Showing 9001 words to 12000 words out of 259716 words
mik’e tsaye ta d’an matsa inda yake kafin tace’’menene,me ya faru?hannun dai?’’
Ta jero masa t
ambayoyin a gigice saboda yadda ta ga
yana yi kmr irin azabar nan yake sha.
Kamar zai yi kuka yace’’zafi sosai har cikin zuciyata’’.
LlAi kuwa babu shiri ta yunk’ura tace’’ Bara in kira Doctor’’da fad’i hakan tana shirin juyawa.
Da sauri ya mik’e
ya tare ta ta hanyar tsayawa a gabanta tukunna yace’’in kikayi murmushi ma kad’ai ya wadatar zai daina,dama kyaliyar da kika yi min ne yasanya ya fara wani irin azababben zugi’’
Shiruu ta yi da farko sai kuma ta d’ago ta kalleshi,murmushi ta ga yana yi
mata suna had’a ido ya d’aga mata gira d’aya,
b’ata rai ta yi sai kuma ta
maida kanta kasa a ranta tace
‘’lalle wannan mutumin da alama garau yake kawai tab’ara ce yake ji da ita’’.
Murmushi yayi kafin yad’an matso kusa da ita ahankali ya d’an lek
’a fuskarta ya langab’ar da kai kafin yace’’ kuma wai a haka ank’i ace mun ana sona’’
Ji ta yi kamar ta nitse cikin k’asa dan haka ta juya da sauri ta bashi baya tana jin yadda yanayin bugun zuciyarta ya sauya lokaci guda.
A hankali ya d’an sake t
aku d’aya izuwa gareta ya tsaya a daidai bayanta yace’’Manu plsss,jan ajin nan ya fara cutar da ni,ki fad’a min wani abun mai dad’i mana ko so kike inyi miki kuka tukunna???’’
Shiru tayi kawai ta kasa cewa komai dan zuwa yanzu bugun da k’irjinta yake
yi ba na wasa bane ba ma ta jin kalmar ‘A’
za ta iya fitowa daga gareta.
Jin da ya yi ta yi shiru yasa yadan sake matsawa kad’an ahankali daidai saitin kunnenta yace ‘’dan Allah ki ce kina so na…plss Baby!….’’
Inaa….she can’t take this anymore s
hiyasa da sauri ta d’an yi gaba kad’an kafin ta juyo da niyyar fita ta yi hakan ne gudun karma ta juyo tashi d’aya taje ta fad’a jikinsa,amman ta na juyowa sai ta ga ba hanya dan gefenta fridge ne d’ayan gefen gado bayanta kujera gabanta kuma shi…
Da saur
i ta sunkuyar da kanta dan wani irin kallo ta ga yana yi mata,ba ta gama dawowa daidai ba ta ga kamar ma tunkarota yakeyi dan haka ta yi sauri ta d’ago tace’’Allah ya k’ara sauk’i,Allah ya ji k’an driver d’in ka ya sa ya huta,z z an wuce ggi d a….’’ta fad’
i hakan cikin in inaa
Tsayawa yayi chak kafin yace’’Saboda na ce kice kina sona shine za ki gudu??haba mana Baby aure fa za mu yi amman har yanzu ban san matsayin na ba kuma daga na yi magana sai a fara gudu na…’’
Juyar da kanta tayi gefe
tukunna
ta girgiza masa kai alamun ‘’A’a’’ kawai.
‘’Good!saboda gaskiya yau ba za ki fita daga d’akin nan ba
sai na san matsayina a cikin zuciyarki.Inaso mu wuce
wannan stage d’in na kauda kai!kasa kallona!jin kunyata da kike yi mu shiga next stage
saboda
in samu in dinga expressing miki how much I feel dan sun cikamin zuciya da gangar jiki dayawa.So I’m all ears.’’
Shiruu ta yi shima haka
duk suna anan tsaye ba wanda ya sake cewa komai
Manubiya ji ta yi inama ba ta zo ba,gashi kwata kwata ya k’i ya d
aina kallonta dede da second d’aya,gashi ya titsiyeta,shiyasa ta ji kamar ta fashe masa da kuka…….
Sun fi minti goma a haka
sam tama k’i ta yarda ta kalli direction d’in shi balle ta fad’i abunda yake son ji d’in.
Ahankali ta ji ya sauk’e ajiyar zu
ciya kawai sai kuma ya koma ya nemi waje ya zauna akan gadon jinyar nasa.’’Na gode ki gaida su Inna
InshaaAllah zan zo in gaida ita da zarar na fita a nan.’’ Ya fad’i hakan cikin kumbura fuska.
Duk kuma sai ta ji ba dad’i,har za ta wuce ta fita sai
kuma ta tsaya kamar wadda ba ta son yin magana tace’’Tun d’azu nake ta tambayar ka ya jiki baka ce komai ba,ya aka yi
hakan ta faru? Ya kuma hak’urin driver d’in ka’’
Numfashi ya fesar kafin yace’’Jikina Alhamdulillah dasauk’i kafin ki zo
amman ya
nzu kam na san in kika tafi kika barni a haka
akwai matsala.Hak’uri da godiya sannan tsautsayi da k’addara ne ya janyo hakan
sai mu yi adduar Allah ya kare gaba’’ya k’arashe maganar tasa yana mai zaro wayarshi daga aljihu ya fara daddanawa
shi ala do
le yayi fushi da ita
watakil in ta ga hakan ya san za ta yi masa yadda yake so.
Yana addua Allah yasa maganarta ta zama positive dukda bashi da tantama akan itama tana sonshi.
‘’Allah ya ji k’an musulmi,Allah ya baka lafiya,Allah ya kare gaba’’ tace
da shi kamar yadda shima ya jero mata kafin ahankali ta fara tafiya towards k’ofar zata fita.
D’an d’agowa yakeyi yana satar kallonta yana kallon wayar tashi ganin tana shirin fice wa ne yasa yayi sauri ya mik’e yace’’au ba za ki tambayeni
me zai dawo m
in da ciwon nawa bayan kin tafi ba ko??’
Duk yadda ta so daurewa sai da murmushi mai had’e da y’ar siririyar dariya ya sub’uce mata a ranta tace’’Mutumin da ya had’e rai shi ala dole yayi fushi yayi zuciya
amma kalli shine ya mik’e yanzu yake wannan b
atu.’’
Sarai ya ji sautin murmushin nata dan haka ya k’araso ya tsaya a gabanta yace ‘’Dariya ma kike yi min ko??’’
Ya fad’i hakan cikin b’ata fuska
kamar wani k’aramin Yaro.
Wani d’an siririn murmushi
wanda ya sanya Yash ya ji kamar zai suma
ta saki kafin a hankali tace’’na san mecece amsar da za ka ba ni shiyasa ban tambaya ba’’
Cikin tarar numfashin ta yace
‘’Mecece amsar??’’
Sai da ta d’an kalleshi kad’an tukunna ta sunkuyar da kanta tace ‘’Cewa za ka yi saboda ban fad’i abunda kake
son jiba,kuma ai na ga ma fushi ka yi da ni yanzun.’’
A hankali cikin yin k’asa da murya yace ‘’ni na yi fushi dake??’’ bai jira jin amsartaba yace ‘’Never’’
kafin ya d’aura da cewa’’Kin san rashin amsar taki ce za ta k’aramin rashin lafiya amma shin
e kika zab’i ki tafi ki barni a haka??saboda kin tsane ni,ko?.Wannan sarkin nacin.’’
Yayi maganar yana nuna kanshi
Dasauri ta d’ago ta kalle sa tashi d’aya tace ‘’A’a’’
Dukda yadda ya ji sanyi a ranshi amma sai ya dake ya sake had’e fuska yace’’t
o yaya ne?’’
‘’Ba sai na fad’a ba na san ka sani’’
Ta bashi amsar tana mamakin yadda sam ba ya gajiya da kallonta tun da ta shigo d’akin
ba ta jin ya d’auke idonshi a kanta in ba lokacin da ya yi fushi ya d’auko waya ba,ita
har tsarguwa da wannan
kallon nashi takeyi….kullum in suka had’u kmr ranar ya fara ganinta…
Muryarshi ce ta katseta jin yana cewa ‘’i’ll love to hear it
ba ki san taimakon da za ki yi min ba in kika fad’a Manu’’
Kamar zai yi kuka yace’’so plssssss’’ ya ja plss d’in sosai
har cikin ranta sai da taji
‘’If your answer is yes just say it yanzu I just need to hear it na garu dayawa a tausaya min
haka mana…….’’
A hankali cikin tarar numfashinsa ya ji tace’’Yes!’’
‘’Yes What?’’
Yayi mata tambayar yana kallont
a yana murmushi
sosai
Turo baki tayi ta saka tafukan hannayenta ta rufe fuskarta da su dan kunya take ji sosai sanann ta yi tunanin da ta ba sa amsar zai kyaleta ne amma ta ga alama wannan so yake su kai dare anan ana abu d’aya
Yashjub kuwa tsab
ar murna ji
yake kamar ya zare hannun ya janyota jikinta ya yi hugging d’inta…..ahankali yace’’ pls mana,kin ce min yess kawai kin barni,elaborate mana,sannan na ce fa bana son wannan sunkuyar da kan a d’an rage wannan kunyar tayi yawa fa…’’
Knockin
g ya ji an d’an yi dan haka da sauri ya juya ya saka key sannan ya juyo gareta yace’’um’’alamun ita yake sauraro.
Zaro ido tayi kafin a rikice tace
‘’Dan Allah ka bud’e maybe su
Jidda ne suka dawo harda Ya Musbah muke tafe dan Allah ka bud’e kar s
u yi tunanin wani abun’’ ta fad’i hakan ahankali k’asa k’asa kmr wani zai jiyo ta sanann duk a rikice.
Ba k’aramin dariya ta ba sa ba ganin yadda ta tsure tashi d’aya a ransa yace ‘’perfect’’
amman ya dake ya mak’e kafad’a yace’’um um,ni kam ba zan b
ud’e ba’’
sai kuma ya d’an sake matsawa kusa da ita kafin ya ci gaba da cewa’’har sai kin fad’a min komai yau
tukunna babu ruwana ko waye ya zo to ya jira Queen ce take zuba mulki da jan aji dan haka shima ta shafe sa.’’
Dai dai nan aka sake yin wa
ni knocking d’in,sai da ta d’an zabura kafin ta kalli k’ofar sannan ta kalleshi a gigice tace ‘’to me kake so ince??
ko waye fa a bakin k’ofar nan na san ya ji lokacin da ka saka key kuma kana bud’ewa sai a ganmu tsulum mu biyu kawai kaga ai hakan babu
dad’i,na riga na ce maka yes ai dan Allah ka bud’e k’ofar nan’’
Cikin tarar numfashi ta yace ‘’waye zai bud’e k’ofar??ai in gaya miki muna nan ni da ke har abada muddin ba ki bani amsata ba,bari ma kiga in zare key d’in in cilla ta window’’
Ya fad’i h
akan yana mai juyawa
Da sauri tace ‘’wait!’’
Sai da ya d’an yi y’ar guntuwar dariya tukunna ya juyo.
Kamar za ta fashe da kuka tace ‘’to me zan ce?’’
‘’Abinda yake a cikin zuciyar ki game da ni’’ya ba ta amsar kanshi tsaye.
Kallon shi ta yi aha
nkali ta d’aga kai tace’’Yes….’’
sai kuma ta yi saurin sunkuyar da kanta tace’’na ce maka yes tun d’azu…’’ta fad’i hakan kamar za ta fashe da kuka dan ita har ga Allah wallahi kunyar gaya masa complete kuma direct take ji.
Juyawa kawai ta ga yayi ya za
re key d’in.
Still kuma har yanzu anata faman knocking k’ofar
Da sauri tace’’me kuma na sake yi?’’
Kallo ta yayi kafin yace’’Yess’’
Da d’an mamaki tace’’yes kuma?me kenan?’’
‘’Yauwa exactly my point,kin ga kema ai ba ki gane ba ko?dan haka
ya kamata ki fahimci nima ban gane me yes d’in ki take nufi ba,if you want to express yourself all you have to say is ‘i love you Yashjub’ ni har ga Allah banga abun wahala a y’an waennan kalmomin ba…’’
Knocking aka yi da k’arfi sosai this time around,
Manubiya ba ta san lokacin da ta fara bubbuga k’afafunta ba kamar wata y’ar yarinya tana cewa ‘’ni kam Allah A’a dan Allah kawai ka bud’e’’.
Shagala yayi kawai yana kallonta,sai da suka suka had’a ido sai kuma ta tsaya chak! tsabar kunya kasa ma cigaba
da fuskantar sa ta yi dan haka sai ta yi saurin juyawa.
Murmushi yayi da sauri yace ‘’a’a pls don’t stop you look cute’’
Bugun da akayi da mugun k’arfi wannan karon ne yasa ta juyo tace’’dan Allah’’
Ta fad’i hakan hawaye suna s
taruwa a kyawawan
idanunta wanda suka sanya idanun suka fara kyalli
wanda hakan ya sake d’imauta Yash
Ahankali yace’’Manu!
ba zan tab’a bud’e k’ofar nan ba idan har ba ki gayamin abunda nakeson ji ba,in ma bakya sona ne to ki fad’a min
Ni a ganina ke kika bari har
aketa bugun nan,and just so you should know in har Doctor ne yake knocking d’innan to mutane zai je ya tattaro a b’alle k’ofar tunda patient ne a ciki
In su ka ji shiru yayi yawa za su yi tunanin ko wani abun ne ya sameni gashi jiya na sanya sun zare cct
v d’in d’akin nan,kinga ana zuwa ba ma mutum d’aya ba mutum dayawa ne za su ganmu tsulum kuma Allah kad’ai yasan tunanin da kwakwalwar kowa za ta basa.
Dan haka it’s up to you ki yanke decision da wuri tun kafin a zo
a b’alla k’ofar nan saboda one thin
g is for sure ‘ni dai ba zan tab’a bud’ewa ba yau har sai na ji ishashshiya kuma gamsashshiyar kalma daga gareki’.’’
Ya k’arashe maganar yana murmushi k’asa k’asa yana kallonta
Dole ta ajjiye kunya a gefe
tun kafin ya janyo mata magana a cikin asib
iti
A hankali ta runtse idanunta da k’arfi tukunna tace’’i love you’’
Ahankali Yash wanda tashi d’aya kasala ta rufar masa ya d’an matsa kusa da ita kad’an
ahankali kamar wanda baya so kowa ya ji yace’’how much’’
Direct daga zuciyar ta tace’’so
very much’’
Wata nanauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace’’za mu yi auren mu soon ko?’’
Jinjina kai ta yi still idonta
a runtse tace ’’inshaaAllah’’
‘’Ki haifamin ya’ya masu kama dake?’’
ahankali tace’’inshaaAllah’’
Wani bugun aka sake
yi
wanda ya sanya Manubiya ta bud’e ido ta kalli k’ofar da sauri,tabbas yau kam ta san babu yadda za’ayi ta iya had’a ido da Yashjub dan haka ta sunkuyar da kanta k’asa tukunna tace’’plss ka bud’e dan Allah’’
Lumshe idanunsa yayi ya bud’e yana mai
ji kamar ya fita wajen ya je ya shak’e koma wanene a bakin k’ofar da yake musu wannan uban knocking haka
me shegen naci…tashi d’aya ya ji ya tsani knocking zai rubuta a diary d’in shi shikam ‘ya tsani knocking ,forever!!’
This is the best moment of his l
ife he needs to be all alone with her
sannan ya samu yayi expressing kansa more and deep amman kawai an kama an zo an dame su gashi ba ya so ya karya alk’awarin da yayi mata ta hanyar k’in bud’e k’ofar.
Da k’arfi aka sake yi dan haka Manu ta sake cewa
‘’dan Allah’’
A hankali ya juya ya zura makullin ya murd’a ya bud’e k’ofar yanajin kmr yana bud’ewa kawai ya fellawa wanda yake knocking d’in mari…………..MANNUBIYA
(Book 2)
Page 05
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writ
ers Association.
Yana bud’ewa suka yi ido biyu da Yasmeen ahankali ya lumshe idanunsa ya bud’e kafin yace’’i wasn’t expecting you!’’
babu Mommy da Daddy a wajen ballantana ta yi rashin kunya shiyasa ta yi shiruu ta d’an sunkuyar da kanta k’asa,kafin
ta d’an d’ago ta kallesa tukunna tace’’Yau ne ranar da na ke shigowa aiki nan asibitin,shine na ce bari in lek’o in duba ka’’
‘’Nagode’’
kawai yace da ita daga haka ya fara k’ok’arin maida k’ofar.
Manubiya tana jin muryar Yasmeen zuciyarta ta fara
wani irin tuk’uk’i….yanayin conversation d’in su ba kad’an ba ya d’aure mata kai gashi ta ji yarinyar sai wani kashe murya takeyi tana wani lallab’asa……
Da sauri Yasmeen ta sa hannu
ta d’an tare k’ofar kafin tace
‘’Those are for you’’
Ta fad’i ha
kan tana mai nuna masa allurar hannun ta.
This time around b’ata rai Yashjub ya yi cikin d’an
fushi yace ‘’i’m fine,na warke. And if necessary
go get the doctor’’
A ranshi yace ‘’lalle ma yaran nan rainin hankalin nasu ya yi yawa,su gama basa rain
i da attitude a gaban mutane shine yanzu dan ta maida shi d’an cikin ta za ta zo kuma ko bada hak’urin rashin kunyar da ta yi masa bata ma da shirin yi.Kamar ma bata yi komai bama’’
Ta ji zafi sosai amman sai ta
dake ta d’an yi murmushi
kafin a h
ankali tace’’nima ai Doctor ce,kuma shi ya shiga surgery,just let me in i…..’’
Cikin fushi sosai yace
‘’Ke!ina miki wasa??’’
Bai jira jin amsar ta ba yace ‘’b’ace min a gani,kafin in karya ki a wajen nan’’.
Dai dai nan Jidda da Siyama suka k’ara
so wajen dan ba su
samu lemo da ayaban a kusa ba shine Ya Musbah ya karb’a suka tafi nema shi da Muhsin bayan ya balbalesu a titi kamar zai rufesu da duka.
Ahankali Yasmeen ta d’an sunkuyar da kanta ta fara k’ok’arin maida kwallar takaicin da take
shirin yin nasarar zubo mata.
Sai da Jidda ta d’an rissinar da kanta
tukunna ta ce’’Ya Yash,Ina wuni’’
Haka ma Siyama
Jinjina kai ya yi kafin a hankali yace ‘’Alhamdulillah’’
Daganan ya juya ya shige bayan ya bar musu k’ofar a bud’e.
Kamar ba
za su kula Yasmeen ba sai kuma jidda tace mata
‘’Sannu Ina wuni’’tunda koda dai ace likitarsa ce(dan sun ganta sanye da lap coat)
but tare suka gansu suna magana.
Dakyar ta iya d’agowa ta kallesu….kyawawan mata ajin farko masu ji da asalin kyau da k
’uruciya gashi sai wani kalar k’amshi sukeyi su duka biyun
sai dai tashi d’aya yanayin kayan jikin su zai sanya ka fahimci suna cikin yanayi na rayuwa,sanye suke da dogayen rigunan Abaya bak’ak’e amma
tsabar yadda kayan sukaji ruwa har bak’in ya d’an f
ara komawa kamar kalar dark ash
sannan rabin stones d’in jiki duk sun goge,tashi d’aya ta ji gabanta ya yanke ya fad’i,kallon
da taga suma sunayi mata ne
yasanya kawai dakyar tace’’fine’’a cikin zuciyar ta tana tunanin’’to wacece budurwar Yash d’in a
cikinsu’’
Sai da suka tura k’ofar suka
shige tukunna ta samu damar yin ido biyu da Manubiya
wadda itanma Allah Allah dama takeyi a d’an bud’a k’ofar ta samu ta ga wacece take magana da