Showing 213001 words to 216000 words out of 259716 words
musu mun zare hannunmu a bikincen sai dai kuma family’s d’in victims d’in Estate d’in naka gaskiya sun kunno wuta dan bincike s
osai suke yi cewa ma ya yi ko mu mun janye yanzu haka sama da mutane ashirin ne tsaye tsayin daka a kan case d’in.”
A hankali Yashjub ya sunkuyar da kansa k’asa ya yi shiruu kafin ya d’ago ya ja hanci yace”kar ka gaya wa kowa inda nake dan Allah…ba wai
iyaka Yassir ne dalilin da ya sanya zan tafi ba”
Sai da ya yi shiru ya sake jan hanci tukunna yace”Yau su Daddy suka aura min Kausar….”
Dalla Dalla ya gayawa Najeeb bayanin komai da dalilinsa na k’in zama da Kausar…tashi d’aya Najeeb d’in ya yi supportin
g d’insa d’ari bisa d’ari.
Sai asubah tukunna suka gama shiryawa da had’a kan komai..
Kamar kar su rabu Najeeb har da hawayensa dan mugun mugun tausayin Yashjub yakeji hakanan suka yi sallama daga haka driver ya d’auke su zuwa hotel bayan Yash ya damk’
awa Najeeb makullan gidan yace da safe ya kaiwa su Mommy dan tace za su kawo Kausar.Dalilin ma da ya sanya ya k’i amincewa su zauna a cikin gidan kenan,gudun kar su ce za su kawo masa ita da safe.
Sai washegari da safe tukunna Ummi ta samu courage d’i
n confronting Hajiya Mama…har ga Allah Hajiya Mama ta yi tunanin Ummi wasa take yi mata da farko dan kwata kwata ba ta tab’a yin tunanin su Daddy za su tafka wannan kwab’etar ba!that too ba tare da sun shawarceta ba.
Sai da ta saka Ummi ta rantse mata tuk
unna ta yarda,Hankalinta a mugun tashe ranta a masifar b’ace ta kalli Ummin da ta fara dibi dibin bata Baki tace”ke kanki kinsan babu ta inda za ki ce mini hakan ya dace ko?”
Shiruu Ummi ta yi ta sunkuyar da kanta k’asa.
Ajiyar zuciya Hajiya Mama ta
sauk’e kafin tace”to ki yi shiruu kawai kar ma ki bawa kanki wahala.”
“Ina shi Yashjub d’in yake ya sani??a gaban sa shima aka d’aura??”
A hankali Ummi tace”a’a..na dai kira na gaya masa nace ya zo a san abunyi, to dai tun jiyan bai zo ba yau kuma inat
a kiran wayarsa daga shi har Manubiyan ba ya tafiya.”
Jinjina kai Hajiya Mama ta yi,fuskarta har ta yi jaaa!
Ta kalli Ummi tace”ki kirawomin su Imam d’in ki ce na ce su zo yanzunnan!”
“Tam”Ummi tace daga haka ta mik’e ta sa kai ta fice.
Ba’a yi
mintuna goma ba,Daddy ya shigo da shirin tafiya office Abhi kuma da jallabiya.
Ko gaisuwar su ba ta amsa ba ta kalli Daddy tace”ashe har kana iya tafiya office bayan masifar da ka k’ulla a gidanka jiya??”
A hankali ya sunkuyar da kansa k’asa yace”ki y
i hkr Hajiya Mama da ma yanzu nake shirin shigowa mu tattauna kafin in wuce!”
Cikin fushi tace”Imam tattaunawa kuma ta nawa?
Sai da ka gama yanke decision da kai da munafuka!muguwa!!makirar matarka!!!!tukunna za ka zo ka ce mini za mu tattauna saboda k
a raina ni??
Me za mu tattauna???
Ina sauraronka gaya mini menene ya rage wanda ba ka riga ka yanke hukunci ba?”
Shiruu ya yi ya gagara cewa komai.
Cikin tsananin b’acin rai ta kallesu su duka biyun tace”da ni da ku duk mun shirya a kan za a sakawa K
hadija ido a bincike ta a gano ta a nunawa Yaranta illarta da illar d’abiar da ta d’aurasu a kai tukunna a sallameta a cikin gidan nan,amma saboda tsabar ku d’in ba jajurtattun maza bane ba a cikin awannin da basu wuce biyu ba Yarinya y’ar k’arama Kausar d
a Khadija sun juya muku tunani kun aurawa Kausar Yashjub!!!
Daga ta yi y’ar drama da shirmenta shikenan har kun kamu??”
Da kyar Abhi ya iya cewa”Hajiya mama cewa ta yi za ta tafi da Yaron shi kuma Yashjub ko
Maganar mu ba ya ji iyaka maganar Manubiya
ya ke bi da farincikin ta..a jiyan fa cewa ya yi wai sai abunda ta yanke tukunna za a yi”
Sakar Baki kawai Hajiya mama ta yi ta na kallonsa har ya dasa aya tama kasa cewa komai.
Da kyar ta iya cewa”idan na fahimce ka, kishi kenan kuke yi da Manubiya ka
mar wasu mataa!!!shiysa kuka aura masa Kausar saboda kar Manubiya ta yi dominating d’insa ita kad’ai ko?”
“This is the dumbest thing da na tab’a ji tunda uwata ta kawo
ni duniya wallahi tallahi!
Ina tunaninku ya tafi ina hankalinku ya tafi??
Kausar faa
a!!”
Cikin son yi mata bayani Daddy yace”ai Kausar d’in ba fa wai mun aura masa ita forever bane mun aura masa ita ne akan idan ta haihu sai su rabu”.
Mik’ewa kawai Hajiya mama ta yi ta nufi wajen kayanta ta fara fito dasu tana cewa”Bari
Ka ji in ga
ya maka,Indai Kausar ce to ba za ta tab’a rabuwa
da Yashjub ba ba za ta yarda ba!
Barr ganin wai da Yassir kuka santa,a yadda Khadija ta tsani Manubiya ba za ta bari Kausar ta bar Yashjub ba,
A tunani na auren ka da Khadija ya isheka ishara ya Isa ka g
ane idan aka auresa ba sa fita tunda tun yaushe kake so ka saki Khadija ta saku???”
Ta yiwa Daddy wanda ya matso ya rik’e trollyn hannunta tambayar.
Ba ta jira jin amsar shi ba tace”kuma saboda ku wawaye ne kuke tunanin Kausar za ta yarda a saketa?
Wai
ma shin ina lissafin ku ya tafi da Kausar d’in tace za ta tafi kuka biye mata kuka yarda??
Khadija fa kad’ai sai Larai gareta a kaff fad’in duniyar nan,Wallahi ko ta tafi k’ark’ari ta yi wata biyu zuwa uku nasan ita da kanta za ta dawo ko su Larai d’in s
u nemota.Kuma indai Khadija ita ta haifi Yashjub ba zata bari Kausar ta b’ata masa suna ba,dan na san duk bakin su d’aya.
Abu simple very simple amma kuka gagara tsayawa ku yi lisssafi mai kyau sam saboda an had’a da asiri da wayo!!!
Saboda Allah kalli
abunda kuka tafka!!ko
Shawara da ni bakuyi ba,kai da ake so a gyara gidanka a kub’utar da kai amma kalli yadda ka
sake damalmala komai!!!dan ba ka isa ka ce ka rabu da Khadija ba muddin Kausar ce matar Yash,ko ka kori Khadija a gidan nan indai Kausar ta
na a
matsayin Matar Yash wallahi ka yi ta banza ne…”
A hankali Abhi shima ya k’araso dan Daddy yana rik’e trolly ta sakar masa ta cigaba da zaro kayayyakinta rai a tsananin b’aci tana magana tana had’a kaya…cikin lallami yace”Hajiya mama ki yi hak’ur
i dan Allah mun yi laifi wallahi ni
kaina sai yanzu na ke ganin rashin dacewar hakan.”
Juyawa ta yi ta kallesa tace”kad’an daga aikin Khadija!ai ba za ku san lokacin da kuka d’aura ba dama…”
Cikin chanja topic d’in tace”ka
fara yi mini shirye shiryen
tafiya meanwhile ka kama mini d’aki a hotel kafin komai ya kammala dan wallahi na gama zaman cikin gidan nan!”
“Innalilla wa Ina ilaihirrajiun”
Daddy yace kafin ya d’aura da cewa”Hajiya mama dan girman Allah ki yi hak’uri!!ina cikin garin nan da gidan
a amma ace kina hotel dan Allah ki rufa mini asiri,in dan har saboda Khadija ne to a yau za ta fita wallahi.”
Ya fad’i hakan kamar zai yi
kuka
Cikin b’acin rai tace”kar ka soma!!!ba zai you ka koreta saboda ni ba no matter what
sai dan halinta wan
da na so in nuna maka ka runtse
Ido.
Ku zauna abunku kai da ita da surukarka Allah ya kareka daga sharrinsu zan dinga yi maka addu’a Ina daga chan…amma ba zan iya ci gaba da zaman a gidan nan ina tufka Khadija tana warware mini ba kai kuma kana biye mata
!!ba zai yiu ba ba ni da wannan lokacin considering my age
yanzu lokacine da ya kamata ace na duk’ufa ibada da neman gafarar Ubangiji na.”
“Hajiya mama a yau Khadija za ta bar gid…”
Cikin fushi tace”wai
Ya ina magana ba ka ji nane??
Na ce maka ban
yarda ba ko?
Ko shima taurin kai za ka yi mini ka nuna min iyaka ta?
A gaban yaranta za ka koreta saboda ni ko me??
Ka manta yadda muka yi ni da kai a asibiti ka manta abunda nace maka??
B’ata mini ran da ka yi ka k’i
jin maganata shiyasa zan tafi
ka yi komai da kanka ni kam na tsame hannuna!ka bincika komai da kanka ka gyara gidanka ta hanyar da ta dace ba wai ka koreta haka kurum a gaban y’ay’anta saboda ni ba.”
Ya bud’e baki zai yi magana tace”Wallahi zan baka mamaki fa?da musu dakai kakeso
I
n ji ko da b’acin ran da kuka d’ura mini?”
A hankali Abhi ya d’an ruk’o hannusa alamun ya yi shiru dan ya san Hajiya mama yau kam ta riga ta gama kaiwa high!!!!
Daddy yana ji yana gani haka Hajiya Mama ta had’a kayanta tsaf tsaff ita da Junior suka t
afi tsohon gidansa dan tace ko Abhi d’in ma kar ya biyo ta shima takaicinsa take ji idan kuma taga d’aya a cikinsu a inda take kafin ta wuce uk to sai dai ta k’arashe kwanakin ta a hotel har zuwa lokacin da za ta wuce uk.
Da Yamma Yashjub ya turo mata d
a message ta inda yake cewa”Jiya an d’aura masa aure da Kausar ba tare da yardarsaba a jiyan ya saki Kausar to kuma a jiyan Mommy ta zo ta sanyashi ya mayar da ita…yana da babban dalilin da ya sanya ba zai
Iya zama da Kausar ba sannan akwai abubuwa da dam
a a halin yanzu da suke damunsa waenda suka sanya ba zai iya ci gaba da zama a gari d’aya da su Mommy ba dan haka yana da buk’atar space da time dan Allah kar su nemeshi yanada buk’atar break daga fitinar family d’insa.”
Sai da Hajiya mama ta yi kuka da
ta karanta message d’in Yashjub sosai ya tab’a mata zuciya,ace mutum shi da k’asar sa shi da gidan Ubansa amma fargaba da fitintinu sun hanasa ya sake ya rayu a wajen!!wannan wanne irin abu ne haka!!
Allah ya Isa tsakaninta da Mommy wallahi!…
Junior ta
kira tace”ya je gidan ya duba mata idan sun riga sun tafi ko driver ne ya tambaya watak’il su gano inda suka nufa,ba wai binsa ko fad’an inda yake za ta yi ba kawai dai taana so ta san inda yake for her peace of mind..saboda itama ta goyi bayan tafiyar da
zaiyi d’in d’ari bisa d’ari.
Har daren ranar Hajiya
Mama a fusace take ta k’i
ta kula kowa ta k’i ta saurari kowa kuma tace in banda Junior ba ta so ta ga kowa a inda take,hatta Yahanasu da ta je ba ta samu ganinta ba dan ta rufe d’akin ma da take cik
i abubuwa da tunani sun yi mata yawa.
…….Tun ranar da su Mommy suka haifi Yashjub da Yahanasu ta kasa gane abu guda d’aya game da Mommy;kwata kwata ba ta d’aukarsa ya dad’e a hannunta kullum tana mak’ale da Yahanasu,a tunaninta kunyar Haihuwar fari ce tak
eyi amma sai ta lura kamar ma haushin Yaron take ji tun ba ma da ta ce a bashi madara ba wai ruwan nononta bai zo ba amma Likita yana zuwa da aka tilastata aka matso sai ga ruwan Nono fall yana zubowa…
Tun daga wannan lokacin ta saka mata ido dan tashi d’
aya kwakwalwarta ta bata ko dai saboda maganar dukiya da Imam ya yi ne ya sanya Khadija ta musanya y’arta da d’an kishiyarta!!saboda a lokacin Yahanasu da take jaririya kamanninta sun yi shige da na Baba Larai da ta fara girma ne dai ta koma kamannin Daddy
.
Shi kuma Yashjub da Daddy yake kama da yana jariri amma yana fara yin wayo har kawo yanzu da Khadija amaryar Daddy yake kama,sam ba ya kama da Mommy.
Har kusan shekara d’aya zuwa biyu Hajiya mama ba ta gano wata hujja da zai sanya ta ce Yashjub ba d’
an Mommy bane saboda yanzun kuma yadda Mommyn take yi masa babu wanda ya Isa yace ba ita ta haife sa ba,kuma a wannan lokacin ba ta san Mommy da mugayen halaye ba,shiyasa kawai ta kawar da komai ta cire shakku ta cigaba da addu’a ta mik’awa Ubangiji lamura
nta ta barshi ya yi ikonsa dan har yanzu zuciyarta ba ta daina yi mata wasi wasin ‘anya Yashjub dan Mommy ne kuwa!!?’Gashi ita Babba ce ba zai yiu ta tada husuma akan wannan gagarumin al’amari haka ba azo a yi bincike aga ba haka bane gashi Ubangiji da kan
sa yace “kar ka tsananta bincike”
Dan haka ta ja bakinta ta yi shiru ta ci gaba da addu’a,A lokacin ne kuma Mai gidanta ya rasu mahaifin su Daddy dan haka zaman ta ya dawo Gidan Daddy tunda shine Babba.
Sai dai ko sati ba ta iya yi a gidan ba ta ji komai
ya fita a kanta ta tsani gidan ta tsani jama’ar gidan hakan ya sanya ta koma Uk da zama.Dukda tana so ta d’an saka ido akan zaman Daddy da amaryarsa saboda a lokacin dukda Daddyn ba ya yiwa Amaryarsa abubuwa a gabanta amma ta fahimci akwai matsala sai dai
kuma ba zata iya zama a gidan ba dan haka ta hak’ura ta tafi bayan ta had’a su su biyu Daddyn da Amaryartasa ta tambayesu Daddy yace mata babu komai ba fad’a suke yi ba.
Itama amaryar haka.
Bayan shekara biyu ta zo hutu,a wannan lokacin ne ta ci karo
da layu da abubuwa a d’akin Mommy k’asan gadonta lokacin Yashjub yana wasa ya tura Abun wasan nasa a k’asan gadon ya isheta sai da ta zo ta duba ta d’auko masa dan su Khadijan duk basa nan sun fita barka…
Hankalinta ba k’aramin tashi ya yi ba saboda har d
a tsaka mai rai a cikin kwalba da abubuwa na tsafi kala kala ta gani a k’asan gadon Yarinyar da kusan rainon ta ma ita ta yi.
A lokacin Mahaifiyar Mommy itama ta rasu,kasancewar Hajiya Mama babbar k’awa ga mahaifiyar Mommy kafin rasuwar ta ya sanya ta ga
ba laifi bane ba idan ta kirata ta zaunar ta yi mata magana ta kub’utar da ita daga kan Hanyar b’ata da halakar da ta d’auka wanda ba ya b’ullewa.
Dan haka suna dawowa ta nemi ganinta, sai da suka keb’e iyaka su biyu kawai tukunna tace mata“ta ga abubuwa
n da ta ajjiye a d’akin ta a k’asan gado”….nasiha sosai Hajiya mama ta yi mata tace “ ta rik’e Allah da addu’a shi zai sa Imam ya so ta ba wai tsafi ba,a duk lokacin da ka yiwa mutum tsafi ya so ka to fa idan abun ya karye tsanar da zai yi maka sai ta fi t
a farko….”
Kan Mommy a k’asa lokaci da Hajiya mama take yi mata nasihar kuma daga ‘to’ sai ‘inshaaAllah’ kawai take ta cewa amma tana ji Daddy ya shigo tashi d’aya kawai sai ta fashe da kuka kuma ya yi tambayr duniyar nan ta k’i magana,ita kanta Hajiya
mama kasa magana ta yi tsabar shock. Sai daga baya tukunna da kyar ta bud’e baki ta gayawa Imam d’in cewa “nasiha take yi mata akan biye biyen malamai”ita ba ma tace masa ta ga abu a k’asan gadon Mommyn ba!,
Ita Mommyn ce da kanta tace”ai Hajiya maman ta
ce ta ga kaza ta ga kaza a k’asan gadon ta waye waye…”
Har da abunda Hajiya Mama bata ce mata ta gani ba duk sai da ta lissafo kaff abubuwan da suke a k’asan gadon nata
Tana magana tana kuka! kukan da duk wanda ya gani sai ya tausaya mata.
A take Hajiy
a mama ta ga alamun b’acin rai a fuskar Imam amma dai bai ce komai ba ya yi shiru,ganin Yarinya tana shirin shiga tsakaninta da d’anta ne yasa tace “to a je a duba”
A take with full confidence Mommy ma tace “ta yarda a je a duba”
Tun daga nan jikin Hajiy
a mama ya yi sanyi dan sai a lokacin ta tuna ba ta gyara katifar sosai ba dan ba zata iya ba ta yi nauyi,maybe Mommy ta gani sun gane an duba wajen watak’il sun kwashe….ai kuwa hakan ne dan ana zuwa in banda k’ura da akwatuna babu abunda aka gani a k’asan
gadon Mommy.
Daddy bai ce mata komai ba,sai bayan kwana hud’u Allah kad’ai ya san mai da mai Mommy ta yi masa ta kuma fad’a masa tsabar an shanyesa hakanan ya zo yana ce mata wai”akwai wani Likita da zasu je ta gani idan mutum yana hallucination shi ake
gani a kaff garin he’s the best”
a lokacin kacha kacha ta yi amsa ta koresa amma tundaga ranar daga ta ga k’adangare a d’akinta sai ta ga maciji kuma idan ta je ta tattaro mutane aka zo aka duba ba’a ganin komai! Hakanan za ayi ta kallonta ana mata kallo
n tab’abb’iya.
Ganin Mommy tana shirin haukatata ne ya sanya ta tattara kayanta ta d’auki Yashjub tace zai je ya yi musu hutu ta tafi da shi,dan abunda Mommy ta yi mata ya sanya ta fahimci tabbas za ta iya aikata fiye da chanjin Yaro ma.Tun da ga lokacin
ta san yadda ta yi ta d’auke Yashjub gaba d’aya daga gabanta dan indai harshashenta daidai ne to kuwa ta san tsaff Mommy zata iya cutar da shi ko ma ta kashe sa,tunda indai saboda dukiya ne ta musanya Yaran to kuwa bata ga reason d’inta da zai sa ta barshi
a raye ba yanzu dan yanzu kam dukiya ta dawo hannunta,ita da su Yassir………
Yanzu kuma da Mommy ta tura su Yasira suka zubar wa da Manubiya ciki hakan ya sake assasa zarginta ta fahimci komai,shiysa ta cewa Daddy ya barta a gidan su yi bincike a kanta so
sai saboda tana so ta gano