Showing 162001 words to 165000 words out of 221574 words

Chapter 55 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

142

ta ja ?wafa ta ce, "to sai ki bar min gidana, ai ba da kuWin ki aka gina gidan ba ko?."

Islaha bata ce komai ba, ta mi?awa Mama tsarabar da ta siyomata ita da Hanan ta ce, "Ga tsarabar Jeddah, babu yawa."

Hannan ta ja ledar tana buWewa ta ce, "Lallai Mama da gaskiyar ki, wanda ya je aikatau ina shi ina tsaraba? Gaskiya da walakin goro a miya."

Mama ta kalli kayan ta kalle ta ta ce, "bazan ?i karSar kaya ba, amma zama a gidan nan ne baza ki yi ba, ki je ki nemi wajen zama, amma ban da gidan nan."

"Wa nake gani kamar Islaha!."

Islaha jin muryar Baffa a bayanta sai ta mi?e tana murmushi ta ce, "Ni ce Baffa."

Baffa ya zauna yana kallon ta da fara'a ya ce, "Islaha saukar yaushe?."

Ta zauna a?asa ta ce, "Tun Wazu na dawo, ina gidansu Safeera. Ya ?arfin jiki Baffa?."


"jiki ya warware Islaha, na ji sau?i kamar ban yi ba."

"Allah ya ?ara lafiya Baffa."

"amin Islaha. Ina kwance sai na nemi ki na rasa, sai da na dawo nake jin labari mara daWi. Me yaasa ki ka biyewa zuciya ki ka bi shanun sarki? Meyasa ki ka amince dar huWubar waWanda basu cancanci a ji kalaman su ba balle a Wauka?."

Islaha ta san Baffa da Mama yake maganar, sai ta Wan yi murmushi ta ce, "Baffa wani abu ne ya kaini, kuma shine ya dawo dani."

Baffa ya ce, "na ji daWi da ki ka dawo lafiya, daga ganin ki an san ba ki sha wahala ba. Ki shiga ciki ki kwanta."

Mama ta ce, "tunda ni ce shanun sarkin, baza ta shiga ta kwanta ba, ta tafi wani wajan amma ba nan ba."

Baffa ya ce, "a nan zata zauna, in kin ga Islaha ta bar gidan nan to ta yi aure, in kuwa bata yi aure ba bata da wani gida in ba nan ba."

"Bazan ajjiye wacce ta je ta gama wayon duniya a gidana ba. A ina ta samu kuWin da ta biya kuWin da aka kaita harda na dawowa gida da tsaraba?."

"Cewa ki ka yi a gidan ki, kin ga nan ai ba gidan ki bane. Sai ki jira ki gina na ki, daga lokacin sai ki hana duk wanda ki ka dama zama a cikinsa, dan wannan kam ba gidan ki bane."

Baffa ya kalli Islaha ya ce, "Safeera jeki ki rakata Waki."

A sanyaye suka wuce zuwa Wakin Islaha suka tarar dashi yana nan yadda yake, sai dai ya yi ?ura sosai.

Safeera ta ce, "ki fita, bara na gyara miki, na ji har kin fara tari."

Islaha ta ce, "Bara na mi?awa Baffa wannan Win sai na dawo." Safeera ta fara gyara mata Wakin ita kuma ta fita da tsarabar Baffa.

Da sallama ta shiga wajan Baffa, ya amsa yana kallon ta da murmushi, ta dur?usa ta ce, "Baffa ga tsarbar da na siyo maka."

Ya klli kayan ya ce, "Tsaraba kuma Islaha! Ke da ki ka je aiki maimakon ki adana kuWin ki sai ki yi tsaraba?."

Ta yi murmushi ta ce, "Babu yawa Baffa."

Baffa ya ce, "Na gode Islaha, Allah ya yi miki albarka."

"Amin Baffa."

"Ki cigaba da ha?uri, kar ki biyewa Maman ku, ki kau da kai ki cigaba da zama jiran lokaci. Tunda kin dawo auren ku bazai wuce sati biyu ba, gwara ta daina ganin ki a huta."

Ta yi murmushi ta ce, "Babu komai Baffa."

Baffa ya ce, "Jeki ki huta."

Ta mi?e a sanyaye, Baffa ya ce, "Ina Labiba da Maimuna?."

Gaban Islaha ya faWi, ta dawo ta du?a ta ce, "Duk suna gaishe ka."

Baffa ya murmusa ya ce, "gwara da ki ka yi dawowar ki, ni zuciyata bata amince da zaman nan ba, kuma ban taSa zargin za ki aikata wani abu mara kyau ba, ko yaushe kyakykyawan fata nake yi miki. Tashi ki je ki huta, Allah ya cigaba da dafa miki."

Islaha ta amsa da amin, sannan ta mi?e ta fita ta koma wajen Mama. Tana shiga falo suka haWu da Mama, ta bita da kallon sama da ?asa ta ce, "ya ba ki goyan bayan zama a gidan nan, kina zaune kina zaman jiran Saheer ya aure ki ko?."

Islsha ya sukuyar da kai bata ce lomai ba, Mama ta ce, "indai ni na haifi Saheer wallahi bazai aure ki ba, in kuwa ya zaSi ya aure ki sai dai ya nemi wata uwar bani ba."

Islaha ta Waga ido ta kalle ta jin abinda ta ce, Mama ta buWe idanu waje ta ce, "kalle ni da kyau, buWe idonki cikin nawa. Wallahi bazai aure ki ba, in kuwa ki ka ga kin aure shi to ki tabbatar bana numfashi!."

Islaha ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, ta Wan motsa zata bar wajan Mama ta ri?o ta ta ce, "ki daina ganin yana ba ki goyan baya, ga dai gida nan ki zauna, amma ban da auren Wana."

A hankali ta bar wajan ta shiga Waki, ta tarar Safeera ta gyara shi ta zauna akan gado ta yi shiru.

Safeera ta ce, "Ya dai?."

"Kwana biyu na fara mantawa da damuwar Mama, hankalina ya kwanta, kunnena ya daina ji min ba?a?en maganganu irin na Mama. Daga dawo ta yau na fara fuskantar ?alubalen da na bari. Ya zan yi da Mama? Me na yi mata bata sona?."

Safeera ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Ina jinta, duk abinda ta faWa na ji, amma bata isa ta hana abinda Allah ya nufa ba."

Islaha ta yi shiru bata ce komai, Safeera ta gama yi mata abinda zata yi sannan ta kalle ta ta ce, "zan koma gida, zan bar ki ki sake hutawa. Amma gobe ki tabbatar sai kin ?arasa bani labari."

Islaha ta kalle ta ta ce, "Gobe za kiraka ni opharnge, ina da bu?atar yin bincike akan inda Zainab ta tafi."

"Allah ya kaimu. Aiki fa?."

"Ba gobe zan koma ba, sai na huta." Safeera ta Waga kai ta yi mata sallama ta fita.


Ya ku ke ganin rantsuwar Mama? Zata karye ko baza ta karye ba?.....

_Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.=?O?
Nana Haleema.
[7/21, 12:05/ PM] KRBBK: RDB2P73
Nana haleema.

Washe gari Islaha bata bari sun haWu dasu Mama ba ta bar gidan ko karyawa bata yi ba. Islaha da Safeera suka haWu suka tafi gidan marayu kamar yadda ta ce.

Tun da suka je gate take gaisawa da da ita har ciki gidan. Office Win Mama suka je, aka ce ta fita bata nan, hakan ya saka Islaha ta tsaya ta rasa abinda zata yi.

Tana na tsaye sai ga Waya daga cikin ma'aikatan gidan, ganin Islaha a tsaye sai ta ce, "?ata Islaha."

Islaha ta kalli matar, sai ta yi dariya ta ce, "Baba Tabawa, ina kwana."

Baba Tabawa ta ce, "Yaushe ki ka dawo? Ance min da bakya nan."

"Jiya na dawo Baba Tabawa, na zo neman Zainab ne."

Baba Tabawa ta ce, "Zainab dai ta ki?."

"Ita fa, nazo ina neman ta ance bata nan, kuma naga Mama bata nan."

Baba Tabawa ta girgiza kai ta ce, "ai Zainab ta kwana biyu bata nan, an nemi inda take an rasa, har maganar an kai gaban hukuma amma babu ita babu labarinta."

Islaha ta sauke numfashi cikin wani irin yanayi ta ce, "Don Allah Baba Tabawa babu wanda suka yi magana da ita kafin ta bar gidan nan?."

Baba ta girgiza kai ta ce, "gaskiya ba mu yi magana ba, amma...." Sai ta yi shiru, ta kalli Islaha ta ce, "ku zo mu je."

A hankali suke bin bayanta, suna tafiya Islaha tana gaisawa da waWanda suka sani har ta ja su kitchen inda Baba Tabawa take aiki.

Baba tabawa ta ce, "Na jawo ku nan ne saboda akwai sa?on Zainab da ta bawa Yafindo, Yafindo ta faWa min ta ce ta bata sa?o ta ce mata don Allah duk ranar da ki ka dawo ta ba ki."

Islaha da zumuWi ta ce, "bara na je wajan Yafindon na same, ba Yafindon kitchen Win nan ba?."

Baba Tabawa ta yi saurin ri?o hannun Islaha ta ce, "Islaha tsaya."

Islaha ta tsaya tana kallon Baba cikin wani irim yanayi. Baba ta ce, "Yafindo bata nan, ta je ?auyensu."

Islaha ta dafe kai ta ce, "Kuma bata ba ki sa?on ki ajjiye ba?."

"bata bani ba Islaha, ita kanta wannan maganar cewa yi kar na faWawa kowa, kema kawai na faWa miki ne. Dan ba mu yi tunanin dawowar ki nan kusa ba, shiyasa itama ta tafi ?auye."

Islaha ta ce, "Ina ne ?auyen na su?."

Ta girgiza kai ta ce, "ba a cikin garin nan take ba gabaWaya." Islaha ta yi ajiyar zuciya mai ?arfi, ta jingina da bango ta yi shiru bata ce komai ba.

"Amma ta faWa min a yadda Zainab ta bar gidan nan akwai matsala a tare da ita."

Islaha ta girgiza kai ta ce, "Ina Hafsa da Fadwa?."

Ta girgiza kai ta ce, "waWnanan sun zama ?an kansu, sai abinda suka ga dama suke yi a gidan nan, kuma da yake sun samu goyan baya babu abinda ake yi musu. Fadwa itace shugaba, duk abinda suke yi a ?ar?ashin Fadwa suke yi."

Islaha ta kalli Baba Tabawa ta ce, "na gode Baba, zan dinga shigowa akai akai, dan na duba ko Yafindon ta dawo."

Ta girgiza kai ta ce, "Duk da dai tana jimawa in ta tafi, amma na san zata dawo nan kusa." Islaha ta gyaa kai suka fita daga gidan.

Suna fitowa Islaha ta ga motar Saleem a ajjiye tana jiransu, Islaha ta kalli Safeera, Safeera ta ce, "Ni ce na kira sa." Bata ce komai ba suka shiga motar.

Suna shiga Salewm ya ce, "Hajiyan Jedda, sai ki ka dawo babu labari ko?."

Ta Wan yi murmushi ta ce, "Dawowar ce ta zo a haka, amma na so na faWa mu ku Allah bai yi ba."


"Ba wani nan, kin tafi kwatsam babu labari, kin dawo babu labari."

Ta Wan yi murmushi dan bata cikin yanayin wasa, suka gaisa ya ce, "ina fatan komai ya zama normal ko?."

Ta Waga kai ta ce, "Alhamdu lillah!."

"Haka ake so. Ina zamu je?."

Islaha ta ce, "Safeera wajan wankin kai zani, kaina ya dame ni."

Safeera ta ce, "mu je sai ayi mana."

Tunda suka fara tafiya bata ce komai ba, ta yi shiru tana tunanin halin da ta jefa Zainab a ciki. Safeera ce ta waiwayo ta kalle ta ta ce, "Yanzu ya ki ke ganin za a yi?."

Islaha ta kalle ta sannan ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Ban sani ba, amma da zan san garin su Yafindo zan je ko dan ta bani sa?on da Zainab ta bata ta bani, hankalina ya kasa kwanciya, zuciyata tana faWa min akwai wani abun da yake faruwa."

Safeera ta ce, "gaskiya dai akwai, sai dai fatan Allah ya kiyaye."

Ta yi shiru kawai ta kwantar da kanta, tana ganin Safeera da Saleem sun kalli junansu suna kallon ta, ita dai ta lumshe ido bata ce komai ba tana tunani. Saleema wajan wankin kan ya sauke su ya tafi.

Basu jima sosai ba su fito, kai tsaye ta ce su wuce office Win Barr Suraj.

Shima ya yi mamakin ganinta sosai, ta ?i bashi damar yi mata tambayar yaushe ta dawo ta ce, "Hamma Suraj ba a ga Zainab ba, tun bayan wannan recording Win ba a kuma ganinta ba."

Barr ya ce, "dole hukuma za a saka a cikin case Win nan, ki bar komai a hannuna, zan kai maganar gaban ?an sanda, za su san abinda za a yi."

"Ko yaushe sai ka ce na bar komai a hannunka, amma in na bari Win bana ganin wani cigaba. Kwana nawa da tafiyata, na bar maka komai Win, amma ni ban ga wani cigaba ba har yanzu."

"Islaha baza ki gane ba, wannan case Win ba ?aramin case bane, ba a yi masa shigar sauri, dole sai an bi a hankali."

"Yanzu daga gidan nake, kuma an tabbatar min da bata nan, sannan akwai sa?on da ta bayar a bani, wacce aka bawa Win bata nan."

"Wa aka bawa?."

"Za ka iya gane Yafindo, wacce take aiki a kitchen?.."

Ya Waga kai ya ce, "na gane ta sosai ma, Ina ta je?."

"Wai ta je ?auye, kuma ashe ba a garin nan take ba."

Ya tallafi haSarsa ya ce, "Amma zan so a same ta, ba mu san me ta bayar ba. Kar ki damu, tunda har ta bawa wani sa?o abin ya zo da sau?i, za a san abinda zamu yi. Ina tare dake ko yaushe, zan san duk hanyar da zan bi na nemo Yafindo."

Islaha ta ce, "na gode, zamu yi magana anjima" ya amsa yana mi?ewa suka fita.

Suna fitowa Safeera ta ce, "Islaha da kin sani ba ki faWawa Barr maganar sa?on nan ba, kar a sake samun matsala irin wancan."

Ta kalli Safeera ta ce, "Duk da abinda ya faru ni bana zargin ko Waya a cikin ku, Hamma ya faWa min na dinga Soye sirrin da na samo, amma bazan iya ba, dan aikin ya fi ?arfina ni kaWai. Ko waye yake da hannu a maganar nan, Allah zai bayyana shi da gaggawa."

"Haka ne, Allah ya ba da sa a."

"Amin."

Islaha haka ta dinga jan Safeera yawo, daga nan su je nan kuma duk akan Satan Zainab, sai da suka yi azahar sannan suka wuce gida.

A cikin napep Win ma ta yi shiru tana tunani, Safeera ta ce, "ki ta addu'a lamarin nan, in sha Allah komai zai dawo daidai."

Ta gyaWa kai ta ce, "ban san me zancewa Hamma akan dawowa ta ba, in na faWa masa maganar Mr Rehaan Yola kina ganin zai amince?."

Safeera ta ce, "gaskiya babu lallai, kuma zai iya jin shakku a ransa. Amma kar ki Soye masa, kin ga kin Soye masa batun Wauke ki da tafiyar ki, kuma ya ji haushi sosai kawai dan yana sonki ne yake mantawa. Yanzu kar ki Soye masa, ki faWa masa gaskiya ko da zai ji haushi."

"Zai ji haushi kam, sai dan kawai faWa masa Win shine mafita. Ni kaina ina neman hanyar da zan fara yi masa bayani, shiyasa har yanzu ko waya ban yi dashi ba, dan ban san me zance ba."

"Dole ki damu ai, amma in ki ka faWa masa irin abinda ki ka faWa min zai ji kamar kin raina masa hankali, in ki ka canja maganar kuma daga baya ya san asalin gaskiyar bazai ji daWi ba. Dole ki faWa masa, tunda daman kin ce masa neman kuWin biyan bashi ne ya kai ki. Abinda zai tambaye ki ta ya ki ka samu kuWin a wannan lokacin, dan ko aikin gwamnati ki ke yi a can baza ki haWa wannan kuWin a albashin wata biyu ba. Sai dai ki faWa masa Win zai fi."

Ta sauke numfashi bata ce komai ba suka cigaba da tafiya, a daidai ?ofar gidan ta hango sa a tsaye cikin jallabiyya ba?a, Sadik yana kan mota a zaune shi kuma ya jingina da motar suna magana.

Gaban Islaha ya faWi ta ce, "Safeera Hamma ya dawo."

Safeera ta kalli wajan ta gan shi a tsaye, ta kalli Islaha ta ce, "ki nutsu, kar ya ga kamar kin tsorota ya yi tunanin wani abun."

Daga can nesa suka sauka daga napep Win, Islaha ta biya kuWin suka nufi wajan su Hamma ?irjinta yana bugawa sosai.

A hankali suke nufar inda suke a nutse, Islaha ta sunkuyar da kai har suka kusa ?araso daf dasu. Sadik ne ya fara gano ta, ya buWe baki cikin mamaki da Waure kai ya ce, "A'a, wa nake gani kamar Islaha?...itace ko gizo take yi min?."

FaWar Islaha da ya yi sai ya ja hankalin Saheer ya kalli wajan da yake kallo, Saheer ya yi arba da bugun zuciyarsa, sai tsayar da idonsa a kanta yana kallon ta, kanta a ?asa tana ?arasowa har suka cin musu.

Suna ?arasowa ta ce, "barkan ku da yamma."

Saheer ya kasa magana sai kallon ta da yake yi, zuciyarsa tana bugawa, yana so ya tantance da gaske itace ko gizo take yi masa.

Sadik ne ya diro daga kan mota ya ce, "Islaha ke ce ko kuma ?an biyun ki ce?."

Ta yi dariya ta ce, "Ni ce Hamma Sadik."

Ya kalli Saheer da ya zuba mata ido kamar zai cinye ta, sai kuma ya ?araso inda yake yana kallon ta, muryarsa a tausashe ya ce, "Matar Hamma?" Ya faWa da sigar tambaya yana nuna da yatsa.

Islaha ?irjinta ya buga, jin muryar masoyinta har tsakiyar kanta, ga kewar ganinsa da take addabar zuciyarta. Ta Wago ido a hankali ta kalli idonsa, sai ta sauke kai ?asa ta ce, "Na'am, mijin matar Hamma."

"Oh my god! Ke ce da gaske? Na kasa yarda fa."

Ta Wan yi dariya ta ce, "Ni ce fa Hamma."

Saheer ji yake kamar ya jawo hannunta ya rungume ta, sai ya tuna a ?ofar gida suke bazai iya aikata hakan ba. Amma yana so ya ji ta a jikinsa ko zai tabbatar itace ko kuma ba ita bace. Ya ri?o hannunta yana kallon bracelet Win daya bata ya ce, "Yaushe ki ka dawo?."

Ta sukar da idanunta ?asa ta ce, "Jiya na dawo Hamma."

Ya wara ido ya ce, "har jiya? Kuma shine ban sani ba?."

Ta Wan kalle sa tana zame hannunta daga cikin nasa ta ce, "Mamaki nake so na baka."

Ya bita da kallon da ya mamaki ita kuma ta kalli Sadik ta ce, "Hamma Sadik ka gama mamakin ko da saura?."

Ya yi ?ar dariya ya ce, "Na tabbatar Islaha. Kuma ki ka sauka tun jiya babu labari?."

"Sai dare na nutsu, kuma da safe ina tashi na fita."

Sadik ya kalli Safeera ya ce, "laifin ki ne, da ba ki faWa mana aminiyar ki ta dawo ba."

Ta yi dariya ta ce, "Wallahi nima ganinta kawai na yi, babu labari babu sanarwa."

Sadik ya ce, "Ma sha Allah! Tunda ta dawo lafiya ai haka mu ke fata. Gashi nan kam Jeddah ta karSe ta."

Ta yi murmushi ta kalli Saheer da ya rungume hannunsa a ?irji yana kallon ta ta ce, "zan shiga ciki Hamma."

Ya Wafa mata kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login