Showing 168001 words to 171000 words out of 259716 words

Chapter 57 - MANNUBIYA COMPLETE

Unknown   

01 Sep 2026

49

tsinceta ne yake sanar da ita cewar”kwananta hud’u da kyar aka samu ta farfad’o a ranar.”

Babu yadda bai yi da ita akan ta gaya

masa inda family d’inta suke ba amma ta k’i magana..ganin kamar ba ta ji kuma ba ta magana ne ya sanya ya hak’ura ya rabu da ita ya had’a ta da nurses ya biya kud’in komai yace “idan akwai emergency a kirasa”daga haka ya tafi.

Duk yadda ya so ya manta

da al’amuranta sam sai ya gagara,gaba d’aya tausayinta ya hana sa sukuni lamarinta ya tsaya masa a rai..ya san tabbas tanada buk’atar taimako.

Ba a yi sati uku da rasuwar k’anwar sa ba,sun yi mata aure sun d’auke ta sun kaita jos ashe mijin ba zaman adalc

i yake yi da ita ba k’arshe sai ciwon zuciya ne ya kasheta…..

Mahaifiyarsu ta rasu kuma su biyu ne kad’ai shiyasa har gobe yake blaming kansa dan in da ace yana yawan zuwa dubo ta kuma ya saka idanu a kanta da hakan ba ta faru ba.

Sai da ya tabbatar ta

warware ta fita a shock,almost 1 month tukunna ya koma,a lokacin ta warke amma wani ikon Allah damuwa ko kad’an ba ta barta ba asalima kuka ya je shi ya tarda ita ta na yi.

Ya kad’u sosai da lamarinta dan haka bayan sun gaisa ya amsa godiyar da ta yi mas

a da kulawa ya zauna ya shiga tambayarta “menene matsalarta har haka?,kar ta damu ta d’aukesa a matsayin yayanta ta fad’a masa komai.”

Sau uku tana bud’e baki da niyyar bashi tarihinta amma tana fara cewa”Mijina ne…”

Sai kuka ya ci k’arfinta……

Zuwa yanz

u ya fahinci inda gundarin matsalar take shiyasa kawai ya ce “ta yi shiru…..ta yi hak’uri ko ma me ya yi mata ta yi hak’uri Allah zai saka mata.”

Sai da ya tabbata ta d’an nutsu tukunna yace”akwai wanda take so ta kira a cikin y’an uwanta?”

Ba b’oye b’

oye tace masa ”ba ta da kowa”

Jinjina kai ya yi yana mai jin tsananin tausayinta,haka kurum take tuno masa da marigayiya k’anwarsa tun ba ma da ya ji itama sunanta Khadijah kamar k’anwar tasa ba.Ya jima yana nazari kafin yace”kina buk’atar ganin shi Mij

in naki ne?a nem…”

Tun kafin ya rufe bakin sa tace”A’a”

Dan ba wai iyaka Lawal da ya k’ulla mata sharri take jin haushi ba har da Imam wanda ya yarda ya aminta ta aikata abunda aka nunawa idanunsa on top of that ya hari rayuwarta.

“In kai ki Gidana za

ki taya matata zama?,Dr ya ce mini a yau zai sallameki inshaaAllah”

Muryarsa ta katse mata tunani.

….Da farko k’in amincewa ta yi tace”ya barta a asibitin ko kuma ya barta ta tafi kawai za ta san abunyi.”Shi kuma ya k’i dan a yadda take da damuwar nan i

dan ba ta samu wani da zai yi mata gata ya tsaya a kanta ba tabbas akwai matsala shi kuma haka kurum ya ji yana so ya taimake ta kuma yana so ya yi making up to negligence d’in da ya yi wa sister d’insa shiysa ya nace ya k’i barinta har sai da ta amince ta

bisa suka tafi gidansa.

D’ansa d’aya mai suna Al’ameen da matarsa suna ce mata Ammi dan shima mai gidan sunan mahaifiyar sa ne da matar tasa.

Dama tun farko Ammi ta fara nuna kishi da Khadija dan ce mata ya yi y’ar uwarsa ce cousin za ta zauna da su. Da

ga baya kuwa da ya fad’a mata gaskiya dan shi bayason b’oye b’oye,da kuma itama y’an uwanta suka zugata shikenan ta fara hauka!……har ta yi haukar ta kuwa ta saduda babu wanda ya biyeta,ita da kanta ta zauna ta yi lissafi mai kyau ta nemi gafarar mijinta da

khadija aka zauna lafiya dan a lokacin sun kusan shekaru shidda tare shiyasa lissafinta ya bata inda ace fa aurenta zai yi tou da tuni ya aura.Kuma yadda Khadija take kula mata da Al’ameen ko ita ba ta kula da shi..mai d’a wawa!ta haka Khadija ta siye zuc

iyar Ammi gaba d’aya.

A kwana a tashi zama ya dawo da su Kano.Sai a lokacin Khadija ta gaya musu tana da y’a Yahanasu.

Addu’ar ta d’aya Allah ya sa ba a chanja musu makarantar da ta san an fara saka su ita da Yashjub tun farko ba,dan haka suka tambayi

baban Al’ameen suka tafi ita da Ammi.

Ba su sha wahala ba dan tashi d’aya matar ta shaida ta ta amsheta hannu bibbiyu har da hawayenta tana cewa”ai ce musu aka yi ta rasu,amma ta je gida an ganta?ko dai nan wajen Yahanasu ta taho direct??ta je su ganta su

ma hankalinsu ya kwanta waye waye…”

Ita dai Khadija ce mata ta yi tou kafin tace”a kawo mata Yahanasu da Yashjub.”

“Yashjub ai ya dad’e da komawa Uk,amma Yahanasu dai tana nan,da tare take ma da siblings d’inta to yanzu basu da nursery section sakamoko

n gobarar da suka yi shine aka chanja musu school.”

Matar ta faiyyace mata hakan tana mai fita domin ta je ta taho mata da Yaha.

Sai da Khadija ta yi kuka,saboda da kyar Yahanasu ta shaida ta.

Tana murna tana kuka kamar ranta zai fita haka ta mak’alk’

ale y’ar tata.

Hatta Ammi da mai makarantar sai da suka yi kuka..

Tun daga ranar duk ran Jumaah kafin su d’auki Al’ameen a school sai sun biya sun ga Yahanasu,Yarinyar ta shak’u da mahaifiyarta sosai zuwa yanzu….Khadija Ammi da Baban Al’ameen suna sh

iryen shiryen zuwa su je a yi magana ta fahimtar juna a samu Imam ya bawa Khadija Yahansu kwasam rannan sun je mai makarantar tace “Mahaifin Yahanasu yace idan ta sake barinta ta shiga makarantar sai ya k’ulle ta!.

Dan Allah dan Annabi ta yi hak’uri ta ta

fi kuma yace idan har ta sake zuwa kusa da y’ar sa wallahi kowa sai ya ji kansu kuma kowa sai ya ji abunda ta aikata har ita y’ar tata”…

….Babu kalar tambayar da su Ammi ba su yi mata ba a kan ta yi musu k’arin bayani amma ta k’i cewa komai,Baban Al’ame

en da har yana shirin shiga kotu a samu a kwato mata y’arta amma ta hana ta kuma rok’esu akan kar su sake yin maganar a bari ya wuce kawai…Zuwa yanzu sun riga sun san Khadija sun san ba muguwa bace ba kuma ba ta da wani mummunan hali,shiyasa ba su dasa aya

r tambaya a kanta game da hakan ba kuma suka bar maganar ya wuce kamar yadda ta rok’a ta buk’ata.

A b’angaren Khadija kuwa,abubuwa da dama ne suka had’e mata!

Kenan har yanzu Imam bai yi bincike ya goge zarginta ba!bai yi nadamar abunda ya aikata mata

ba?

Sannan ko kewarta

ma bai yi ba all this years bai nemeta ba bai nemi ta dawo garesa ba instead yana so ma ya yi cutting duk wani ties da suke da shi,y’ar cikinta ma ya raba ta da ita kenan yanzu.!

Abu na uku kuma ta san tana da gaskiya akan sharrin

da Lawal ya yi mata amma kuma har ga Allah idan akwai Al’amari mafi k’ololuwar tozarci da Muni da masifar tashin hankalin da ba ta son

tunawa a rayuwar shine wannan incidence d’in,ita kanta ita kad’ai idan ta tuno ji takeyi kamar ta binne kanta tsabar ta

shin hankali ba don k’arfin addu’a ba da tuni ta zauce tsabar yadda abun yake addabar ta a ko da yaushe idan ta tuna,A yadda Imam ya zama wani irin mugun mutum ta san zai yi mata terere ne kamar yadda mai makarantar su Yahansun ta ce yace “kowa sai ya ji k

ansu shi da ita,har Yahanasu”.A ganinta idan ba ta samu damar shak’uwa da Yahanasu ta bata tarbiyya da kulawar da ta kamata ba bai kamata ta bada gudun mawa wajen goga mata bak’in fenti ba!Yahanasu mace ce aure za ta yi ta san muddin ta bawa Imam k’ofa ya

tozartata tabbas abun sai ya shafi rayuwar y’arta.

Mommy Uwa ce ta gari kuma za ta iya rantsuwa a kan soyayyarta ta gaskiya ga Yahanasu shiysa ta zab’i ta bisu ta addu’a dama rayuwa ba a yi ta dan ka samu komai perfect yadda kake so ba…tsakaninta da lawal

Allah ne kad’ai zai Isar mata dan ya cuceta ta koina,Imam kuma ya tarwatsa ta gaba d’ayanta!kaico!da rashin sa’ar Miji na gari wanda zai tsaya mata ya bugi k’irji ya yi shaidar ta ya kareta a gaban kowa,asalima shi harin rayuwarta da duk wani sauran farin

ciki da darajarta yake yi…

ko maganar tozarcin da wannan rana ta k’unsa ba ta so ta tuna ballanta a yi mata terere a bainar jama a a gaban y’arta.

Dan haka ta zab’i ta bi y’arta da fatan alkhairi kawai tare da addu’ar samun Miji na gari dan tabbas duk m

acen da ta yi rashin sa’ar Mijin kwarai a rayuwa to ta yi babban rashi…..shiyasa tun jiya Hankalinta yake a tashe take addu’ar Allah ya kawo abunda zai tarwatsa maganar auren Jidda da Yusuf dan tabbas Yusuf bai dace da Jidda ba mutumin da ba a san silar ar

zik’in sa ba ta ya za a d’auki y’a a basa saboda Allah…………..

Sallamar su Manubiya ce ta katsewa Mama dogon tunanin da ta lula!a hankali ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya ta shiga goge hawayen da ita kanta sai yanzu ta san suna zubo mata.Sai da ta ga

ma goge fuskarta tukunna ta d’ago ta kallesu tana mai amsa sallamar tasu.

Cikin tsananin mutuwar jiki Manu ta k’arasa inda take suka gaisa da Mama da Aisha da Anty Umma,ta gaida Ammi wadda daga ita har Siyama suka yi mamakin ganinta a parlourn nasu tukunn

a tace musu “Ina su Inna”

Aisha ce ta mik’e tace”mu je wajen nasu”

Daga haka ta yi gaba suka bi bayanta.

Su biyu kawai suka tarar a cikin d’akin,Jidda ta rame a cikin kwana d’aya tak ta fita a haiyyacinta..

Suna zaune Inna ta na yi mata nasiha a haka

su Manu suka shigo suka tarar da su.

A gefen gadon suka zazzauna suka sakata a tsakiya kowa idanunta ya cicciko.

Bayan gaishe gaishe Inna ta yi sauri ta mik’e ta ce”ga su Manu Aisha ku yi mata fad’a kuma Baba yace ana d’aurawa za a wuce a kaita gidanta.



Siyama ce ta iya cewa”Inna kuma babu abunda za a yi?”

Murmushin da ya ki fi kuka ciwo Jidda ta yi ta rik’o hannunta tace”ba komai Siyama,Allah ya sa hakan ne ya fi alkhairi”

Siyama na shirin yin magana suka had’a ido da anty Umma wadda shigowarta kena

n dan haka ta yi saurin d’aura yatsanta a kan labb’anta alamun ta yi shiru kafin ta kalli Manubiya tace”Manu d’an zo”

Suna fita ita da Inna suka ce mata “tunda har Jiddan ta yi shiru ta hak’ura itama to kawai su ci gaba da kwantar mata da hankalli,kar wad

da tace wani abun da zai d’aga mata hankali a cikinsu.

Baba ya riga ya yi nisa ba zai ji kiran kowa ba ga Ammi Chan a parlour har ita aka had’u aka dinga bashi hak’uri d’azu amma ya k’i hak’uri dan haka kawai su zuba mishi ido.Zab’in Allah suke nema a ko

da yaushe ba su san meye a k’asa ba,su dai su ci gaba da addu’a kawai…”

Da “to” kawai Manubiya ta amsa su daga haka ta nufi d’akin da ke opposite na Jiddahn dan ta san watak’il shine na Inna,tana shiga ta mayar da k’ofar da rufe dan har ga Allah ba ta s

on had’a idanu da Jidda ba za ta iyaba,she can’t believe wai Jidda za ta auri Yusuf amma ba abunda za ta iya yi a kai.

Waya ta d’auko ta kira Yashjub,a tunaninta har yanzu za ta ji fushi a muryarsa amma sai ta ji sa wasai kamar ba ta yi masa laifi jiya ba

har yana tambayarta akwai abunda take so ya siyo ya taho mata da shi?yana hanya Daddy ya d’an kirasa zai je ya dawo.”

“A’a”kawai tace.

Daganan ta tambayesa ya suka yi da Baba,komai ya gaya mata daga haka shima yace su yi ta addu’a he’ll call her back ya

na shiga office d’in Daddy yanzun”

Sallama suka yi ta ajjiye wayar tana tunani barkatai a cikin ranta.

K’arfe 10:30am guri ya cika taff da jama’a dan Yusuf da kaka mallan sun yi gayya ba laifi,cikin gida kuwa kowa hankalinsa a tashe yake suma su Ya Naf

i’u hankali a tashe dan yanzu suka dawo daga kai gado shiyasa suka kuma tabbatarwa eh fa Jidda Yusuf za ta aura…kaff wajen daga y’an gaiyyar sod’i da suka ga anata sauk’e kulolin abinci da lemuka da snacks da kajii sai Yusuf da kaka mallan ne kawai suke fa

rin ciki dan hatta Baba hankalinsa ba a kwance yake ba ba a son ranshi zai aurawa Jidda wanda ranta ba ya so ba especially ma yanzu da Baban Al’Ameen ya zo ya ja sa gefe ya basa hak’uri yace”a shirye yake ya aurawa Al’Ameen Jidda a yanzu.Ya yi trusting Al’

ameen har ma da ita kanta Jiddan amman indai har zargin su yake yi kamar yadda labari ya iske masa to tabbas babu wanda ya fi chanchanta Jiddan ta aura idan ba Al’ameen d’in ba.”

“Ya je ya sake tunani,da shi da wakilin Al’ameen suna nan babu inda za su je

,fatan Allah ya sa su ji alkhairi.”

Tun daga nan jikin Baba ya yi sanyi tun ba ma da Baban Al’ameen yace”ya yi trusting har ita kanta Jiddan” ba!

A take a lokacin ya ga rashin adalcinsa ga Jidda…..tabbas ya biyewa dokin zuciya ya yanke d’anyen hukuncin

da har abada zai dinga damunsa dan ya san zuwa yanzu kam ba zai yiu ya chanja d’aurin auren nan daga kan Yusuf ya koma kan Al’ameen ba….MANNUBIYA

(Book 2)

Page 34

Na

Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

“Na gaya miki dama,ni ne Mijinki…in da ace ba ki tsaya b’ata mana lokaci ba da tuni abubuwa da dama basu faru ba!.

Allah ya bamu zaman lafiya Jidderty”

Yusuf yana gama turawa Jidda message kamar haka ya juya ya nufi cikin masallacin yana zuba wani faffad

’an murmushi yana ji kamar an yi masa bushara da Gidan Aljannah.

A gefen Baba ya nemi guri ya zauna,idaunsa a kan Baban Al’ameen wanda tun d’azu ya ke ankare da shi yana sane da shi ya san so yake a fasa auren a bawa d’ansa,har ga Allah bai yi niyyar yiwa

Baban Al’ameen ko Al’ameen d’in wani abun ba amma abunda mutumin yake ta yi tun d’azu ya sa ya k’ullacesu kuma sai ya nuna musu waye Yusuf! bari a gama d’aura masa aure da Jidda a kaita gidansa lafiya Wallahi sai ya b’atar da su.

Ana shirin fara d’aurin

auren.

Sojoji da y’an sanda masu fararen kaya sun fi mota ashirin suka danno kai cikin layin a dai dai wannan lokacin.

Sojoji uku da ss guda d’aya ne suka shigo cikin masallacin suka ce “kowa ya fito!”cikin dakakkiyar murya,aikuwa tashi d’aya waje ya h

autsine,

cike da fargaba jama’ar suka fara kiciniyar fita ana hayaniya da tambayar “mai ya faru”

Baba ne ya juya da niyyar cewa Yusuf”mu je mu ji mai ya faru,a samu abun ya lafa sai a dawo a d’aura”..amma kamar walk’iya da ikon Allah sai ya ga babu Yusuf

babu mai kama da shi bayan yanzunnan suka gama magana.

A b’angaren Yusuf kuwa tun da ya ga Sojoji hankalinsa ya yi masifar tashi,tsoro ya rufesa in banda dukan uku uku babu abunda k’irjinsa yakeyi, dukda kuwa ya san cewa fuskarsa is not known a cikin y

aran black snake kuma he’s not wanted amma hakan bai hanasa tunanin watak’il shi aka zo nemeba,dan yanzunnan yaga message d’in Abokinsa ta inda yake cewa”an zo kama Black snake a airport ya yi yunk’urin guduwa an harbesa ya mutu sannan an bud’e wayarsa an

fara binciken neman yaransa,dan haka a duk inda yake ya gudu kafin a samu komai ya lafa.”

Yana gama karanta message d’in ko numfashi bai ja ba ya ga Sojoji sun shigo shiyasa ana fara hayaniya ya sulale ya bi ta k’ofar liman da sauri ya fice amma yana fit

a yaci karo da wasu a ta gaban k’ofar saboda dama zobe suka yiwa masallacin….tashi d’aya suka damk’esa dan an raba musu hotonsa shiysa suka yi saurin shaidasa.

Baba Yashjub wanda k’arasowar sa kenan sai su Ya Musbah sojojin suka yiwa bayanin arresting Y

usuf da aka yi……

…..”A cikin wayar black snake suka hararo Yusuf ta hanyar bibiyar chat d’insu da suka yi,an gano yana d’aya daga cikin manya manyan yaransa masu tayashi safarar kwayoyi da y’an mata dan yanzu haka ma a wannan ranar if not ba a kamasu ba t

o suna shirye shirye ne a kan shi Yusuf d’in zai taimaka a sacewa Black Snack wata Yarinya ‘Mannubiya’…..”

Dan haka za su tafi da shi kuma babu bailing har sai sun gama interrogating d’insa daganan idan suna so za su iya d’aukaka k’ara zuwa kotu kafin a y

anke masa hukunci….

Suna ji suna gani aka datsawa Yusuf ankwa wanda yake ta turje turje aka wuce da shi,shi dai Baba bai gama gasgatawa ba amma su Ya Musbah da Yashjub wanda yake ji kamar ya bisa ya fara nad’a masa shegen duka tun a nan saboda tunanin s

ace masa mata ma da ya yi,duk sun yarda.

Kaka mallan kam har da kukan sa a take ya nemi adaidaita sahu ya nufi gida yana tafe yana kiransu Baba Habu a waya…..

Limamin ne ya matso ya yiwa Baba jaje kafin yace “yanzu a yi sanarwa Akan an fasa d’aur

in auren kowa ya watse kenan?ko za a d’aura ko babu shi?”

Murmushi ya Nafi’u ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login