka iya gane ta ba sannan idan baka santa ba in har ba bakinta ta bud
’e ta yi maka Hausa ba to ba za ka tab’a cewa y’ar Nigeria bace ba…..
Wani k’ululun bak’in ciki tashin hankali da kishi ne ya tokare mata mak’oshi!dama tun d’azu da aka fara maganar tsayar da numfashi Siyaman kawai ta hararo…inshaaAllah ana gama na Manu
biya itama za ta san yadda ta yi ta nemo nata yanzu haka ma dan ta