Showing 21001 words to 24000 words out of 221574 words

Chapter 8 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

111

?yale ta ba wallahi sai na faWa mata. Tunda baka jin magana, in ita ta yi maka magana zaka ji ai" yana gama faWar hakan ya kashe wayar.

Ya bi wayar da kallo yana taSe baki ya ajjiye ta a gefe yana rufe ido.

Tunda suka taho wajansa da Shams gabanta yake faWuwa, girman gidan ma tsoro yake bata, bata tsaya tana kallo ba dan ba kallo ne a gabanta ba.

A hankali take tafiya har suka ?arasa babbar ?ofar, Shams ya nuna mata ya ce, "in ki ka shiga yana falo a zaune."

Ta Waga kai ta ce, "na gode."

Bai amsa ba ya juya ya fita, ita kuma ta ?arasa wajan ?ofar a hankali.

?ofar a buWe take, ta tura a hankali sanyi da ?hamshin turarensa da ya gauraye waje Waya ya daki hancinta, ta Wan lumshe ido dan ?hamshin ya yi mata daWi, kuma sanyin bai yi yiwa yanayinta yawa ba.

Slowly ta shiga da sallama, tana sake gyara mayafinta dan gani take kamar tsirara ake kallonta.

Ya amsa sallamar a iya laSSansa dan bai bari ta ji ba, ta ?araso a hankali ta tsaya daga gefe tana ?arewa falon kallo.

Dakatawa ta yi daga kallon falon, ta kalle sa ganin ya canja shiga ba ta Wazu bace, yanzu ba?ar riga ce a jikinsa mai dogon hannu, sai ba?in jeans da ba?in slippers. Gashin kansa a sake, ya saka har wuyansa.

Ta Wauke kai daga kallonsa, ta Wan sauke numfashi tana tattaro nutsuwar ta gudun kar ya raina ta, ta sauke numfashi tana kallonsa.

Ta daure ta ce, "Ban san sunan ka ba, amma don Allah ka barni na tafi ina da abu mai mahimmaci wanda ban yi ba. Ban ga amfanin Wauko ni ka ajjiye ni a nan ba, iyayena suna can suna ta nemana cikin tashin hankali. Ban san me nayi maka ba, ban san me na aikata maka ba, ka bar ni na tafi gaban iyayena. Babana bashi da lafiya, za a yi masa dashen ?oda, ka bari na je a gama ya samu lafiya sai ka sake aikawa a Wauko maka ni."

A hankali take maganar babu rashin kunya ko tsiwa kamar yadda ta saba, shi kuma jira yake ya ji tace ya yi ha?uri, amma shegen taurin kai ya saka ta?i faWa. Tana cewa yi ha?uri ko minti goma baza ta sake yi a gidan ba zai saka a mayar da ita, in kuma bata faWa ba wallahi ta zo gidan kenan.

Ya Wago ya kalle ta ya ga kanta a sunkuye tana wasa da abin hannunta kamar wata mutuniyar kirki, ta wani nutsu kamar ba ita ba:

A hankali ya buWe baki kamar baya son magana? ya ce, "So......you can't say sorry for your mistake?."

Anya Islaha zata ce sorry Win nan?>?#?>?#?>?#?

Nana Haleema.
[6/18, 10:05/ AM] KRBBK: RDB2P09
Nana Haleema.

Kamar a sama haka ta ji maganar, ta Wago da sauri ta kalle sa sai ta ga kamar ba shine ya yi maganar ba, dan tunda ya sato ta bai taSa yi mata magana ba sai yanzu.

Da ta ji yadda ya furta maganar da english sai ta tabbatar da ba bahaushe bane, dan ko kaWan turancin sa bai yi kama da irin na wanda ya koya ba, kana jin yadda english Win yake fita ka dan yaren sa ne, kuma british english yake yi.

Ta Wan kalle sa kallon up and down, da ta tabbatar baya jin hausa, sai ta taSe baki ta ce, "Ji shi don Allah, wai jira yake na bashi ha?uri daman? To me na yi masa da zan basa ha?uri?" Ta faWa ?asa-?asa cike da mamaki ba tare da ta san ya ji ba.

Rehaan ya Wan Wago ya kalle ta suka haWa ido, ta Wauke ido dan ba ji yake yi ba. Ta mayar da idanunta gefw ta ce, "ji shi yana kallona, kamar ji me nake faWa. Ni dai bazan ba da ha?uri ba, sai dai ya kashe ni."

Rehaan ya girgiza kansa yana mamakin wannan yarinya mai kama da aljanu, ya Wauke kai bai ce komai ba.

Ta ce, "Ni ban yi laifin da zan bada ha?uri ba, kaine ka yi min laifukan da zaka bani ha?uri ba ni ba. Ka zuba min tea a hotel, ka kalle ni ka share kamar baka sanni ba. Ka fasa min wayata a asibiti, amma ka share ko sannu baka ce min ba, yanzu kuma ka sato ni ka kawo ni nan, kuma duk jira ka ke na baka ha?uri?. Lallai sannu Malam bature...Ko zan iya sanin sunanka?" Ta faWa tana kallonsa.

Bai motsa ba baice mata komai ba, ta Wan girgiza kai zata yi magana aka kira wayar sa. Ya kalli wayar sai ya Wauke kai bai Wauka ba ta cigaba da rining har ta katse.

Islaha ta ce, "kai! Daman waya tana aiki a gidan nan? Kenan ni aka kashewa services?" Ta faWa a hankali tana kallo wayarsa da waya ta kuma shigowa.

Wayarta ta gani a ajjiye a akan table, ta kalle sa ta ga kamar ya manta da ita a wajen a zaune, harda lumshe idanunsa kamar mai jin bacci.

Islaha ta ce, "bawan Allah baka ce komai ba, ka bar ni na tafi yanzu, duk abinda ka ke ji dashi a kaina daga baya sai mu tattauna."

Bai kalle ta ba dan bazai sake yi mata magana ba, ko me zata ce ya gama da ita, shi dai bazai yi magana ba. Ya mi?e zaune sosai yana sauke ?afa daga kan table ya Wauki wayarsa yana dannawa.

Hawaye ya sakko daga idon Islaha, ta tsani wula?anci a rayuwarta, musamman ta yi magana an jita kuma a share, yana daga cikin abinda yake tunzurata sosai, yanzu zata fusata ta birkice ta hau bala'i. Ta bi sa da kallo zuciyar ta tana tafasa sosai ta ce, "ka kashe ni mana kawai ka huta."

Bai ko kalle ta ba ya cigaba da abinda yake yi, sai daga baya ya kalle ta, ya ga ta zuba masa ido, ?iris take jira ta sha?e shi saboda takaici. Bai ce komai ba ya mi?e ya hau sama ya bar mata wajan bai sake kallon inda take ba.

Isaha ta bisa da kallo bata motsa daga inda take ba, yana Sacewa ta ?arasa ta Wauki wayarta ta danna taga tana yadda take, ta kalli saman wayarta amma har lokacin no services.

Abin ya bata mamaki, ganin shi gashi har waya tana shigowa wayarsa amma ita wayarta babu services. Inda ya tashi ta kalla, ta ga rafar dala Wari ne guda biyu a ajjiye, ta Wauke kai ta nemi waje ta zauna dan bazata fita ba, so take ayi ta ta ?are kawai, in zai barta ta tafi ya barta, in bazai barta ba ya faWa mata me yake nema da ita,

Shi kuwa yana hawa sama Shams ya kira a waya, yana Wauka ya ce, "Da gaske tana da mara lafiya?."

Shams ya ce, "yes Sir. Wanda yake ri?on ta za a yiwa dashen ?oda."

"Meyasa baka faWa min ba?."

Shams ya yi shiru dan bai san me zai ce ba, lokacin da ya yi niyar faWa masa shine ya dakatar dashi daga faWar, amma a yanzu ya san halin ogan nasu bazai taSa karSar uzurinsa ba.

Rehaan ya ce, "Is okay " daga haka ya kashe wayar ya zubawa madubi ido yana kallon kansa kamar mai son gano wani abun.

So yake ya ajjiye ta tayi shekara Waya a gidan bata je ko ina ba, so yake ya nuna mata waye shi ta tabbatar yana da ikon da zai iya Satar da ita daga duniyar babu abinda aka isa ayi masa.

So yake ya saka ta saduda, bakin tsiwar ya mutu, so yake ta zube tana bashi ha?uri tana ro?an ya ha?ura ya fitar da ita daga gidan. Bai Wauko ta don ya azabtar da ita ba, ko dan ya yi mata wani abun ba. Kawai iko yake so ya nuna mata, ta san waye shi.

Ya sauke nunfashi yana kallon kansa, saboda mara lafiyar da aka ce dole zai yi ha?uri ya ?yale ta, tunda har aka ce babanta ne, kuma yana da matsalar kidney ba abin wasa babe, babbar damuwa ce da ya kamata ya ha?ura ya janye ?udurinsa. Ya san daWin iyaye, ya san ya ake ji in basu da lafiya. Ba dan ta isa ba, sai dan girma da darajar iyaye, in ba dan haka ba sai ta shekara a gidan ko compound baza ta fito ba, sai ya nuna mata iko da matsayin da yake dashi.


Ya yi tsaki a bayyane ya ce, "amma bata bani ha?uri ba, sannan...." Sai ya yi shiru yana cigaba da kallon kansa kamar mai son gano wani abun a fuskarsa ko jikinsa.

Ya furzar da iska a bayyane, ya lumshe ido ya buWe, ya shafa gashin kansa yana Wan girgiza kai ya ce, "is okay Rehaan, stop this drama please, allow her to go, saboda lafiyar babanta. Allow her Rehaan."

Ya faWa yana rarrashin kansa, dan so yake ya nuna mata shima babban mai taurin kai ne da kafiya, duk rashin jinta ya fita, ba ita kaWai ta iya taurin kai ba, shima ya iya, ba ita ce mara kunya ba, shima ya iya. So yake kawai ta tabbatar ba kowa ake Wagawa murya a kwana lafiya ba, shiyasa yake rarrashin kansa akan ya barta ta tafi, rashin lafiya tana gaba da ?udurinsa.

Bakin gado ya koma ya zauna, ya Wauki wayarsa ya shiga camera falon da aka ajjiye ta yana ganin lokacin da suka yi magana da Shams da abinda take faWa masa. Ya ajjiye wayar ya rufe ido yana fatan bacci ya Wauke shi, amma da ya rufe ido sai ya tuna da ita, zuciyarsa tana faWa masa yanzu in ya bari ta tafi ta yiwa banza kenan. Ya ja numfashi da ?arfi, ya sake rufe ido ya rasa abinda ya kamata ya yi.

Islaha kamar mayya ta ?i barin falon, tana zaune akan kujera, daga ?arshe ta zame ta zauna a ?asa ta kwantar da kanta akan kujerar tana rufe ido cikin tunani kala kala da ya tokare mata zuciya.

Ta yi alwashin babu inda zata je, a wajan zata zauna sai da in ya dawo ya saka a kashe ta, ta gaji da rainin hankalinsa.

******

"Yauwa Malam Sadik. Tun Wazu nake neman ku. Na ga sanarwa an sace Islaha?" Dr Isma'il ya faWa yana kallon Sadik cikin damuwa.

Sadik ya ce, "Wallahi an sace ta, mun yi iya abinda zamu yi ba a ganta ba. An yi cigiya a inda aka san tana zuwa ba a same ta ba. Daga ?arshe wani mai napep yazo ya ce a gabansa aka Wauke ta."

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Kuma an kai repost wajen ?an sanda?."

"An kai Dr. A gaban ?an sandan ake faWar an ga lokacin da aka sace ta. Ana ta bincike a kan hakan."

"Allah ya bayyanata cikim aminci, Allah ya sa ba garkuwa aka yi da ita ba."

"Amin ya Allah."

Dr ya ce, "Akan maganar aikin mahaifin ku ne."

Sadik gabansa ya faWi, amma bai nuna ba ya ce, "Ina ji Dr."

"ya kamata a haWa kuWin aikin nan a kawo, sai kuWi yazo sannan zamu saka file Win ku a layin waWanda za a yiwa aiki. Duk da na faWawa wanda muke saka ran zai yi aikin, kuma ya amsa zai yi Win. Shine mai asibitin gabaWaya, na faWa masa zancen aikin ya ce na tuna masa ranar lahadi. Aikin mahaifin ku shine kaWai dashen ?oda da za a yi a ranar, dan haka dole ya kasance an shirya komai yadda ta kamata. Inda kuWin a hannun ku aje a biya yanzu, in aka biya zasu tura file Win, in ya ga komai ya tafi yadda ya kamata sai ya fi mayar da hankali akan aikin."

Sadik ya ja numfashi ya ce, "zuwa yaushe kenan?."

"Gobe ko jibi, ya kasance an biya kuWin. In aka biya kuWin ma kafin ranar, in ya san da maganar za a iya yin aikin a wuce wajen."

Sadik ya gyaWa kai ya ce, "in sha Allah za mu san abinda ya kamata mu yi, za a haWa kuWin kafin lokacin."

Dr ya ce, "Haka ya kamata ayi. In ka biya kuWin ka faWa min, duk da zasu tura min amma ka faWa min ta yarda zan sanar da Dr Win."

"Shikenan Dr, na gode" ya faWa yana mi?ewa ya fito jikinsa a sanyaye.

Yana ?arasowa reception ya ga su Mama suna jiran ya ?araso. Ya ?arasa suke ya ce, "Akan maganar kuWin aikin ne Adda, an ce ana so a biya kuWin daga gobe zuwa jibi. Kuma ni wallahi tunda Islaha ta Sace hankalina ya rabu biyu, har yanzu bazan ce ga abinda aka samu ba."

Adda ta ce, "ai dole hankali ya rabu biyu, ga aiki ga kuma Satan Islaha. Yanzu ya zamu yi?."

"Zan kira Saheer na faWa masa, ka kawo kuWin da ya tara a haWa a ga abinda za a yi. Daman ni da Islaha muka ce zamu karSi loan a bank, to bamu kai ga karSar bashin ba aka neme ta aka rasa."

Mama ta ce, "ba kace za a ba da jinginar gida ba?."

"Wallahi Mama an rasa wanda zai karSa ya bamu kuWin. Abin ne sai a hankali, mutane babu yarda a lamarinsu. Amma zamu yi magana da mai gidan mu ni da Saheer, ko gidan ne ya karSa ya bamu kuWin, tunda har aka fara haka gwara ayi aikin a huta kawai."

Adda ta ce, "Ta ya miliyoyin kuWi zasu fito a wanann lokacin?."

"Mu cigaba da addu'a Allah zai dafa mana."

Mama ta ce, "Duk da haka Sadik, sai mun nema sannan Allah zai dafa mana. Baza mu zauna mu naWe ?afa mu ce Allah ya kawo mana wannan kuWin ba, dole sai mun fita mu nema."

Sadik ya yi ajiyar zuciya, sun kasa gane ruWanin da yake ciki ya ce, "In Allah ya yarda za a san yadda za a yi, tunda muka shigo nan ai baza mu fita ba, iya kuWin wankin ?odar da ake yi masa ma zaman kansa yake yi, dole mu biya su kafin mu tafi." Suka yi shiru kowa yana tunani, ya bar wajen ya tafi wajen Saleeem da yake yi masa waya.

Yana zuwa ya same shi a compound Win asibitin, ya ?arasa ya ce, "Saleem ya ake ciki akan maganar Islaha?."

Saleem ya ce, "Wallahi babu wani update, har yanzu shiru, babu wanda ya kira ni a waya yace an ga mai kama da ita balle ita. Zuciyata tana faWa min anya ba yan garkuwa da mutane ne suka Wauke ta ba?."

"Wallahi tunanina kenan nima, bana so na gasgata ne. Ga Baffa, ana neman kuWin aikinsa daga nan zuwa gobe. Daman Islahan ce mai taimakmin akan neman kuWin, gashi ta Sace bamu san inda take ba. Abin ya yi min yawa, na rasa wanne irin tunani zan yi. Mama ta kira ni, Adda ta kira ni, dangin Baffa su kira ni, Saheer ya kira ni, gabaWaya na ruWe."


"Gaskiya ne, kana cikin ruWani mai yawa. Allah dai ya bayyana mana Islaaha, ya ba da ikon samo kuWin nan."

"Amin. Amma tun farko mun san asibitin nan ya fi ?arfin mu, ?arfin zuciya da karanbani ne ya saka muka kai har yanzu a cikinsa."

Saleem ya ce, "to ya za a yi? Haka Allah ya rubuta zai faru."

Wayar Sadik ta fara ?ara, ya Wauko wayar ta ga ba?uwar lamba ce, a yanayin da suke ciki na jiran waya ko yaushe baya ?in Wauka, ya Wauka ya saka a speaker ya ce, "Hello."

Daga cikin wayar aka ce, "Muna magana da Sadik, abokin Saheer, saurayin Islaha?."

Gabansa ya faWi sosai, ya kalli Saleem da yake sauraren wayar ya ce, "eh ni ne."

"Islaha tana hannun mu, mu ne muka Wauke ta."

Gaban Sadik ya faWi matu?a, cikin wani irin yanayi ya haWWiye yawu ya kasa magana.

Daga wayar aka ce, "Muna bu?atar kuWin fansar ta naira miliyan ashirin, ko a bayar ko kuma mu kashe ta!."

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Sadik ya faWa cikin firgici yana saurare su.

"Kai kawo ta su ji muryar ta, dan su tabbatar da ita Win ce a hannun mu."

Sadik ya nutsu yana so ya ji maganar Islaha, sai kuwa ga muryar ta ta ce, "Sadik!."

Gabansu ya faWi sosai, tashin hankalin da bai taSa ji ba yana ratsa shi, kafin su yi magana ya ce, "In an shirya kuWin zamu faWa muku yadda za a yi dashi. In ku ka saka hukuma a cikin maganar wallahi sai mun kashe ta!" Yana gama faWa ya kashe wayar........
[6/19, 10:26/ AM] KRBBK: RDB2P10
NanaHaleema.

Sadik da Saleem baki a buWe suka bi wayar da kallo dukkansu cikin ruWani da tashin hankalin da basu taSa shiga irinsa ba. Ko a mafarki basu taSa tunanin za a yi musu irin wannan wayar ba, sai gashi ta faru a lokacin da suke tsaka da tashin hankali.

Suka yi shiru na wani lokaci kafin Sadik ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Saleem kaji abinda suka ce fa."

Saleem ya sauke numfashi mai nauyi ya ce, "na rasa abinda zance ne Sadik, abin ya Waure min kai. Muna jin irin wannan kalaman a wani waje, yau gashi yazo kan mu. Yanzu ya za a yi?."

"Mu je mu samu Dpo mu faWa masa, babu zancen kar mu saka hukuma a maganar, dole mu saka su saboda mafita mu ke nema."

"Amma sun ce in aka saka ?an sanda zasu kashe ta, bai kamata mu saka hukuma a ciki ba."

"To Saleem muna da kuWin da zamu basu ne? Da kuWin fansar ta zamu ji ko da kuWin aikin Baffa? Yanzu na faWa maka halin da ake ciki akan aikin, gidana da nake ginawa, dana Saheer da yake yi zamu siyar a samu ayi abinda ya kamata akan lafiyar Baffa. Ban san taustsayin da ya kawo mu asibitin nan ba wallahi."

Saleem ya ce, "to mu je mu samu Dpo, Allah yasa bai tashi ba, dan dare ya yi."

Har Sadik ya Waga ?afa zai fara tafiya ya ji wayar sa tana ?ara, yana dubawa ya ga Saheer ne, ya dafe kai ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Saheer ka yi ha?uri bazan iya Wauka ba" ya faWa yana kashe power wayar.

Ya kalli Saleem ya ce, "Saheer indai akan Islaha ne baya fahimtar komai, ba ya ji baya gani. In ya samu mummunan labarin nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login