Showing 225001 words to 228000 words out of 259716 words

Chapter 76 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

16

gama shirye shiryen tafiya….sai bayan sati biyu tukunna suka isa Copenhagen Denmark suka yi settling

Cikin rarrashin da tsoron shiga Hakki ta shiga k’ok’

arin fahimtar da shi cewa “ko ba komai fa Kausar matarsace!!”

Har ga Allah sai da ya yi mata bayanin da shi kansa sai a cikin jirgi da kwakwalwarsa ta d’an huta tukunna ya tuna sannan itama ta tuna tabbas fa da gaske babu aure tsakanin Kausar da Yashjub

saboda ba a d’aura aure da ciki!!

A ranar tsakanin Manubiya da Yashjub ba za a ce ga wanda ya fi wani murna ba……daga nan suka kawar da duk wani b’acin rai suka shiga shimfid’a rayuwarsu mai dad’i a Copenhagen dan basu ga ranar dawowaba….

Mommy kuwa

zuwa yanzu ta san me za ta yi game da auren Kausar da Yashjub…………MANNUBIYA

(Book 2)

Page 41

Na

Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

A b’angaren Mommy kuwa zuwa yanzu ta san me za ta yi game da auren Kaus

ar da Yashjub.

Ta riga ta san zuwa yanzu Yashjub ya san babu aure a tsakaninsa da Kausar..kuma ita kanta zuwa yanzu ta san ba ta da lokacin da zata ce sai sun cire Manubiya tukunna za su kashe Yashjub! shiyasa kawai ta ma hak’ura da sake k’ulla auren Yash

da Kausar d’in a karo na biyu.

Ta dai ji Daddy yana cewa Ummi”Kausar d’in tana a matsayin matar Yash a idanun duniya har zuwa lokacin da za ta haihu.Gudun b’acin suna.”

So ita kuma kafin nan da zuwa lokacin da Kausar d’in zata haihu inshaaAllah barinta

zai cika kud’irinta zai cika kuala ta san barin Kausar d’in ma da aka yi a mazaunin matar Yash d’in Allah sai nuna hanyar da za su yi taking advantage d’in hakan inshaaAllah..

Kawai ita yanzu wuyarta ta san inda Baba Larai take,she really needs her yanzu

kam saboda ta riga ta gama tsarawa akan duk bala’i wuyarta Yashjub da Manubiya su sako k’afa a cikin k’asar Nigeria wallahi sai ta ga bayan su!!

Dole a yita ta k’are abun ya yi yawa kuma anzo gab’ar da dole ta yi musu hakan cikin gaggawa idan ba haka ba k

uwa to tana cikin masifa!!!!

Zuwa yanzu idanunta sun rufe..as far as she knows Ita da Yassir suna cikin gadon Yashjub dan haka ba sai ta wani jira sun yi abunda suka yi an mallaka masa dukiya ba,iyaka kason da za su samu ma idan an raba gado ya isa!

Daga

nan su kuma su Daddy da Ummi da su Hajiya Mama duk za ta saka su a saiti InshaaAllah ta san me za ta yi musu,gara kawai a yita ta k’are……

amma kuma rashin sanin whereabout d’in Baba larai babban fullstop zai sakawa mission d’in nata saboda Baba larai d’in

ce za ta yi komai tun daga kan dawowar da take so suyi da gaggawa har mutuwarsu.

Tsakanin Mommy da Yahanasu sam ba jituwa kwata kwata Yahanasun ta k’i yarda ta ba ta chance har y’an gidan sun fara lura da yadda Mommyn take binta ita kuma tana kaucewa



Mommyn har da ce mata “InshaaAllah za a karya abunda aka yi mata a samu ta yi aure!”

Ita kuwa Yahanasu tace”dan girman Allah kar su karya komai!

su barta a yadda ta ke ta yi Imanin Ubangiji ne kad’ai zai iya yin ikonsa a kanta.”

Kamar yadda Mommy ta

yi zato Yahansun ba ta tona mata asiri ba ammafa tun daga wnanan ranar ko had’a hanya Yahanasu ta daina yarda ta yi da Mommy,k’ofar d’akinta kuwa kullum a rufe.

…..

……Wata d’aya wata biyu tun su Mommy suna d’aukar b’atan Baba Larai abun kamar wasa har su

ka zo suka fara tsorata dan yau kwana sittin kenan babu ita babu alamarta wayarta ba ta shiga gashi suna tsananin buk’atarta dan Ya’isha ta d’aga musu hankali akan auren Najeeb da Siyama gashi Yash da Manubiya babu su babu dalilinsu ba ma ta jin za su dawo

bikin,Yassir kam ya sake tab’arb’arewa company d’in da Yash ya bud’e masa ma ya tashi a aiki Hatta building d’in nasa ya sayar motocinsa masu tsada ma ya siyar kuma har yau ba a san Ina yake kai kud’in ba..

Kausar kam ba k’aramin Namijin k’okari take yi

wajen danne zuciyar ta game da shi ba gashi mutanen da ta addaba da kira a kan su tona masa asiri a samu a kashe sa ta hutu!sun daina sauraronta kamar waenda ya yi musu tsafi!

A fannin lamarin Yash kuwa ita kad’ai ta san me take going through ta kira sa

ta yi message amma duk baya shiga ba ya tafiya tsabar bala’i har depression ta kamu da!

da kyar ta samu ta nutsar da kanta ta ke shan magani ganin tana shirin haukacewa!!

Inda ace babu aurenta a kan Yash ya yi wannan dogon zangon da baza ta tab’u sosai b

a

amma wannan zumar da aka lasa mata a baki aka janye shi yafi komai haukatata!!

……saboda Allah ace ranar da ake shirye shiryen kai ka gidan Miji mijin ya gudu kuma har yau bai dawo ba!(dan ita har yau ba ta san ba matar Yashjub bace ba ita.)

Dukda wan

nan bala’in da take ciki amma tana namijin

k’ok’ari wajen rik’e kanta da controlling kanta,zuwa yanzu ba ta da komai against su Mommy amma haka kurum take jin she can’t share matsalarta da su she can’t trust anyone anymore….. abunda Mommy ta yiwa Baba

larai ma ya sanya Kausar d’in ta d’an tsorata da Mommyn,ta ja jikinta sosai

Doctor d’inta dai yace mata hakan sign ne na depression d’in da ta kamu da shi saboda ta yi going through a lot a rayuwarta da yawa shiyasa ba za ta iya sake trusting kowa ba(ta

zama so secretive)sai dai sam ita ba ta wani yarda ba,ta fi raja’a akan kawai dai shekarunta da suka ja ne suka sanya ta yi wayo ta zamo silent ta kuma koyi rik’e sirrinta.

A kaff y’an matan gidan har ma da Mommyn babu wanda ya lura da cewa ba ta ma da l

afiya saboda kamar yadda take cikin masifa hakanan suma kowa a cikin masifar take!

Su Yasira zuwa yanzu rashin aure ne matsalarsu dan auren Yadira da suka ga ya taho gadan gadan ya sake uzzura musu son aure a cikin zuk’atan su especially ma Yasira da ta f

issu shekaru sai dai kuma ko talakan saurayi babu mai shi a kaff cikinsu,Ya’isha kuwa tata damuwar daban ce dan ji take muddin Najeeb ya auri Siyama a gaban idanunta to kuwa sai ta mutu!!!

Mommy kuwa nata tashin hankalin ya fi na kowa dan itama rashin aur

en nasu yana damunta amma ba kamar yadda komai ya rinchab’e mata ba!!

Ta ko’ina babu haske babu sauk’i babu nasara……Kausar d’in ma da ta shirya akan za ta yi mata Abu da Yashjub a kan Daddy gashi yanzu babu auren,kuma a yadda take ganin Daddy kwana biyun

nan in dai ba irin wannan aikin aka yi ba tabbas akwai gagarumar matsala.

Da kyar ta samu ta dake ta sanarwa Kausar d’in da su Yasira babu fa maganar aure dan tausayinta take ji gara kawai ta sani ta cire hope,aikuwa ranar duk dauriyar Kausar kasawa ta

yi,sai da suka yi sati d’aya a asibiti tukunna ta dawo dai dai da kyar ta fara gane waye a kanta.

Dole ta sanya Mommy ta fito mata a mutum ta ce mata kawai ta hak’ura da Yashjub!!!

Ta yi trusting d’inta sannan ta taimaki kanta ta cire Yash a ranta zuwa y

anzu ya kamata ace ta fahimci zuciyar Yash ta Manu ce,dan haka dan Allah ta hak’ura kawai!

Tana cikin masifa gashi babu Baba Larai dan haka dan Allah ta ajjiye komai a gefe ta tashi ta tsaya mata

she should stand by her side as her only realative ta ts

aya mata ta taimaka mata akwai labarin da zata bata amma ba yanzu ba sai nan gaba.

Ta ajjiye batun soyayya haka ta taimaka mata ta rai da tsira ake yanzu dan duk abunda ya sameta to itama ya sameta farinciki da nasara ko kuma akasin hakan…sannan su Daddy

sun ce har ta haihu a idanun duniya tana a matsayin matar Yashjub ne…InshaaAllah a tsakankanin nan Ubangiji ta san zai nuna musu hanyar da za su bi komai ya tafi musu dai dai.”

Ita dai Kausar tace mata “to” ne kawai amma bata gama fahimtar inda zancen nat

a ya nufa ba sakamokon bala’in da take a ciki,ita kanta yanzu kam ba ta san ta Ina za ta b’ullo ta sake zama mata ga Yashjub ba!!she can’t believe gaba d’aya hard work d’inta ya tafi a banza kenan???inaa da sake!.

Har yanzu babu Munirat babu labari

nta Ummi ta kuma zama abun tausayin Hankalinta gaba d’aya a tashe!

Daddy ne yake dan tausar ta shi da su Hajiya mama wanda shima Hajiya Maman ce take tausar sa take tsayar da shi if not da tuni ya san na yi da Mommy…dukda ya san ba shi da wata hujja a kan

ta amma kawai shi he can’t tolerate her no more,ya tsaneta.

A bangaren Mama itama zuwa yanzu ba ta da wani burin da ya wuce ta saka Yahanasu da Yashjub a idanunta dukda tana tambayar Manubiya ya suke tana jin komai dan har gaisawa

sukeyi ma da Yashj

ub but tana buk’atar ta saka su a idanunta musamman ma da ta ji har yanzu Yahanasu ba ta yi aure ba!,ta san dole tana da buk’atar ta…..

Bayan watanni uku!!!

An yi auren Siyama da Najeeb gidansu yaana unguwar Badawa,haka shima Junior ya auri Yadira

suna zaune a d’aya daga cikin gidajen Daddy dake a Unguwar Darmawa kafin ya kammala abunda ya zo yi ta karb’i transcript d’inta su wuce Uk.

Duk cikin aure biyun nan da aka yi su Manubiya ba su zo ko d’aya ba sun dai turo gudunmawa sun kuma yi addu’a.

Su

Hajiya Mama ma da suka zo na su Junior ba su wani dad’e ba suka juya dan ita dama da kyar ma ta yarda ta zo.

Ya’isha tana nan yau lafiya gobe ba lafiya dan yadda ta kad’u ta damu da al’amari sai da ya girgiza su Mommy gashi har yanzu batama da shirin hak

’ura da Najeeb.

Kausar ma tana nan tana fama kullum ba lafiya ga ciki ya tsufa..jira kawai take yi su Yashjub su dawo wllahi duk bala’i sai ta san yadda ta yi ta koma masa sai dai ta rasa ranta a hanyar raba sa da Manubiya da kasancewa tare da shi.

Ya Musbah ma ya kammala karatun da ya yi takardar tana fitowa ya fara shirye shirye successfully ya zana waec ya yi jamb yanzu haka neco ya ke yi kuma ya ci jamb d’in dan haka Najeeb ya sake zage damtse wajen nema masa gurbin karatu a fannin Business Admi

nistration a jami’ar Bayero uni,Kano.

Gwaggo Suwaiba ma ta zo,yanzu Mijinta shima Allah ya fara nuna masa k’arshensa kuma Itanma ta dage da addu’a sosai dan cikin ikon Allah tana cikin wnnan hali na ha’ula’i Allah ya kawo mata wasu makwabta jajirtattu

wajen fanni addu’a har Al’k’urani suke rubuwata da littafai,sama sama suka fara gaisawa su kad’ai suke iya shiga gidan,sai da zama ya yi dad’i labari ya yi labari tukunna suka fahimci ashe ma Matar tana da relationship da Mahaifiyarsu Innar(very distant r

elative)amma.

Ita ta bata addu’o’i,kuma ta ce ta dage da Azkar da sallolin dare..Aikuwa da taimakon Ubangiji cikin ikonsa yanzu Mijinnata har islamiyya ya barta ta shiga sannan yanzu kam ana iya zuwa wajenta kuma wannan tsangwama ta kyarar duk babu,ba s

hi ma da lafiya ya kwanta jinya.

Ko da ta tambayesa zata zo ta ga Inna an yi auren su Jidda duk ba ta zo ba! Nan ma sam bai yi yunk’urin hanaawa ba dukda ba ya so amma shi kansa ya san yanzu kam surk’ullensa sun daina tasiri a kanta…hakanan ta taho kano i

ta da d’aya daga cikin y’ar mak’oftan nasu mai suna Hadiza bafulatanar Yarinya mai shekaru 17 kyakkyawar gaske siririya doguwa fara sol gashi har gadon baya.

Tunda suka zo da Ya Musbah ya kyalla ido ya ga Hadiza itama ta gansa suka kamu da k’aunar juna a

bun kamar had’in baki.

Satinsu biyu ya ga dai ba zai iya daurewa ba ya amayar da abunda ke zuciyarsa itama kuwa Hadiza ko irin d’an jan ajin nan na mata da kunyar fulani gagara kwatantawa ta yi tashi d’aya tace masa ‘Yes!!’

Dama su Inna sun fahimci tak

e takensu ai kuwa Yarinyar tana gayawa Gwaggo Suwaiba suka hau murna itama kuma Inna Ya Musbah ya gaya mata,ba kad’an ba Inna ta ji dad’in had’in shiyasa Murna ta zame mata biyu,ga farin cikin ganin y’ar uwarta ga kuma farin cikin had’in Hadiza da Ya Musba

h da Ubangiji ya had’a!

Hausawa sun ce ba ‘a yabon d’an kuturu sai ya shekara da yatsu amma tabbas ita kam za ta yabi Hadiza saboda Yarinyar tana da hankali ga ilimin addini ga son mutane da girmama na gaba da ita,sannan gwaggwo Suwaiba ma da suka yi wata

nni goma sha uku tare da su ta bada kyakkyawar shaida a kanta kuma itama ta ji dad’in had’in matuk’a.

Dama su Inna so suka yi a b’oye abun sai an saka rana komai ya kankama tukunna a fito da maganar ba dan komai ba sai dan Baraka amma Allah da ikonsa tu

n kafin kowa ya ji ma ita Barakar ce ta fara ji kamar wata mai duba…aikuwa nan da nan ta kunno masa wutar bala’i ta koina,ba ta tashi masifar ta sai dare ya yi ya zo bacci nan za ta hanasa bacci sai dai su kwana idanunsu biyu..amma har gobe shi nuna mata m

a yake yi bai san a kan me yake take bala’in nata ba!!!shi inama ya ga lokacin yin wata budurwa???

Dukda hakan bai sa Baraka ra hak’ura ba hakanan itama Hadizar ba barinta ta yi ba dan yanzu tun safe har dare a wajen su Inna take wuni dukda fuskarta kullu

m kamar hadarn Kaji idan ta shiga wajen nasu amma kuma hakanan za ta zauna ta yi ta fad’an maganganu a Hadizan har ma da su Inna ko

a jikinta kuma zuwa yanzu hakanan ta hana Ya Musbahn keb’ewa ko da Innar ne wai duk dan gudun kar ya samu time da momment d

a Hadiza.

Kamar mai gadin sa haka ta koma ta kafa ta tsare,haka za ta yi ta zaman jiransa yana dawowa daga aiki zata fara hamma har sai sun tafi ko wajen Baba ya je haka za ta yi ta safa da marwa a bakin k’ofar parlourn nasa ta baya har da lab’e har sai y

a fito sun wuce tukunna hankalinta zai kwanta.Tsabar bala’in da ta sakawa kanta ko girki ba ta iya zama ta yi ballantana gyaran gida koina ya yi datti gashi ba girki gida duk tsami kuma a da Baraka kam tanata tsafta gwanin ban sha’awa.

Sai dai kullum idan

ta gama gadin nasa suka koma b’angaren su yace mata’ta d’an saka turaren wuta ta kimtsa gidan yana kyankyami’ shi kuma ya fita ya je ya siyo musu gurasa da nama…abunda Baraka ba ta sani ba shine idan ya yi fitar siyo gurasa da naman ne yake samun ganin Ha

diza,dan sam ba shi ne yake zuwa siyowa ba almajirin su mai wanki da sharar gidan yake bawa shi kuwa ya dawo ciki ya wuce wajen Hadiza inda suke had’uwa kullum wajen wanke wanke ta baya.Yana lura da sa idon da Baraka take yi masa dan ko fitar zai yi sai ta

lek’o ta tabbatar ya fita d’in tukunna take komawa ba ta san yana kallonta ba.

A yadda yake son Hadiza ba ya so a samu matsala a aurensu kuma zuwa yanzu ya fahimci Baraka ta hau Buzu,shiyasa ko su Inna da suke ta cewa ya fad’a mata idan auren ya rage sau

ra sati biyu jin su kawai yake yi sai ya samu kansu zai nutsu ya zauna ya yi musu bayani sosai,domin shi kam inshaaAllah sai dai kawai Baraka ta ga Hadiza a d’akinsa matsayin matarsa ko kuma ta ji ana d’aura aure.

A b’angaren Baraka kuwa har yau ba ta

kama Hadiza da Mijinta ba amma ta san something is going on gashi wayarsa koina password ballantana ta yi masa bincike…Bokan ta ne ya fara sanar mata yanzu kuma ya sake d’aga mata hankali ta inda yake ce mata ai maganar aure ma ake yi…dama chan a cikin ma

sifa take sakamokon yadda komai ya k’i tafiya yadda take so Ya Musbah ya k’i ya dawo mata kamar da ta gagara mallakesa kwata kwata sannan so take a raba gidan biyu ko a sayar da gidan a sayi wani su rabu da su Inna amma abu ya ci tura!!!

Gashi gaba d’aya

ta rasa soyayyar sa kuma ta gagara dawo da hankalinsa gareta kuma sai yanzu ita kanta ta fahimci masifaffiyar k’aunar da take yiwa mijin nata musamman ma da ta ji zancen maganarsa da wata….shiyasa ta tashi ta tsaya tsayin daka wallahi indai ta haifu Ba’a

isa a yi mata kishiya ba kuma Inna da take zugasa ta hana ruwa gudu ta toshe mata duk wata hanya wallahi sai ta haukatar da ita ko kuma ta maida ita kamar farko ta kwantar da ita ta yadda za ta zama da ita da gawa babu maraba!saboda Bokan ta yace mata”Inn

a ce take yin addu’o’i ba dare ba rana babu ji babu gani shiyasa komai nata ba ya ci komai nata yake tab’arb’arewa.”

Yahanasu ma ta yi sabon saurayi mai suna Egnr

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login