Showing 108001 words to 111000 words out of 259716 words
zai fita.
Ta jima tana kuka ka
fin ta mik’e da kyar ta fad’a toilet sai a lokacin ta lura da gari gari a zuzuube a cikin bathtub d’in ta da kuma k’asan tiles d’in..
Tashi d’aya ta fahimci mai ya faru a wajen ta kuma fara tunanin ko dai shiyasa ta ji ta tsani Yash lokaci guda
kawar da
tunanin tayi da sauri ta yi ta’auzi da isthigfari a ranta tace”Mutum bai Isa ya yiwa bawa komai ba sai abunda Ubangiji ya riga ya tsara”
Sai da ta fara yin fitsari ta zuzzuba a duk wajajen da ta ga garin daganan ta wanke band’akin ta yi wanka ta d’aura al
wallah ta fito still tana jin b’acin rai da takaicin da kuma tsanar Yash amma ba kamar
d’azu ba….
D’aukar wayarta ta yi da niyyar kiran Jidda taci karo da text na rashin mutunci daga Ya’isha ita bata ma san wa ya bawa Ya’ishar numberta dan itama ba ta
da tata sai da taga ta rubuta sunanta a farko kafin ta d’aura da zage zage…hatta kakanninta saida ta zage tass gori kala kala zage zage kuwa har da ashar haka ta dinga rubutu sunan musu tana danna masa zagi…kuma ta tabbatar mata wallahi ko budad’e ko bujum
a sai ta ramawa Yadira marin da ta yi mata…
A zuciye Manubiya ta fara typing d’in reply kamar kuma wadda ta tuna wani abun sai ta ta tsaya ta danne yatsar ta akan delete ta goge tass!
Hawaye ne suka fara sintiri akan kyakkyawar fuskarta kafin ta yi jif
a da wayar a kan gado ta zube a wajen ta fashe da wani irin kukan wanda ta dad’e rabon ta da tayi irinsa…
Ta jima tana kuka kamar ranta zai fita kafin ta d’auki waya ta kira Jidda…
Jidda tana zaune kiran Manubiya ya shigo wayarta dama ita take jira dan
d’azu bata kaiga tambayar ta daliin kukan da suka sameta tana yi ba Manubiyan tace mata tana zuwa za ta kirata…
Tana d’auka ta kara a kunneta tace”assalam alaikom”
Muryar jidda da Manubiya ta ji ne ya sa ta sake fashewa da wani sabon kukan.
A rikice Ji
dda ta mik’e tsaye sai kuma ta d’an kalli Inna ganin tana baccinta ya sa ta fita da sauri.
Tana fita tace “subahannallah Adda Manu mai ya faru???..dan Allah ki yi shiru.”Ta fad’i hakan wasu hawaye suna zubo mata itama……
Da kyar Jidda ta samu Manubiya t
a yi shiru ta shiga gaya mata abunda su Yasira su ka yi mata tun safiya har izuwa yanzu.
Sai da Jidda ta yi da gaske tukunna ta iya hanta kanta kuka dan ta san tana fara kuka za ta karya wa Manubiya kwarin guiwa ne.
Ahankali cikin rarrashi tace
“Ad
da Manu sai da su Innaa suka gaya miki zaman aure dama duk hak’uri ne…ki yi hak’uri kar ki d’aga hankalinki ki yi k’ok’ari ki cinye jarabawarki…kuma ni har ga Allah na d’an ji sanyi a raina tunda matsalar ba daga ya Yash take ba.Su waennan sisters d’in nas
a nasan dolen ki ne su amman tunda basuda kirki sai ki ja jikinki ki rabu dasu gaba d’aya,ita kuma Yadira idan nice ke Allah sai na ga dama zan had’u da ita.
Karki d’aga hankalin ki ki lalata rayuwar aurenki tun kafin ki soma saboda su.
Idan suka zo inda
kike ki yi musu iya ka mutuncin da ya kamata da zarar sun fara miki rashin mutunci ki tartara su ki watsar ki shige d’aki nasan ya Yash zai fahimta.
Sannan kamar yadda kika fara yau karki basu fuskar shige miki d’aki dan nan ne turakarki nan ne kaff gida
n zaki shige ki zauna in sun fara haukar su ba tare da sun biyo ki ba wannan ni kaina na baki goyon baya ki tsaya ki sanar wa ya Yash kar su dinga shigar miki anyhow.
Sannan maganar fad’uwar gaba da garin da kike tunanin ta zuba miki kar ma ki saka haka a
ranki balle ya yi tasiri..babu bawan da ya isa ya yiwa mutum abunda Ubangiji bai k’addara ba. Ke dai kawai ki yi ta addua ki dage da Azkar zan turo miki da wasu addu’o’i ma dana gani an turo a group na y’an class d’in mu sannan zan san yadda zan yi in san
ar wa Inna ba tare da ta fahimci komai ba itama ta dinga yi miki addua.
Sannan dan Allah Adda Manu abunda kika ce kin yi masa muna gama wayar nan ki tashi ki je ki basa hak’uri tunda ma ya nuna cewa ki tafi d’akin nasa ni a gani na kawai ki kwashe kaya
nki ki koma chan saman sannan ki ce masa ba kyaso kowa ya dinga shigar muku,idan ya yarda hakan ya fi tunda dama ai turakarku ba kowa ne ya dace ya dinga shiga ba kuma d’akin yana da girma zai isheku.
Dan Allah ki kwantar da hankalinki ki cire komai a ran
ki sanann batun Kausar d’innan itama kar ki ma bari ta d’aga miki hankali ke dai ki dage da addua a ko da yaushe da sallar dare InshaaAllah ba su Isa su yi miki komai ba Wallahi….”
Ahankali Manubiya ta share hawayenta tana jin
sanyi da nutsuwa suna r
atsata sakamakon shawarwari da kwarin guiwar da ta samu daga wajen Jidda.
Sai da ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna tace “na gode jidda”
kamar itace k’aramar.
Ko da ta yiwa Jidda zancen makaranta tace”ta ga kamar yanaso ya hanata ci gaba da karatu”
Tash
i d’aya cike da bata kwarin guiwa Jidda tace
“Yashjub ba zai tab’a hanata ta k’arasa karatun ta ba.
Kawai yanzu tunda tafiya za su yi ta hak’ura ta bi sa su je su dawo ta san daganan zai
san abun yi kamar yadda ya fad’a maybe yace ta k’arasa Online tun
da ya fad’a mata baya son cud’anyar ta da maza ne.
Amman ita kam tana ba ta assurance d’in ‘Yashjub ba zai hanata makarantaba’ tunda shima ya fad’a da kansa yace yanaso ta yi karatun kuma ai gidan su y’an boko ne so karma ta saka hakan a ranta…..”
Sai
da Jidda ta kuma jaddada mata ta dage da addua tukunna suka yi sallama da juna suka katse kiran.
A hankali ta kife kanta akan gadon ta saki wani siririn kuka…
Sam ita ba ma ta san lokacin da Yashjub ya shigo ba sai da ta ji ya zauna nan bakin gadon kusa
da ita.
A hankali ta d’ago da fuskarta…gaba d’aya sai hankalin sa ya kuma tashi sakamokon yadda ya ga fuskartata ta yi har ta kumbura idanuwanta sun yi luhu luhu.
Kamar zai fashe da kuka sannan kamar mai tsoron tab’ata haka ya matso ya ruk’o hannuwant
a ahankali yace”I’m not supposed to make u cry dan Allah ki daina”
Ya fad’i hakan hawaye suna masu ciccikowa a idanuwansa.
A hankali ta share hawayen nata ta matsa jikinsa bai yi wata wata ba ya rungumeta yana mai sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya.
Hak
a kur’um sai ta tsinci kanta da jin tausayinsa da kuma jin kunyar sa da ta tuna yadda ta dinga turesa d’azu tana korar sa amma kalli sai da ya dawo…ahankali cikin sanyin murya tace ‘’ka yi hak’uri’’
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e mai tafe da
murmushi yana mai jin nishad’i da tsantsar k’aunarta suna ratsashi,d’ago ta ya yi ya yi cupping face nata a cikin hannunsa kafin yace ‘’Manubiya ba ta laifi a wajen Yashjub! ko ta manta ne?’’
Wani irin kuka ta saka ta sake cusa fuskarta a k’irjinsa..rung
umeta kawai ya yi shima yana mai sauk’e ajiyar zuciya a jejjere yana bubbuga bayan ta alamun rarrashi.
Sun jima a haka dan har ta yi shiru bata d’ago ba ta yi lamo kawai tana sauraron bugun zuciyar sa.Tukunna a hankali tace”Ina so zan koma d’akin naka,mu
biyu kawai”
Murmushi ya yi kafin yace
“Whatever u say love..hakan za a yi”
Daganan ya gyara musu position suka kwanta a kan gadon ya shiga lallashinta kamar zai yi mata kuka……
Daman ba ta fara girki ba..kamar yadda Jidda ta gaya mata washegari
da safe ta had’a kayanta har waenda ta rufe a jaka kaff ta kwashe Yash ya tayata kaiwa d’akin sa dan ta gama tsarawa akan ko sun dawo to ta bar d’akin ta muddin Yadira ta na gidan.
Tunda kuwa ta haye sama ba ta sauk’o ba dan hatta abinci delivery man yana
kawowa idan ya bawa Yadira nata zai wuce da nasu sama…ba ta tashi sauk’owa ba sai bayan azahar lokacin da suka zo fita.
Ita a tunanin ta ma tare za su fita da Yadirar amman sai ta ga sun tafi iyaka su biyu kawai.
Haka suka je suka kammala komai na shiry
e shiryen tafiyar su.
Sai dare wajajen k’arfe takwas tukunna suka dawo.
Suna shigowa suka tarar da Yadira da Yassir a zaune a parlourn shi yana waya ita tana kallo
…..tabbas idan Yassir bai daina yi wa matar sa wannan d’an iskan kallon ba wallahi zai y
i abun mamaki sai dai duk abunda zai faru ya faru
tsabar Iskanci har wani lashe Baki yakeyi gashi ya k’ank’ance idanu yana kallonta tun daga sama har k’asa
Tsabar takaici Yashjub bai san lokacin da yace mata “ta wuce ta tafi d’aki”ba
Sai a sannan Yas
sir ya yi murmushi ya mik’e tsaye ya k’arasa inda suke Manubiya tana shirin wucewa ya sa hannu ya karb’i ledar hannunta wanda sai da ya had’a da hannnunta da ledar ya runtse ya murza tukunna ya k’arba ledar yana wani kalar murmushi sannan yace “barka da da
re antynmu”
Da kyar tace “lafiya”
Har ga Allah ta tsani Yassir especially ma yanzu da ta gama tabbatarwa d’an iska ne saboda kalar yadda ya runtse mata hannu ko ita Yarinya ce ta san kalar na y’an duniya ne har wani murzawa ya yi..
Shi kam Yassir l
aushi da taushin hannun nata ne ma ya fi komai d’aga masa hankali dakyar ya juya ga Yashjub wanda ya kafe sa da idanu yace “Ina wuni”
Yana wani killer smile.
Dakyar Yashjub ya iya danne fushin sa dan ya kul’e ba kad’an ba ya san case d’in Yadira ya Isa
wajen Mommy da Daddy bashi da tantama dan Yahansu tace “tanada magana da shi in ya zama free ya kira ta”
Shiyasa kawai ya danne kan sa dan gudun kar a kuma yin wani case d’in.
Cikin kawar da kai yace “lafiya”
Kafin ya d’an kalli Yadira itama yace mata
“lafiya”wadda sai da ta bari Manubiya ta wuce tukunna ta gaida shi,daga haka ya juya yana mai bin bayan Manubiya wadda ta wuce sama da sauri da kallo,kafin ya maida dubansa ga Yassir..da mamaki ya k’ura masa ido ya shiga k’are masa kallo dan idan idanuwan
sa ba k’arya suka yi masa ba tou kamar kayan bacci yake gani a jikin sa shi sai yanzu ma ya lura sannan ya tuno bai ga motar sa a waje ba..
Cikin son fahimtar sa yace
“Banga motar ka a waje ba
ko dawowa za a yi a d’auke ka?”
Murmushi ya yi kafin ya
ce
“Bello ne ya kawo ni ya koma
wai zan kai ku airport ne da safe gobe daganan sai mu wuce gida ni da Yadira”
Shiruu Yashjub ya yi a ransa yace ‘’a tak’aice dai kaima a nan za ka kwana!”
A fili kuma kawai sai ya jin jina kai ya sa hannu yace “bani
ledar”
Da sauri Yassir yace
“No,ga guda biyu masu nauyi a hannunka,bari kawai in kai muku d‘aki
Cikin d’an tsare gida Yashjub yace ‘’bani nan, sai da safe’’
Ya fad’i hakan yana sa hannu ya k’arba ledar…
Ba dan Yassir ya so ba ya basa
dagan
an ya zura wayar sa a aljihu ya wuce d’akin bak’i na nan k’asan zuciyar sa tana turiri…so ya yi ya d’an fara k’addamar da shirin sa akan Manubiya tun yau!ya so ace ya
bata ajiyar sak’o mai nauyi mai tsayawa a rai wanda har ta je honeymoon d’in ta dawo yan
a mata yawo a rai.Ya san rik’e mata hannun da ya yi ma wani abu ne amman ya so ace ya yi wanda ya d’an fi haka…
Bai kamata ya dinga jin kishi ba tunda ba Kausar baceba amman har ga Allah haushi yakeji idan ya tuna Yashjub zai tafi honeymoon da ita wata uw
a duniya!anya kuwa ba k’aunar Manubiya yakeyi ba kuwa!
dan yanzu haka ma da ya tuna da cewa tare za su kwana ita da Yash wani irin tafarfasa zuciyar sa takeyi….
Ya na shigewa Yadira ta girgiza kai a ranta tace
‘’Ya Yassir kenan!”
Shi yasa fa ta k
’i yarda da Junior saboda duk kusan halinsu d’aya da shi da Ya Yassir sai dai Ya Yassir ya fisa sosai dan nasa kam ya fara zama disorder….babban dalilin da ya sa bataji haushin Kausar a lokacin da ta yi futun futun tace ba ta son Yassir ba shine
ta san s
hima ba ita kad’ai yake kulawa ba kuma duk macen da take son zaman lafiya da kwanciyar hankali da ruhi to ba za ta tab’a zab’ar Yassir a matsayin Mijin aure ba…
Dan Tabbas idan aka bincika Ya Yassir tou yanada matsala it’s either psychological ko kuma a
siri aka yi masa da mata dan tunda take bata tab’a ganin confused d’an iska kamar Ya Yassir ba….za ta iya cewa indai mace sunan ta mace tou Ya Yassir yanaso..
Ta san Kausar yakeso da aure amman fa y’an matan da yake so da lalata sam ba za su k’irgu ba kum
a shi sam babu ruwan sa da class ko wani abun..
Yanzu haka a iyaka cikin gidan su kawai ta lura akwai abu a tsakanin sa da Munirat ga Kausar yanzu kuma yadda ta ga tun d’azu da ya zo yana ta faman tambayar ta Manubiya ta fahimci akwai matsala dama tun jiy
a yadda ta ga yana ta shishshige mata ta san da walakin.
Bata san mai yake damun sa ba bata tab’a ganin Namijin da bashi da tsayayyen choice irin Yassir ba wani zubin tana lura da shi idan ya ga mata jikin sa har karkarwa yakeyi,gashi yanzu tsabar idanuns
a sun rufe matar yayan sa yake shirin farmawa!”aikuwa za’ayi murder!indai ya Yash ne”ta fad’i hakan a chan k’asan ranta kafin kuma ta tab’e baki ta mik’e tanajin haushin Manubiya yana ratsata
a hankali a fili tace ‘’su suka sani’’
daganan ta nufi sama d
’akin ta…….MANNUBIYA
(Book 2)
Page 26
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
Dukda Manubiya a k’ule take da Yassir amman sam sai ta k’i yiwa Yashjub maganar sa dan kamar yadda Jidda ta gaya mata inshaaAl
lah ba za ta sake basu k’ofa su zamo silar b’acin ranta ko na mijinta a rayuwar aurensu ba sannan ba za ta sake da su ba….addu’a kuwa tun a jiya ta duk’ufa da yi dan ko shiru ta yi to a zuciyarta addu’a takeyi….
shima Yash d’in bai yi mata maganar Yassi
r ba
shiyasa ita bama ta san a gidan zai kwana ba.
Hira kad’an suka tab’a daganan sukayi nafila suka tofa addu’o’i suka bi gado.
Tun k’arfe uku ta tashi ta yi wanka ta fara shiri,har breakfast yau ta d’an had’a musu ta ajjiye wa su Yassir nasu a k’
asa na ta da Yash kuma ta hau sama da shi ta ajjiye a d’akin…
Yassir kuwa wanda yake ik’irarin ya zo kai su airport ne sai da Yashjub ya zo tafiya sallah tukunna ya tashe sa da kyar…
Doguwar rigar abaya ta saka bak’a ta yafa mayafin..babu kwalliya ko
k’adan a fuskarta amma ba k’aramin kyau ta yi ba.
Ahankali Yashjub wanda dawowar sa daga masallaci kenan ya k’araso ya tsaya a gabanta a hankali ya amsa gaisuwar ta kafin ya yi shiruu ya shiga kallonta,sai da ya gama k’are mata kallo tukunna yayi cupping
face d’inta a cikin tafukan hannunsa yace‘’I’ll forever love you!a ko da yaushe inaso ki yi ruk’o da wannan kalmar dan daga zuciyata da ruhina ta taho babu hijabi’’ya karashe maganar tasa yana mai sakar mata light kiss a saman lab’b’an ta.A hankali Manubi
ya ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya dan kamar yadda yace mata maganar ta taho daga zuci da ruhinsa itama haka maganar ta shiga cikin zuciyarta ta samu mazauni dan har kwalla sai da suka d’an taru a idanunta.
Cikin nutsuwa ya d’auke lips d’insa ya m
annna mata wani light peck a kumatunta da forehead kafin yayi hugging nata yana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya, sun d’an jima a haka tukunna
ya cikata dakyar ya d’an gyara tsayuwar tasu ya koma gefenta ya sak’ale hannunsa na dama a cikin na hag
un ta yace “shall we?’’
Yayi mata tambayar yana mai d’aga mata gira sama.
Murmushi ta yi tana jin tsananin son mijin nata da k’aunarsa suna ratsata dan har wani irin kallo Yash ya ga tana yi masa mai tafiya da imani da zuciyar wanda akeyi ma wa.Ahankali
ya ce
‘’Baby wannan kallon fa?so kike ki sumar da ni?’’
Ahankali itama yadda yayi mata maganar kamar mai rad’a tace
“Ka yi kyau yau sosai,sosai!!’’
Ta fad’i maganar cik’e da shauk’i.
Wani irin blushing Yashjub ya shiga yi mai had’e da dariya
yana
jin sa a sama……
“Mu wuce ko’’?
Muryar Yassir ta katse musu dogon kallon kallon da suke yi wa juna suna masu murmushi,mai cike da shauk’i da sak’onni.
Runtse ido Yashjub ya yi yayin da Manubiya ta yi saurin zare hannunta a cikin