Showing 138001 words to 141000 words out of 259716 words
/>
onta musguna mata zai ta yi…amma yanzu na fahimci masifaffiyar soyayya take yi masa,no matter what she’ll stick around and always love him unconditionally….abunda Yasmeen ta yi mini akan batun zubar da cikinnan ya sanya na fahimci Yaran nan ba za a dad’e b
a kowacce za ta fara fito da nata view d’in tana jayayya da ni,kuma indai har Yasmeen y’ar cikina za ta iya yi mini hakan to abu mai sauk’i ne ga Kausar dan ta bijere mini,shiyasa na gama yankewa akan’babu maganar Kausar da Yashjub za mu san yadda za mun y
i amma I can’t trust Kausar akan wannan Lamarin gaskiya…..”
Shiruu Baba larai ta yi kafin tace”to amma kuma ta ya za mu samu wanchan abun kenan?ko mun b’ata shekaru a banza kenan?ki duba future d’in Yassir ki sake tunani….”shiruu Baba larai da maganar ta
d’an yi tunani kafin tace”to ko Manubiya za mu jira ta haihu idan ta haifa sai mu rik’e…….”
Cikin katseta da d’an b’acin rai Mommy tace”haba larai!ke fa da kanki ki ka sanar da ni illar kasancewar Manubiya a tare da Yashjub kuma gashi muna gani muraran!
…besides ko dan masifar da wannan cikin da Uwarsa da Ubansa suka sakani a ciki wallahi dole sai ya fita!ko ana ha maza ha mata……”
K’ausar tana hawaye,a haka ta k’arasa side d’in Mommy ta shiga ta wuce parlourn ta nufi bedroom,har za ta tura k’ofar d
’akin ta shige ta ji Mommy tana cewa”za dai mu san abunyi za mu nemo mafita amma cikin jikin Manubiya ya zama dole ya fita,sannan ba zan tab’a bari Kausar ta auri Yashjub ba!.”
Wani irin duhu duhu dishi dishi Kausar ta fara gani…ita da ta zo a kan ta cewa
Mommyn ‘mai zai hana a yi tricking Yash ta samu ciki ta yadda dole sai ya aureta…’
amma shine take jin wannan batun daga bakin Mommy??
Dama ita ba ta yi shirin gaya mata tana da ciki ba dan ta san ba za ta yarda a aurawa Yash ita da cikin Yassir a jikin
ta ba,shiyasa take so ta bata wannan idear ta yadda ko shi Yassir d’in bai Isa ya san cikin nasa bane kawai kowa a tafi a kan cikin Yash d’in ne,ta samu ta rufawa kanta asiri burinta ya cika.Sam ba ta yi expecting haka daga Mommy ba,wato ta barta ta gama l
alacewa shine yanzu take kyamar ta had’a d’anta da ita kenan ko yaya?
tabbas blood is thick! Ita kuma ta tabbata all alone….
Wani Irin kuka ne ya taho mata dan haka ta yi sauri ta juya gudun ma kar su jiyo ta ta nufi k’ofar parlourn hannunta a kan bakint
a tana mai k’okarin hana sautin kukan nata fitowa.Kusan karo suka yi ita da Daddy wanda ya turo k’ofar parlourn ya shigo.
Shi ya wuce ya nufi d’akin ita kuma ta fice ta nufi d’akinta tana kuka kamar ranta zai fita.
A tsaye ya same su ita da Baba larai…
.sum sum haka Baba larai ta sa kai ta fice bayan ta yiwa Mommy wani kalar kallon da su kad’ai su ka san me take nufi.
Tana fita ya lumshe idanuwansa ya d’an bud’e kafin ya k’arasa kusa da ita yana mai kallon cikin idanuwanta yace”mallan lawal ya rasu”
Gefe da gefe ta kalla kamar irin tana tunani d’innan kafin tace”Daddy mai ya faru??? Kai fa ka ce a daina maganar nan kuma yau kai da bakinka ga shi ka kawo ta?”
K’ura mata ido ya yi,dama yana so ne ya ga reaction d’inta ko zai iya kamata da laifi amma
babu alamun hakan a tartare da ita!
Ya san yadda Mommy ta kula da mahaifiyar Yahanasu suka zauna lafiya idan ya zargeta a kan incidence d’innan to bai yi mata adalci ba,amma kuma tunda mallan lawal ya kirasa d’azu ya fara basa hak’uri yana cewa yana son m
agana da shi to tun daga nan ya fahimci anya ba sharri aka k’ulluwa Khadijansa a wannan lokacin ba kuwa! sannan kuma kan sa ya d’aure matuk’a ta inda yana da tabbacin mallan lawal d’in ya mutu tun shekaru wajen ashirin da bakwai baya amma yanzu gashi ya ji
sa a raye dan ko a mafarki idan ya ji muryar mallan lawal sai ya gane,shiyasa tashi d’aya ya tabbatar akwai k’umbiya k’umbiya a cikin al’amarin..
Khadija ba ta shiga ko mak’ofta sai tare da Mommy kuma ko hayaniya ba ta tab’a yi da kowa ba ita ba ma ta iy
a fad’an ba,duba da haukar da Mommy ta yi a lokacin da yace zai k’ara aure da kuma yadda ta shiryu lokaci guda ta rungumi Khadija tashi d’aya dama tun a wannan lokacin ya ke zarginta kuma ya ke ganin kamar akwai abunda ta ke shiryawa amma bai yi tunanin za
ta iya yi mata wanchan sharrin ba!
Dan Khadija ko y’an uwa ba ta da shi balle ace wani ne ya yi mata sharri tabbas wannan aikin Mommy ne…
Sannan a cikin gidan ya yi waya da Mallan lawal ya san maybe Baba larai ce za ta gaya mata,shine ta kashe sa kena
n??gudun kar asirin ta ya tonu?Tabbas kuwa indai hakan ya tabbata to bai ma san wanne kalar hukunci zai yanke mata ba!
Matsalar guda d’aya shine yadda ta yi d’innan ba dan shi da kansa gaba d’aya alamomi suna masa nunin kamar ita ce master ba,to ba dalili
n da zai sanya ya zargeta.
A b’angaren Mommy kuwa in banda lugude babu abunda zuciyarta take yi!k’arfin hali ne kawai yake amma a mugun Muhsin hargitse take tun da ya shigo ta firgice…
“Daddy ka yi shiru”
D’in da tace ne ya katse masa tunani…
A han
kali yace”yanzunnan ya rasu”
Wata zabura ta yi tace”innalillahi wa inna ilaihirrajiun,
Daddy dama chan bai rasu ba??me ya faru?kiranka ya yi?”.
Ta fad’i hakan ita kanta ba ma ta san ta fad’a ba tsabar rashin sanin tudun dafawa,kar ta yi shiru ya zargeta
shiyasa ta zab’i ta yi maganar da ta zo mata.
Wani kalar mahaukacin bugawa zuciyar Daddy ta yi dan tabbas Mommy ta k’ulle kanta da kanta..ta ya aka yi ta san kiransa ya yi?
Jin jina mata kai ya yi yana jin kamar ya shak’e ta ya kashe ta right away,d
a kyar ya iya cewa”kira na ya yi ya ce in yafe masa yana buk’atar gani na da gaggawa.”
Zuwa yanzu yadda Mommy ta fara gumi ya gama tabbatar masa da komai,dama abunda ya zo tabbatar wa d’in kenan shiyasa ya zo mata a haka,cikin son sake ganin reaction d’
inta yace”tun lokacin da ya kira ni ya fara magana gaba d’aya hankalina ya karkarta ne a kan watak’ilan Khadija ma tana raye.”
A take ya ga idanuwanta sun fara ciccikowa da hawaye kamar za ta yi kuka…da kyar bakinta yana wani irin karkarwa ta samu tace”
Noo Daddy it can’t be,idan shi ya rayu ita ba zai yiu ta yi rai ba,ko ka manta yadda ita d’in da hannunka fa ka c….”
Yadda taga idanuwansa sun yi jaaa a take ne ya sa ta had’iye maganarta ta sunkuyar da kanta,kafin da kyar ta sake d’agowa tace”amma ban sa
ni ba sai dai mu fara bincikenta,watak’il itanma she made it out alive..saboda ka san dama na gaya maka wajen yadda ya koma ba mu iya detecting ko da biro ba ballantana gawa komai ya kone k’urmus ruwa kawai muka yayyafa aka yi musu salla a haka…..”
Wuff
kawai ta ga ya juya ya fita zuciyarsa ta na wani irin tafarfasa dan ya san tabbas idan ya ci gaba da zama to zai iya aikata abun ban mamaki ga Mommy…Mommy ta yi masa abubuwa daban daban tun daga kan yadda ta tilasta masa aurenta har kawo yanzu kullum a ci
kin b’acin ranta ya ke,amma bai tab’a tunanin za ta iya aikata haka ba,sannan gashi still k’ok’arin b’oyewa amma ya san ta yadda zai kamata dumu dumu yadda zai k’ulleta da jijiyoyin jikinta ya tona mata aisiri kowa ya ganta…hacking wayarta kawai zai yi ta
yadda ko typing take yi sai ya gani.A nan ne kawai zai ji komai da take yi ya ga komai ya kamata dumu dumu ya tabbatar da zarginsa a kanta.
He really can’t believe this!he can’t believe Mommy ta saka shi ya kashe Khadijah da hannunsa ba tare da laifin ta
ba,dan kamar yadda ita ma Mommy ta fad’a idan mallan lawal ya samu ya yi making out alive ita Khadijah ba ta Isa ta fita da rai ba.
Tabbas kisan kai it’s too easy for Mommy…shi kansa yana jin tsoron abunda zai yi mata Wallahi.
Kasancewar Yass
ir a napep ya taho ya sanya sai yanzu ya samu ya shigo cikin gidan…..
Yana zuwa a fusace ya haye sama ya nufi d’akin Kausar,zuciyarsa tana wani irin tafarfasa.
Kausar ta na wani irin kuka haka nan ta shiga d’akin ta ta fad’a kan gado…..ta yi kuka
a wannan rana kamar ranta zai fita kafin ta mik’e ta fad’a toilet ta shiga wanke fuskarta a ranta kuwa ta gama aiyyanawa “wallahi
daga yau ita ma ta kanta za ta yi farin cikin ta kawai za ta duba!kowa ya yi ya kansa….inshaaAllah sai ta mallaki Yashjub ko
ta halin yaya ne,daga nan za ta nunawa Mommy wacece Kausar,sai ta san ta yi betraying d’inta wallahi daga kanta ko d’an aiki ba za ta sake betraying ba.”
Tana wannan lissafin ta fito daga toilet d’in…a d’akin ta tarar da Yasira,cikin rashin kwarin jiki
Yassirar ta mik’e ta k’arasa ta ruko hannunta kafin tace “ta zo ne akan ta yi mata gargad’in ta bi Yassir a hankali kar ta bari ya fahimci wani abun gudun kar yaje ya yi mata kwab’a.Dan yadda ya yi mata d’azu a asibiti ita kanta ta d’an tsorata gaskiya”da
“to” kawai ta bi ta daganan Yasirar ta juya ta fita dan ta fahimci kamar Kausar d’in ta na buk’atar space.
Tana fita Kausar d’in ta girgiza kai a ranta tace’’kwab’a kuma ta nawa?bayan abunda ya aikata,’’wannan shine karo na biyu da ya so ya kashe Yashjub
kuma ta lura Mommy ma ta fahimci wani abun amma ta ga kamar k’ok’ari ma take yi ta b’oye…
A hankali tana jin kanta yana wani irin mahaukacin sarawa
ta nemi guri ta kwanta.
Lumshe idanuwanta tayi
atake hawaye suka shiga sintiri a kan farar fuskarta
Wannan wacce irin rana ce ta risketa?…ga ciki tana d’auke da shi,ga Mommy wadda ta juya mata baya ga kuma Yassir wanda take zargi da wannan
shirmen a karo na biyu
sannan bata Isa ta tunkare sa da maganar ba dan ba ta so ya
fahimci wani abun
Sann
an ga rayuwar Yashjub dake a cikin hatsari ga Manubiya ga shi Yashjub d’in ma kansa har yanzu ta kasa samun sa!,ta Ina za ta fara ne?dan abubuwan sun yi mata yawa.
K’arar bud’e k’ofar d’akin nata ta ji da mugun k’arfi dan haka ta tashi a d’an rikice duk
da kuwa da ma ta riga ta san waye ne.
A tsaye a bakin k’ofar ta gansa yana huci kafin ya juya ya rufe k’ofar ya murza key tukuna ya nufota gadan gadan…
Duk tsaurin idon Kausar sai da ta tsorata dan haka tun kafin ya k’araso ta mik’e tsaye tana mai gyara
doguwar rigar jikinta ta hau inda inda cikin in’ina tace’’Yassir I’m sick dan Allah ka bar….’’
Mahaukacin marin da ya d’auke ta da shi ne ya sanya ta gagara k’arasa maganar tata,sai da numfashinta ya d’auke na y’an seconds tsabar tsananin shock d’in da t
a shiga,a rikice ta d’ago fuskarta da ta yi jajir ga shatin y’an yatsunsa sun fito rad’o rad’o a fuskar tata tace ‘’Yassir ni ka mara??’’
Cikin karsashi yace‘’appetizer ne wannan kar ki damu,if you like ki bari in yi miki tambaya ki yi mini k’arya…’’
Ya
fad’i hakan yana mai kunce belt d’in wandon sa.
Cikin fushi tace “dukana za ka yi?baka da hankali ne?duk abubuwan da ka yi basu ishe ka ba???’’
Dakatawa ya yi daga nad’e k’asan belt d’in da ya ke yi around his fingers kafin ya d’ago jajayen idanuwansa
ya zuba su akanta tukunna yace ‘’abubuwan da na yi?me da me na yi kenan?’’
Ya fad’i hakan cikin matsowa daff da ita yana mai tsare ta da dara daram idanuwansa da suka yi jajir hatta fuskarsa ta yi jaaa tsabar bala’i.
Ahankali ta d’an ja da baya dan a m
ugun tsorace take dashi
Sai da ta d’an kauda kanta gefe tukunna ta yi k’asa da murya tace’’ Wallahi zan tona maka asiri,in har ka tab’a lafiya ta sai kowa ya san kai ne ka tura y’an fashi estate d’in Yashjub yau’’
Cak!haka ya k’ame,kafin ya juyo da fu
skarta cikin karsashi yace ‘’Kausar ni za ki yiwa sharri da borin kunya saboda kinga na kama ki dumu dumu?’’
Ganin yadda jikinsa ya yi sanyi kuma ta ga ta d’an samu galaba a kansa ne yasanya ta fincike fuskar ta tace’’ba iya wannan ba ma Wallahi har tay
ar motar sa da ka cire kwanakin baya sai na fad’a kowa ya ji ,tun da dama son da nake yi maka ne yasanya nake rufa maka asiri amma in har zaka iya d’aga hannu ka mareni to na san ka daina sona dan haka nima ban ga amfanin ci gaba da son ka Ina bin bayan ka
ba ,’’
Ta fad’i hakan tana mai rushewa da wani uban kuka wanda yayi tsananin tasiri akan Yassir.
Ganin kamar so take ta bugi cikinsa sannan kamar wayo take so ta yi masa ne yasanya ya dake yace’’ke!Kausar bana son hauka da shirme da sharri…idan ba so
kike in yi miki more than abunda na yi niyyar yi ba to kawai ki bani amsoshina da na zo k’arba mu yi ta ta k’are,”
‘’How dare you!ta ya ma zaki k’ala mini sharri wai ni Ina so in kashe Yashjub! baki da hankali ne?kuma wa kike tunanin za ki gayawa wannan
maganar ya yarda?bari ki ji ko Mommy idan kika gayawa wallahi ba za ta tab’a yarda da ke ba,za ki sha mamaki idan ta juya miki baya har abada ,dan babu uwar da za ta yarda wata tazo ta ce mata d’anta yanaso ya kashe d’anta!’’.
Goge hawaye Kausar ta yi t
a d’ago ta fuskance sa tukunna tace’’Yassir cewa na yi ‘zan fad’awa kowa kaine ka cire tayar mota sannan zan fad’awa kowa kaine ka saka bomb a estate d’in Yashjub’.A kaff cikin maganata ka ji ta inda nace ‘kana so ka kashe Yashjub’?’’.
Cikin fushi harga
gi da hargowa yace’’Kausar zan illataki fa! ni za ki yiwa wasa da tunani?ai indai aka ji kince na cire taya to an san kashe sa nake son yi kenan!’’
Tsit!haka muryarsa ta tsaya chak!yana mai recalculating what he just said yanzun a cikin kwakwalwar sa’’
Kafin ya yi cilli da belt d’in hannunsa tukunna ya d’aga hannu kamar zai damk’i wuyanta kamar kuma wanda ya tuna wani abun sai ya tsaya chak!! kafin ya juya mata baya yana wani irin huci kamar mayuncin zaki….
Wata bahaguwar ajiyar zuciya Kausar ta sauk
’e kafin ta d’an matsa garesa tace’’ Bari kaji abunda baka sani ba! Ko da ace Mommy bata tab’a shiga aji ba,wallahi ba zan yi kaffara ba itama ta d’an fahimci wani abun,sakamokon yadda ka dinga k’ok’arin tonawa kan ka asiri tun a crime scene d’in,har sign
na dinga yi maka da ido amma sam ka kasa fahimta
Shiyasa ka ga hankalina ya tashi raina ya b’aci,ga kuma rashin lafiyar da take damuna,’’
Ahankali ta sake taku d’aya ta kamo hannunsa ba tare da ta zagaya gaban sa ba ta ci gaba da cewa’’ranar a d’akinka
na gaya maka we re on this together,Yassir tunda har na iya danne zuciyata na had’a ka da Munirat inaso ka san na d’auki mission d’innan da mahimmanci,duk da na san cewa kashe Yashjub ba ya cikin tsarinmu amma idan har ka gaya mini dalilinka zan goya maka
baya,kai ko da ace ba za
ma ka gaya mini dalilin naka ba Yassir zan goya maka baya I love you I want to see u win akan komai kai kuma a ko da yaushe zargina kake yi ban san ta ya zan nuna maka ina sonka ka yarda da ni da gaske ba, da ace na san taimakon k
a da muka yi da ni da Mommy zai janyo mini haka daga gareka da ban yi ba tunda na lura tun lokacin da na d’an ja baya da kai saboda mu samu a fasa aurenmu a k’ara maka share har gobe baka yarda da ni ba Yassir’’
Ta k’arashe maganar tana mai durk’ushewa a
wajen ta fashe da kuka.
Ahankali Yassir ya sauk’e ajiyar zuciya tashi d’aya ya fara ganin rashin kyautarwar sa,how can he not trust Kausar?despite irin gogayyar da take yi wajen ganin ta taimaka masa,shi sai yanzu ma kwakwalwar sa ta d’au charji amma kw
anaki da d’azu gaba d’aya duk kishi ya rufe masa ido,tabbas everything is fair in love and war!’they are at war’ dan haka komai is fair kamar yadda ta fad’a dan ta had’asa da Munirat saboda su samu su yi achieving abunda suke so bai kamata ya dasa ayar tam
baya a kanta ba wanda hakan ne farkon zargin nata da ya fara,tunda in komai ya yi daidai ya tafi yadda suke so ai sune da win.
Ahankali ya juyo yana jin tsananin tausayi da k’aunarta suna ratsa sa ya ce ‘’stand up’’
A ranshi yana mai cewa “inshaaAllah
zai yi k’ok’ari ya goge tunanin’watak’il Kausar tana son Yashjub’ daga cikin zuciyar sa.But for last time akwai abunda yake son confirming ta yadda zai yarda da ita d’ari bisa d’ari.
Ganin ta k’i tashi ne ya sanya shi ya durk’usa ya kamota ya d’ago da ita
tashi d’aya ya sakata a jikinsa yana mai bubbuga bayanta