Showing 207001 words to 210000 words out of 259716 words

Chapter 70 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

44

side d’in Kausar har tana tuntub’e.

A b’angaren su Daddy kuwa ba a tab’a d’aurin auren da babu wanda

yake farinciki ba sai a yau! Kaff wajen babu wanda yake

farin ciki da d’aurin auren hatta drivers d’in da aka kira su ka yi

shaida ba su yi murna da wannan al’amarin ba dan su kansu sun san Kausar ba ta dace da Yashjub ba gashi bai dad’e da yin aure ba

.

Junior ji yake kamar yayi kuka dan takaici saboda gani yakeyi kmr hakan duk laifin sa ne

amman kuma shima bashida yadda zai yi,ba zai je garin taimakon Yashjub ya lalata nashi relationship d’in da bai ma samu ya fara ba along with his image and reputa

tion.

Su Daddy suna gama d’aurawa kuma sai suka fara da na sani..kamar irin ba a cikin haiyyacinsu suka d’aura d’innan ba.

Babu tsoron wadda ya fi rufe su kamar Hajiya mama

dan haka suka d’aura alhakin gaya mata a kan Ummi…a ganinsu tunda tana ji da it

a

tabbas za ta san yadda za ta yi mata bayani ta fahimta ta kuma taushe ta ta hak’ura.

Tana gama jin bayanin su tace”to”kawai daga haka ta juya ta fice ranta a mugun b’ace.

A b’angaren Yassir ma zuwa yanzu ya rikice dan yana k’asa drivers d’in suka s

auk’o ya tambayesu suka ce “eh an d’aura”

bai ma san next step d’in d’auka ba shiyasa kawai ya zauna yayi shiru dan kwakwalwarshi ta d’auke ta tsaya daga aiki.

Mommy tana shiga d’akin Kausar ta sameta a tsaye dan itama shigowar tata kenan.

Murmus

hi Mommyn tayi kafin ta k’arasa inda Kausar d’in take ba ta damu ta yadda ta turo Baki ba dan ta san yanzunnan za su shirya…

Cikin tsananin farin ciki tace

“Ki yi mini alk’awari

goron albishir d’innan da zan baki yanzu shine za ki daina fushi da mu!!”

Gaban ta ne ya yanke ya fad’i a ranta ta shiga adduar “Allah ya sa hasashenta dai dai ne Allah ya sa tarkonta ya kama kurciya”

A fili kuma sai ta kalli Mommyn tace”Inajinki”

Cupping fuskarta

Mommy tayi kafin tace

“Ki yi mini alk’awari first!”.

Juya ido Kausar ta yi

kafin tace “okay fine!yawan farin cikina yawan daina fushi da ku”

Dariya Mommy ta yi sannan tace mata”Y’a ta ta girma ta zama matar aure

Matar Yashjub imam kura

yanzunnan Ubangiji ya yi ikonsa.”

Tun Mommy tana murmushi mai ha

d’e da dariya har ta zo ta daina dan Kausar ta k’ame k’am!!!

Ta ma kasa yin ko motsi.

Sai da Mommyn ta d’an jinjigata tukunna hawayen farin ciki suka zubo mata,a hankali ta kama Hannunuwan

Mommy biyu da suke rik’e da kumatunta idanunta na zubar da h

awaye tace

“Mommy da gaske kike

Dan Allah ki yi mini wasa da komai banda wannan”.

“Wallahi da gaske nake”

Mommy ta fada mata tana murmushi tana goge mata hawayenta.

Fad’awa tayi jikin Mommy kawai ta fashe da kuka…dai dai nan su Yassira suka shig

o ita da su Yusra cikin farin ciki sukace

“Mommy da gaske ne abunda muka ji Ummi tana waya yanzu tana fad’a???”

Jinnjina musu Kai ta yi still tana rik’e da Kausar dan ta k’i ta cika ta har yanzu…

Aikuwa a take gaba d’ayansu suka taho suka had’asu suka

rungume…

Farin ciki a ranar dai ba mahaluk’in da ya kai su Mommy.

A ranar Kausar ta nemi yafiyarsu dukkansu na ganin kamr sun daina sonta da ta yi dan yau kam ta tabbatar da suna k’aunarta duba da yadda suke taya ta murna.Kowa in ga kalla baki a washe Y

asmeen ce kawai babu a wajen.

A ranar har Baba larai suka yi alk’awarin had’e kansu guri d’aya su taimaki Kausar su tsaya mata ta yak’i Yashjub

su ga bayan Manubiya.

Cike da farin ciki Mommy take kallon y’an matan nata batasan lokacin da wasu hawaye

suka zubo mata ba

Ahankali Baba larai ta kamo hannun Mommy tace

“Kar ki damu, na san hawayen me kikeyi inshaaAllah family d’inki ya kusan zaman complete.“

…..

Yassir so yake ya je wajen Kausar amma ya san tana tare da su Mommy dan tun d’azu da ya ha

wo da niyyar sake dubata ya ga su Yasira sun shiga bai ga sun fito ba.shiysa ya hak’ura ya d’aga musu k’afa dan ya san yana shiga a haka akwai matsala kuma ya riga ya gama yi mata alk’awarin ba zai fallasa plan d’insu a kowa ba za su yi komai cikin sirrine

.

Kishi da tashin hankali da bak’in ciki sun rufesa,ya san Kausar ba ta haramta a garesa ba kuma ya san a yau idan ya ce a warware auren ba shi da matsala da ita sai dai Mommy dan haka ya tsara za su zauna shi da Kausar da Yashjub gobe inshaaAllah a war

ware ba tare da su Momy sun ji ba ,tunda duk su ukun ba so suke yi ba.

Sai da ya yi reaching to this conclusion tukunna ya d’an ji sanyi a ransa..amma fa dukda haka kishi sai da ya sauk’ar masa da wani zazzafan zazzab’i..dan idan ya tuna cewa yau fa Kausa

r matar wani ce sai ya ji kamar ya cinnawa gidan wuta.

Shiyasa kawai ya wuce side d’insa bayan ya tura mata message yace”ta kirasa idan ta zama free.”

Yana shiga d’akinsa ya ware ac ya rage kayan jikinsa

ya kwanta akan tiles flat

daga shi sai boxer y

anajin yadda kansa yake wani irin sarawa.

Assurance yake ba wa kansa yana sakewa cewa”Yashjub ma ba zai yarda da wannan had’in ba dan haka ba shi da matsala ta koina InshaaAllah a gobe za a ware auren daganan duk abunda su Daddy za su yi wannan daga baya

kenan! kuma ko sun yi fushi ya san za su huce.”

Yana waennan tunane tunanen

zazzab’in jikinsa ya nunku!….ya dad’e yana fama kafin ya samu ya d’an ragu, daga haka wani bacci mai nauyi ya yi gaba da shi………..

Yashjub Yana fita gida ya nufa…har yanzu k

wakwalwarshi ta k’i ta bashi kwakkwaran dalili kwaya d’aya wanda ya sanya su Daddy suke tunanin ya kamata ya auri Kausar saboda shi duk wannan bayanin da Daddy ya yi sam baiga ta inda hakan ya zamo hujja akan ya auri Kausar ba.

Zai iya kula da ita da ‘d

anta ba tare da ya kalli inda take bama

Idan kuma tafiya takeso ta yi

ta na iya wucewa ta tafi duk inda takeso ita ta sani!Abu d’aya that is for sure shine idan ta riga ta haihu duk inda take indai a cikin duniyar nan ne to zai nemo ta kuma ya karb’o d

’ansa daganan kuma ita da shi har abada wallahi.

Maganar b’ata suna kuma ta je ta yayata dan shikam tunda har ya sab’awa Ubangiji sannan Iyayenshi y’an uwanshi da Manubiya kowa ya san abunda ya aikata to tsoro ko kunyar ubanwa kuma zai ji??

Wallahi ba

ya shakkar ta d’auki loudspeaker ta hau helicopter ta yi Yekuwaaa! sam hakan ba zai damesa ba,bai damu da mutane da abunda za su ce ba…kawai dai ya san duk shekarunsa da k’arfin tunaninsa bai Isa ya hango abunda su Ddaddy suka hango ba shiysa ya yi puttin

g maganar su into consideration.

Tunda ya taho yake addu’a Allah Ubangiji ya sa kar Manubiya ta amince dan wallahi ba ya jin zai iya shak’ar numfashi muddin akace Kausar ta zama matarsa…ya ma san manu ba za ta yarda a yi mata kishiya ba ta na son shi ba

zata amince ya auri wata ba no matter what,kuma zai yi ta nuna mata hujjoji har ya yi convincing d’insu.

Tunda ya taho ya ke jin yadda wayarsa da ke a aljihu take ta faman vibrating…

Ganin an jera masa misscalls sama da ashirin ne yasa ya hak’ura ya z

aro wayar zai amsa shi a tunaninsa ma daga gida ne amma sai ya ga bak’uwar number…tana katsewa yana shirin mayarwa aljihu dan driving yake yi bayaso ya rik’e wayar a Hannu gudun samun distraction kamar gizo haka yaga message ta notification bar an rubuta”k

a duba watsapp an turo maka evidence akan wanda ya saka aka kaiwa Estate d’inka hari duk dan a kashe ka.”

Sai da sitiyarin motar ya kufcewa Yashjub da mugun sauri ya rik’e Allah ya rufa asiri bai bugu ba bai bige kowa ba dan haka ya yi sauri ya yi parki

ng a gefen kwalta yana jin yadda k’irjinsa yake bugawa zuciyar sa take tsinkewa kansa yana juyawa.

Wata zuciyar tana hana sa bud’ewa dan bai san mai zai gani ba wa zai gani ba Yayinda wata zuciyar take azalzalarsa da ya hau ya gani.

Sai da ya yi addu’o’i

ya ce Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi tukunna ya danne zuciyar da ta ke hanasa bud’ewa..tashi d’aya ya kunna data ya hau Online k’irjinsa yana wani tafarfasa,yana tunanin to waye wannan mai turo evidence haka ko dai pulling legs d’insa ake so a yi to a

mma ai ba kowa bane ma ya san a na binciken.

Sai da messages suka gama shigowa tukunna ya hango number da ta kirasa d’in a ta chan k’asa ga kuma video nan alamun an turo tun d’azu, da messages wajen ashirin a cikin chat d’in.

Yanzun ma sai da ya yi da

gaske tukunna ya shiga chat d’in ya yi scrolling chan sama ya fara daga farko inda aka turo abubuwa har wajen guda biyar aka goge,kafin a sake turo bayanai da pictures da videos.

Maganar farko da idanunsa suka fara yin tozali da ita itace”K’aninka jininka

Yassir Imam kura shine ya yi hiring d’inmu ya bamu hoton ka ya bada bayanan ka ya tsara mana yadda komai zai tafi a tsari mu samu mu kasheka.

A k’asa idan ka yi downloading za ka ga komai za ka ga yadda ya bamu kud’i da duk wani shiri da muka yi tare da

shi.”

Wani irin jifa Yashjub ya yi da wayar jikinsa yana wani irin karkarwa!!ba dan kan kujerar mai zaman banza wayar ta fad’a ba da tuni ta tarwatse!!!!

Wani irin karkarwa da huci ya shiga yi yana jin yadda numfashinsa yake shirin d’aukewa!

Da ky

ar a hankali a fili ya shiga cewa”innalillah wa inna ilaihirrajiun ya Allah kasa hakan ba gaskiya bane ba!”.

Ba shi da wani option d’in da ya wuce ya sake lalumo wayar ya yi downloading ya bud’e ya kalla saboda yadda aka taso masa da tashin hankalin nan

idan ba ganin ya yi ba ya tabbatar ko kuma akasin haka tou ya san tsaf nan da y’an mintuna zai iya samun heart attack……..

Hakanan ya lalumo wayar ya bud’e ya shiga downloading hannnunsa suna wani irin mugun karkarwa da kyar ya danna play yana addu’ar

Ubangiji ya sa kar ya ga Yassir amma sai dai kash!videon yana fara tafiya fuskar Yassir ce farkon abunda ya fara gani ya fahimta,tare da mutumin da yake custody d’insu da wasu guda biyar Yassir d’in ya na yi musu bayani dalla dalla yana jaddada musu kar fa

a samu matsala su tabbata ya mutu.

D’ayan videon kuma inda yake basu mak’udan kud’ad’e ne sai ragowar kuma call recoding ne wanda ya k’unshi yadda suka dinga communicating, har wayar da suka yi d’azu yace su goge suka yi negotiating akan zai basu 3m d

uk sai da suka tura da receipt d’in 2 da 1m d’in da ya turo daga baya……..

So yake yi ya yi kuka hawaye su zubo daga cikin idanunsa amma k’aff!!yau kam babu hawaye sun k’afe sun k’are…

Wani Irin jaa!idanunsa suka yi jijiyoyin kansa duk suka baiyyana…so

yake ya k’aryata amma babu hanya dan idan ya ce fuskar Yassir aka saka bai Isa ya ce muryar ma sakawa aka yi da yanayin maganarsa ba…..

Ya fi awa biyu a cikin motar dan har sai da Manubiya ta fara waya sakamokon daren da ta ga yayi,tukunna ya kira drive

r d’insa ya kwatanta masa inda yake.ya zo ya d’auke sa suka nufi gida dan kwata kwata ba zai iya yin driver d’in ba.

Shi kansa driver d’in sai da yanayin Yash ya bashi tsoro!Kamar wani zombie d’in robot haka ya zama da kyar ma ya chanja waje ya koma maz

aunin mai zaman banza.

Ko da suka isa gida ma bai sani ba har driver d’in ya zagayo ya bud’e masa ya ce masa”mun iso” har sau hud’u tukunna ya yi firgigit ya d’an kallesa kafin kusan bayan mintunan uku ya samu da mugun kyar ya motsa ya fito ya nufi k’of

ar entrance.

Ba zai iya komawa ya d’auko key a cikin mota ba dan haka ya tsaya yana danna doorbell..

Lokacin da ya dawo Manubiya tana kitchen tana k’arasa soya wainar fulawar da suke yi ita da Siyama kafin su Ya Nafi’u su zo su d’auketa ta tafi.….j

in door bell ya sa ta yi tunanin ko dai su Siyaman ne suka dawo maybe sun yi mantuwa dan basu dad’e da tafiya ba.Da wannan tunanin ta fita dan sam ba ta kawo Yash bane da kansa ya tsaya yana knocking instead of ya bud’e kawai ya shigo.

Manubiya tana bud

’e k’ofar suka yi ido biyu da shi a hargitse..dan fuskarsa ta yi jaaa idanunsa ma haka jijiyoyin kansa sun fito sannan gaba d’aya babu nutsuwa a tattare da shi.

Yana ganinta sai ya sake karaya tashi d’aya ya zama emotional cikin tsananin damuwa da neman

agaji ya fad’a mata a jikinta ya fashe da kukan da ya nema ya rasa d’azu!jikinsa yana wani irin karkarwa har abun tsoro.

Duk k’ok’arinta kasa rik’esa ta yi dan ya yi mata nauyi…a wajen suka zube nan bakin k’ofar ko rufewa ba su yi ba….tsoro da al’ajabi

ne suka sanyata fashe wa da kukan itama tana yi tana tambayarsa “me ya faru??”

Shiruuu bai ce komai ba dan ya kasa magana ya kasa cewa komai kawai ya k’ank’ameta yana kuka bilhakk’i da gaskiya.

Sun jima a wajen sosai kafin ta ji ya shiga sauk’e ajiy

ar zuciya a jejjere yana wani irin numfashi.

Cikin sake fashewa da kuka tace”Ya Yash dan Allah ka fad’a mini koma menene kana dad’a tsoratani fa!”

Ahanakali ya d’an cikata har yanzu jikinsa bai daina karkarwa ba…da kyar suka mik’e da taimakon juna,ya

tura k’ofar ta rufu tukunna suka k’arasa cikin parlourn suka zauna ya ruk’o hannuwanta duka biyu ya runtse su a cikin nasa…..

Sau biyar yana bud’e Baki da niyyar yin magana amma sam sai ya kasa,

Ajiyar zuciya ta sauk’e k’irjinta yana dukan uku uku tac

e”i’ll always stand by you!no matter what!

Ka yi mini magana Mijina dan Allah ka fad’a min ko ma menene.Mu nemo mafita mu magance matsalar tare.”

Da kyar ya samu ya iya bud’e Baki ya shiga yi mata bayani daki daki a kan case d’in Kausar komi abunda ya

faru yau sai da ya zaiyyane mata.

Kafin yace”duk abunda kika ce hakan za a yi amma dan Allah dan Annabi kar ki ce in aureta,wallahi ba zan iya rayuwar aure da ita ba!”

Manubiya ba ta iya cewa uffan ba tsabar matsanancin tashin hankalin da ta shiga…is s

he dreaming??da gaske wata ce take d’auke da cikin Mijinta a jikin ta!kuma ake shirin aura masa ita?!!

Yashjub d’inta fa!inaa!!!duk kawaicin ta ba zata iya ba wallahi ba za ta iya ba!!!!

Ashe dama haka mata suke ji idan za a yi musu kishiya?ashe kwanakin

baya da ta ji kishi da haushin Kausar duk wasa ne!!

Dan sai yanzu ne ta san menene kishi ta san zafin sa ta kuma san yadda ake ji…wani irin feeling take ji feeling d’in da ko mak’iyin ta ba za ta so

ya ji ba!

Ji take yi kamar ta yi hauka!!!

ji take ka

mar za ta mutu!!

Hatta b’argo da tsokar dake a jikinta yau kam tabbas sun san tana cikin masifa….

Yanayin da ta shiga ya isa ya sanya Yashjub ya fahimci amsar ta ‘no’ce dan haka cikin tsananin farin ciki ya rungumota yace”na ji dad’in wannan decision

d’in naki,na ji dad’i….”

A hankali jikinta da kwakwalwa da zuciyarta har yanzu suna kan karb’ar azaba tace”a yi mata adalci,na yarda ta zo nan ta zauna da mu har zuwa lokacin da za ta haihu…daga nan idan Babyn ta ya yi wayo zan rik’esa kamar ni na Haif

a da zuciya d’aya,ba na son Kausar amma na yarda ta zo

ta zauna da mu zan jure!zan jure komai banda kasancewar wata mace matarka Ya Yash!!!”

Ta k’arashe maganar cikin fashewa da kuka…

Wani irin sauk’i Yash ya ji dan ya san su Daddy idan suka ji wannan

shawarar da Manubiya ta bayar Hatta Mommy duk za su ji sauk’i kuma an yiwa Kausar adalci tunda har za ta zauna a gidansa ya d’auki d’awainiyar ta har ta haihu ai kuwa an yi adalci kuma itama Kausar d’in ya san tunda ba ta riga ta san su Daddy suna shirin

had’asu aure ba tsaff za ta yarda da shawarar Manubiya….ko dan ta zo ta zauna gida d’aya da shi,ya san za ta so ta yi abubuwa da dama idan ta zo d’in amma InshaaAllah shi kuma ba zai bata fuska ba kuma zai taka mata burki ba zai bata dama ba.

Cikin sa

mun sauk’I ta b’angaren case d’in Kausar ya sake rungumo Manu ya yi kissing forehead d’inta ya share hawayenta yace”inshaaAllah ke kad’ai ce mace d’aya tak

Matar Yashjub,inshaaAllah.”

Ajiyar zuciya ta shiga sauk’ewa kafin ta d’aura kanta a k’irjnsa ta

yi shiruuu.

Dukda tana jin tsananin tashin hankali idan ta tuna Kausar tana d’auke da ciki amma ba

ta kishi da da Yaro ko

Yarinyar da za ta haifa tunda ba laifin sa/ta bane ba,InshaaAllah zata rik’e da zuciya d’aya dan ba ta Isa ta tsani d’an

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login