Showing 84001 words to 87000 words out of 259716 words

Chapter 29 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

94

ya barta anan a tsaye zuciyarta tana wani irin tafarfasa.

Ta so ta shiga d’akin Manubiya dayake a nan saman ta zuba abunda Baba la

rai ta bata ta ce ‘ta zuba’ amman sai akayi rashin sa a ko taku biyu ba ta yi ba Manubiya ta hawo saman

dan Yashjub yana tashi su Ya’isha suka fara yada mata da maganganu marasa dad’i! dan dama a wuya suke da ita ji sukeyi kamar su rufeta da duka.

Tana

d’aga kanta dake dama kana iya hango parlourn sama daga nan k’asan ta ga Yashjub ya wuce ya sake hawa bene ya nufi d’akinsa Itakuma Yassira tana tsaye a nan parlourn shiyasa ta mik’e da sauri ta wuce su ta nufi saman ba tare da ta ce musu uffan ba.

Takaic

i da bak’in ciki da rashin jin dad’i duk sun kanainayeta a lokaci guda,zuwa yanzu ta riga

ta gama sanin Allah ya had’ata da dangin mijin da ba su san darajar d’an Adam ba sam kuma ba sa k’aunarta.

Ita ko a labari bata tab’a jin labarin jahilan dangin m

iijin Irin nata ba.

Tana wannan tunanin ta hayo sama idanunta taff da kwallah,

Yassira ta ji motsinta tun a stairs shiyasa ta jiyo….ta na juyowa kuwa su ka yi ido biyu,da sauri Manubiya ta d’auke kanta dan sam bataso Yassirar ta ga idanunta shiyasa tas

hi d’aya ta kauce ta nufi d’akinta ba tare da ta nuna ta ma ga Yasirar a wajen ba…dai dai ta zo wucewa kenan kawai Yasira ta sha gabanta ta ja ta tsaya,lumshe idanu kawai Manubiya ta yi kafin ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya tana mai k’ok’arin rik’e k

anta dan tabbas in ta d’ago a yanzu da wannan temper da take ji ta na taso mata to ba Yaseera ba ko wacece sai ta d’auke ta da mari.

Sun kusan second ashirin a haka kafin Manubiya ta kauce ta chanja hanya amma sai Yasira ta sake shan gabanta ta tare mata

hanya…a hankali Manubiya ta d’an d’ago still tana mai k’ok’arin danne zuciyarta tace”Anya ba daga gidan mahaukata kuka gudo ba kuwa?”.

Murmushi mai had’e da dariya Yassira ta yi kafin tace “eh to tare da tsohon da ya d’aura miki aure muka gudo!

Anyways

dama I just want to see your eyes,Ina so inga how strong u can be kuma na riga naa gani..yadda idanuwanki suka cicciko ya tabbatr min da cewa ‘u are weak!’

shiyasa a take a yanzu wallahi har kin bani tausayi saboda bakiga komai ba!there is a lot coming yo

ur way!”

Sai kuma ta kalleta sama da k’asa tukunna tace

“Da ni da y’an uwana ba ma yin ki!ba ma sonki ba ma k’aunarki!

Kausar ita mukeso ta auri d’an uwan mu amma kika shiga kika fita,amma karki damu dan wallahi idan sama da k’asa za su had’e sai Kausa

r ta auri Yashjub

Mark my words!”

Tana gama fad’in haka ta wuce fuuu cikin tsananin takaici da bak’in ciki….dukda maganganun da ta gayawa Manubiya sun d’an rage mata takaici amma ji takeyi kmr ta mutu…wai ace yau itace ta zo gidan yayanta for the first

time amman ya koreta saboda ba ta gaida matarsa ba,ga shi ba ta zuba maganin da ta ci burin barbad’awa ba kuma Yash yace su tafi ta tabbatr ko sun zo gobe ko da ace su Mommy sun shiga maganar tou it’s either ya ki sake musu ko kuma ma ya sake ce musu su ta

fi gaba d’aya!.Ga kuma takaici da tsantsar tsanar Manubiya da ta ke ji tana ratsa ta…ta ya ma Yashjub zai kalle ta ya ce ta gaida wannan Yarinyar,saboda Allah idan shi ya yi lowering class d’inshi ya zubar da kansa ya zubar da mutuncinsa ai bai kamata ya y

i expecting same thing da ga garesu ba…ai ita Manubiyan ce ya kamata ta gaida su after all ta auri Yayansu an rufa mata asiri ta shigo cikin family dinsu y’ar talakawa da ita.Amman ba ta san na gaba da ita ba wato daman zaman da ta yi da kuma tare k’ofar d

a ta yi tun farkon zuwan su jira takeyi su gaishe ta kennan shi

kuma Yash ya biye mata dake bai san darajar su ba…saboda giyar amarci tana d’ibaar sa shine zai ci musu tuwo aka a gabanta ya wulakanta su saboda ita.

Waennan tunane tunanen ne suka sa duk d

auriyar Yassira ta kasa daurewa dama har yau akwai takaicin dukan da Daddy yayi mata saboda su shiysa ta na sauk’a k’asan da suka had’a ido da su Yasmeen kawai sai ta fara sakin hawaye.

Gabad’ayansu kanta suka nufa suka shiga tambayar ta “mai ya faru?”

D

akyar ta iya controlling kanta tace musu “Ku d’auko handbags d’inku mu tafi”

K’asa k’asa da murya Yasmeen tayi kafin tace

“Kin zuba ,har kin gama?”

Girgiza kai kawai ta yi kafin ta sake ce musu “ku taho mu tafi!”

Cikin rashin jin dad’i Yasmeen t

ace “Kamar ya mu tafi?ba tare da mun yi abunda ya kawo mu ba?”

Ahankali Kausar wadda ta fi kowa nad’ar takaici ta d’an dafa Yasmeen d’in tace “mu je kawai ma dawo wata rana”

Saida Yasmeen ta kalli Yassira tuukunna Yassirar tace mata “ku taho mu tafi

kafin ya sak’k’o”

Cikin fushi Ya’isha tace

“Ba dai shi ya ce mu tafi ba??”

Bata rai Yassira ta yi kafin tace

“Shikenan!ni dai kunga tafiya ta…idan ya sak’k’o ya same ku ba bu ruwana”

Ta fad’i hakan tana mai yin gaba ta nufi k’ofa.

Cikin tarar

numfashinta Ya’isha ta ce”Ai yau sai dai ya kashe ni wallahi amma babu dalilin da zai sanya in fita a cikin gidan nan!aikin banza ku kuke jin tsoronsa…za a ga ikon Allah yau a cikin gidan nan!”

A hankali Yasmeen wadda itama jikin ta yayi sanyi ta matsa

ta shiga bawa Ya’isha baki.

Itakam Kausar juyawa kawai ta yi ta bi bayan Yassira suka nufi k’ofa dan tunda uwarta ta kawota duniya ba ‘a tab’a mata disgi irin wannan ba

Yashjub bai aureta ba

sannan tunda ta shigo ko kallonta baiyi ba kuma saboda ba

ta gaida matarsa ba yace

su fitar masa daga gida.!

Dakyar da mugun kyar Yasmeen ta lallab’a Ya’isha

tukunna ta yarda za ta tafi.

Su Yassira suna bakin k’ofar dan a yadda sukaga Ya’isha ta burkice sun san idan har Yashjub ya sak’k’o ya tadda ita ba

za su k’are ta sauk’i ba.

Tana zuwa ita ta bud’e k’ofar da k’arfi dan a wuya take

tana bud’ewa suka yi ido biyu da Siyama wadda ta d’aga hannun ta da niyyar yin knocking…tun jiya take kiran sir Najeeb a waya amman ya’ki ya d’aga kuma bata da tantama sab

oda wannan shegiyar Yarinyar ne.

Hannun nata ta kalla wanda ta dunk’ule da niyyar yin knocking d’in tukunna ta kalli fuskarta tace “Er mallan Shehu bell ake dannawa ba kwankwasawa ba!”

Murmushi kawai Siyama tayi kafin ta matsa gefe ta tsaya ta hard’e

hannuwanta akan kirjinta,kawai.

Zuwa yanzu Ya’isha ta fara bawa Yassira haushi dan ta ga alamun ta rantse sai ta janyo abunda ransu zai kuma b’aci

dan haka tayi gaba kawai ta barta a wajen hakama su Yasmeen suka wuce aka barta daga ita sai Yadira.

Ya’isha so tayi ta hana su Siyama shiga dan ba zai yiu ita ta gidan yayan ta ace bata samu zama ba amma wasu kuma su zo su shige a gaban

idanun ta!

amma kuma ganin da tayi su Yasmeen duk sun watse sun barta sai kawai itama ta watsawa Siyama tsaki ta wu

ce tana jin tsanar Yarinyar tana ratsata!ji takeyi kmr ta koma ta yi mata illa.

A harabar gidan suka tarar da Aisha ita da su ya Musbah da ya Nafi’u sunata faman sauk’e kayan gara daga motar ya Nafi’u da d’ayar y’ar k’urk’urar da suka zo da ita.

Taka

icine ya sa tunda su Yassira suka yi musu kallo d’aya ba su yarda sun maimaita na biyu ba….tsabar tsiya kalli kayan garar da aka kawo gidan d’an uwansu kamar an rok’o!

A haka wai amma har wani so yake a gaida ita

Inaa da sake wallahi

dama sunsan ba za

su barta ta rayu a cikin gidan ba amman dukda haka dole ta gane kuranta ta san matsayinta kafin ta fita a gidan dan ruwa ba sa’an kwando bane ba.

Dama tunda suka tunkarosu

Aisha tace wa su ya Nafi’u kar ma su kula su kar su ce musu komai basu da mutu

nci.

Haka kuwa suka zo suka wuce bayan sun sake tamke fuska tamau kamar ba su tab’a dariya ba.

Ba k’aramin tashi hankalin Ya Musbah ya yi ba tashi d’aya ya shiga tunanin tayaya k’anwar sa za ta yi rayuwa a tsakanin waennan Yaran….

Tashin motocinsu n

e ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya afka,a hankali ya Nafi’u ya matso kusa da shi ya d’an dafa sa dan shi dama tun ranar da aka kaita Aisha ta basa labarin iskancin da su Yassira suka yi.

Sai da ya fesar da iska tukunna yace “InshaaAllah komai zai

yi dai dai ka kwantar da hankalinka”

Cikin rashin jin dad’i ya Musbah yace “Nafi’u kaga d’aya daga cikin illolin yin aure ba tare da anyi kwakkwaran bincike ba ko?

Abunda na ke gudu kenan shi kuma Baba….”

Da sauri ya Nafi’u ya katse shi ta hanyar cewa

“Karka ce haka!babu ruwan bincike da abunda Ubangiji ya riga ya tsara kaida kawai mu taya ta da addu’a”.

Lumshe idanuwa ya yi ya bud’e daganan suka fara jidar kayan suna kaiwa bakin k’ofa

Siyama kuma ta fara kiran Manubiya a waya dan ya Musbah yana zu

wa yace “kar su shiga kai tsaye su jira Yashjub ya zo ya shigar da su tukunna.”

Tun lokacin da Yassira ta wuce ita kuma ta shige d’akinta ta zauna ta fashe da wani irin kuka,zuwa yanzu ta riga ta gama amincewa babu ta yadda za ayi su zauna lafiya ita

da sisters d’in Yashjub - Yahanasu.

Wanann wacce irin k’addara ce ace wai k’annen mijin ka ne zasu fito k’iri k’iri su ce maka “ba sa sonka”

Kuma sai sun aura masa y’ar uwar su!tayaya za ta yi rayuwa a cikin su taya y’ay’anta za su rayu a tsakanin su?

……

Tana cikin wannan tunanin ta ji an bud’e k’ofar an shigo dan haka ta yi saurin juyar da kanta gefe ta fara k’ok’arin share hawayen ta.

Murmushi ya k’ak’alo shima dakyar tukunna ya k’arasa in da take ya tsaya ya shiga k’are mata kallo kafin chan ya f

esar da iska ya zauna a gefen ta yana mai ruk’o ta izuwa jikinsa cikin sigar lallashi yace

“Wanne d’an gangancin ne ya tab’a min matata?ko Inna kike missing?”

Shiruu ta yi ba ta ce k’ala ba kuma bata daina sauk’e ajiyar zuciya akai akai ba.

Murmus

hi ya sake yi ya d’ago da fuskarta yana kallonta kafin yace

“Ki yi hak’uri”

Girgiza kai kawai ta yi ta fara k’ok’arin mik’ewa…a hankali ya ruk’o ta yace “Ki yi hak’uri!ko..na baki hak’uri ai,next time idan sukazo za su yi miki magana,it’s only a matt

er of time za ku fahimci juna da su inshaaAllah

Yanzun akwai abunda ya d’an faru ne….”

Ba tare da ta kalle sa ba kanta a k’asa tace “saboda kak’i yarda ka auri Kausar?”

Sai da gaban Yashjub ya yanke ya fad’i ba na wasa ba dan sam bai yi tsammanin jin

hakan daga gareta ba, bai so ace ta ji wannan maganar ba!maganar da yake rok’on Allah Ubangiji kar ya tab’a nuna masa ranar tabbatuwar ta ko da a cikin mafarki ne.

Besides waye ma ya gaya mata sannan ai shi ba saboda yak’i yarda ya auri Kausar bane yaus

he ma aka tab’a maganar auren sa shi da Kausar??

Ya yi tambayar a cikin ransa.

Shiruu yayi ya fad’a duniyar tunani….sai yanzu kansa ya d’au chaji! wato hatta su Yasira sun san zancen maganar Kausar tana son shi kuma sun so ya aureta ne,abunda shi da ka

nsa bai sani ba….shiyasa kenan suke fushi suke wannan haukar.To amma Mommy ma a bayansu take itama ba ta son aurensa da Manu!ba ta son farin cikin sa kenan?! ita da y’an uwansa duk so suka yi su manna masa Kausar saboda ba su damu da farin cikin sa ba ko y

a abun yake ne???

Tashi d’aya ya ji kansa ya d’aure……

Ajiyar zuciya ta sauk’e ganin yadda yayi shiruu ya sha jinin jikinsa,a hankali tace”Ba ka tab’a cemin Kausar family d’inka sukeso ka aura ba,ko a ranar da muka fara had’uwa da ita cemin ka yi she’s

just a sister”

Ahankali ya fesar da numfashi ya kamo hannayenta tukunna yace”Wallahi Allah nima yau na fara jin zancen nan

Wai ‘Kausar family d’ina suke so na aura!’ban san maganar ba

In da na sani kin san da zan fad’a miki,but a Ina kika ji zancen?”

Girgiza kai tayi tace “Shikenan”

daga haka ta fara k’ok’arin barin wajen

A ranta kuma tana mamakin yadda still yake k’ok’arin b’oye mata zancen bayan ga mamaki nan k’arara a kwance a kan fuskar sa wanda hakan yake tabbatar mata da ya san da maganar.

A b’angaren Yashjub kuwa

mamaki yakeyi…shi dai ya san ya ji lokacin da Kausar tace tana son shi ya san dama Mommy za ta iya goya mata baya amma bai san abun ya kai har haka ba kuma harda su Yassira ma sun san maganar kuma suna so ya aureta bayan sun sa

n ita d’in budurwar Yassir ce,

to me yake faruwa ne a cikin gidan nasu wanda shi bai sani ba dan ko Manubiya bata gaya masa ba ya fahimci a zuwan su na yau ne aka samu wata ta gaya mata wannan maganar domin a shiga tsakanin ta da shi!me yasa su Yassira za

su zama haka ne!wannan wacce

iriyar halayya ce suka k’irk’iro da ita sabuwa…..

Ji yayi kawai ta bud’e k’ofar ta fita har ga Allah bai san lokacin da ta mik’e ta isa k’ofa har ta fita ba…tana fita wayar ta ta d’auki k’ara dan haka ta d’auka ta kara a

kunnenta

Jin Siyama ce yasa ta yi iyakar bakin k’ok’arinta ta tsayar da hawayen ta d’an share ta sauk’a k’asan da sauri dan ta ji kamar Yashjub d’in zai fito ita kuma har ga Allah a yanzu ko fuskarsa bata k’aunar gani!zuciyarta ta gama aminta da cewa

‘ya san da zancen Kausar amman ya k’i gaya mata’

dan haka tashi d’aya ta yi concluding akan shima yana son Kausar d’in maybe dai akawai wani abu da yake b’oyewa amman dai yanada niyyar auren Kausar duba da yadda ya yi shiruu ya gagara cewa komai.Wani irin

mahaukacin tafarfasa zuciyarta takeyi ita kanta ba ta san ta na son Yashjub kuma tana kishin sa irin haka ba sai yanzu da ta ji maganar aure na shi da wata

sannan kuma reaction d’in sa da kame kamen da ya hau yi mata ya tabbatr mata akwai zancen b’oye m

ata kawai yayi.

Kafin ta k’arasa k’asan har ta fara haki tsabar yadda k’irjinta da zuciyarta suke lugude

ga kuma sauk’an stairs.

A bud’e ta hango k’ofar dan haka ta k’arasa da d’an sauri sakamokon fara hango ahalinta da ta yi dan chan ta hango Muhsin

yana fama da roba sai k’ok’arin d’auka yake yi.

Da sauri ta k’arasa ta na fita sukayi karo da su jidda dan haka ta fad’a jikinsu cikin murna da kewar su.

Sai da ta yi da gaske tukunna ta samu ta hana kanta kuka

dan ganin su da tayi ba kad’an ba yas

a ta sake zama emotional.

Murmushi kawai suke ta zubawa suna kallon ta tana faman bin su one by one tana huggin d’insu har ya Musbah ya Nafi’u ne kawai batayi hugging ba

Daga nan ta fara jan hannun Jidda tana cewa”su shigo”ba tare da ta kalli kowa ba da

n sai yanzu ta tuna yadda ta sauk’o ba tare da ta wanke fuskar ta ba…ta san tabbas idan suka yi mata kyakkyawan kallon kurilla tsaf za su fahimci kuka takeyi sai dai kuma abunda ba ta sani ba shine tan fitowa duk suka lura da hakan.

Ya Musbah ne ya t

saida ita ta hanyar cewa”ki bari ya zo ya shigar damu mana”

Dariya Siyama tayi

kafin tace “Allah ya Musbah ka iya abun dariya,”

Sai kuma ta kalli Manu tace”

Tun d’azu fa shi ya tsayar da mu wai ala dole sai Yashjub ya ce masa ya shiga tukunna zai sh

iga.”

Ahankali ta juyo tace

“Dan Allah ku shigo mana”.

Yana shirin yin magana Yashjub d’in ya k’araso shima yana d’an murmushi yace “bismillah,amma dai next time ba sai na ce ka shigo ba gaskiya”.

Duk murmushi sukayi banda Ya Musbah wanda hankalin s

a ya tashi da ganin yanayin Manubiya dan ya tabbatar da kuka ta yi kukan ma bana wasa ba dan gashi hatta kan hancinta yayi ja!……MANNUBIYA

(Book 2)

Page 23

Na

Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Ahankal

i ta juyo tace

“Dan Allah ku shigo mana”.

Yana shirin yin magana Yashjub d’in ya k’araso shima yana d’an murmushi yace “bismillah,amma dai next time ba sai na ce ka shigo ba gaskiya”.

Duk murmushi sukayi banda Ya Musbah wanda hankalin sa ya tashi da ga

nin yanayin Manubiya dan ya tabbatar da kuka ta yi kukan ma ba na wasa ba dan gashi hatta kan hancinta yayi ja!……

Anan parlourn k’asan suka nemi guri suka zazzauan

tukunna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login