Showing 126001 words to 129000 words out of 259716 words

Chapter 43 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

88

hawayensa da kyar tukunna ya cika ta ya d’ago fuskarta ya yi cupping a cikin tafukan hannuwansa sannan yace

‘’Thankyou Manu,I become complete and happy because of you,sannan gashi yanzu za ki bani gift d’in

da na dad’e Ina kwad’ayi,na gode Baby I love you more than life itself….”

Ahankali ya sake sakata a jikinsa ya rungume.

Sun jima a haka yana ji kamar kar ya cikata su tsaya a haka har abada,kafin da kyar suka saki juna ya wanke fuskar sa suka fita.

Fuskar Yash kawai Yahanasu ta kalla ta fahimci kuka ya yi kuma tana da tabbacin kukan farin ciki ne dan haka ta k’arasa garesu da sauri ta had’asu ta rungume cikin tsananin murna tace ‘’congratulations’’a hankali

yayi murmushi ya ce ‘’Thankyou Yaha,‘’wa

nda hakan ya sake tabbatar mata ai kuwa Baki har kunne haka ta hau murmushi mai had’e da dariya tana jin tsananin farin ciki.

Ita ta k’arba abun gwajin ta kaiwa Dr.

Cike da murna ya matsa kusa da su ya yi congratulating d’insu sannan ya d’aura da cewa

“a halin yanzu ba zai ce ga exact weeks na cikin ba amma anytime from now suna iya zuwa clinic d’insa a yi gwaje gwaje a tabbatar da lafiyar Baby.”

A take Yashjub ya ce “su tafi yanzu tare da shi kawai”

Murmushi Dr d’in ya yi yana yaba tsananin kulawar

Yashjub ga Babyn da matar sa..sai a lokacin tukunna Yasmeen ta matso tana murmushi ta yi congratulating d’insu

Dariya Yashjub ya yi yace “young Dr! sai na bawa Baby labarin yadda kika kusa d’ura masa allura ai saboda rashin kwarewa…”

Ahankali ta sunkuy

ar da kanta k’asa tana murmushi a ranta tana jin kamar ta fashe da kuka tsabar regret da kunya da takaicin Mommy…a d’ayan b’angare na zuciyarta kuma tana jin wata nutsuwa dan tabbas ta ji dad’in zuwan Doctor if not because of him da tuni ta aikata abunda i

ta kanta ba za ta tab’a yafewa kanta ba.

Waje suka nufa gaba d’ayansu ban da Mannubiya…

Ba iyaka Manubiya wadda ke daga d’aki tana jiyo su ba hatta Yahanasu wadda dama ba ta so ma maganar ta fito ba,sai da ta ji kunyar yadda Yashjub ya zage yana mai

sanar wa y’an parlourn ai Manubiya ciki gareta!.

Har gaban Daddy ya je ya tsaya ya gaya masa cike da tsananin murna da farin ciki..

Sai da ya gama fad’a ya ga kowa ya yi shiruu yana kallonsa a take kuma sai wata kalar kunya ta lullub’esa.

Murmushi Daddy

ya yi yana jin wani farin cikin da ya dad’e bai ji ba kafin ya dafa kafad’ar Yashjub d’in yace

‘’Allah ya inganta Allah ya raya ya kawo mana sanyin idaniyar mu duniya lafiya.

Tun da nake da kai zan iya cewa ban tab’a ganin farin ciki irin wannan akan f

uskar ka ba.”

Sai da ya d’an k’ura masa ido kafin yace “har kukan murna ka yi ne??”

Ya yi masa tambayar da alamun sigar zolaya wanda

hakan ya sa Yash d’in sake sunkuyar da kan sa k’asa sai kuma ya juya da sauri yace

‘’Bari mu je asibiti’’

Ya fad’i h

akan yana mai ficewa waje.

Sai da Yahanasu ta koma d’aki tukunna suka kimtsa suka fito.

Manubiya ta ji dad’in rashin ganin kowa a parlourn dan dama ba ta san ta Ina za ta fara had’a ido da su ba…..

Had’ad’d’en checkup ya sa aka yi mata.

Hankalins

a bai kwanta ba sai da ya sa akayi masa scanning da taimakon bayanin likitan ya ga location d’in jininsa d’an sati biyu tukunna..

Dr kan sa ya sha kyauta…sai bayan sallar magrib bayan an gama yi mata allurai da k’arin ruwa leda d’aya suka karb’i magunguna

tukunna suka nufi gida cike da murna da farin ciki…

Shi yake driving sai Manubiya a gefen sa da Yahanasu a baya.

Sun zage da shi da Yahanasu suna ta lissafin kayayyakin Baby da abubuwan da ya kamata a fara siya…

Murmushi kawai Manubiya ta yi tana sa

uraron su tana jin wani sanyi a ranta tana kuma sake godewa Allah wanda ya bata Yashjub a matsayin Miji.

Sam murna da zumud’in da ya ke yi a kan cikin ya gagara b’oyuwa,dan ko baka tab’a ganin sa ba tashi d’aya za ka fahimci yana cikin tsananin farin ciki

a yau.

Wayar ta ce ta d’auki k’ara, wanda hakan ne ya katse musu hirar ta su

shi da Yahanasu.

Kamar ba za ta d’auka ba

sai kuma ta sa hannu ta d’auka.

Tana nan kishingid’e a yadda take haka ta saka wayar a kunnenta ba tare da ta bud’e idanunta

ba tace ‘’Assalam alaikom’’

Ahankali Abbakar ya lumshe ido daga d’ayan b’angaren yace ‘’Wslm Manu,ykk kwana dayawa’’

Shiruuu ta yi ta k’i yin magana ta k’i cewa komai

Cikin yanayin sanyin muryarsa yace ‘’Abbakar ne’’

Yanzun ma shiruu ta yi dan dama t

un farko ita ta fahimci shi d’in ne..

Wato sai yanzu zai waiwayeta sai yanzu zai nemeta haka kurum ya d’auke kafa ya yi shutting nata out

sai yanzu zai wani kira ta!.

Muryar sa take ji yana magana amma ba ta fahimtar sa sakamokon aman da ya taho mata

tashi d’aya…dan haka kawai ta kashe wayar ta ajjiye a gefe ta d’ago ta kalli Yashjub. Wanda yake mamakin waye ne ya kira ta haka ta gagara cewa komai

Kuma kamar muryar Namiji ya ji yana magana.

Da sauri ta toshe bakinta ta na yi masa nuni da ‘za ta y

i amai’

dan haka ya ja ya faka a gefen titin da sauri ya bud’e motar ai kuwa ta shiga shek’awa…

Aman da ta yi sai da ya ba su tsoro tsabar yawan sa.

Ba yadda ba ta yi da shi kar ya koma ba amma haka ya juya akalar motar aka maida ita asibitin.

Suna zuw

a kuwa Doctor ya yi admitting d’inta,sai a sannan Yahanasu ta kira su inna ta sanar da su haka ta kira Ummi itama dan ta ji ta shiru bata neme su ko ta ce za ta zo ba kuma d’azu bata ganta a k’asa a parlourn ba dama.

Ba ta yi mamakin jin Ummin bama ta san

ciki ne da Manubiyan ba

Tace mata “d’azu ta je side d’in Daddy ta tarar ya fita da ta sauk’o ta tambayi Yadira kuma tace mata wai sun je gidan su Manubiya ne za ta gaida iyayenta”

“Hmm”kawai Yahanasu tace

Daganan ta mik’awa Manubiya wayar suka gais

a da Ummi har ma da Yashjub ta yi musu murna daga nan tace musu gata nan zuwa inshaaAllah.A daren kuwa ta zo.

Su inna ne dai Yashjub ya kira ya lallab’a su yace “jikin nata da sauki su bari gobe su zo yanzu dare ya yi”.

Aikuwa washegari da sassafe d’

akin ya cika taff su Inna da Ummi duk suka baiyyana,

Manubiya har da kukan shagwab’a da ta ga su Innaa.

Gata kam ranar ta ganshi har da d’an hawayen farin cikin ta.

Abinci kala kala daga wajen Ummi Inna har da Mama wadda shigar ta gidan kenan ta tara

r ana shiri dan haka ta ce “su jira”

Haka taje ta had’o mata d’an Malale mai d’an karen dad’i tace a kawo mata bayan ta kira ta ji ya jikin nata….

Yassir gaba d’aya ya fice daga haiyyacinsa

A tsarin sa sai bayan kamar kwana d’aya zai aiwatar da

shirin sa amma kuma farin cikin da ya ga Daddy yanata yi ne ya sake hassala shi dan d’azu ma da Daddyn zai fita ji yayi yana waya a kan Yashjub d’in ya san kuma gift ko wani abun zai k’ara masa in ba da kyar ba.

Ga Kausar kuma da ya lura da yadda ta burk

ice itama tashi d’aya…abun ba k’aramin sake hassala shi ya yi ba.

Shiyasa kawai ya shiga d’aki ya rufe ya shiga aiwatar da shirin nasa.

Suna zaune ana ta hira da Ummi da Innaa kawai sukaga an turo k’ofa an shigo.

Ita kanta Manubiya ba ta yi tsamma

nin ganin Mommy ba

duba da yadda kaff cikin su babu wanda ya d’au waya ya kirata har ta kwana ta ke shirin wuni….

Cike da sallama faram faram Mommy ta shigo suka hau gaisawa Yasira da Ya’isha suna a bayan ta.

Yahanasu ce ta bawa Mommy kujera ta zau

na bayan sun gaisa.

Cike da girmamawa su Jidda da Muhsin ma suka gaida ita sab’anin su Ya’isha da suka koma gefe suka k’ame kamar ba su ga su Innaa ba.

Suna zaune d’akin ya yi jugum tun shigowar su Mommy

Yashjub suka shigo shi da Najeeb wanda ya d’an

rame kana ganin sa ka san yana cikin damuwa…

Karairaiyar da Ya’isha ta dinga yi da shishshige masa har zuwa lokacin da ya fita saida ya bawa Jidda kunya,shi kuma yanata basar da ita kamar bai ma san ta na yi ba.

Hakanan ya yi wa Manubiya ya jiki bayan

ya ajjiye uban tulin laidojin hannusa ya juya ya yiwa su Innaa da Mommy Allah ya k’ara sauk’i ya fita.

Murmushi kawai Jidda ta yi a ranta tace”kina nan kina iyayi”

“Yana chan yana ziryar zuwa gadon k’aya ba a kula sa.”

A d’akin su Inna suka zo su

ka tarar da Ummi shiyasa Ummin ta mik’e ta fara haramar tafiya dan ta na so ta d’an ba su guri kuma ta lura kamar akwai maganar da Innar ta ke so su yi saboda taga matar sai yawan yin shiru ta ke yi kamar tana ta tunani.

Ummi tana mik’ewa Yahanasu ma ta m

ik’e tace “Bara itama ta je ta d’an shirya tanada client da za su had’u in the next 2 hours”

Ta riga ta san Yashjub yananan ba inda zai je 24/7 shiyasa hankalin ta kwance sukayi musu sallama ta bar su Mommy a d’akin suka tafi tare da Ummi wadda take ta ad

du’ar Allah ya sa su Mommy ma su yi kan gado su bar Manubiya da y’an uwanta su d’an keb’e dan ta san rabon da su yi eyes to eyes tun kafin ta tafi honeymoon..

Ita kanta Manubiya so take ta keb’e da ahalin nata dan ta lura ba iyaka Inna ba hatta Jidda ka

mar tanada damuwa

bayan ta Al’ameen wadda ta riga ta san ta da ita..

Sannan kwana biyu ba ta ji Ya Musbah ba kuma ta kirasa a waya ko jiya ma bai d’auka ba! “anya kuwa lafiya??”

Ta yi wa kanta tambayar a cikin ranta.

Illai kuwa! wannan itace damuwar s

u Innar saboda tun bayan sati 6 da suka wuce

da Baraka ta tare Abu bai yi dad’i ba…zuwa yanzu Inna ta fahimci ashe ladabin kura Baraka ta yi musu,

tunda gashi yanzu ta rabasu da Ya Musbah…

Tana tarewa ko sati ba ta yi ba tace “ita ta tsani unguwar”

Haka nan jikin sa yana rawa ya d’auki d’an kud’in da ya tara zai biya kud’in registration d’insa dan lokaci ya kusa cika

Suka tashi a unguwar suka kama wani gidan a Na’ibawa chan nesa da su Inna tsabar rashin adalci irin na Baraka.

Kuma ta hanasa fad’a m

usu sai a ranar da za a tashi d’in.

Da dafarko da suka tashi yana zuwa duk bayan kwana biyu a d’an mashin d’in sa,sai ya dawo zuwa bayan sati d’aya tou tun daga nan basu sake saka shi a idanunsu ba gashi kayan abincin su ya k’are. Jiya babu kalar kiran

da Jidda ba ta yi masa a waya ba amma ya k’i d’auka….

Tabbas sai yanzu Innaa ta yi data sanin barin shi ya dawo da Baraka

Dama baba yace mata “Indai Baraka ce tou kuwa za ta sha mamaki…”

Gashi kuwa k’iri k’iri ta rabata da d’anta kuma tun da ta dawo ab

u guda da inna ta fara noticingm shine Yaa Musbah mugun mugun tsoron ta yakeji.Gashi baka Isa ka ce abunda ta yi bai kamata ba tashi d’aya zai hau kumbure kumbure

Tun a kan issue na tashin su da Innaa ta so ta hana tashi d’aya ya nuna hakan fa ba zai yiu

ba!.

Muhsin kuwa da ya yi alk’awarin d’auka ko kalar k’ofar gidan sa na Na’ibawa bai sani ba.

Ya Nafi’u kuwa ko waya basa yi,tun lokacin da ya dawo da Baraka dama ya fice a harkar sa,ko da ya zo tashi ma bai gaya masa ba dan ya san zai hana shi shima

kuma ya Nafi’un har yau bai ce masa

Musbahu Ashe ka tashi ba,

K’ark’ari ya kan je ya duba su Inna shi da Aisha da Khairat duk bayan kwana biyu amma shi da Ya Musbah kam ko a waya sun daina gaisawa,Baba ne dama ya kamata ya tsawatar ya dawo da Abotar tasu

to shi kuma Baba tun lokacin da Inna ta amince a dawo da Baraka tashi d’aya ba tare da ta shawarci kowa ba

Ya ce “case in dai na Musbahu da Baraka ne to ba zai bada shawarar komai ko ya ce zai saka baki a kai ba…”

Gashi issue na Baba da su Baba Habu ab

un ba dad’i

Kaka mallan ma ya fara gulmace gulmace wai Baba ya bi kud’i ya aurawa mai kud’i y’arsa amma gashi ya barsu a talauci har yau bai tab’a ganin an kawo ko kwayar shinkafa k’ofar gidan ba.!”

Inna tana wannan tunanin Yashjub ya dawo d’akin yana

ta faman sussunnar da kai,

so yake ya tambayi Manubiya mai take so ta ci dan tun yoghurt d’in safe sai d’an malelen Mama da ta ci daga su bata sake cin komai ba gashi Doctor yace “ana so ta dinga cin abinci sosai saboda lafiyar ta da lafiyar Babyn”…to kum

a shi har ga Allah kunyar Inna yakeji

dan d’azu ma sai da Ummi ta sa ya ji kunya

Haka nan ta tisa shi a gaba tana tsokanar kalar zumud’in da yake ta yi a gaban su Innar…

Yana wannan tunanin ya ji wayar sa ta d’au k’ara kamar ba zai d’auka ba dan da

ya zaro bak’uwar number ya gani sai kuma ya d’auka ya kara a kunnen sa yace ‘’Assalam alaikom,’’

A gigice ya ji wata murya kamar ta security d’in sa yana cewa”Sir wuta!wuta!! ya kama a estate na kano ka zo

da wuri…….’’yana gama fad’in haka ya kashe wayar

daga background d’in in banda hayaniya da k’arar y’an kwana kwana ba abunda yake tashi.

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”ya shiga ambata a fili.

Da sauri Yasira ta matsa tace ‘’mai ya faru?’’

Cikin karkarwar murya da kyar ya kalleta yace

“Estate

d’ina ne ya kama da wuta’’

Salati gaba d’ayan su suka saka suka mik’e tsaye.

Cikin tsananin gigita Yasira tace “subahanallah!!

mu je mu je da sauri…”

Ta fad’i haka tana yin gaba.

Da sauri ya ruk’o hannunta yace

‘’noo it’s not safe kar ki damu za

n je ni d’aya zan kira Yassir a hanya sai mu had’u a chan.

A hankali ta d’an dawo ta tsaya kafin tace “Allah zai mayar da alkhairi inshaaAllah’’

Jinjina kai yayi yace”inshaaAllah”sannan yace”ku yi addu’a Allah ya sa mutane ba su mutu ba!”

Jin jina

kai ta yi,daga haka ya zare hannunsa a nata ya k’arasa inda Manubiya take zaune a kan gadon ya ce “bara in je ko?”

sai kuma ya d’an sunkuya yace

“Dan Allah kar ki d’aga hankalin ki I’ll be back soon okay?”

Ba ta san lokacin da wasu hawaye suka zubo m

ata ba,ita ya kamata ta lallashe sa amman kalli shi yake lallashin ta.

Da sauri ta sunkuyar da kanta tana jin jina kai…

Murmushi ya yi yai sallama da su Innaa daganan ya juya ya fita gaba d’aya suna jajanta masa tare da adduar alkhairi.

Yana fita ta s

ake sakin kukan ta tana jin wani iri a cikin ranta

A hankali Innaa ta koma kusa da ita ta zauna ta shiga lallashin ta tana bata baki,Mommy kuma ta shiga kiran Daddy domin ta sanar da shi halin da ake ciki.

Cikin rashin jin dad’i Ya’isha tace

“Ai d

ama matsalar had’a jini da mai farar k’afa kenan!

Dama ace a iyaka aure aka tsaya to da na san abun zai zo da sauk’i”.

Shiruu duk suka yi d’akin ya d’auki shiruu

Kafin Ya’isha ta sake cewa “Allah dai ya rufa asiri ya kuma tsayar a iya nan’’

Zuwa ya

nzu Manubiya ta ji ba za ta iya jurar cin fuska a gaban ahalin ta ba Ashe dama jiya da suka dawo saboda a gaban Yashjub ne shiysa suka yi mata kissa kenan suke wani nan nan da ita…

Shiyasa kawai cikin wani irin fushi da ba ta san tana da shi ba ta mik’e t

a cewa Inna “ta zo su tafi”

Cikin rashin jin dad’i Mommy tace “Kamar ya ku tafi?

Me kike nufi?

Idan tafiya kike son yi ai mu za mu tafi da ke ba Innaa kad’ai ba ko?”

“A’a inaga tana nufin za ta koma gidan ubanta ne!

Ai ta shafa farar k’afar tata y

adda ya kamata shiyasa ta ga ya ci ace ta tafi…”

Ba k’aramin mamaki Innaa ta yi ba ganin yadda ko gezau Mommy bata yi ba balle asa ran za ta cewa Ya’isha tayi shiru wadda ta cigaba da fad’o zafafan maganganun kamar tab’ab’b’iya.

Cikin nutsuwa Innaa

ta mayarda Manubiya ta zaunar da ita tace”kar in je zance mara dad’i ki zauna ki yiwa mijinki addu’a ki jira dawowarsa”

tukunna ta kalli su Jidda wadda har ta fara kwallah tace mata ‘’ku tashi mu tafi’’

Sai da suka mik’e tukunna Innaa ta juya ta k’arasa

in da Mommy take tace mata ‘’Hajiya mun tafi,Allah ya k’ara sauk’i’’

Daga haka ta fice ta na jin yadda kukan Manubiya yake dira a cikin zuciyar ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login