Showing 30001 words to 33000 words out of 259716 words

Chapter 11 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

86

ya dace,na yi magana da friend d’ina already, za a yi

maka booking appointment so y

a kamata ku tafi soon a je a dubaka da wuri,ko?’’

Da kyar Yash ya d’ago rinannun idanunsa da kyar muryarsa har wani karkarwa take yace”…….”MANNUBIYA

(Book 2)

Page 1 1

Na

Humayrah Bulama

Mikiya Writers Associatio

n.

Da kyar Yash ya d’ago rinannun idanunsa da kyar muryarsa har wani karkarwa take yace”duk yadda kuka ce Abhi Allah ya sa hakanne ya fi alkhairi.”

Ba k’aramin dad’i suka ji ba kuwa dan haka suka shiga saka masa albarka tare da fatan alkhairi.

Ganin

yana shirin fashewa da kuka a gabansu ne yasanya ya mik’e har wani jiri jiri yake ji yace musu”sai da safe”daga haka ya sa kai ya fice yana mai ji kamar ya kurma uban ihu,so yake ma ya yi kuka amma sam ya kasa,shiyasa ya nufi side d’insa ya na zuwa ya shi

ge d’aki ko bi ta kan Junior bai yi ba ya shiga ya rufe kanshi ya kashe wayoyinsa…….

Sai washegari da safe tukunna Manubiya ta ji labari,duk yadda take ta cewa itadai 2weeks ya yi kad’an a d’aga amman sai ta ji ba dad’i musamman ma da Yash ya kira ta ta

ji kamar kuka ma yake shirin yi mata…gaba d’aya sai ta sake gigicewa.

Suna kashe wayar itama ta nemi fashewa da kuka sai da Jidda ta d’an kwantar mata da hankali ta had’a da tsokanarta tana cewa”au dan an d’aga aurenta shine za ta yi kuka?”

Tukunna ta

wayance ta fake da borin kunya.

Dukda su Mommy sun ji kuma sun san d’agawa kawai aka yi ba wai fasawa gaba d’aya ba amman hakan bai hanasu shiga cikin tsananin farin ciki ba ji suke yi kamar su zuba ruwa a k’asa su sha dan Baba Larai tace’’d’agawan da a

ka yi hakan ma nasara ne,kuma za su samu enough time d’in da za su tarwatsa maganar inshaaAllah,dan wata uku is more than enough for them su yi abunda ya dace,”Shiyasa murna a wajen su har kasa b’oyuwa ta yi tun daga kan Baba Larai har izuwa kan Yadira ko

wannen su in ka kalla tashi d’aya za ka san yana cikin tsananin farin ciki wanda hakan ba k’aramin sake ingiza Hajiya mama ya yi ba dan tabbas ta sake tabbatar da cewa ‘dukkansu ba son auren suke yi ba.’

A b’angaren su Manubiya kuma kaka mallan ne yaket

a b’ab’atun sa shi kad’ai duk inda ya zauna ya tashi sai ya sanar ai an fasa auren Manubiya a cewarsa ‘’babu wani d’agawa da akayi Yaron ne ya fasa saboda ya gama lalubeta dan kusan kullum sai ya zo ya d’auketa sun fita kuma basa dawowa sai dare…tun mutane

n layi basa biyeshi har aka fara k’usk’us dan in ya zauna har rantsuwa yake yi yana cewa”Yaron nan fa ba zai auri Manu ba tunda ta kasa rik’e kanta ta bi kud’i ta bashi abunda dama ya kawo sa wajenta,dan wallahi akwai ranar da a gaban idanunsa suka dawo da

daddare har da Muhsin amman sai aka cewa Muhsin d’in ya fita shi da driver su kuma suka zauna a bayan mota wallahi wallahi sun fi awa uku a cikin motar har motsi yaga motar tanayi,shikam daga k’arshe ma hak’ura ya yi ya shige ciki bai san lokacin da suka

gama ta shigo gida ba.”

Duk wannan gulmace gulmace da gutsiri tsoman da yake yi hakan ba ta ishe sa ba sai da ya sa aka kira masa Ya Musbah takanas yace masa”ai ga irinta nan,ranar a masallaci sune har da yi masa rashin mutunci saboda yaga y’ar uwarsa t

a shiga daula to ga irinta nan ai tun kafin a je koina saboda abunda suka yi masa gashi an fasa auren,waye waye..”

Hakanan dai ya yi ta b’ab’atun sa,uffan!ya Musbah bai ce da shi ba har ya yi ya gama,sai da ya dasa aya tukunna ya mik’e yace”Allah bamu alk

hairi”daga haka ya sa kai ya fice.

Sati d’aya da d’aga bikin Yashjub ya zo yi mata sallama.a cikin sati d’ayan nan zazzab’i sosai yake yi shiyasa ko iya fita ma bayayi balle ya je wajenta sai dai kullum suna waya.

Ko da ya zo a waje ya tsaya ta fito,ta

shi d’aya hankalinta ya yi tsananin tashi dan ba kad’an ba ya rame sosai ashe shiyasa

kullum take jin muryarsa wani iri idan kuma ta tambayesa sai yace mata”ba komai.”

Cikin tsananin mutuwar jiki ta k’arasa ta gaida shi da kyar ya iya amsawa har da d’an

k’ak’alo murmushi duk dan kar ta gane.

Cikin rashin jin dad’i tace”ba ka da lafiya ne?”

Murmushi ya yi kafin ya girgiza mata kai kawai,ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna yace”gobe da asuba za mu tafi,”

Sai

Da ya sake fesar da numfashi tukunna ya gyara tsa

yuwarsa sannan yace”ni kam har ga Allah na fara da na sanin amince musu da na yi,kawai inaga gara a d’aura mu wuce tare,na so in same su da maganar amman sai na ga gara in fara yi miki maganar in ji ta bakinki,but still dan Allah baby kar kice A’a kawai ke

ma ki amince a d’aura a yau dan hakan nake so”

Ya k’arashe maganar kamar mai shirin fashewa da kuka.

Da kyar Manu ta iya danne kukan da ya taho mata ta d’ago idanunta da suka cika taff da kwallah tace”na san ba za ka ji dad’in abinda zan fad’a maka ba

amma hakan shine daidai….ana barin halak ko dan kunya,kai fa da kanka ka ce min kawaici da alkunya ne suka sanya ka amince da buk’atar su,yanzu kuma kawai sai ka zubar ka je ka samesu ka ce ka chanja shawara?

Kuma kowa gani zai yi saboda ka zo ka yi magan

a da ni ne”

Cikin sanyin murya yace”baby gani nake yi kamar idan aka d’aga wani abun zai iya…”

Cikin katsesa tace”duk abunda ka ga ya faru to muk’addari ne daga Ubangiji,wayonmu ko saurin mu bai Isa ya k’ara ko ya rage lokacin da

ubangiji ya riga ya

tsara za’ayi ba….dan Allah inaso kamar yadda ka ji kunyar su ka yi kawaici a farko to yanzun ma ka zauna akan bakarka ka yi musu biyayya baka san dad’in da hakan zai sanya su ji ba, amman yanzu idan ka bijire kowa rashin hak’uri da karar mu zai gani,kuma h

akan ne. Dan haka gara kawai mu yi musu biyayya mu yi hak’uri mu mik’awa ubangiji komai inshaaAllah za mu dace”

Ganin yadda ya yi shiruu ya kasa cewa komai sannan idanunsa suka yi jajir yasanya manubiya ta kawar da kunya direct daga cikin zuciyarta tace

masa”inshaaAllah i’ll forever be yours,no matter what”

Sai da ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya dan ba kad’an ba kalamanta sun yi tasiri a kansa.

Cikin tsareta da lumsassun idanunsa da suka k’ank’ance suka yi

jaa yace”promise??”

Ahankali tace”I promise”

Lumshe idanunsa ya yi wanda hakan ya bawa kwallar da yake ta k’ok’arin rik’ewa damar zubowa, da sauri Manubiya ta kauda kanta ta sunkuyar k’asa dan tashi d’aya itama taji tata kwallar tana shirin zubowa.

Ahankali ya share idanunsa ya d’an ja hanci kafin yace”3 weeks zan yi in dawo na san kuma zan koma follow up kamar sau biyu haka kafin auren namu”

Cikin yin k’asa da murya yace”I’m going to miss you so much,take care of yourself ki dinga rik’e wayarki a

lways pls”

Ahankali ta d’ago ta kallesa tace “inshaaAllah”

Cikin wata kalar kasalalliyar murya ta ji yace”I love you,always and forever”

Ahankali ta sunkuyar da kanta k’asa duk yadda ta so ci gaba da rik’e kwallar kasawa ta yi da n tashi d’aya suk

a zubo mata, gudun kar ya gane yasanya ta sa hannu ta goge a hankali tukunna itama tace”I love you too”

Murmushi ya yi daga haka yace”see you in 3 weeks time”

Ahankali ta d’ago ta ce”bye”

Waving nata ya yi shima yace”bye”

Daganan ta yi sauri ta

juya ta shige cikin gidan dan tabbas Idan ta ci gaba da tsayawa a gabansa tou za ta yi kukan ne mai yawa ba d’an kad’an ba.

Ai kuwa tana shiga ta zauna a d’an dakalin hanyar d’akin su ta saki kukan ta, ta yi k’ok’ari ta kwantar wa da Yash hankali bayan

ta san tabbas ta fisa shiga damuwa dauriya ce kawai take yi…ta jima ta na kuka mara sauti mai cin rai kafin da ga bisani ta goge fuskarta ta tashi ta shige cikin d’akin,a da ba ta ganin nisan watanni dan nan da nan indai aka saka rana sai ta ga lokaci har

ya yi,amman tabbas a yanzu watannin ukunnan da aka k’ara jin su take yi kamar shekaru d’ari uku…..

Bayan wata uku.

Kwanci tashi…..yau gashi har wata ukun da aka k’ara a kan bikin su Manubiya ya cika cif cif….wasu suna cikin tsananin murna wasu kuma

suna bak’in ciki yayinda waensu suka ji kunya….Cikin nasara Yash ya je aka duba masa hannusa aka yi masa duk wasu abun da ya kamata,kafin wata biyu ya ware sosai shiyasa a lokacin Hajiya mama tace ko za’a d’aura kawai amman sai su Daddy suka ce kar ma ta b

ari yaji kawai a jira dan dai wata d’aya da kwana 7 ai kamar yau ne….yadda auren ya sake taho wa su Mommy suka fara d’aga hankalinsu sai da kowa a cikin gidan ya lura,shiyasa Hajiya mama da dage ta tsaya tsayin daka a kan al’amuran gidan dan matar nan da

ta kira ta yi musu feshi kwanakin baya yanzu kusan kullum sai ta zo haka aka dage da addu’o’i a cikin gidan ba kama hannun Yaro. Idan kuwa anayi Baba Larai ji take kamar ta mutu dan har ga Allah ba k’adan ba Hajiya mama take b’ata mata aiki gashi ta kasa

korar ta a gidan.

Kamar yadda Yash ya fad’a sau biyu ya je follow up a UK..a yau ya gama da ganin likita shiyasa suka tarkota har da mom suka nufo Nigeria.

Suna zuwa aka shiga murna da oyoyo Hajiya Mama tana ta tsokanar Yash tana cewa”ba ga shi lokaci

har ya yi ba,amman da har da kwallar sa da aka ce za’a d’aga auren,Itafa gaskiya tana kishin wannan kishiyar tata tun kafin ta zo dan yadda yake wannan rawar k’afar ta san tana zuwa zai manta da ita”

Dariya duk akayi banda Mommy wadda take jin kamar zata

mutu,cikin tafiyar tsofaffi Hajiya Mama ta nufi kitchen..yau dan rigima da kanta ta dafawa Yash jalof d’in taliya dan ta san yanaso ba yadda Ummi ba ta yi da ita akan ta kawo ta yi ba amma tace “ta yanka mata albasa kawai”(shima saboda matsalar idon ta ne

)

daganan ta girka abunta tsaf kuma ya yi dad’i sosai.

Mom da Ummi ne suka bi bayan Hajiya Mama yayinda Daddy da Abhi suka nufi waje dan suna da wajen zuwa,junior kuma ya bi bayan Yadira da ya ga ta nufi garden alamun waya take yi.

Yash yana zaune yana

murmushi ya ji kawai an damk’i hannunsa yana d’agowa suka yi ido biyu da Mommy dan haka ya sauk’e ajiyar zuciya kawai yana kallonta…dan tun d’azu da ya shigo bayan ya je sun gaisa ko ‘ya hanya’ ba ta ce masa ba,kamar ma fushi ta ke yi da zuwan na sa,kuma a

cikin watanni ukun nan ya lura kamar ma gudun sa take yi dan idan ya je k’ofar ta kullum a kulle. Yana cikin wannan tunanin ya ji tace “biyo ni,Inada magana da kai”

Daga haka ta juya ta nufi parlourn bak’i.

Sai da ya fesar da numfashi tukunna ya mik’

e ya bi bayanta,yana wucewa su Yasira da Baaba larai suka yi sama dan kar ma a zo a tambayesu yana ina.

Yash ba k’aramin shock ya shiga ba dan yana shiga parlourn Mommy ta rufesa da fad’a kamar za ta had’iyi harshe abunda ba ta tab’a kwatantawa ba kena

n,babu abunda ya fi b’atawa Yash rai kamar akan abunda take yin fad’an,in da ma wani abunne ya faru recently har ta kai ta ga yin fad’an to da dasauk’i amman fa tana fad’an ne akan wai ‘lokacin da za’a d’aga auren sa ba ‘ayi mata magnar ba ba’a tuntub’eta

ba sai ji ta yi kawai an d’aga.Kuma wai Manubiya ba ta kiranta ta gaida ita amma tana ji suna yawan yin waya da Yahanasu har ma da Ummi…idan so yake ta yafesa a cikin

y’ay’an ta kawai ya fito ya fad’a dan abunda ya ke yi mata ya isheta,in ba rashin sanin c

iwon kai da wulak’anci ba ta ya zai dinga fifita kishiyar ta da y’ar kishiyarta sama da ita a rayuwarsa???….”

Yash ya so ya yi mata bayani ta fahimta sannan ya bata hak’uri amma yadda ta k’i sauraronsa da kuma yadda ya fahimci kamar ma baki take shirin

yi masa ne ya sanya shi kawai ya fice ta k’ofar baya ya bar mata parlourn zuciyarsa tana wani irin tafarfasa.

Sam ya rasa dalilin da ya sanya Mommy take bak’in ciki da farin cikinsa.

Bai nufi side d’insa ba direct mota ya nufa ya shiga ya kunna ya fi

ce daga mansion d’in gaba d’aya,ya nufi gidansu Manubiya.

Ya na yin parking a k’ofar gidan ya ji zuciyarsa tana yin sanyi ahankali ahankali,rabonsa da ita tun last month dan wannan karon da yaje uk ya dad’e sosai shyasa yake ji kamar ya yi shekara uku bai

ganta ba,suna waya da chatting har ma da video call kullum amman yayi mugun mugun missing d’inta……tana zaune suna hira ita da mai gyaran jikin ta da su Siyama a parlourn su Siyama ta ga kiran sa,murmushi ta yi tana wani Irin blushing kafin ta yi picking,a

hankali ta ji yace”surprise!ina waje”

Kad’an ya rage ba ta tsala

Ihun murna ba,da kyar ta iya cewa “ok” tukunna ta katse kiran ta kalli siyama tace”yana waje”ta fad’i hakan fuskarta tana baiyyana tsananin farin cikin da take a ciki.

Dariya Jidda ta yi

kafin tace”Allah adda idan aka zo kaiki kika yi mana kuka kowa ya san kukan murna ne,”

Dariya duk suka saka wanda hakan ya sa Manubiya ta d’an nutsu ta bar zumud’in rufa mayafin da take yi kafin ta kalli Jidda ta galla mata harara tukunna ta kalli mai g

yaran jikin tace”an gama?”

Murmushi matar ta yi kafin ta mik’e ta shiga harhad’a kayayyakin ta tace “ai ko ba’a gama ba jeki kawai”

Dariya sosai suka yi kafin siyama tace”ki shigo da shi nan bari mu tartare”

“To” kawai tace, da ga haka ta sa kai ta fi

ce.

Tunda ta taho ya kafeta da idanu har sai da yasa ta ji kamar ta nutse dan yau kalar kallon nasa na daban ne….a b’angaren Yash kuwa har wani jiri jiri ya fara ji tsab’ar kasalar da ta rufar masa tashi guda,ya san yana son Manubiya so mai tsanani na

tsanakani da Allah amma tunda yake bai tab’a jin kalar sha’awar ta da yake ji a yanzu ba,ya na ji from time to time ba wai ba ya ji ba amman abun na yau ya girmama,dan har wani ciwon ciki ne ya ziyarcesa tashi d’aya,ta yi wani kyau ta yi fresh kamar wata y

’ar baby,har wani murmurewa ya ga ta sake yi gwanin ban sha’awa.

Cikin d’an turo baki tace”ni dai ka daina kallona”

Murmushi ya yi ya bi bakin da ake turo masa da kallo wanda yakenan kamar na y’ar jinjira ma’abociyar tsotso kafin da kyar ya d’an k’ura

wa fuskarta ido tukunna yace”gani na yi kin sake zama baby,y’ar babyn Yashjub”

A hankali ta sunkuyar da kanta tana murmushi k’asa k’asa kafin tace” kaima ka k’ara kyau sosai”dan Itanma tunda ta fito ta lura da haske da kyan da ya k’ara….wani irin blushing

Yash ya shiga zubawa kamar mai

tallar makilin kafin dakyar ya samu ya tsayar da murmushin tukunna ya amsa gaisuwa da ya hanyar da take yi masa.

Daga nan ta yi masa iso zuwa parlourn su Siyama wanda har sun gyara tsaf sun kunnu turaren wuta…..Tabbas Yash

da Manu sun yi missing juna dan sai da suka kashe sama da awa uku ba tare da sun ma sani ba,dukda kuwa Yash dauriya ce kawai yake yi dan yau kam shi kanshi mamakin kansa yake yi saboda bai tab’a jin desire irin wannan ba ga kuma ciwon ciki amman kuma ba ya

so ya tafi so yake kawai ya yi ta kallonta…da kyar dai yana jin kamar kar ya tafi ya yi mata sallama dan Najeeb yana chan yana ta jiransa. Har mota ta raka sa yana ta zuzuta yadda ta yi kyau dan ba kad’an ba ta tafi da imaninsa…..itan ma santin kyan da ya

k’ara take ta yi a cikin zuciyarta,a haka suka rabu kowa yana muradin d’an uwansa.

Bai yi tunanin za su yi dare shi da Najeeb ba dan har sha biyu na dare ba su samu sun kammala abubuwan da suka tisa a gaba ba,

Sai da yaje mota domin d’aukar wasu abubu

wa tukunna ya ga wayarsa tana haske dan haka ya yi saurin d’auka ya k’ara a kunnensa

Yana d’agawa ya ji muryar Daddy yace”come home yanzu,Hajiya mama tana nemanka ta d’agawa kowa hankali”

“Okay tam”

Kawai yace daganan Daddy ya katse kiran sai a sann

an Yash d’in ya lura da uban jerin misscalls d’in da aka jera masa,ajiyar wayar ya yi ya je ya cewa Najeeb zai tafi sukayi sallama tukunna ya nufi gida.

Yana zuwa

bai tsaya ma yin tunani ba gudun kar ya ji ba zai iya shiga ba dan har ga Allah ba ya so

n

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login