Showing 195001 words to 198000 words out of 221574 words

Chapter 66 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

158

rainin hankali ta ce, "Ai ban san arhar ta ka ta kai haka ba, ban san rashin class da ?aryar iyayin naka a nan ya tsaya ba. Tunda aka Wauko tallan auren ka, aka zo har gida aka samu mahaifina, ana neman na amince na taimaka na aure ka, ka dawo zero percent a idanuna..."

"Ka jira lokacin da aka kai maka tallan Islaha, daga lokacin ne ka ke da bakin cewa ta canja tunani, amma daga lokacin da aka je aka zauna da mahaifinta, aka ce an gani ana so na amince nace ina yi, na fi ?arfin waWannan kalaman na kan harshen ka. Ba ni da lokacin Satawa, ka bar maganar, dan bazai yu ba har abada!."

Shiru ya yi bai ce komai ba, zata sake magana ya buWe idanunsa cikin nata ya ce, "shut up! Bana bu?atar ki yi magana...."

Ya nuna ta da yatsa ya ce, " Kin yi nasarar shiga rayuwata, kin yi nasarar da ki ka saka iyayena suka amince dake, kuma kin yi nasara ina yia iyayena biyayya akan duk abinda suka ce na yi."


Zata sake magana ya katse ta ya ce, "I will marry you for five months as a contract, because of my father's command."

Banzan kallo ta yi masa sannan ta ce, "bana bu?ata, bani da ra'ayi balle har na aure ka na zauna da kai a ?ar?ashin contract. Ka je ka samu wata amma ba Islaha ba, ita tace bata yi ka ha?ura ko ka yi danassani. She's not your type, and she's not your class. An kawo min talla na ce kuma bazan siya, a kai wani gidan zasu iya tayawa!."

Ta kalli Jafar da yake kallon ikon Allah, duk da ba Waga murya take yi in tana maganar ba, amma ya san maganar tana shigar Rehaan. Shi dai yana so ya ga an yi auren nan dan ya ga ya abin zai kasance, amma ya san abu ne mai wahala matu?a wajan yuwar auren.

Islaha ta kalli Jafar ta ce, "please ka saka a mayar dani, bana son tsayuwa a nan ko kaWan."

Jafar ya mi?e yana murmushi ya kalli Rehaan da kamar bai san abinda aka yi ba.

Ya buWewa Islaha ?ofa ya ce, "ki je mota, zasu mayar dake Miss."

"Na gode....."

Ta Wan waiwayo tana kallo Jazy, ta nuna masa Rehaan da hannu sannan ta ce, "Ka faWa masa kar ya sake gangancin sace ni, ni ba toy ba ce da zai Wauko duk lokacin da ya ga dama, ni ba sa'arsa ba ce, ya sace wasu ya zauna lafiya, amma ban dani. Maganar aure kuma a kai tallah social media, a rabawa bloggers details Winsa wata?ila a dace, baza a rasa masu bu?ata ba. Wannan Islahan ta Saheer ce, ya je ya dage ya cigaba da advert, zai iya dacewa wata ?ar wahalar ta gani ta ya, amma ba da nan" ta faWa tana nuna kanta sannan ta juya ta fita da sauri.

Wai ta ya auren nan zai yu ne? Rehaan ya Sullo da auren yarjejeniya, ya abin zai kassance ne?=؃??#?
[7/28, 12:20/ PM] KRBBK: RDB2P89
Nana Haleema.

Jafar ya kalle shi bayan ta fita ya ce, "Rehaan wanne irin auren yarjeniya kamar a america? Meye hakan?."

Bai kalle sa ba sai shiru da ya yi ya zubawa waje Waya ido, yana tuna kalamanta yana jin zafi a ransa, kuma ba kowa ya jawo masa wannan rainin ba sai Abba.

Jafar ya Wauki takardar da ya ajjiye ya ga takardar contract Win ce, har ya tsara rules da komai, an yi printing, ga inda zata saka hannu ga inda zai saka hannu.

Jafar ya kalle shi cikin fusata ya ce, "wani lokacin in ka yi wani abun kamar a rufe ka da duka wallahi, yanzu meye wannan don Allah? Kana musulmi gaba da baya za ka wani ?ir?iri auren yarjejeniya?."

Ya Wago ya kalle shi ya ce, "Na yiwa Abba al?awari, Abba bai taSa neman abu a wajena ba sai wannan lokacin, kuma na ce zan yi. Ka fi kowa sanin bana son auren nan, kuma bazan so ba, bana son yarinyar, kuma bazan so ta ba. Gwara a gina auren a ?ar?ashin contract, in na san auren yana tafiya akan lokacinsa zai fi min sau?i."

Ya girgiza kai ya ce, "hakan bai kamace ka ba ko kaWan, bai kamata ka gina auren a ?ar?ashin yarjejniya ba. Kuma in na yarjejeniyar ne, ina laifin na shekara Waya, sai ka saka wata biyar?."

Ya Wago ya kalle sa ya ce, "kwana na yi ina tunanin maganar nan, ban taSa tunanin wani abu a rayuwata kamar wannan ba. Wata biyar Win ma ya yi min yawa, in kwanakin basu yi ?asa ba bazai yi sama ba."

Jafar ya ce, "to ga shi nan ai ta ?i yarda."

Ya Wan girgiza kai ya ce, "daman saboda Abba nake yi, kuma ya ce baya so ya ji wata matsala daga side Wina, in daga Sangarenta ne wannan bai dame ni ba daman ba so nake yi ba. Me zan yi da wannan abar?."

Jafar ya murmusa ya ce, "Ikon Allah, ni dai zan ga ta wannan abin nan zai yu."

"Shiyasa nake ji kamar na je na matse tsohuwar can na zuba mata poison ta haWWiye ta mutu. Allah ban taSa jin haushinta kamar wannan lokaci ba."

Ya yi dariya ya ce, "gaskiya dai, haka kawai ta Wauko maka aure."

"Auren ma da wannan yarinyar, wacce ta gama...." Jafar ya yi dakatar dashi ya ce, "za ka yi bayani da larabci a gaban Allah, babu ruwana."

Ya girgiza kai Jafar ya cigaba da karata rules Win takardar, ya kalle shi ya ce, "auren ka bazai zama na sirri ba fa, dole za a sani."

Ya girgiza kai bai ce komai ba Jafar da yake kallon abinda yake cikin takardar ta ce, "wannan aure dai za ku gina shi akan abinda ku ka ga dama ne, babu ruwan wani da wani kenan?."

Rehaan bai ce masa komai ba, Jafar ta gama karanta takardar kafin ya ajjiye masa ya mi?e ya shiga ciki. Shi kuma Rehaan fita ya yi daga gidan yana so ya je inda dangin Mamy suka sauka.

Islaha tana fitowa ta ga ba?ar motar tana jiranta, ta kalli mutumin da ya tare ta a daren jiya yana cewa ta shiga motarsa. Ba dan bata san hanya ba wallahi babu abinda zai saka ta shiga motar, ta yi ?wafa ta shiga suka tafi.

A ?ofar gidan suka ajjiye ta, tana sauka daga motar suks haWa ido da Sadik shi da Safeera sun fito daga gidan.

Ta ?araso wajan duk kallonta suke yi Safeera ta ce, "Daga ina haka?."

Islaha ta kalle su ta ce, "wani waje."

Safeera ta ce, "ina ne wajan?."

Ta kalle ta sannan ta kalli Sadik ta ce, "in na faWa mu ku ba yarda za kuyi ba, za ku ce ?arya nake yi. Gwara na yi shiru da maganar."

Safeeta ta ce, "baza mu ?aryata ki ba, ki faWa kawai."

Ta Wan shiru kamar mai tunani sannan ta ce, "ina zuwa, bara na yi sallar la'asar" ta faWa tana shiga gidan suka bita da kallo.

A zauneta same su a harabar gidan cikin inuwa, ta ?araso ta zauna ta ce, "Hamma Sadik ya batun mutanen nan? Sun sake yin wayar ne?."

Ya girgiza kai ya ce, "basu yi ba, har yanzu shiru."


"Batun kuWin fa."

"To an dai saka gidan nan a kasuwa, har yanzu ba a samu masu siya ba wallahi. Gona dai an taya, muna jira mu ji ko zasu siya."

Islaha ta ta yi shiru bata ce komai ba. Safeera ta ce, "muna jin ki."

Ta Wago ta ce, "Ban san me yasa ba, amma ina ji a raina akwai wani abun ba daidai ba."

Safeera ta ce, "na me kenan?."


"Akan Baffa nake magana, washe garin ranar da aka rasa Hamma ya kira ni wai wasu sun zo neman aurena kuma ya amince musu, dan kar ya bada ni ne naga kamar bai kyauta min ba, amma da yanzu ya ce ya basu ni."

Sadik ya ce, "Nima ya faWa min maganar."

Ta Wan kalle sa ta ce, "ashe ka sani ma. Ban san meyasa Baffa ya yi haka ba, kamar ya manta da Hamma? Kamar ba shine yake cewa zai aurawa Hamma ni na kusa ba."

Safeera ta ce, "wai Baffa da kansa ne ya ce haka?."

"Shine."

"to ya batun auren ki da Hamma?."


"Nima ban san meyasa ya ce haka ba, ban san meyasa Baffa ya canja ra'ayinsa akan aurena da Hamma ba. Abinda na sani ko waye bazan amince ba, auren Hamma ya fi min auren kowa a duniyar nan. Duk kuWin mutum ba ya gabana, indai Hamma yana da rai ni mallakinsa ce."

Sadik ya numfasa ya ce, "abin ne da Waure kai, ba a satin nan Baffa ya ce zai Waura auren ku ba?."

Islaha ta ce, "juma'a mai zuwa ya ce, amma yanzu an canja ya koma wani daban ba shi ba."

Ya Waga kai ya ce, "Kuma na tabbatar Saheer Win bai sani ba, kuma wannan maganar cutar dashi zata yi ba kaWan ba."

Islaha ta ce, "shine abinda nake ji, tsakani da Allah ta ya za a ce haka?."

Safeera ta ce, "Wai waye wanda za ki aura Win? Su waye suka zo neman auren ki?."

Ta Wan kalle su sai kuma ta ja tsaki ta ce, "Lokacin da ya faWa min bai faWa min sunan waye ba, ya dai faWa min sunan mahaifinsa mutumin. ?an gidan Alhaji AbdulAziz Yola ne."

A tare suka zaro ido waje cikin mamakin sunan wanda ta faWa Sadik ya ce, "kai! Wai shi ne da kansa ya aiko nemawa Wansa auren ki?."

Islaha ta ce, "abin kamar plan ko? Ni kaina ina ganin abin kamar tsarawa aka yi."

Sadik ya ce, "Gaskiya akwai ayar tambaya a kan maganar nan."

"Ni dai taimako bai yi min rana ba, haka kawai na tsinci wata tsohuwa a hanya na taimaka mata, ashe wai itace babar AbdulAziz Yola Win."

Safeera ta ce, "Gaskiya dai lamarin nan kamar plan, kawai dan kin taimaka mata sai a aura miki jikanta?."

Sadik ya ce, "Wanne Wan nasa a cikin yaran? An ce yaransa kaf suna da aure, wanne daga ciki ne zai ?ara aure a cikinsu?."

Ta Wan yi jimm tana tunanin ta faWa musu ko ta yi shiru, ta kalle su ta ga duk ita suke kallo alamun suna jiran amsa.

Sai ta Wan ja tsaki ta ce, "ku share kawai, sanin waye ba shi da mahimmaci a halin da mu ke ciki. Yanzu ma da ku ka ga an sauke ni a mota shi mutumin ne ya saka aka kai ni can...."

Sai ta kalli Safeera ta ce, "Jiya da wani yake bina yana cewa na zo na shiga mota? Ta faWa da sigar tambaya.

Safeera ta ce, "eh."

"Ashe shine ya aiko shi wajena. Har yana faWa min mahaifinsa ne yake son auren ba shi ba, shi bazai aure ni dan yana so ba, dan haka zai aure ni saboda mahaifinsa ya ce ya aure ni. Mtsw! Sai ka ce an faWa masa nima aurensa zan yi, ko maza sun ?are a duniya ba gwara na mutu babu aure ba, balle ina da Hammana."

Sadik ya ce, "Ba ki faWa mana waye ba."

Ta Wan sake yin shiru kafin ta ce, "ba shi da wani mahimmaci, ku manta kawai. Mu caigaba da neman kuWin fansar Hamma." Suka cigaba da tattaunawa akan yadda za a yi.

Islaha abu kaWan sai ta yi tsaki saboda takaicin Rehaan, a haka suka gama zaman basu samo mafita ba, ta shiga gida Safeera ta tafi shima ya tafi gida.

Rehaan tunda ya shiga gidan da dangin babarsa suke yake jin kansa cikin ?anci da walwala. Dukkansu indiyawa ne, gabaWaya basa jin wani yare in ba hindi ba sai english. Har gwara Yayar Mamy tana iya yin hausa kaWan-kaWan.

Suna ta hira gabaWaya, sun hanashi motsi kowa yana bashi labari ana bashi tsarabar da aka kawo masa. Shi dai tana kusa da Mamy a zaune, sai Yayar Mamy a zaune a gefensa sun saka shi a tsakiya.

Yana murmuahi ya ce, "Fateema bata zo ba?."

Mamy ta ce, "Tana wajan aiki, ta ce aiki ya yi mata yawa, amma ta ce zata zo."

Ya Wan gyaWa kai bai ce komai ba yana kallon su gabaWayansu. Yayar Mamy mai suna Sanah ta ce, "ga mu gabaWaya mun haWu, amma babu Sofia, ko tana da rai, ko bata da rai Allah ne ya sani."

Rehaan ya ce, "Mama wai meye silar barinta cikin ku? Ya aka yi ta Sata har aka neme ta aka rasa?."

Wacce ya kira da Mama ta ce, "Tunda mahaifiyarka ta auri Wan Nigeira kuma bafutalani take sha'awar auren irinsu. GabaWaya sai aka ?i bata goyan baya kamar yadda aka bawa Mamy goyan bayan auren mahaifin ku...."

Ta Wan sauke nunfashi kaWan ta ce, "Shine aka wayi gari ta bar gida, daga baya sai ta tura mana hotunan Waurin aurenta da mijin. Amma ita mijin ta Wan Kano ne ba nan ba, mun nemi ta dawo bata dawo ba, kuma bata faWa mana inda take ba. Tun muna samunta a waya har muka daina, mu neme ta ko ina bamu samu ba. Gashi bamu san mijinta da ahlinsa ba balle mu neme ta. Shekarun da yawa, dan ba a jima da haihuwar ka ba aka yi hakan.

Rehaan ya Wan yi shiru sannan ya ce, "in tana da rai za a ganta wani lokacin, in bata da rai kuma Allah ya nuna mana ahlinta in ta bari."

Ya ri?e hannun Mama da Mamy ya ce, "ku cigaba da addu'a, Allah zai bayyana ta."

Sanah ta shafa kansa ta ce, "Allah ya sa." Ya Wan yi murmushi kawai.

Sanah ta ce, "ashe da kai za a haWa ayi auren."

Ya Wan sauke kai ?asa kafin ya ce, "Mama bana so kowa ya san da maganar nan, zan bi umarnin Abba ne ba dan ina so ba."

Sanah ta Waga kai tana shafa kansa ta ce, "Allah ya cigaba da Waukaka ka." Suka amsa da amin kafin ya yi musu sallama ya tafi bayan ya ci abinci.

Da daddare Baffa ya kira Islaha akan maganarsu, Islaha ta shiga da sallama ta zuna akan carpet.

Ya kalle ta ya ce, "Islaha mun yi magana ranar nan ba ki ce min komai ba, ni kuma ina jiran amsar ki na ke yi."

Islaha ta kalli Baffa ta ce, "Baffa wacce magana kenan?."

"Akan auren ki da Wan AbdulAziz Yola, ranar juma'a suke son Waura auren."

Ta sunkuyar da kai ta ce, "Baffa don Allah ka daina faWar maganar nan, in wani laifi na yi maka ka ke so ka aurar dani ga wanin Hamma don Allah ka yi ha?uri ka yafe min. Baffa in kuma shine ya yi maka laifi har ka ke so ka aurar ga waninsa don Allah ka yafe masa, amma ka daina faWar maganar auren don Allah."

Baffa ya Wan yi shiru yana kallon ta sai ya yi sauke ajiyar zuciya ya ce, "Islaha Saheer ba ya nan, babu lallai ya dawo, ni a jikina nake jin Saheer ya tafi kenan, sai dai mu yi masa fatan Allah ya sa ya cika da imani."

Islaha ta Wago kai ta kalli Baffa hawaye ya sakko daga idonta, ta girgiza kai ta ce, "Baffa Hamma bazai mutu ba, ka daina faWa don Allah."

Baffa ya ce, "Islaha kalle ni."

Ta Wago a hankali ta kalle sa sai ta sauke kai ?asa saboda biyayya bata son kallon idanunsa.

Baffa ya ce, "A wanne matsayi ki ka Wauke ni a duniya?."

Muryar ta tana cracking ta ce, "a matsayin mahaifina, ban san waye ya haife ni ba, kai nake kallo a matsayin mahaifi wanda ya kawo ni duniya."

Baffa ya ji daWin amsar ta sannan ya ce, "To ki yarda bazan yi miki zaSi wanda zai cutar dake ba. Na fi kowa ?aunar auren ki da Saheer, na fi kowa son ki auri Saheer saboda yadda nake son tarbiyyar ki, ina ?waWayin ki amsa sunan ?ata kuma matar Wana, in ?waWayin na samu iri daga jinin ki. Islaha tunda ki ka ji na janye kalamaina akan auren, tunda ki ka ji na ce ga wani ba Saheer ba, kin san ina da ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????hujja mai ?arfi akan hakan. Ko kina ganin zan cuce ki ne?."

Ta girgiza kai tana hawaye, ta kasa magana sai hawayen da yake sakko mata, kalaman Baffa hr jininta take jinsu.

Baffa ya ce, "To ki saka a ranki ina guje miki faWawa inda za ki sha wahala ne shiyasa na zaSi wani na bar Saheer. A matsayina na uba a gare ki, bazan so na ga za ki faWa wuta na ?yale ki ba, duk yadda zan yi zan ri?e hannun ki na tabbatar kin wuce ba tare da wutar ta taSa ki ba."

Islaha ta yi shiru bata ce komai ba tana goge hawaye ta kasa magana kwata-kwata.

Baffa ya ce, "Ki yi ha?uri, na san kina son Saheer, kuma kina burin mallakar Saheer a matsayin mijinki. Kuma na san abin zai zo miki bazata, amma nan gaba za ki gane abinda nake hango miki a yanzu. A yanzu bazan amince da auren ki da Saheer ba, ko da yana nan bazan yarda ya aure ki ba balle kuma baya nan. Masu garkuwa da mutanen nan in suka kama kashewa suke yi, ni jikina yana bani bazasu taSa sakin Saheer ba. Shiyasa nake so ki amince da abinda na zo miki dashi, dan ni na ari bakin ki na ci albasa, na sanar da su kin amince."

Iskaha ra fashe da kuka mai sauti ta rarrafa ta ri?e ?afar Baffa ta ce, "Baffa Hamma ba ya nan, an sace Hamma, an yi garkuwa dashi ana neman kuWin fansa. Don Allah Baffa ka bar maganar nan, ni bazan iya auren wani in ba Hamma ba, bazan iya yin aure Hamma ba ya nan ba, ko da yana nan bazan iya kallon wani namiji a matsayin mijina ba in ba shi ba. Don Allah Baffa ka daina faWar za ka aurar dani ga wani, don Allah ka bar maganar nan, tana saka min bugun zuciya."

Baffa ya bita da kallo ganin yadda take kuka da zuciya da jikinta, sai ta ba shi tausayi mai tsanani, amma duk da haka ba ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login