Showing 114001 words to 117000 words out of 259716 words

Chapter 39 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

84

malaria ne? Ko mu je a duba ki sosai sosai..kin san yawanci y’an mata fa kunada matsalar da ku kanku baku sani ba sai likita ya duba da ikon Allah sai kiga an dace…”

Shiruu ta yi ta sunkuyar da kanta k’asa alamun ta shiga damuwa shiyasa tashi d’aya kamar zai yi kuka yace “Shiyasa fa kika ga na kasa yi miki maganar tun tuni

Banason b’acin ranki ni kuma har ga Allah a matse nake inji good news…”

Murmushi ta yi tace

“ba b’acin rai bane kawai dai nima kasa na fara tunani ne..”

Sai kuma ta d’an yi shiruu kafin ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya tace”Mu yi addu’a !mu yi ta addu’a!”

Daga haka tayi shiruu ta fa’da duniyar tunani….itanma babban burinta a yanzu shin

e ta ga babyn ta da Yash amma gashi shiru har yanzu, da farko tana gani kamar ya yi wuri amman itanma yanzu ya jefata a damuwa…wat if ta kasance a cikin matan da basa haihuwa ya kenan?ta san shikenan ta rasa soyayyar Yashjub

Dan a yadda ta ga k’ulafucin

son haihuwa a kwayar idanun sa ba lalle ya iya zama da ita kad’ai ba tare da yara ba sannan ba lalle ya ci gaba da sonta kamar yadda ya ke yi ba.

Yashjub ya riga ya saba mata da zazzafar soyayyar sa

Idan ya juya mata baya ba ta san ya zata yi ba.

Da s

auri a cikin ranta tace

“Ya Allah ka sa zan haihu nima Ya Allah ka bamu y’a y’a masu albarka.”

Ahankali yace”kar fa ki saka damuwa a ranki

Ki yi hak’uri idan na d’aga miki hankali”

Girgiza kai kawai ta yi tace “ba komai”ta d’an yi murmushi dagana

n ta mik’e ta fara shirin ta shi kuma ya fad’a toilet yin wanka.

Har ya fito a yadda ya shiga ya barta hakan ya dawo ya tarar da mood d’in ta shiyasa ya yi ta janta da wasa yana k’arfin halin ganin ta sake dan shima a damuwar yake

Ya san it’s too soon

amman mostly ana samu da wuri ai.

A haka suka yi breakfast d’in kowa da abunda yake tunani kafin yace “ta zo su je su d’an kammala shirin tafiyar tasu dan jibi suke so su wuce uk su duba jikin Na’ima su yi musu two weeks inshaaAllah daga nan sai su wuc

e Nigeria.

Ko da suka fita gajiya ga ciwon marar period d’in da take yi ne ya sa Yash ya dawo da ita bayan ta gama duk abunda ya kamata shi kuma ya koma.

Sai dare ya samu ya dawo

Washegari komai nasu ya kammala ta inda zasu bar Cyprus nan da kwana

biyu.

A cikin kwana biyun nan saida Yashjub ya san yadda ya yi ya cire mata damuwa dan ya lura tunda ya yi maganar ciki hankalin ta a tashe yake.

Ba wai dan hankalin nata ya kwanta ba ta sake ta ke walwala dan ta lura ba zai barta ba idan har ba ta sak

e d’in ba

Amman a chan k’asan zuciyarta tana da damuwa da ta duk’ufa gayawa Allah.

Tun daga nan zaman su ya dawo kamar farko in ka gansu kowa wasai dan shima Yash d’in daurewa yayi sosai ya ke k’ok’ari wajen b’oye tasa damuwar.

A ranar tafiyarsu Manu

biya ji ta yi kamar kar su tafi.Ta ji dad’in Cyprus kwarai ta ji dad’in gidan ta ji dad’in rayuwar da sukayi fiye da komai a rayuwarta rayuwar da ta tabbata ko wacce mace idan ta samu za ta ji dad’i za ta yi alfahari da sannan zata ajjiye a kwakwalawar ta

har k’arshen rayuwarta.

dan tabbas rayuwa ce mai tsada mai dad’i da mutun bai Isa ya mance ba…

Da rana wajajen 2:34 british airways ya sauk’e su a Heathrow Airport London.

Suna fitowa Yashjub ya hango Junior ya nufosu yana murmushi dan haka shima

ya sake rik’e hannun Manubiya suka nufe sa.

Yana zuwa ya yi hugging Yashjub kafin ya juya ga Manubiya suka gaisa cikin girmama juna daga nan suka nufi inda ya yi parking motarsa da su da waenda suka d’aukar musu luggage d’insu.

“Ga inda ake k’anin mij

i mai hankali”

Manubiya ta fad’i hakan a k’asan ranta.

A bakin wani babban gida mai d’ankaren kyau Junior ya yi parking ya danna horn

kafin mai gadi ya ja musu suka nufi ciki.

A bakin entrance na shiga babban parlourn gidan suka tarar da Hajiya mama

tana jiran su….tunda Manubiya ta fito ta kafeta da ido ta shiga yaba Yarinyar a ranta gata da nutsuwa dan tunda ta tunkaro ta kanta yake a k’asa kuma tana lure da yadda ta zame hannunta a cikin na Yashjub a hankali a time d’in da ta lura da ita.

Murmushi

tayi lokacin da suka k’araso Manubiya tana shirin durk’usawa Hajiya mama ta yi sauri ta tarota ta sakata a jikinta ta rungume

dai dai nan mom ma ta fito…haka itama ta yi hugging Manubiya cike da so sunata murna kamar za su maida ita ciki kafin su nufi c

ikin parlourn da ita

Saida suka zazzauna tukunna Manubiya ta samu da zamo daga kan kujerar ta gaida su da girmamawa

murmushi kawai sukayi suka amsa

kafin Hajiya mama ta d’aga Kai ta kalli Yashjub tace

“To fad’o mini a ka…yau kenan miskilancin ta ka

ina ya biyo”.

Da sauri Junior yace

“Inaaaaa!Hajiya mama ai this a new B Yashjub fa”ya fad‘i hakan yana mai nuna Yash kafin ya d’aura da cewa”ai ya daina miskilanci yanzu,tunda fa muka taho yake zubawa sweetheart d’insa surutu yana nuna mata wajaje da

favorite places d’insa.

Love ya chanja sa ya koma mai surutu”

Dariya duk sukayi yayinda Yashjub ya d’an yi murmushi ya na mai sunkuyar da kai a ranshi kuwa shi kansa yana mamakin yadda soyayya ta chanja shi.

Sai da ya kuma yin wani murmushin mai cike da

ma’anoni tukunna ya kalli Hajiya mama yace”Ba fa ki kulani ba

A bakin k’ofa kika barni kika ja hannun kishiyar ki ko ‘hi’ baku ce min ba daga ke har mom..”

Murmushi mom ta yi ta mik’e ta k’arasa ta je ta yi huggin nashi tace”welcome welcome”

Daga nan

ya yarda ya bita ta zaunar da shi kusa da ita.

Lek’awa Hajiya mama ta yi ta rankwashe sa tace

“Da wani katoton kan sa!wa za ka yi wa shagwab’a??”

Kwashe wa da dariya Junior ya yi dan haka Yashjub ya d’ago yana masa irin kallon ‘ka fa fita a idona’d’in

nan wanda ya sa Junior d’in saurin gimtse dariyar tasa ya shiga yin ta k’asa k’asa sai kuma duk aka sa dariya

banda Yashjub wanda ya ke kallon Manubiya da kalar tausayin irin ‘har da ke ake mini dariya’…….

Masu abinci ne suka fara gabatar musu da kalo

lin dishes saida aka kaisu d’aki suka yi wanka suka yi sallah tukunna aka kaisu wajen Na’ima,jikin nata da sauk’i dan k’afar tata ta d’auko warkewa ma

Ba yabo ba fallasa ta amshi Manubiya har da y’ar tsokana

daga nan aka fita parlourn har ita.

Suna za

ma Abhi ya shigo dan haka suka shiga gaida shi, ya ji dad’in ganin su kuwa dan haka aka zauna har da shi aka shiga hira…

Dakyar kuwa Manubiya ta samu ta iya cin abinci a cikin su dan da har Yashjub ya d’auka zai kai mata d’aki da ya lura ba za ta iya ci a

tsakiyar su ba amman sai Hajiya mama tace ya barri a bar ta ta saba ta sake da su ita batason wannan takurawa da ake kira da kunyar surukai…ta d’auketa kamar best friend d’inta.

Da wasa a dariya da raha haka suka dinga janta har ta samu ta d’an sake ta

d’an ci abincin tana ta yaba kara da kirkin su

A ranta tace”inama ace sune family d’in Yashjub na Nigeria da ta more…”

Gashi dai sunada komai amma da ta basu tsarabar Cyprus ba kad’an ba ta ga murna a fuskokinsu nan ta sake tabbatarwa tabbas waennan s

un san darajar d’an Adam.

Sosai take jin dad’in yadda Junior yake respecting d’in ta ba wai respect in the form of seniority ba no,respect ta yadda ko a kusa da ita baya zama kamar yadda Yassir yake yi

tsakanin ta da shi mutunta juna.

Hajiya mama kuwa

da gaske take da tace wa Manubiya ta d’auke ta kamar babbar k’awarta dan janta ta ke yi a jiki suna hira sosai tun Manubiya tana nok’ewa har ta d’an sake dan Hajiya mama har labarin shagalin bikin ta ta bata tace “lokacin maman Mommy itace babbar k’awarta…

…..”

Kamar yau sukazo Uk sai gashi har sun yi two weeks gobe za su tafi tare da tarin alkhairin su Mom

Tabbas Manubiya ta ji dad’in zama da su ta ji d’adin yadda suka jata a jiki basu nuna kyama ko wani abun ba

Dan har gaisawa da Inna da Baba suk

ayi a waya kuma yanzu haka ma sunada number Innar

A bangaren mutumin nata kuwa abun ba a cewa komai

tana yin wanka ya ci gaba da honeymoon d’in sa babu kama k’afar Yaro dan shi ba ruwan sa da a inda suke sam bai damu da su Hajiya mama ba…

Haka nan

ranar da za su tafi Hajiya mama da Mom suka had’awa Manubiyan goma ta arzik’i kayan alkhairi kala kala suna ji kamar kar su rabu da Yarinyar….Sai da Hajiya mama ta yi musu addu’o’i sosai tukunna suka yi musu rakiya compound d’in gidan Junior ya ja su ya

kai su airport kamar yadda ya d’ukosu suka tafi da kewar su da kuma tsammanin su dan Hajiya mama tace “nan da sati biyu zatazo inshaaAllah”saboda akwai aikin da Junior zai yi anan kano har na tsawon shekara d’aya so za su taho tare da shi….”

K’arfe 2:0

0pm daidai jirginsu ya yi landing a Aminu kano international airport Nigeria….

3 months ago…

Da farko su Mommy b’oyewa Kausar batun tafiyar su Yashjub sukayi dan sun san zata d’aga hankalinta…

Ko da labarin ya je mata ba ta yi komai ba dan zuwa yanz

u tama kasa kuka amma fa sai da ta yi kwana uku bata runtsa ba..sai da Yasmeen ta yi mata prescribing magani tukunna aka samu ta yi bacci..gabad’ayan su tausayi Kausar d’in ta ke basu ta zama so silent kamar ba Kausar ba,wani zubin har sai ka zo ka na yi m

ata magana amma ba ma ta sani ba ko kuma kawai ta zuba maka ido ta yi ta kallon ka har ka gama baza ta iya cewa komai ba.

Lamarin ta ba k’aramin sake d’agawa Mommy hankali yayi ba gashi ita ta ma kasa lallashin ta dan batasan mai za ta ce mata wannan karo

n ba

Ita tace ta yi hak’uri kar ta yi komai zata nema musu solution amman sai da Manubiya ta basu mamaki

saida ta shigo gidan yashjub..amma ba komai!dan wallahi ko da ace za ta bada ranta ne wallahi ba za ta tab’a bari kud’iranta ya tafi a banza ba,eno

ugh is enough kome zai faru along the way sai dai ya faru bata damu ba dan sai ta cimma manufarta.

Hankalinsu bai sake tashi ba sai da suka ga su Manubiya sun yi fiye da sati biyu amma shiru ba su ma da niyyar dawowa…dukda Mommy ba ta kasance mai yawan la

ulayi ba amma sai ga ta a asibiti wannan karon jininta ya hau matuk’a,matar da ko a ciki ba ta laulayi iyaka ciwon nak’uda kawai ta sani.Sai da suka shafe sati d’aya cur ba su zauna ba sunata jerawa Yash da Manubiya kiranye amma ko kyallin dawowarsu ba su

hango ba,ganin Mommy tana shirin susucewa ne ya sa Baba larai nemo musu sabon solution ta inda ta kawo shawarar kawai su yi wa Manubiya ajiya a ciki sannan su cire mata Yash d’in a rai kwata kwata ta yadda duk nacin sa ba za ta tab’a bashi kanta ba. A gani

nta wannan kad’ai ce mafita dan ta san maganar kunce jini da tayi zuwa yanzu har sati uku ba lalle ya yi musu yadda suke so ba…

Dan tsabar bala’i a jeji Mommy da Baba Larai suka je suka binne abunda suka yi,a ranar suka yi wa Daddy k’arya suka ce masa an

yi musu rasuwa a k’auye suka je suka kwana washegari da yamma suka dawo sunata murna su ala dole sun yiwa Manubiya ajiya a ciki sannan sun saka mata tsanar Yash a rai.

A tunanin su su Manubiya bai fi su k’ara sati d’aya ba daga haka su dawo amman har fiye

da wata biyu suka ji shiru hakan ya sa Mommy ta sake d’aga hankalinta a ganinta indai har abubuwan da suka yi suna aiki ai Yash da Manubiya bai kamata ace sun yi zaman su a chan shiruu kamar haka ba cike da assurance Baba larai tace”ta kwantar da hankalin

ta watak’il har yanzu jinin da aka kunce mata tun farko bai daidaita ba maybe yana on and off saboda ita dai bata karya abun da ta yi ba dan haka watak’il sunachan sunata yawon neman magani ne amman ba dai honeymoon ba.

A b’angaren Yassir kuwa yana nan

zargin Kausar ya dasu a ransa fiye da ko yaushe dan ya lura Yashjub yana tafiya ta fara rashin lafiya….sai dai kuma Maganin da take sha na saka bacci ba kad’an ba ya ke taimaka masa dan in ta sha ta kwanta haka zai shige d’akin nata ya yi ta bidirin sa wa

ni lokacin ta nuna masa bata so wani lokacin kuma kawai ta rabu da shi dan ta san ba hak’ura zai yi ba ita kuwa bata da k’arfin hana sa ko yin fad’a da shi a wannan lokacin…rannan kad’an ya rage Yasmeen ba ta kama sa ba tsabar yadda yake zirya ba d’aga k’a

fa sam,amma ko a jikinsa bai damu..yana sonta kuma hakan yana taimakawa wajen kawar masa da damuwar da yake a ciki saboda kamar yadda damuwa ta yi wa Kausar d’in yawa hakanan shima damuwa ta yi masa k’ad’abaibai

Shi babban tashin hankalinsa a yanzu shine

Yashjub yana chan yana hutawa tare da kyakykyawar matar sa shi kuma yanannan duk wani plan d’in da ya had’a sai ya tarwatse dan a tafiyar nan da Yashjub d’in ya yi sau uku yana k’ok’arin yashe sa amman ya kasa

Har company d’in sa yaje amman komai thumbp

rint ne bayan thumbprint d’in kuma hadda password

Sannan ga zargin sa a kan Kausar ga Munirat da ta fara k’ular da shi da nacin ta….

Ba zai yiu Yashjub ya fi sa komai ba sannan ya fi sa kwanciyar hankali ba…shiyasa kawai ya gama deciding rufe chapter

Yashjub as soon as possible dan ya gaji da nad’ar takaici…tunda yayi yayi ya kasa to zai b’arar kawai kowa ya rasa…

Wallahi ko sunansa ba ya so ya ji an ambata Allah Allah ya ke ya ga babu shi a doron k’asa,ba don he can’t stand him anymore longer ba da z

ai so ace ya fara tura masa bak’in cikin da watak’il ma shi ne zai zamo ajalin sa dan tabbas idan akace Yashjub ya mutu da takaici bak’in ciki da kuma tashin hankali abun zai fi yi masa dad’i fiye da komai.…tsabar yadda Yassir ya kwallafa rai da son ganin

bayan Yashjub har wata y’ar rama ya yi…..

Today.

Daddy Yash ya gayawa time na landing d’insu

Yaso ace driver d’insa aka turo masa amma suna fitowa sukayi ido biyu da Yassir.

Sai da Yassir ya ji numfashin sa ya d’auke na y’an dak’ik’u tukunna ya

dawo da kyar sakamokon hango Manu da yayi..ta yi wani irin fari ta yi fresh ta k’ara kyau

kamar ka sace ta ka gudu!.

Da kyar ya d’auke idanuwan sa daga kanta ya maida akan Yash yace ‘’Wlcm”

Sai kuma ya yi musu jam’i yace

“Ya hanya?”

“Alhamdulilla

h”suka ce daganan suka nufi motar da ya faka Yashjub yana mamakin yadda ya ga jikin Yassir d’in yayi wani irin sanyi kamar mara lafiya..

Sosai Jeep d’in ta cika taff da kaya dan sun yo tsaraba ga kuma kayyakin su da suka tafi da su…Ana gama lode kayayya

kin a cikin motar suka shiga ya ja motar suka yi gaba.

Har suka d’au hanyar gidan Daddy Yassir ya kasa magana,

wani irin kishi da zafi da takaicin Yashjub yake ji ta koina,ji yakeyi kamar ya juya ya shak’e sa kokuma ya cika sitiyarin kowa ma ya mutu

Am

ma da ya tuna ya kusan kawo k’arshen Yash d’in sai ya yayyafawa zuciyar sa ruwan sanyi dan ya riga ya gama had’a plan d’insa Allah Allah kawai yake ayi ayi lokaci ya cika bayason ganin sa baya son jin ko da muryar sa ne ya kag’u ya rufe chapter d’in Yashju

b ya fad’a wata sabuwa dan a yadda Manubiya take yi masa d’innan ya san zai d’an sha fama da ita kafin ta yarda ta auresa bayan mutuwar Yashjub.

“Ya naga ka d’au hanyar gida?”

Muryar Yashjub ta katse masa lissafin sa

Sai da ya d’an d’au lokaci tukunn

a ya juya ya kalle sa ya ce

‘’Mommy ce tace in kai ku chan ku huta.Zuwa gobe sai su Yasira su je gaba d’aya a tayata gyaran gida dan ta san ba za ta iya ita kad’ai ba’’

Ba Manubiya ba hatta Yashjub sai da ya ji gaban sa ya yanke ya fad’i..shiruu kawa

i ya yi a ransa yace

“Allah ya rufa asiri”

Daga nan motar ta d’au shiru tsit kawai kakeji har suka k’arasa bakin mansion d’in aka bud’e musu suka shiga ba wanda ya sake cewa komai.

Tun kafin motar ta tsaya ya ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login