Showing 45001 words to 48000 words out of 259716 words

Chapter 16 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

14



shi kuma tabbas a yanda yake jin Baraka a halin yanzu in dai har bai dawo da ita ba tou akwai matsala…….

Jidda ce ta wuce d’akin dan sanar da su inna yayin da Siyama ta nufi parlournsu ta shiga tattarewa bayan ta cewa bak’in ciki “dan Allah angwaye za

su shigo”,sun fita

Tana cikin tattarewa Jidda ta kirata tace “su inna da anty umma sunce a bari su Yashjub d’in su gaida su a d’akin kawai saboda akwai matar mai unguwa kuma gurguwa ce so idan akace sai ta sake jan kujerarta zuwa parlourn su Siyaman wani

sabon aiki ne,”

“But gata nan zuwa ita da Manu su inna sunce ta je parlourn su zauna su yi hotunan a ciki”

Mata wajen biyar ne a d’akin ga kuma matan uncle da su anty umma suka cewa su Jidda su je su kira shiyasa anty umma da mama suka nemi waje a bay

an gidan suka zauna dama abunda maman take so kenan shiyasa ta San yadda ta yi ta ja anty umma dan har ga Allah bata so ta had’u da angon dan bata san wanne hali za ta shiga ba idan zarginta ya tabbata ko kuma akasin hakan tsabar yadda ta rud’e ita ba ma t

a san me zata ce tana so ba a halin yanzu…ya tabbata ko kuma kar ya tabbata.

Sai da aka d’an tartare d’akin aka saka turaren wuta tukunna

akacewa su Jidda suje su shigo dasu,matan su baba habu kuwa ko da aka gaya musu ma basu tashi zuwan ba dan yadd

da suke ganin ran mazajen nasu a mugun b’ace kuma sun san akan auren ne aka b’ata musu rai yasanya bama su gwada tambayr su zuwa su gaisa da angwayen ba gudun b’acin rai……

Yashjub yana tsaye suna waya da Yassira ya hango Yassir yana sallama da Abokan

sa,suna wucewa ya ga shima ya bud’e mota yana shirin shiga ya wuce dan haka ya yi saurin cewa Yasira”ina zuwa” daga haka ya kashe wayar ya d’an d’aga murya ya kira sunan Yassir.

Sai da yayi tsaki tukunna ya rufe motar ya juya ya na kallonshi,yaffito sa

Yashjub d’in ya yi da hannu daga haka ya d’auke kai ya ci gaba da magana da Najeeb.

Kamar zai kama da wuta!haka

Yassir yakeji tsabar takaici..sai da ya taushi zuciyarsa da kyar tukunna ya fara k’ok’arin zuwa inda Yashjub d’in yake dan sai da suka yi

shi da Daddy da Abhi suma kafin su wuce akan yadda yake ta faman ciccin magani yake kuma k’in

shiga ayi abu dashi sune har da zaginshi Abhi yana ce mishi mai bak’in hali tukunna suka wuce,shiyasa tun d’azun yake a wuya yanzu kuma ga Yash shima yana shir

in k’arasa kaishi bango…sam sun kasa la’akari da yadda ya danne kanshi ya shigo cikin wannan mugun layin dukdan saboda su amma still babu godiya babu jinjinawa kalli abubuwan da akeyi masa…..da kyar ya dan danne kansa dan wani mugun takaici yake ji tukunna

cikin takunshi fuskar nan tamau ya fara takawa izuwa inda suke a ranshi yana aiyyana”tabbas ya san sai ya sha maganin allergy dan he’s allergic to warin kwata kuma kwatocin layin kusan duk a bud’e suke,gaba d’aya koina wari yake yi…he definitely has to s

ee a doctor”

Yana cikin tunanin asibitin da ya kamata yaje ya k’arasa inda suke tsaye ya tsaya kawai ba tare da yace komai ba.

Kallonsa Yashjub d’in yayi

kafin da mamaki yace “ya na ga kana shirin tafiya?ba za ka

shigo mu gaishe da su ba?.

Ka tsa

ya idan muka gaida su muma duk wucewa za mu yi,sai mu tafi tare.”

Yassir ji yayi kamar ya d’aura hannu aka ya kurma uban ihu tsabar takaici….yanzu dan rainin hankali wannan mugun gidan yake so ya shigar da shi tsabar son wulakanci,iyaka layin da ya shi

go da su bai ishe sa ba sai ya danna sa a cikin gidan kenan!a ranshi yace”Tabbas na ga alama sai na yiwa mutumin nan da gaske tukunna zai d’aga min k’afa”

A fili kuma cikin tsananin tsageranci da wulak’anci ya kalli idon Yash d’in tukunna yace”ka san dai

Allah d’aya ne ko!to wallahi idan na shiga gidan nan sai anyi deworming d’ina!yanzu haka I’ve fallen sick,na san ka san Ina reacting

to dirt and disgusting items amma sai k’ok’arin forcing d’ina kake yi,haba mana!…”

Sakar baki kawai sir Najeeb yayi ya

na kallonshi shi

Yashjub kuwa ya zo iya wuya jira kawai yake ya kai aya ya fara cin ubanshi tunda ya lura

bashida hankali

Manubiya da family d’in nata ne disgusting items ko

me?tabbas yau kam Yassir ya kuma kaishi bango zai kuma sha mamaki…..

Yassir ya lura da yadda Yashjub yake kallonsa amma sam bai damu ba”besides gwara ma ya kaishi

bango ya k’ular da shi ta yadda zai yi misbehaving a k’ofar gidan surukan sa!

Oho!shikam dad’i ma zai ji”

Ya aiyyana hakan a ransa,sai kuma cikin son sake fusa

ta shi a fili Yassir d’in ya ci gaba da cewa

“Har ga Allah ka fara kaini bango kark……”

Maganar tasa ce ta mak’ale sakamokon hango Siyama da ya yi tsaye a bakin k’auren gidan tana magana da alamar akwai wani a ciki da take magana da,

‘Anya ba gam

o na yi ba kuwa?’

Ya yiwa kansa tambayar a cikin ransa yana mai jin wani sanyi yana ratsashi,bai gama

dawowa daidai ba

Jidda ta fito tana hararar Siyama wadda ta tare hanya ta hanata fitowa har sai da ta sauk’e mayafinta daga kai tukunna ta bata hanya

ta fito daga gidan,ahankali Yassir ya motsa bakinshi yace “woow”

ba tare da sautin woow d’in ya fito ba.

Girgiza kai sir Najeeb ya yi kawai ya juya dan ya san tabbas maata Yassir ya gani….

Wani tashin hankalin takaici ne ya lullube sir Najeeb sakamok

on had’a ido da sukayi da Siyama dan yana juyowa kamar ance ta d’ago suka had’a ido,wato ita Yassir yake k’arewa kallo shine ya k’ame haka….

Dakyar ita kanta ta sunkuyar da kanta k’asa ta ci gaba da takawa inda suke tana jin yadda k’irjin ta yake bugawa

ahankali ahankali…..MANNUBIYA

(Book 2)

Page 16

Na

Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Sai yanzu Jidda ta hangesu

dan haka itama ta bi Siyaman suka jera suka nufesu.

Duk yadda sir Najeeb yaso sam sa

i ya gagara d’auke idanunsa daga kan Siyama ya so ya yi hakan amman sam sai ya kasa…babu kwalliya a fuskarta dan ko kwalli ba su samu sun saka ba sakamakon saurin da suke ta yi amman

ba k’aramin kyau ta yi masa ba shiyasa ya shagala da kallonta yana ma

i zuba wani Irin murmushin da shi kanshi bai san yana yi ba.

Hatta Yashjub wanda juyowar sa kenan sai da ya lura ya kuma fahimci kalar kallon da Najeeb d’in yake yi wa Siyama shiyasa kawai ya tsaya yana kallon shi da d’an mamaki kwance a kan fuskarshi.

J

idda ce ta samu ta ce mishi “ina wuni”

Dan gaba d’aya Siyama ta d’an rikice sakamokon yadda takejin idanuwanshi suna yawo a jikinta….

Da kyar yad’an kalli

Jidda yace mata”Alhamdulillah”sannan ya juya ya amsa gaisuwar Siyama wadda ta Isa har cikin zuciya

ruhi da kwakwalwarsa.

Ahankali sukace “Ya Yash ina wuni”

Sai da ya d’an yi murmushi tukunna yace “Alhamdulillah”

Daga haka suka yi masa Allah ya sanya alkhairi ya amsa cike da fara’a kafin ya sake duban Najeeb wanda still yake satar kallon Siyama ya

na murmushi.

Dakyar jidda ta iya cewa Yassir “Ina wuni”

Siyama kuwa ko kallonsa ba ta yi ba dan kwata kwata gayen bai mata ba.

Cike da fara’a Yassir d’in ya amsa kafin ya d’aura da” ya taro?”

Girgiza kai kawai Yashjub yayi

kafin ya kalli Siyama

wadda take cewa”ya Musbah yace mu shiga da ku wajen su inna,Manu ma ku take jira”

Sai a sannan Yashjub ya yi murmushi yace”Lead the way”

Ya fad’i hakan yana nuna mata hanya.

Juyawa ta yi hakama Jidda daga haka suka yi gaba su kuma suka mara musu baya

.

Najeeb ji yake kamar ya janyota ya sakata a bayansu shi ya shige gaban Yassir,ya san yadda shi kansa ta d’au hankalinsa bashi da tantama Yassir ma k’are mata kallo

yakeyi shiyasa kwata kwata yak’i yarda ya kalli Yassir d’in dan ya san idan yaga yana

kalle masa ita tsaf zai iya bige masa ido…ba wai iyaka Yassir kad’ai ba hatta Yashjub wanda shi danna wayar sa ma yake yi sai da Najeeb ya ji kishin shi,yana mai jin takaicin dalilinta na rufa mayafi bayan ta san yau maza za su taru!…”

Yassir kuwa gaba

d’aya lissafinshi ya kunce…yana ganin Munirat mai shape da kyau to ga iyayenta a shape da kyau da komai

Yara kamar aljanu!!.

Tabbas yanzu ya fahimci dalilin Yashjub na zuwa nan ya mak’ale….

A bakin k’ofar gidan me hoton da yaransu suka zauna dama

dan haka suna zuwa suka kutsa suka shige a tare gaba d’ayansu.

Har d’akin su Manubiya suka shiga,dukda d’akin yana da girma sosai amma da kyar su kansu angwayen suka samu wajen zama masu video coverage da hotuna kuwa a waje suka tsaya suka yi y’ar dabara

suka d’auki abunda ya sauwwak’a.….Yadda alada ta tanadar haka suka gaida iyayen mata su kuma suka sanya musu albarka daga nan sukayi musu y’ar guntuwar nasiha suka basu amana….

Dubu d’ari uku su Yash suka ajjiyewa ko wacce uwa daganan suka mik’e suka yi

musu sallama suka fita

suka barsu cikin shock,inna ta ji ba dad’i da ta ga su mama ba su samu shigowaba ba har aka gama…ba wai dan kud’in ba ita a ganinta a hidimar bikin nan ai mama da anty umma sune iyaye..matan d’akin kuwa suma sunyi

kara dan sun lura

da yadda suke ta hada hada shiyasa aka had’a kud’in guri guda aka raba daidai har da su.

Sai da suka fito tukunna Yashjub ya lura da Yassir dama kamr ya ji muryarsa a bayansa

yanata ‘Ameen Ameen’

“Hmm”kawai yace daga haka suka mik’a su Siyama suka k

aisu har parlournsu inda Manubiya take ba kowa da ga Manubiya sai Aisha wadda ta gama gyarawa Manubiya

kwalliyarta dan duk ta chab’e saboda kuka….parlourn tas

da shi sai tashin k’amshi yakeyi.

Jidda ce ta yi musu introducing Aisha as sister d’insu itam

a, da kulawa suka gaisa da ita ta yi musu Allah ya sanya alkhairi suka amsa da fara’a…yanzunnan da wani brother d’inta zai wuce ta basa khairat tace ya kaita wajen mamanta anjima idan za su taho sai su zo da ita,kuma sam idan ka kalleta ba za ka ce ta ma y

i auren fari ba shiyasa har ita kanta bata tsira daga kallo da mugayen tunanin Yassir ba,kan Manubiya a lullub’e yake cikin mayafinta har yanzu amma yana iya ganin yanayinta kad’an kad’an…shiyasa gaba d’aya ya sake

gigicewa,hatta k’afafuwansa karkarwa su

ka fara yi,ya san bazai yiu ya had’e su su duka hud’u ba amman kuma dukkansu yake so…

Manubiya matar yayansa ce

dukda bai ga fuskarta ba

amman itama ta yi mishi ya san ba shi da damuwa a case d’inta he’ll find his way ko ta halin k’ak’a ne tunda kamr

a gidansu ma take

Aisha kuma bata kai su Jidda

kyau ba dan haka zai yi hak’uri ya cire ta a lissafi ba dan yana so ba,a yanzu matsalarsa itace ta yadda zai samu both Jidda da Siyama dan har ga Allah bai ga ta yarwa a cikinsu ba.

Dariyar Najeeb ce ta

katse masa tunani….cikin sigar tsokana Najeeb d’in ya cewa Yash “ya dai?ko kawai mu ce a

bamu amaryar mu tafi da ita tun yanzu mu da kanmu?”

Sai a sannan hankalin Yashjub yad’an dawo jikin sa,a hankali

yayi murmushi yanajin wani farin ciki mara mi

saltuwa yana sake lulub’esa tukunna a hankali ya taka ya k’arasa inda take zaune ya yi

bismillah ya zauna a daff da ita kamar zai shige cikin jikinta,a tare daga shi har ita suka sauk’e b’oyayyiyar ajiyar zuciya kafin ya sunkuyar da kanshi yana wani irin

murmushi…..

Su Jidda har ma da masu hoto suna nan tsaye suna jira ya bud’e mata fuska a yi hotuna amman sai suka ga ya d’ago ya kallesu yace”Bismillah ku zo ayi hoton

Jidda bismillah”

Ya fadi hakan yana nuna mata gefen Manubiya alamun ta zo ta zauna.

Mai hoton ne ya d’an yi gyaran murya kafin yace”Am ranka ya dad’e ai sai ka yaye mayafin nata tukunna za’a fara d’add’auka…haka naga ana yi in naje d’aukar hoto”

“Haka ka yiwa taka kenan??”

Yashjub ya yi masa tambayar ba tare da ya kalle sa ba dan

zuwa yanzu hanakalinsa ya tafi kan y’an yatsun ta da take

wasa da vail d’inta da su,tun ranar da ya rik’e mata hannu a office d’insa yake muradin ranar da zai sake samu ya rik’e,shiyasa without thinking twice ya ruk’o hannun nata cikin nasa duka biyu.

A tare duk su biyun suka sauk’e ajiyar zuciya wanda duk sai da sukaji sai kuma ta yi sauri ta sunkuyar da kanta k’asa….jin shiru ba a fara d’aukar hotunan bane yasanya Yash ya d’ago dakyar ya zubawa me hoton lumsassun idanuwansa.

Najeeb ya kalla wanda

ya ce masa” ka d’auke su a hakan mana” tukunna ya matsa ya fara saita camera…..wajen kalar biyar zuwa shida aka yi musu,shikam me hoto yau ya ga amarya mai lullub’i.

Sai da aka gama yi musu su biyu tukunna su Jidda ma suka shiga, Yassir kuwa har da zama k

usa da ita,aka yi musu su uku…wanda zaman da yayi a kusa da itan saida ya sanya Yashjub ya ji kamar ana zare masa numfashi. Najeeb kam ya san halin kayansa shiyasa ya tsaya a tsaye a gefenshi akayi musu.

Zuwa yanzu hatta masu hoton sun lura da yadda N

ajeeb yake kallon Siyama wadda gaba d’aya take a takure da shi shi kuwa sai wani nan nan yake da ita abun har mamaki ma yake bata…shiyasa ita da Jidda harma Aisha suka d’an fara fahimtar inda mutumin ya dosa .

Masu hoto suna fita Aisha tace

“Yauwa mu z

amu wuce,muna d’an sauri akwai kayan jere da za mu kai gidan nata”

Da mamaki Yashjub ya d’an d’ago ya kalle ta kafin yace”ai all the rooms are full”

Sai kuma ya kalli Manubiya yad’an matsa hannunta dake a cikin hannayensa har yanzu kafin yace”Baby ba m

un riga mun gama shirya komai dake ba?me ya kawo zancen kaya kuma??”

Yayi mata tambayar yana murza hannunta dake a cikin nashi.

Itakam Manubiya kasa ma cewa komai ta yi dan yadda yake yi mata da hannu gaba d’aya ya burkita mata lissafi shiyasa duk yadd

a ta so sai ta gagara cewa komai.

Wani shu’umin murmushi Yashjub ya yi mai had’e da dariya kafin ya sake cewa”

Babyn Yashjub,kin yi shiru….”

Dariya Sir Najeeb yayi kafin yace”Keys d’in suna hannu na,za mu iya barinka anan ko??”

“Yeah,”

kawai ya

ce ba tare da ya kalleshiba dan har yanzu idanunsa suna kan Manu yana murmushi sannan yak’i ya daina murza hannunta.

Sai da Najeeb ya sake sakin murmushi tukunna ya kalli Siyama yace “muje za a san inda za a saka kayan”

“Dagaske Najeeb ba waje ka sani

kuma”

Yashjub d’in ya fad’a still ba tare da ya kallesa ba.

Cikin sigar zolaya Aisha tace

“kai dai ka ji da amarya ka barmu da jere”

“Yauwa abunda nima zan fad’a kenan”

Siyama tace hakan tana d’an dariya.

Murmushi Najeeb yayi kafin yace “Ashe

kin iya magana”

Ya fad’i hakan yana kallonta

wanda ya sa ta d’an ji kunya.

Yashjub ya yi tunanin Yassir zai zauna da shi amman sai ya ga shima ya mik’e yana cewa”bari mu je gidan,sai anjima”

“Okay”kawai Yashjub yace

a ranshi yana aiyyana

“In dai

har Yassir ya nuna yana son d’aya a cikin yaran nan

InshaaAllah zai tsaya mishi yaga ya aura”dan ya lura da yadda suka nutsar da shi a cikin awa d’aya kacal. Yasan tunda har so ya chanja sa ya maida shi mutum mai walwala raha da dariya to ya yi imanin i

nshaaAllah so zai iya chanja Yassir shima ya nutsar da shi ya shiryar da shi.

Yash bai ma san sun fita ba sai da ya ga d’akin ya k’ara haske tukunna.

A hankali ya d’an cika hannunta ya kamo k’asan vail din ya d’aga shi sama,ko a kan kafad’unta bai bar

sa ba sai da ya kai chan k’asa tukunna ya ajjiye shi akan kujerar kawai

ya shiga kallonta.

Ahankali tana mai jinta duk a takure ta d’an juyo ta kallesa kad’an…..d’inkin babbar riga ne a jikinshi na wani irin yadin da bata tab’a ganin irin sa ba tunda

take a rayuwarta.

Yanayin kwalliyar d’inkin anyi sa ne da bak’in zare mix with white,da d’inkin da yad’in da kwalliyar d’inkin sunyi mugun tafiya da imanin ta…..ba ta san yanayin d’inkin maza da kyawunshiba asalima ba burgeta yakeyiba amman wannan kam ta

yi declaring nashi as the best dan ya matukar yi masa kyau,wankan nasa ya bi jiki.

Ya murza bak’ar hula kmr zanna bukar itadai bata san ko akwai hula zanna bukar kuma bak’a ba amma yau ga ta anan,sannan hatta cuff links da agogon sa ma duk bak’ake ne ga k

amshin mayataccen turarenshi wanda tun lokacin da ya shigo cikin parlourn

shi ya fara yi mata sallama….kallonshi take yi sam

ta gagara d’auke idanunta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login