Showing 51001 words to 54000 words out of 259716 words
Jidda chan,bari in je mu tafi tare,ke
kwa taho”.
Dasauri Aisha tace”a’a bari ni in je mu tafi tare da su,ku kwa taho ku biyu.”
Tana gama fad’in haka ta yi gaba,dan ita harga Allah had’in nasu ya burgeta gashi Najeeb d’in
nutsattse dashi daga gani…..ko bai fad’a ba ta san yana ciki ne da Siyama shiyasa ta basu space ta barsu su biyu ita kuma ta nufi motar da akace mata Jidda tana ciki mai uban tint
Ita kanta Jiddan sai da ta shiga ma tukunna ta lura da tint d’in tsabar b’
acin ran datake a ciki.
Ko minti biyu batayi da zama ba Aisha ta bud’e gidan baya ta shiga dan haka Yassir ya kunna motar bayan sun gaya mishi inda za su je su kwashi kayan daganan su wuce gidan amaryar,sam Yassir bai so
Aisha ta shigo ba so yayi a bash
i chance da guda d’aya kawai especially ma Jiddan
dan shi a rayuwarsa yana
matuk’ar son mace fara fat!ga ta wannan ga shape ga kyau ga ta she’s young,
Kuma zuwa yanzu ya lura she’s very calm and innocent dan ba ya jin tayi magana sau uku tun
daga fa
rkon ganinta da yayi har izuwa yanzu..
Ba dan yaso ba ya kunna
Motar yayi gaba yana tuk’in yana satar kallon Jidda yana mamakin abun da yake shirin sakata kuka.
Aisha tana wucewa
Najeeb ya lura da yanayin Siyama…dariya yayi ganin yadda ta yi da f
uska kafin yace
“Savior d’in taki ta tafi ko?”
Shiruu ta d’an yi kafin ta d’an girgiza kai kawai.
Murmushi yayi yace “ki fad’i abunda ke ranki fa”.
Shirun da ta yi ne yasa ya sake cewa “to tunda ba za ki fad’a ba bari ni in bada hak’uri dan
ni kaina
na san na takuraki,sorry i can’t help it ne shiyasa ayi min afuwa…um..?”
Ya fad’i hakan yana had’e hannuwanshi alamun rok’o.
Kamar ba zata yi magana ba sai kuma tace”ba komai fa”.
“Really?to ya naga sai faman had’e rai kike yi,especially ma a wajen hot
o.
Ya fad’i hakan cikin tarar numfashin ta.
Kamar za ta ce masa
Yassir ne bataso sai kuma tayi shiru dan sun fahimci Yassir k’anin Yashjub ne,kar ta je ko shima sunada dangantaka da Najeeb d’in sosai apart from
Abota ta je ta kwafsa..
Wucewar motar s
u Yassir ne yasa shi cewa”mu bi bayansu
kar mu b’ata,kin d’auke
hankalina
Like seriously banma san lokacin da ya kunna motar ba.”
Ya fad’i hakan yana kallonta
sannan ya d’an matsa ya nuna mata hanya da hannunshi.
Wucewa ta yi shi kuma ya bi ta a
baya yana mai jin wani shauk’i da annashuwa suna ratsashi….tun a asibiti ya kamu yau kam ya sake kamuwa katamau ya fad’a tsundum!Adduar shi d’aya Allah ya sa babu wani sannan Allah ya sa ta amince da shi,dan shi kam ya ga mata kuma inshaaAllah sai ya samu
da izinin Allah.
Ba kad’an ba ta ji kunya da nauyinsa da ya bud’e mata marfin motar,dan ta san wannan ya fi sa’an su ya Yusuf ma a shekara sosai…..
Sai da yace “bismillah”tukunna ta d’an d’aga kafarta dakyar ta haye motar dan irin kirar jeep d’innan c
e mai
tudu da fad’i sosai amma ba ta cika tsayi ba.
Sai da ya rufe mata murfin motar tukunna ya juya ya koma side d’inshi ya bud’e ya shiga ya kunna da sauri dasauri dan ya daina hango Yassir,kuma ya san ba gidan amarya a ka nufa direct ba.
Da kyar kuw
a ya hango sa bayan sun fita titin dan haka ya shiga binsa har ya samu
ya tadda shi suka jeru…
Sai da ya jeru da Yassir d’in tukunna ya d’an kalli Siyama wadda take ta ke faman danna wayarta yace “ku dai Mata bakwa gajiya da chatting!”.
Kashewa ta yi
ta d’an sauk’e ajiyar zuciya kafin tace”ba chatting nake ba,pictures d’in d’azu da na yi da wayar nake
dubawa”.
Kallon hawaii d’in tata yayi kafin yace”ai mai hotunan zai turomin clear ones…”ganin ya
samu opportunity yasa ya yi sauri ya mik’a mata waya
rshi tukunna ya d’aura da cewa”ki saka min numberki sai in yi miki sendin ta watsapp idan ya turo”.
Kamar ba zata karb’a ba sai
kuma ta karb’a ta rik’e wayar ahannunta ta shiga jujjuyawa…..da kyar ta gano inane gaba sakamokon hasken da ta yi sai kuma ta
rasa ta yadda za ta yi sliding dan babu alamun touch ko hanyr dake nuna mata ta inda zatayi sliding keyboard d’in ya fito,kuma ita harga Allah bata shirya basa number ta ba!bata dad’e da fita daga bak’in cikin ex boyfriend d’inta ba wanda
har ya gama c
in amarcinshi ya dawo sai faman naci yake yi mata tsabar ya raina mata wayo ko me yake nufi da ita oho. Bata shirya samun 2heart break ba..had’in su Manubiya is from heaven
Allah ne yayi had’insa, ita kuwa ba za ta d’aukowa kanta dala babu gammo ba…..
S
hirun da yaga tayi ne ya sanya ya d’an sosa k’eyara
kafin yace”okay fine!can i have your number,actually i need it..ba wai saboda sending pictures ba”
Ya fad’i hakan yana mai yin kalar tausayi da fuskarshi.
Murmushi kawai ta d’an yi..ba tare da ta s
an ya za ta yi ba ta d’an shafa kan wayar, da
ikon Allah kuwa sai taga ta bud’u,tashi d’aya ta hango
Phone dan haka ta shiga ta juye masa digits d’in nata daga haka ta mik’a masa wayar tana da ta sanin bashi.
“Tnx”yace
Sai da ya kira ya ji ya shig
a wayarta tukunna yayi saving ya ajjiye wayar yaci gaba da janta da hira. Sama sama ta ke d’an biye shi..ya lura Siyama irin y’an matan nan ne masu jan aji shiyasa tashi d’aya ya fahimci zai sha wahala..sam bai damu ba dan shi indai za ta kulasa to ba ruwa
nsa..tabbas ya san sai yanzu zai fara soyayya!a lokacin da Ya’isha take ja mishi rai k’ulewa yakeyi ya ji haushi amma da ikon Allah ko fushi ya kasa yi anan,duk kalar basarwa da cin maganin da Siyama take ta yi sam ya kasa yin ko da fushi sau d’aya d’an ka
d’an ne.
A b’angaren Siyama kuwa ba wai jan aji bane kawai ita bata so ta zak’e da shi dayawa ne
har ga Allah ba ta so ta saki jiki dashi gudun kar ta je ta fara sonshi
A samu matsala.
Suna tafe kuwa Ya’isha ta kira shi,sarai ta lura da yadda ya y
i da farko kamar irin baya so ya amsa a gabanta d’in nan.
Sai da Ya’ishan ta sake kira tukunna ya d’auka ko tsayawa jin me zata ce bai yi ba yace”ina driving zan kiraki”
Ba ta ji me akace daga d’ayan b’angaren ba sai ji ta yi shi yace”Nndc quarters!
da sunan layi da number gida…..”
Yana gama fad’in haka yayi sauri ya kashe.
Ba ta san wacece ta kirasa ba amman tabbas ta sake yin dana sanin basa numberta da ta. Ba ta yi mamakin yadda ya ci gaba da flirting yana mata hira ba dan ta riga ta san halin
maza,shiyasa kawai ta bisa da “um,um um…”
A haka suka tsaya suka d’auki
gado da ragowar kayan kitchen aka had’a su da manyan motocin d’aukar kaya da masu kafi
suka wuce.
Sun d’anyi tafiya mai nisa kafin suka k’arasa gidan Yashjub
dake a unguwar sh
arad’a nndc quarters..dank’areren gida mai hawa uku!
Tun daga waje suka fara kallon aljannar duniya,tun kafin a shiga ciki kuwa suke fara ganin ikon Allah dan gate d’in gidan ma……MANNUBIYA
(Book 2)
Page 17
Na
Humayra
h Bulama
Mikiya Writers Association.
Da remote aka bud’e musu.
Gaba d’aya motocin harda na kaya ciki suka shige dan atleast compound d’in gidan zai ci motoci sama da bakwai.
Sai da suka gama shiga tukunna gate man d’in ya rufe musu daga inda yake
sannan ya ajjiye abun ban ruwan da yake yiwa flowers ya tunkarosu
dan already daman ya san da zuwansu.
Basu kai ga fara fitowa ba suka ga ya koma da sauri ya d’an lek’a tukunna ya d’anna wani abu a jikin gate d’in ya bud’u.
A tunanin su ma Yash ne,
shiyasa basu juya dubawa ba.
Aisha ce kawai ta fito dan
Yassir yana ganin Jidda tana shirin fita yace mata”please wait”.
Ganin masu kaya sun fara k’ok’arin sauk’ewa sannan
motoci har uku sun shigo
ne yasanya Najeeb yace bara suma su fita,sam ba
i lura
da motocin da kalar su ba kawai shi dai ya san an shigo.
Bai bud’e side d’in Siyama ba,kamar d’azu yanzu ma sai da ya zagayo sannan ya bud’e mata da kansa.
Cikin rashin jin dad’i dan ita
har ga Allah bata so tace”ka daina,ba na jin dad’i”
Murfin motar ya rik’e yana kallonta kafin yace”dan ma ban nemo red carpet na shimfid’a miki daga nan har bakin k’ofar entrance d’in ba!…”
Ya fad’i hakan yana kallon ta yana murmushi,a ransa
yana mamakin yadda ya koma…dan gaba d’aya ya nemi
jan aji!
muzurai!da duk wani class d’insa ya rasa.”
Ba ta sake tanka sa ba,sai
matan da suka fara fitowa daga motocin ta d’an kalla,ta gane Yasmeen dan sun had’u a asibiti shiyasa tashi d’aya ta fahimci dangin Yash ne.
Ganin inda take kallo ne yasa Najeeb d
’in shima ya d’an juya….
…Ya san dama ko ba yau ba dole za ta ta sani amman dukda haka sai da ya d’an ji wani iri,kuma yana juyawa da Ya’ishar suka fara had’a ido.
D’auke kai ya yi ya juyo ya kalli Siyama yace “Bismillah”
ya yi maganar fuskarsa
ba yab
o ba fallasa.
Fitowa ta yi ya maida k’ofar ya rufe mata.
Zuwa yanzu Siyama ta fahimci wani abun tsakanin sa da Ya’isha sakamokon kalar kallon da taga Ya’ishan tana ta yi mata har ana yi mata magana ma bata sani ba.
Sai da Yassira ta ce mata “keee
!”da d’an k’arfi,tukunna Ya’isha ta samu ta d’auke dubanta daga kan su sir Najeeb idanunta suna masu
ciccikowa da hawaye.
A hankali Yasmeen ta matso ta tsaya a gabanta ta d’an kareta daga Najeeb d’in tukunna tace”ba ce miki mukayi karma ki kallesu ba?am
ma kalli yadda kike..….
Shiruu Yasmeen d’in ta yi sakamokon hawayen da ta gani taff a idanun Ya’ishan suna shirin zubawa…ta san in har tace wani abun ko kuma tace za ta lallasheta to fa hawayen nan da suka cika suka yi mak’il sai sun fito duba da yadda id
anunta suka cika taff sannan sukayi jaaa!hatta farar fuskarta ta yi jaa.
Hakan ya sa Yasmeen d’in kawai sai ta jaa hannunta da sauri suka nufi k’ofar parlourn.
Suna zuwa suka tura k’ofar
Allah ya so su akwai masu goge goge a ciki so k’ofar already a
bud’e take, ba ta
tsaya da ita a parlourn ko sama ba dan hanyar saman akwai masu guga har biyu haka ma cikin parlourn,kuma ta san kafin su Isa kukan zai iya kufcewa Ya’isha shiyasa ta nufi d’akin da ta gani anan k’asan da ita.
Suna shiga suka rufo k’of
ar tukunna Yasmeen ta cika mata hannu….ko magana Yasmeen ba ta yi ba Ya’isha ta fashe da kuka,da sauri Yasmeen ta toshe mata baki tana yi tana
dan kallon k’ofa cikin yin k’asa da murya tace”so kike a jiyo ki?
wanne Irin rashin lissafi ne wannan?
ce mik
i akayi wani abun ne a tsakanin su?ki tsaya ki tabbatr mana!.”
Ingije hannun Yasmeen Ya’isha ta yi kafin tace”Haba Yasmeen!yanzu ke ba ki fahimci komai ba?ba ki ga yadda yake murmushi yana kallon ta ba?,da kansa fa ya bud’e mata mota ta fito kuma ya ma
yar ya rufe abunda bai tab’a gigin yi min ba kenan.
Ki duba ki ga ya ganni fa mun had’a ido da shi amman bai zo inda nake ba ko sake kallon inda nake ma fa bai yi ba…..”
Kukan da ya taho mata ne ya sa ta kasa ci gaba da magana dan haka ta yi shiru da mag
aar ta ci gaba da kukanta.
Cikin d’an fad’a fad’a
Yasmeen tace “Yanzu kuka za ki tsaya kinayi ko tunani mai kyau??kalle ki yadda kika koma a cikin y’an sakannni
saboda shi wanda hakan yana nuni ne da tsananin son da kike yi masa,dan haka sai ki tashi
ki nemi mafita tun kafin dare yai miki ba wai ki tsaya kina kuka ba.
Sannan kar ki bari su ga kukan ki ballantana su rainaki.
Tun farko kuma ai ke kika yi wasa da damarki,abunda naketa gayawa Yadira akan Junior kenan amman sam ta k’i fahimtata..haka kuk
e sai kun shure abu da k’afa kuma sai ku dawo kuna rarumowa da hannu.!
Kuma Ya’isha har yanzu fa ba kya lallab’a Najeeb ba kya yi masa yadda ya kamata…a yanzu duba da yadda Najeeb ya yi kud’i haka sosai dole fa sai da tarairaiya kwantar da kai lallami da
lallashi dole sai kin bi ta koina kin mamaye kin rik’esa da kyau kin ajjiye kishi da girmankai a gefe dan wallahi one mistake idan kikayi tashi d’aya zai cika wandon sa da iska sai dai labarin wani ba shi ba. A da ma ya aka k’are y’an mata sun yi masa cha
a ballantana yanzu.”
Cikin kuka kamar za ta shid’e Ya’ishan tace”Yasmeen shekaran jiya fa da kuka ce idan ya zo in je in basa hak’uri wallahi da na je har k’asa na durk’usa na basa hak’uri!
How much more good can I be ???”
Ya’isha ta yi mata tambayar
tana kuka sosai.”
Tausayinta ne ya rufe Yasmeen
shiyasa ta ma kasa ci gaba da magana,ahankali ta sa hannu ta rungomota…ita kanta ta jijjiga da lamarin, babu abunda ya fi d’aga mata hankali kamar yarinyar.
Itama Ya’ishan haka dan dukda ta san tana da
kyau amman fa ta san ba ta Isa ta tsaya tace za ta kara da Yarinyar da ta gani yanzu a fannin kyau ba.
Ba za ka kira Siyama doguwa chan ba sannan ba gajeriya ba ce,tanada haske sosai itama
sai dai yanayin hasken ta ba kalar na Jidda bane dan ita ba far
a bace fat!ta fi kama da kalar half caste din da sukai had’i da turawa.
Kamar yadda fuskarta take round haka idanuwanta suke suma ba manya chan bane ba kuma ba k’anana ba y’an madaidaita sannan farare k’al waenda sukayi daidai da yanayin tsarin fuskarta,t
ana da cikar gashin gira kuma kwance suke.
Pointed nose gareta,sai bakin ta d’an k’arami lips d’in masu d’an tudu wanda hakan ya taimaka wajen k’arawa bakin nata asalin kyau. Bata da jiki sosai amman kamar su Jidda itama tanada structure mai kyau tubarka
llah………
Su Ya’isha suna wucewa
Jidda ta fito daga motar Yassir ranta a b’ace.
Inda Aisha take ta k’arasa ta tsaya bayan ta karb’i d’ayan flask d’in da aka mik’o mata daga motar kayan,dama flask biyu ne kawai a cikin kayan sai
robar turare.
Dan
haka Aisha ta d’au k’aramin flask da robar ita kuma Jidda ta d’auki babban mai d’an girma.
Ganin su Yassira ma duk sun fito ne yasa Aisha tace”inaga dangin angon ne dan ga wata mai kama da Yashjub d’in sosai,ku taho mu je a gaisa sai mu wuce ciki gaba d
’aya a tare.
Dai dai nan Siyama wadda ta samu ta zille wa sir Najeeb da kyar ta k’araso wajen.
Tana shirin yin magana ta ji shi a bayanta ashe tare suke tafe ita bama ta sani sani ba,cikin nutsuwa ta ji yana cewa Aisha “ga sisters d’in Yash da aunty d’i
nsu mu je ku gaisa dasu”
“Ok”Aisha tace daga haka ya wuce gaba suka bi sa a baya.
Kamar Siyama za ta tambayi Jidda mai ya b’ata mata rai har haka sai kuma kawai ta kyaleta tana mamakin abunda ya sake fusatata daga shigowarsu cikin gidan.
Yassira Baba
larai sai Yadira da Yusra ne suka tsaya a bakin motar,suna jiran fitowar Yahanasu dan wallahi yau ba za su raga mata ba,rainin wayon nata ya yi yawa! matar da ta ce musu ba ta san kwatancen gidan ba shine suna zuwa suka tarar da ita a bakin gate tana jira
a bud’e mata….
Yahanasu kuwa ba k’aramin dad’i ta ji ba da taga su Aisha,dama tunda su Yasira suka je suka tambayeta ta san su da naci shiyasa hankalin ta bai kwanta ba tace bari dai ta zo ta tabbatar da ba su zo d’in ba…..da farko da ta ga motocin su Y
asirar a bayanta hankalinta ba k’aramin tashi ya yi ba ta shiga lissafin yadda za ta yi ta taka musu burki amman da suka shigo ta ga su Aisha sai ta ji wata nutsuwa da kwanciyar hankali sun rufar mata ga shi har da sir Najeeb! ta san duk bala’in su ko ma m
enene suka zo yi ba su isa su yi a gaban sir Najeeb ba,ga kuma Ummi a hanya itama wadda ta tsaya yin waya da ita ne ma shiyasa ba ta fito ba har yanzu…d’azu da Ummin taga sun fito ne ta fahimci gidan za su je shiyasa ta ce su jira ta ta d’auko mayafi itam
a tana so ta zo gidan amman tana fitowa sai wayam ta gani sun ta fi sun barta,shine a take ta kira Yahanasu ta yi mata kwatance,yanzu kam da suka yi wayar ma tana bayan layi….
Su Baba larai suna tsaye suna jiran fitowar Yahanasu suka ga su Aisha sun tun
karasu.
Baba larai ji ta