Showing 204001 words to 207000 words out of 221574 words

Chapter 69 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

177

balle har ta samu damar yi masa shirme?.

Ya yi tsaki mai sauti ya mi?e tsaye ya ce, "ki turawa Jazy account details Win" ya faWa yana barin wajan ko takarda Waya bai Wauka ba.....

Nana Haleema.
[7/29, 12:06/ PM] KRBBK: RDB2P93
Nana Haleema.

Islaha ta bi shi da kallo cikin takaici da Sacin rai, kafin ta yi tsaki ta kalli Jafar da yake kallon ta ta ce, "shiyasa na ce ka kasance a nan, saboda ina so ku zama shaida da kai???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? da ?awata. Bana so a samu matsala nan gaba, duk ?an?antar matsala bazan jure mata ba. Na saka hannu na amince da auren nan saboda Hamma, zan rayu tsahon wata biyar saboda shi, in ba dan haka ba da ba mu sake haWuwa ba."

Jafar ya ce, "saboda wanda za ki aura ki ka amince za ki auri Rehaan?."

Ta Wan yo murmushi ta ce, "ba iya auren yarjejeniya ba, zan iya sadaukar da komai saboda shi."

Ya girgiza kai ya ce, "Wow! Ban taSa ganin irin wannan sadaukarwa ba. Yanzu fifty millions suka nema kuma za ku basu?."

Ta Wan yi ajiyar zuciya ta ce, "haka suka ce, da farko sun ce one hundrend millions, amma daga baya sun rage ya dawo haka."

"?an sanda fa, kun yi magana dasu?. Haka kawai za ku Wauki kuWi a bawa wasu mutane a cikin daji, meyasa baza ku basu dama su yi aikin su ba?."

Islaha ta ce, "an yi komai Mr Jafar, abin ne kamar bazai yi aiki ba. Ni kuma ganin na samu dama sai na ce bara na gwada, in ya yi aiki shikenan, in bai yi ba sai mu nemi wata hanyar."

Jafar ya ce, "shikenan, za a tura miki kuWin."

Islaha ta ce, "Thank you." A lokacin Rehaan ya dawo falon ya Wauki wayarsa.

Jafar ya kalle sa sannan ya kalle ta ya ce, "Thanks him."

Islaha ta kalli Rehaan sannan ta ce, "Da na godewa wannan ai gwara na kwana babu ci babu sha."

Jafar ya yi dariya mai sauti, ya kalli Rehaan da ya Wauki wayarsa ya koma ko kallonsu bai sake yi ba, kamar ma bai san dasu a wajen ba.

Islaha ta mi?e tsaye tana jinta wani iri, sai take ji kamar zuwa ta yi ta ro?osa kuWi ya bata, sai ta ke jin kamar ta zubar da ajinta a wajensa. Sai kuma ta tuna zama dashi zata yi na wata biyar, shi kuma ya ba ta kuWi.

Ta kalli Jafar ta ce, "na gode." Bai ce komai ba ya Waga mata kai, ta kalli Safeera da ta ma?ale a waje Waya ko motsin kirki ba ta yi ta ce, "Safeera mu je." Safeera ta mi?e suka fita daga falon.

Tana fita Jafar ya Wauki takardun yana karantawa, rules Win ya dinga bi yana karantawa, dan gabaWaya shi bai wani nessecery abu a ciki ba, daga nata rules Win har nasan. Ya Wan yi murmushi ya ajjiye musu, ya mi?e tsaye a lokacin Rehaan ya dawo.

Rehaan ya kalli Jazy ya ce, "amma wannan yarinyar nan bata da wani plan a ?asa? Daga zancen contract sai ta kawo maganar kuWi?."

Jafar ya ce, "Da gaske an yi kidnapping Win wanda take so kuma zata aura, a gidanau take rayuwa, shine ya Wauki duk wani responsibilities Winta. Zata iya Waukar komai saboda dashi, dan ta yarda ta zauna da kai na wata biyar saboda shi a wajenta ba komai bane."

Rehaan ya girgiza kai cikin ko in kula ya ce, "dole ta yi komai saboda shi, abokin Wan iska shima Wan iska ne."

Jafar ya kalle sa ya ce, "auren ta da dai za ka yi, bai kamata a dinga jin waWanan kalaman a bakin ka ba."

Ya ce, "Ikon Allah, shi kuma ita yake so, ya rasa abinda zai so sai wannan."

Jazy ya ce, "ni na tafi, ina da abinda zan yi. In ta turo min details Win zan tura maka, ni ba Wan aikin ka bane" ya faWa yana fita daga falon.

Islaha yadda aka Wauko su haka aka mayar dasu, Safeera duk ta gigice ta kasa cewa komai sai da suka sauka daga motar, suna shiga gidan su Saheer ta ri?e hannun Islaha ta ce, "Islaha daman da gaske ki ke? Wayyo Allah, ban taSa tunanin zan ga Rehaan ido da ido ba sai yau. Ashe haka yake da kyau? Ashe a zahiri ya fi kyau Islaha. Wow! Gaskiya kina da sa'a ?awata, ke me sa'a ce."

Islaha ta kalle ta cike da takaici ta ce, "ji don Allah, akan wancan banzan duk kin wani rikice, ni ki sakar min hannu" ta faWa tana ?wace hannunta.

Sai kuma ta ce, "Don Allah ki bar wannan shirmen, ni bana so kowa ya ji maganar nan, ki ri?e wannan amanar don girman Allah. Bani da bu?atar a san na yi aure balle a san wanda na aura, ki rufe maganar nan, ko Saleem kar ki faWawa, na yarda dake shiyasa na je har can da ke."

Safeerq ta ce, "Meyasa bakya so a sani?."

"Kin ga yanayin da auren ya zo, ba aure ne da zai dawwama ba, ba aure ne kamar ko wanne ba. Na rantse da Allah bana son ganin fuskarsa, ko sunansa bana so a kira, ni kaWai na san wula?ancin da ya yi min, ni kaWai na san irin Wacin da dasa min a zuciyata...."

Ta dakata da maganar tana tuna yadda ya dinga jifanta da kalaman banza sannan ta ce, "amma na amince saboda Hamma kawai, zan je na zauna dashi saboda Hamma, zan dawo saboda Hamma."


"In sha Allah bazan faWa ba, za ki same ni da ri?e miki amana in sha Allah, kar ki damu."

Sai kuma ta dafe kai ta ce, "Ni wallahi danasani nake yi, sai nake ji kamar na cutar da rayuwata, kamar ban yi daidai ba, kamar abinda na yi zai canja rayuwata, kuma duniya zata ce na aure kafin na auri Hamma, za a dinga cewa bazawara Hamma ya aura. Innallahi, wallahi bana son hakan ko kaWan."

Safeera ta girgiza kai tana binta da kallon daga baya kenan sannan ta ce, "Islaha kenan, sai da na faWa miki, na ce ki tsaya ki yi tunani, amma ki ka ?i."

"Ni ba danasani nake yi ba, kawai bana so a dinga jifana da kalman da zasu yiwa Hamma ciwo. Ina yin auren nan zan koma bazawara a idanun mutane, ba kowa ne ya san ya zaman auren zai ya kasance ba. Amma tunda zai bani kuWin a karSo Hamma duk abinda mutane zasu ce ba komai bane."

Safeera ta ce, "Amma kina ganin zai ba da kuWin nan kuwa?."

Ta gyaWa kai ta ce, "zai bayar, sanin zai bayar Win ne ya saka na amince. Zai amince saboda Babansa, ni kuma na amince saboda Hammana."


"To wai shi wanne irin kuWi ne dashi haka? Miliyan hamsin fa da yawa."


"Shi ya sani, ni dai ya tura min kuWin na bayar a yi fansar Hamma."

"To me za ki cewa Baffa in aka bada kuWin?."

Ta Wan yi shiru sannan ta ce, "zan faWawa Sadik ya faWa masa kawai sun sako shi ba tare da an bada komai ba, a rufe maganar kar ya sani.....Ke ni fa da akwai yadda zan yi, da na yi dan na tabbatar Hamma bai san da maganar nan ba, da na faWa masa wani abu a madadin na ce masa na yi auren yarjejeniya."

Safeera ta ce, "Gaskiya za a yi daru dashi akan auren nan, yadda yake kishin nan na ki in ya ji kin auri wani kafin shi, sai ya haWWiye zuciya ya mutu."

"Wannan shine tashin hankalina Safeera, shine kaWai abinda nake jin tsoro wallahi. Amma in sha Allah zai fahimce ni."

Safeera ta ce, "Allah ya sa."

Ta amsa da amin ta ce, "zo ki raka ni wajan Baffa na faWa masa na amince da auren."

Safeera ta ce, "amma bakya so."

"Wallahi Allah bana so, Allah ya sani bana ?aunar auren nan."

"Sai ha?uri, dan dai ki ki karSi kuWin nan shikenan komai ya fara." Ta yi shiru bata ce komai ba suka tafi wajen Baffa.


A zaune suka same shi dan tunda aka samu damuwar nan ta sace Saheer ya daina fita, ko ya fita da wuri yake dawowa saboda ana neman maganin damuwar da suke ciki.

Islaha ta zauna ta ce, "Baffa ina yini."

Baffa maimakon ya amsa sai ya ce, "yau ban gan ki ba."

"Eh Baffa, na Wan fita ne."

Baffa ya ce, "Na san da kina gidan nan da yanzu muna tare akan maganar Saheer."

Islaha ta ce, "Baffa akan maganar auren nan ne."?

Baffa ya ce, "ina jin ki."

Ta haWWiye yawun takaici da ba?in cikin kalaman da zasu fito daga bakinta ta ce, "Ka yi ha?uri da abinda na ce maka a akan auren."

"Babu komai Islaha, kar ki damuwa, ai ba matsala bane."

Ta yi shiru bata ce komai ba tana kallon ?asa, Baffa da yake kallon ta ya ce, "FaWi abinda yake ranki, ina jin ki."

Islaha a sanyaye ta ce, "Daman...." Sai ta kasa magana ta kuma yin shiru.

Baffa ya ce, "ki nutsu, ina jin ki. FaWi abinda yake zuciyarki, kar ki saka tsoro ko fargaba."

Islaha ta ce, "Daman cewa zan yi na amince da auren Baffa."

Baffa ya yi murmushin jin daWi ya ce, "da gaske ki ke?."

Islaha ta ce, "Da gaske nake."

Baffa ya ce, "Allah ya yi miki albarka. Duk da ba ki san waye mijin ba ki ka amince da abinda na ce miki, ki ka yarda da maganata ki ka amince da kalamana. Islaha ba ?in ki nake yi da Saheer ba, akwai abinda nake dubawa akan auren ki dashi shiyasa na soke shi da kaina."

"Islaha In sha Allah wanann auren da za ki yi baza ki yi danasani ba. Kuma daman na faWa miki ni tuni na faWa musu kin amince, amma tunda yanzu kin amince da kan ki kin ga faWuwa ta zo daidai da zama. Allah ya yi miki albarka, Allah ya taimaka miki, Allah ya shiga lamarin ki, Allah ya sa auren nan ya zama silar farin ciki a rayuwar ki."

Islaha tana so ta amsa da amin, amma kuma addua'ar ?arshe ce bata so ta tabbata, sai kawai ta yi shiru bata amsa ba.

Baffa ya ce, "tashi ki je, Allah ya yi miki albarka." Ta mi?e a sanyaye suka fito suka shiga wajan Mama.

Nana Haleema.
[7/29, 12:06/ PM] KRBBK: RDB2P94
Nana Haleema.

Islaha suna shiga wajen Mama suka bita da kallon raini da ?as?anci, sai suka yi dariya ita da Hanan har suna tafawa. Irin dariyar nan ta rainin hankali, mai saka ciwo da raWaWi a zuciyar wanda aka yi dariya dan shi.

Mama ta ce, "Ka ga matar mahaukaci, yanzu duk wannan iyayin a auren mahaukaci za a ?are."

Islaha bata ce komai ba ta waiwayo ta kalli Safeera da take tsaye bata ce komai ba.

Hanan ta ce, "Yayanmu dai ya fi ?arfin wata, sai dai mahaukacin wallahi."

"To in ba mahaukacin ba ya za a yi mata tayin auren Wan AbdulAziz Yola? Sai dai mai taSin hankalin, shine daidai da ita, shine bazai banbance budurwa da ragowar wasu ba. Hanan ance sunansa Salman ko?."

"Eh Mama, ance haka sunansa yake, kuma in ya kashe ta ya kashe banza wallahi. Ita ba uba ba balle ya shige gaba a ?waci ha??in ranta, kuma waye yake shari'a da mahaukaci?."

Suka yi dariya suka sake tafawa kamar ba uwa da ?a ba. Mama ta ce, "Ga idanu ga hanci, ga gashi har baya ga iyayi, ga farin jini da za?in murya, amma duk mallakin mahaukaci ne."

Islaha ta ja Safira suka shiga cikin Waki, ta tsaya ta jingina da bango bata ce komai ba. A fusace Safeera ta ce, "Matar nan bata da kirki wallahi, wato mahaukaci ne zai aure ki ko? Basu san....."

Islaha ta dakatar da ta ce, "Don Allah kar ki faWa, ki barsu a je a hakan, sai me?."

Sai ta Wauki waya ta kira Sadik yana Wauka ta ce, "Hamma Sadik zan iya samun account details Win ka?."

"Me za a yi dashi?."

"KuWin fansar Hamma za a saka, account Win ka zai cire wannan kuWin lokaci Waya?."

Cike da mamaki ya ce, "Islaha a ina ki ka samu wannan kuWin masu yawa haka?."

Ta ce, "zan yi maka bayani. Amma yanzu ka turo min kawai" ta faWa tana yanke wayar, ta ga Safeera tana kallon ta.

Ta kalli Safeera ta ce, "meye ki ke kallona kamar na ci bashin ki?."

Safeera ta ce, "kina da sa'a wallahi." Ta yi tsaki ta shiga banWaki ta bar mata wajan.....

Bata jima da shiga ba ta fito, ta ga Safeera ri?e da takardar yarjejeniya tana karantawa. Safeera ta kalli Islaha da take tsaye a wajen kayanta tana bincika kayan ta ce, "ni ban ga wani rules na Waga hankali a rules Winsa ba. Ya ce ba ya so mutane su san ya aure ki kema bakya so, ya ce babu ruwansa dake kema kin faWa...."

Islaha ta yi tsaki bata ce komai ba, Safeera ta ce, "Amma Islaha rule Win nan na ki na ?arshe anya zai yu kuwa?."

Islaha ba tare da ta juyo ba ta ce, "wanne kenan?."

"Da ki ka saka no intimacy, kina ganin zai ba ki waWnanan kuWin ba tare da wani abu ba?. Kuma in ki ka duba a cikin na sa rules Win bai saka haka ba, ni sai nake ganin kamar bazai yu ba."

Islaha ta waiwayo a fusace ta harare ta ta ce, "Ita yarjerjeniya ko Waya bai saka rules ba indai Waya ya saka kuma ka saka hannu ciniki ya faWa. Ba gwara ya hana ni aikina da fita daga gidan akan abinda ki ke faWa ba? Na yi miki kama da wacce zata saurari wancan banza?. Na rantse da Allah Safeera kina da abin haushi, har kin Sata min rai."

Safeera ta Wan yi dariya sannan ta ce, "Ba banza bane, tunda aurensa za ki yi."

"Auren contract ba. A cikin wata biyar Win nan ko hannuna ya ri?e ya karya mana rules, kuma in ya sake ya yi wannan gangancin daga ranar bazan sake zama dashi ba. Daman saboda me na yarda da auren? Saboda Hamma ne, kuma na san zuwa lokacin ya dawo, bazan tsaya ina Sata lokacina a gidansa ba. Da gangan zan yi abinda zai karya Waga daga cikin rules Wina ko da ba ya so, daga nan zan yi terminating contract Win kowa ya kama gabansa."

Safeera ta yi dariya ta ce, "mugunta kawai ki ka shiryawa bawan Allah. Da dai kawai ya saka hannu ne, amma ajjiye macen da ka san matar ka ce ta aure, addini da al'ada sun baka ko wacce irin dama a kanta, ka ajjiye ta har tsahon wata biyar kana kallon ta ba tare da wata ala?a ba akwai wahala, a wannan zamanin dai kafin a samu wanda zai yi wannan jan halin za a jima."

Islaha ta ji kamar ta tsinkawa Safeera mari ta ce, "Yana rayuwa a cikin turawa, ya san girman karya rules Win da ka yi signing akan amincewar ka a kai. Ni mallakin Hamma ce, babu wani banza da bawa kaina matu?ar Hamma yana da rai."

"Hmmm Islaha kenan!. To kina nufin za ki cigaba da son Hamma bayan wannan yarjejeniyar?."

"Ban gane ba, da sai na ajjiye son nasa kenan?."

"eh mana, na ga matar aure ce ke, son wani ta fuskar soyayyar babban zunubi ne."


"Da yake zuciyar tawa whatsapp ce, da zan kunna data na hau lokacin da nake so na sauka lokacin da na ga dama ko?. Kuma da ki ke zancen aure, ki dinga haWawa da contract."

Safeera zata yi magana ta ce, "Dallah malama ki yi min shiru, kina Sata min rai."

Islaha ta Wauki wayarta ta ga Sadik ya turo acc details Win. Ta Wan dafe kai tana tunanin anya abinda ta yi daidai ne kuwa? Sai yanzu abin yake damunta take ganin kamar ba daidai ta yi ba, sai yanzu take gani kamar ta dakusar da rayuwarta ta lalata carrier ta.

Ta bi account number da kallo tana tunanin turawa Jafar, ta zauna a kan gado ta ce, "Safeera ina cikin damuwa, kamar ban aikata abinda ya kamata ba. Contract marrige na yi, wayyo Allah!."

Safeera ta ce, "Ai na faWa miki ki ?a ji, yanzu da muka dawo ma na sake maimaita miki. Kin yi gaggawar yanke hukunci babu dogon nazari gaskiya, amma tunda kin bawa Allah zaSi wata?ila shine alkhairin ki."

Ta Wago a fusace tana hararar ta ta ce, "Ta ya wannan auren zai zama alkhairi a gare ni?."

"ki daina faWa, ba ka yankewa kan ka hukunci akan abinda ba kai za ka yiwa kanka ba. Kawai ki cigaba da addu'a Allah ya shiga cikin lamarin."

Islaha ta yi shiru, ta yi forwading acc detaila Win zuwa ga lambar Jafar da ko saving ma bata yi ba.

Ta jima a zaune a wajan daga ita har Safeera babu mai cewa komai, sai daga baya Safeeta ta ce, "Su wai ?an gidan nan Wauka suke yi Wansa da akace yana da taSin hankali za ki aura? Da yake ga ki ?arshen mara gata, sai kawai Baffa ya Wauke ki ya aurawa mahaukaci."

"don Allah Safeera mu bar maganar nan haka, kin yi min al?awarin babu wanda za ka faWawa."

Safeera ta yi ziping bakinta ta ce, "shikenan, bara na koma gida."

Tana mi?ewa wayar Islaha ta fara ?ara, Islaha ta ga kiran Sadik ne sai ta Wauka ta saka a kunne. Daga can Sangaren ya ce, "Islaha an saka min kuWi fa, an saka kuWi har naira miliyan hamsin. Fito ina waje."

Ta kalli Safeera da take tsaye ta ce, "An saka kuWin, mu je waje mu same sa" ta faWa tana mi?ewa ta yafa mayafi.

Suna fita basu tarar da babu kowa a falon suka fita zuwa ?ofar gida. A jikin motarsa suka sake shi a tsaye, suka ?arasa dan wajan da ya tsaya rana sosai.

Tana zuwa wajen Sadik ya ce, "Islaha kuWin waye wannan?."

Islaha ta ce, "kuWin fansar Hamma ne, ya za a yi a mayar dasu cash, ka yi musu waya kace musu an haWa kuWin? Amma bana son Baffa ya san kuWin aka samu."

Sadik ya dakatar da ita ya ce, "in na yi magana sai ki ce ina yi miki wani kallo na daban, yanzu meye wannan?. Wancan lokacin na gan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login