Showing 27001 words to 30000 words out of 221574 words

Chapter 10 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

169

falon, ta lumshe ido tana ji kamar da zuciyar ta yake tahowa, duk taku Waya da zai yi bugun zuciyar ta ?aruwa yake yi, kamar wacce ta aikata masa laifi take jin tsoron zai kamata. A daidai lokacin ta ji an buWe ?ofar an shigo, ta juyo tana kallo sa ganin ko kallon falon bai yi ba yana niyar wucewa sama.

Da sauri ta ?arasa inda yake, muryar ta tana rawa ta ce, "ban san sunan ka ba..." Sai ta kasa ?arasawa saboda hawayen da take ri?ewa suka sakko daga idanunta.

Ta ja numfashi mai tsaho ta ce, "Babana yana asibiti........" tana faWa ta fashe da kuka tana zubewa akan guiwar ta tana kuka sosai.

Kamar an dakatar dashi ya tsaya bai hau saman ba, ya juyo ya ga yadda take kuka kamar wacce aka yiwa rasuwa a lokacin. Ko maganar ta bata fita yadda ya kamata, kuka take yi sosai tana haWe hannunta waje Waya.

Islaha ta ce, "Ban san me na yi maka ka kawo ni nan ba, ban san me na aikata ka saka aka kawo ni ba. Da nace bazan ba ka ha?uri ba, tunda ban yi maka laifin komai ba, kaine ka yi min laifi bani ce nayi ba. Amma na ha?ura, saboda rayuwar Baffa zan sauke kai ?asa, saboda rayuwar Baffa zan yi abinda ban taSa yi ba. Baffa ya cancanci fiye sa haka a gare ni, ya cancani nayi komai saboda shi."

Ta ja numfashi tana goge hawayenta ta ce, "ka yi ha?uri....." Ta faWa tana lumshe ido hawaye yana cigaba da zuba a idonta. Hawayen ba?in ciki da takaicin sauke kai ?asa da tayi, amma bata da mafita dole ta saka ta bashi ha?uri.

?an murmushi ya yi, ya Wan girgiza kai ya ce, "finally."

Islaha ta kalle sa ta ce, "Don Allah ka bar ni na tafi, ka ?yale ni naje na cigaba da abinda yake gabana. Tunda na baka ha?uri, komai ya ?are daga wajen nan."

A lokacin ya juyo a hankali ya kalle ta, bai yi magana ba sai Waga kai da ya yi kawai, ya hau sama bai sake kallonta ba.

"Mugu kawai, Allah ya isa tsakanina da kai, kar ka bari na tafi Win, in ka ga dama ka bari sai naman jikina ya koma ?ashi sai ka bawa karnuka. Saboda Baffa kaWai na baka ha?uri, wallahi da baka isa na sauke kai ?asa ba. Bana bada ha?uri akan ha??ina, in ka ga na bada ha?uri nasan laifi. Zamu sake haWuwa wani lokaci, a lokacin zaka tabbatar da bana sauke kai ?asa wallahi."


Rehaan yana jin ta, ya yi murmushi dan shi kallon mai taSin hankali yake yi mata, yanzu zata yi maganar hankali in anjima ta yi maganar shirme.

islaha tun tana kukan da ?arfinta har ta gaji, ta koma sauke nunfashi idanunta biyu har gari yayi haske. Shiru gidan babu motsin kowa, ko ina tsitt kamar babu mutane a cikinsa.

Motsi ta dinga ji, ta zubawa wajan ido sai ta ga an fito daga wata ?ofa an shigo inda take da sallama, ta kalli wanda ya shigo ganin Chef ne bature, Waure da apron a ?ugunsa, ya ?araso ya ajjiye mata tray bai ce komai ba ya koma ?ofar da take tunanin kitchen ne.

Ta kalli abincin ta ga gabaWaya english breakfast ne, sai wani munafukin kofin shayi kamar na yara. Ta yi tsaki ta Wauke kai ta cigaba da zama har bacci ya Wauke ta.

Shi kam Rehaan tunda ya hau sama ya manta da wata Islaha, bai tashi daga bacci ba sai sha biyu na rana. Ya shiga ya yi wanka ya shirya zai fita, tunawa sun yi da Mamy zai je su yi lunch a gida.

Tsaf ya shirya cikin ?ananun kaya, riga red colour, sai saka black Win jeans, ya kawo jacket black ya saka. Ya Wauki comb ya gyara gashin kansa da gashin fuskarsa, ya zubawa kansa ido, har zai naWe gashin sai ya fasa ya bar gashin sa ya sauka har wuyansa. Ya kawo face cap ya saka, yana gyara ta yana kallon kansa.

A hankali yake sakkowa ?hamshin turarensa ya mamaye ko ina. Islaha ta Wago kai ta kalle sa dan tashin ta daga bacci kenan. Basu haWa ido ba dan hankalinsa yana kan waya yana dannawa, sai da ya ?araso falon sannan ya ganta ya yi kamar bai ganta ba.

Ya Wan yi tsaki dan ya manta da ita, yaso yace su mayar da ita tun asuba sai ya yi bacci, daga nan bai sake tunawa da ita ba.

Ganin ta zuba masa ido tana kallonsa sai ya kira kira Shams, ya ?arasa ya buWe ?ofar Shams ya shigo yana gaishe sa cikin girmamawa, da kai ya nuna masa ita yayi alamun a fita da ita.

Shams ya ce, "Okay Sir."

Rehaan ya fita Shams ya ?arasa ya Wauki tarkacen kayansa da suke ajjiye, waya ce guda Waya, zai laptop. Ita dai bata motsa ba har suka fita tana kallon su. A haka Shams ya dawo yana kallon ta da fara'a ya ce, "?ar jarida kin yi free, mu je a mayar dake gida."

Ta mi?e a zabure ta ce, "da gaske ka ke ko wasa?."

"Da gaske nake, ?ar jarida Islaha."

Ta gyaWa kai cikin tabbatarwa ta ce, "Wallahi sai nayi repoting Winku a wajan ?an sanda."

Da mamaki yake kallon ta yana Wan murmushi ya ce, "Lahh, lallai yarinyar nan kina tsaurin ido, shikenan sai kin dawo" ya faWa yana dariya sosai, dan shi kam tana bashi dariya.

Ya ce, "ina jiran ki" ya faWa yana fita ya bar ta a falon dan ta Wan kimtsa yadda ya kamata.

Islaha duk ta ruWe saboda murna, ta gyara hular kanta ta gyara zaman mayafin kanta, har zata wuce sai ta dawo da baya ganin rafar dalolin nan suna wajan har lokacin.

_Islaha monday ta kusa, kuma lokacin aikin Baffa ne. Na tabbatar har yanzu Sadik bai samu kuWin aikin Baffa ba, kuma in ba mu biya kuWin nan ba daidai yake da mun rasa Baffa._

Magana take da zuciyarta tana kallon kuWin gabanta yana faWuwa matu?a a karo na farko a rayuwar ta.

_Ba fa sata zaki yi ba Islaha, kuWin wahalar dake da yayi zaki Wauka, ko banza kin fashe zaman da ya saka ki ka yi ba tare da kin yi masa laifin komai ba. Ki Wauka kawai, ai bai san kin Wauka ba, Allah ya san ba sata ki ka yi masa ba._

Da wannan shawarar zuciyar ta ta mi?a hannunta wajen kuWin, hannun yana rawa ta Wauki rafa Waya tana juya ta a hannunta. Bata taSa ri?e dala ba balle rafar ta, sai dai ta ganta a waya ko a wani abun, amma bata san ya take a zahiri ba.

Tsoro ya mamaye ta, ta mayar ta ajjiye tana tunanin abinda ya kamata ace ta yi.

_Islaha in baki Wauka ba a ina za ki sake samu wannan damar? Ki ara kawai, in yaso sai ki biya shi wani lokacin. Ba sata zaki yi ba, aro zaki yi kawai. Bashi ki ka ci, kuma gwamnati ma tana cin bashi, kema dan kin Wauki bashinsa ai ba wani abun bane. Haka kawai ya kawo ki ya ajjiye ki a gidansa, da ya bar ki ai da yanzu kin nemo kuWin. Dan haka ki Wauka kawai, Allah ya san baki da mafita ne._

Da wannan tunanin ta sake saka hannu ta Wauki guda Waya cikin wani irin yanayi na bugun zuciya.?

Ta sake mayarwa ta ajjiye tana furzar da iska, ta dafe kai tana tuna yanayin da ta ga Baffa a mafarki, kuma ta san tashin hankalin Satanta bazai bari su nemi kuWin aikin Baffa ba. Kuma ga kuWi tana gani, in ta Wauka ma ba sata ta yi ba, kuWin wahalar da ita da ya yi ne.

Islaha ta sake mi?a hannu ta sake Waukar kuWin, tana kallonsu a hannunta jikinta da zuciyarta suna rawa.

Ta Waga kai sama taga cctv tana Waukar ta, ta sake ajjiye kuWin gabanta yana faWuwa matu?a, abin ka da baka saba gani ka Wauka ba, duk ta ruWe ta firgice.

Sai ta kuma Wauka kuWin tana kallon camerar, ta nunawa camerar kuWin ta ce, "Aron kuWin nayi, ba satar maka kuWi nayi ba, zan dawo dasu in na samu. Ni ba Sarauniya ba ce, ban taSa sata ba. Wannan ma aro nayi, zan dawo maka dasu duk daren daWewa..... in ma ban dawo dasu ba, fansar wahalar da ka bani ce."

Sai kuma dafe kai ta ce, "To kuma ai baya jin hausa" ta faWa still tana kallon camerar.

Shams ya le?o ya katse mata tunani ta ce, "Yar jarida ke nake jira."

Ta zubura tana neman inda zata boye kuWin hannunta, shi kuma bai kawo komai ba dan ya san kaWan daga cikin aikin Rahaan ya bata kyautar kuWin.

A sanyaye ta Soye kuWin a rigarta tana takawa a hankali, sai kuma ta tsaya tana tunanin ta mayar da kuWin, tana sake tunawa sata ce ba bashi ba, zuciyarta tana sake zugata akan ta tafi da kuWin kawai ai kuWin fansar sace ta da ya yi ne. A haka ta saka ?afa ta fita daga falon.

Ta ganshi a tsaye a jikin range rover ba?a, ya buWe mata gaban motar shiga, ya zagaya ya shiga suka bar gidan gabanta yana faWuwa sosai, ta waiwayo tana kallon gidan tunawa da ta bar undies Winta a ciki.

_Hmm rashin mafita da neman mafita, ya kan ja mutum ya aikata abinda zai yi danasani. Kamar dai Islaha>?z?_


Nana Haleema
09030398006.
[6/19, 5:37/ PM] KRBBK: RDB2P12
Nana Haleema.

Tunda suka tafi take kallon hanyar, bata taSa shiga mota irin wacce take ciki ba, ji take kamar ba tafiya suke yi ba saboda daWin motar. Abin mamaki sai taji wayar jikinta tana ta ?ara alamun? shigowar sa?o. Tana dubawa taga services Win wayar ya dawo, abin ya bata mamaki, tana tunanin da gangan aka kashe mata services Win wayar kenan. Ta girgiza kai tana jinjina girman makircin mutumin, ta tabbata ba ?aramin mutum bane tunda ya saka aka kashe mata services.

Tana shiga camerar wayar sai taga ta daina nuna mata blank ta dawo aiki, ta ri?e haSa cikin mamaki da Waure kaita ce, "kai!."

Shamas ya juya ya kalle ta, ta girgiza kai tana kallon inda suke shiga suna fita, wani babban estate ne da dole ya rikita ka in baka san kansa ba, kusan gidajen duk iri Waya ne, layikan ma duk iri Waya.

"Ina zan kai ki?."

Ta wani kalle sa, irin kallon? ban sani Win nan ba ta ce, "inda ku ka Wauko ni."

Ya yi dariya ya ce, "?ar Jarida, kina bani dariya sosai."

Ta girgiza kai ta cs, "na baka dariya a yanzu, da na koma gida kuma zan baka kuka, dan kaine mutum na farko da zan fara kai ?ara, in yaso sai kazo ka faWi sunan ogan naku a kama shi shima."

Ya yi dariya yana ta mamakin rashin sanin fuskar Ogansa da bata yi ba ya ce, "kina tunanin a ?asar nan akwai hukumar da zata iya kama sa?."

Cike da gadara ta ce, "Shi ba mutum bane?."

"Mutum ne kamar kowa ?ar jarida, amma yana da ?arfin ikon da bazai kamu ba a ?asar nan ba."

"Hmm, za a fara daga kaina kuwa, in ban zama silar kama shi ba kace ba sunana Islaha ba."

Ya yi dariya bai ce komai ba, ?arfin halinta da rashin tsoronta ya burge shi, sai yake ji ina ma ta shiga harkar tsaro, ta zama jami'a a hukumomin tsaro na nigeria.

Islaha ta kalle sa ta ce, "Kai baka jin tsoron nayi maka hoto na nunawa ?an sanda fuskar ka?."

Ya Wan kalle ta ya ce, "wanda ki ka yi min fa? Ko kina tunanin banga kin Wauke ni a hoto ba?."

Ta bisa da kallon mamakin ya aka yi ya gane, ya yi dariya ya ce, "ba zauna gari banza bane ba ni ?ar jarida, na wuce tunanin ki. Kar ki ga ba kallon ki nake yi ba, ina sane da duk abinda ki ke yi." Ba tace komai ba tayi masa banza, sai gani tayi ya tsayar motar a ?ofar gidansu.

Ta kuma kallonsa ta ga Waure fuska kamar ba shine yake murmushi ba, ya nuna mata gidan ya ce, "ki shiga gida."

Bata ce komai ta buWe ta fita, sai da ta tabbatar ta fita daga motar, yadda ko sake kamata zai yi kafin ya fito ta shiga gida sannan ta ce, "ai daman zan shiga gidan, ba sai ka bani umarni ba. Kuma dukkan ku sai Allah ya saka min, kuma wallahi bazan bar maganar nan ta tafi a banza ba, ku jira na kammala abinda yake gabana ku ga abinda zan aikata. Sai na bawa ogan naka mamaki, sai na saka ya kwana a cell akan case Win nan. Mu zuba nu gani" tana gama faWa ta bar wajan da sauri ta shiga gida.

Shams ya bita da kallo yana dariya, ya girgiza kai ya ce, "Ko ina Oga ya samo wannan ?ar rigimar oho, yarinya kamar mai aljanu? Babu tsoro ko kaWan a idanunta." Yaja motar ya bar unguwar da gudu.


Islaha da sallama ta shiga falo, sai ta Wauke kai ganin abinda yake faruwa a cikin falon. Hanan ce da wani saurayi, tana zaune akan cinyarsa yana bin ko ina na jikinta da kiss.

Ganin Islaha babu zato sai ta zubara ta mi?e daga jikinsa, cikin borin kunya ta ce, "Islaha! Kin dwwo? Su waye suka sace ki?."

Takaici bai bari Islaha ta bata amsa ba ta wuce Waki ta kulle kanta. Ta ?arasa ciki a sanyaye, ta ajjiye kuWin da ta Soye a rigar ta, ta shiga wanka a gaggauce. Ta fi minti talatin tana wanka sannan ta fito ta shirya ta yi sallar azahar.

KuWin da ta ajjiye ta Wauka da wayarta, sai ta kai su hancinta ta ji ?hamshin turaren mutumin kawai suke yi, musamman wayar ta kamar shafa mata turaren ya yi. Ta yi tsaki tana hararar wayar, ta fita daga gidan da sauri.

Tana fita ta hangi motar Saleem a ?ofar gidansu Safeera, da sassarfa ta ?arasa ?ofar gidan, tana zuwa ta ga Saleem da Safeera a tsaye yana rarrashin Safeera tana ta kuka.

Islaha ta ce, "Safeera!."

Da hanzari Safeera ta juyo jin muryar Islaha, suna haWa ido tayi murmushi ta ce, "Hamma Saleem rarrashi ka ke yi kenan, to na dawo ai."

Safeera ta fito da sauri ta ce, "Islaha!" Tana faWa ta rungume ta cikin tsananin kewa da farin ciki.

Islaha ta yi murmushi ta ce, "na dawo, ki daina kuka."

Safeera ta Wago tana kallon Islaha ta ce, "Ina ki ka shiga? Su waye suka yi garkuwa dake? Ya aka yi suka sake ki ba a biya kuWin fansar ba?."

Ta kalli Saleem da yake kallon ta a rikice cikin mamaki ya kasa magana. Islaha ta ce, "kuWin fansa kuma? Wanne irin kuWin fansa?."

Saleem ya ce, "Islaha an kira mu an nemi naira miliyan ashirin kuWin fansar ki, ko mu bayar ko a kashe ki."

Ta Wan yi shiru tana nazafi kafin ta ce, "kuna ji, mu je asibiti wajan Baffa."

Saleem ya ce, "wajan ?an sanda ya kamata mu fara zuwa kafin mu je can."

"A'a Hamma Saleem, mu fara zuwa asibitin akwai abinda zan yi a can da gaggawa, in mun gama daga can sai muje duk inda zamu."

Safeera ta bita da kallon mamaki ta ce, "ni ban ga alamanun an yi garkuwa dake ba, gabaWaya baki yi kama da wacce aka sace ba. Islaha daga ina ki ke?."

"Duk za ku ji komai, muje kawai" ta faWa tana shiga motar Saleem, shima ya shiga yaja suka tafi asibiti.

A kan hanya ma bata ce komai ba har suka je asibitin, tana shiga wajansu Mama duk suka taso ana tambayar ta abinda ya faru. Bata basu amsa ba ta ce, "Lafiya lau nake Mama, ina Hamma Sadik?."

A lokacin Sadik ya ?araso ya ce, "Islaha! Ke ce?."

Ta Waga masa kai ta ce, "ni ce Hamma Sadik, ya batun kuWin aikin Baffa?."

"Mu fara da gama case Win nan naki, ya aka yi ki ka dawo? Waye ya sace ki?."

"Na fi so mu gama da batun aikin Baffa, in yaso komai sai ya biyo baya, kazo muje" ta faWa tana yin gaba ya bi bayanta da hanzari.

Sai da suka bar wajan sannan ta kalle sa ta ce, "ina takardar biyan kuWin aikin Baffa? An samu kuWin?."

Shi dai kallon ta kawai yake yi dan bata yi kama da wacce aka sace ba, duk da fuskarta a ta Wan kumbura kuma ta Wan rame, amma babu wahala a tare da ita ko kaWan. Ya kamata wahala ta bayyana a kan fuskar ta ko ya ya ne, amma shi bai ga wata alama da zata nuna ta sha wahala ba.

Ganin ya?i magana sai ta ce, "Hamma Sadik kai nake jira."

Ya Wan sauke numfashi ya ce, "Naira miliyan biyar kawai aka samu, ita ce kawai a hannuna a halin yanzu."

Islaha ta fito da kuWin daga jakar ta nuna masa ta ce, "wannan zasu isa?."

Gaban Sadik ya faWi ganin rafar one hundrend dollors cikakkiya a hannunta. Ya bita da kallo cikin wani irin yanayi na firgici da mamaki ya ce, "Islaha!.....A ina kika samu kuWin nan? Waye ya baki rafar dollors?."

Ta dafe kanta dan bata so maganar ta yi tsaho ta ce, "ka amsa min kawai Hamma Sadik, waWannan zasu isa?."

"Akan me zan amsa miki bayan ban san a inda ki ka samu ba?....Islaha meye haka ne? Me nake shirin gani a tare dake? Kin fara bani tsoro, an nemi rasa, kwatsam kin dawo da waWnanan kuWin a hannun ki, me yake faruwa haka?."

Islaha ta Wan yi tsaki, ta buWe datar wayarta messages suka fara shigowa kamar hauka, ta san daman za a samu haka, saboda ta jima bata buWe data ba, kuma ga yanayin da ta shiga wanda kowa ya ji labari, ta san za a dinga tura mata da sa?o. Wayar ta fara hooking, amma a haka ta shiga google ta yi converting one hundrend dollor to naira.

Bayan ta ga kuWin dala Wari, sai lissafa adadin kuWin hannunta gabaWaya, dala Wari-Wari sau Wari, ta ga kuWin hannunta miliyan sha bakwai ce da wani abun a lokacin.

Ita kanta sai da gabanta ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login