Showing 135001 words to 138000 words out of 221574 words

Chapter 46 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

131

murmushi ya Wauki waya yana dannawa yana jin daWi, a bayyane ya ce, "Auren babu lallai ya yu, ni daman na fi son haka wallahi, dan zaman sa da Islaha ?ar ?aramar matsala" yana gama faWar hakan ya ajjiye wayarsa ya ja mota ya tafi.

? ? ? ? ? ? ? ? " " " " " " "

Islaha tunda Baffa ya kashe wayar take jingine da gado cikin sanyin jiki, a kasa motsawa saboda rashin ?arfin jikinta. Ta kasa yarda jibi juma'a za a Waura mata aure, ta kasa amincewa igiyar auren Hamma har guda uku zasu hau kanta nan da wasu awanni masu zuwa. Bawai bata son Hamma bane, tana sonsa so na tsakani da Allah, kawai bata shirya aurensa a lokacin bane, ta fi so sai ta gama abubuwan da suke gabanta, sai auren ya biyo baya.

Ta zame ta kwanta a wajan tana tunani, tana so ta faWawa Safeera amma sai ta ji baza ta iya ba, ta yi shiru cikin tunanin da bata san dalilinsa ba. Ta yi tunanin Saheer zai kira ta, amma sai ta ji shiru, hakan ya yi mata daWi sai ta ji bata so ma ya kira wayar ta

Sai dare mutanen gidan suka dawo, aka kira ta suka bata tsarabar doguwar riga ba?a mai kyau irin ta larabawa. Ta je ta ajjiye a Waki tana tunanin halin da Zainab take ciki, da kuma auren da Baffa zai Waura mata.

Washe gari bayan ta gama komai ta yi nufin zuwa gidan Rehaan, duk da bata so amma tana son samun kuWi, tana ji a jikinta dole ta je ko dan kuWin da take so ta haWa ta bashi ta bar ?asar da wuri. Ko dan saboda Zainab dole ta dage da neman kuWi, dan hankalinta ya yi kan ta koma fa je ta ga halin da take ciki.

Tana typing code Win ?ofar ta buWe, ta shiga a hankali da sallama. Babu kowa a a falon hakan ya saka ta wuce kitchen.

Sai da ta tsorata ganin Jazy a tsaye ya Wora mai akan wuta zai soya irish.

Ya juyo suka haWa ido ya ce, "Miss Islaha, ?araso mana."

Ta shigo a hankali ta kalle sa, kamar bazata yi magana ba sai ta ce, "ina yini."

Ya juyo ya kalle ta ya ce, "jiya sai ki ka ?i zuwa, ina ta jiran zuwan ki."

Bata ce komai ba, ya mi?a serving spoon Win da yake juya dankalin dankalin ya ce, "za ki iya taimaka min?."

Ta gyaWa kai ta karSa, shi kuma ya Wan matsa gefe ya ce, "na gode" ya faWa ana fita daga kitchen Win.

Ta bi sa da kallo dan gabaWaya ?hamahinsa ya mamaye kitchen Win. A bayyane ta ce, "Ka rasa turaren dubu nawa suke siya, turare ya ma?ale ko ina kamar yanzu aka saka" ta faWa tana zuba dankalin a mai.

Man ya yi zafi sosai, hakan ya saka ya taso sama, ya yi haya?in da ya shiga hancinta kai tsaye ya sar?e ta. Ta Wan ja baya da sauri ta fara tari, ta Wauka abin kaWan ne tunda haya?in bai kai ya sar?e ta haka ba, sai ta ji numfashinta yana neman tsayawa, ta mi?a hannu ta kashe wutar stove Win, ta fito ta zauna a falon tana jan numfashi da ?arfi.

Ta sama Jazy ya hango ta ta fitoc ganin yadda numfashinta yake sauka sai ya sakko da sauri, ya Wauki ruwa ya ?arasa inda ta ke ya ce, "Sannu, ki nutsu."

A hankali take jan numfashin yana sauka a hankali, a hankali nunfashinta ya dawo daidai, ta saka hannu ta kwance roll Win kanta ta bar mayafin a kanta bai cire gabaWaya ba.

Ya bata ruwa ya ce, "karSi ki sha." Ta karSa a hankali ta sha, ta jingina da bango kujera tana lumshe ido cikin wani irin yanayi mara daWi.

Sai da ya ga ta nutsu sosai sannan ya ce, "kina da asthma ne?."

Ta Wan sauke nunafshi tana Waga kai alamun tana da ita, ya ce, "ban sani ba, da ban baki aikin da zai saka ki sanu attack ba."

Ta Wan sauke numfashi ta ce, "ina yin aiki sosai, yau an samu incidence ne kawai."

"Sannu. Ina inhaler Win ki? Meyasa bakya yawo dashi?."

"Na manta shi."

"Meyasa?."

"Ba a tabbtaar da akwai asthma Win ba sai few days back, a nigeria an ce babu, amma a nan ance akwai itama babu yawa, tana first stage. Ban saba da yawo dashi ba, shiyasa ban Wauko ba."

Ya Wan girgiza kai yana kallon ta, ita kuma ta mi?e ta ce, "zan ?arasa."

Ya dakatar da ita ya ce, "A'a ki bar shi, na gode." Bata zauna ba tana tsaye, ya kalle ta ya ce, "Dawo ki zauna." Ta zauna a hankali tana sunkuyar da kanta.

Ya sauke numfashi ya ce, "zan iya tambayar ki?."

Ta Waga kai alamun eh za iya, Jazy ya ce, "kuma za ki faWa min gaskiya?."

Nan ma ta Waga kai alamun eh. Ya Wan girgiza kai yana kallon ta kafin ya ce, "Wanne irin aiki ne ya kawo ki ?asar nan?."

Ta Wago suka haWa ido sannan ta ce, "ga shi nazo gidan nan ina yi."

"Dalilin zuwan naki nake so na ji. Na bibiyi contents Winki daga shekaran jiya zuwa yau, na bibiyi na dah dana yanzu, kuma na ga har tattaunawa kin taSa yi akan disadvantges na aiko yara aiki wata ?asa. Yanayin kalaman ki yana nuni da bai kamata a dinga tura yaran ba aiki irin wannan ba, hakan sai ya tabbatar min da ba ?aramin dalili ne ya kawo ki nan ba. Miss Islaha Ina so na san dalilin ki na fara aiki a nan."

Ta Waga kai ta kalle sa tana gyara mayafinta da yake son zamewa, ta Wan sauke numfashi ta ce, "ni dai na san ban zo saboda bibiyar abokin ka ba, dan ban san zan haWu dashi a nan ba, na zo da niyar na samu kuWi kawai, ban san yana zuwa Jeddah ba balle na san gidan nan."

Ya gyaWa kai ya ce, "na san ba ki san shi ba, na ji kin ce silar zuwan ki yana da ala?a dashi ne, shiyasa nake so na sani."

Ta sauke numfashi ta ce, "in na faWa maka babu lallai ka yarda."

Ya Wan yi murmushi ya ce, "Na yi bincike a kan ki, na san komai na ki Islaha. Halayen ki, da wanda za ki aura, ?awar ki, wajen aikin ki, inda ki ka taso, da komai na sani. Zan yarda da duk abinda za ki faWa min, in bazan yarda dake ba bazan ce ki faWa ba."

"Meyasa baka bincika ka san dalilin zuwana nan Win ba? Yadda ka san komai a kaina shima ya kamata ka nemo ka sani, Mr Jafar."

"Ina so na ji daga bakin ki, ki faWa min Miss Islaha."

Ta Wan yi shiru kamar bazata ce komai ba, sai kuma ta ce, "Na faWa maka ya sace ni daman, a lokacin da ya sace ni ni kuma mahaifina yana Nadira hospital da yake Yola, za a yi nasa dashen ?oda, ana neman kuWin har miliyan goma sha biyu, ban da ?ananun abubuwa da aka kashe a asibitin. Ana tsaka da neman kuWin aikin Baffa sai ya sace ni, ya kaini aka ajjiye ni a wani gida, sai dai a buWe ni a bani abinci a rufe. Da na ga ji sai na nemi ganinsa, muka haWu na nemi ya ?yale ni sai yake nuna kamar sai na basa ha?uri."

Ta dakata tana turo baki tana kallon Jazy ta ce, "Haka kawai ban yi masa laifi ba ha?urin me zan ba shi?."

Ya Wan girgiza kai bai ce komai ba yana kallon ta. Ta ce, "Ni kuma na ?i ba da ha?uri, daga ?arshe da na dinga mafarkin Baffa ya mutu na ha?ura na bashi ha?uri, amma ba akan laifin da ya yi min ba, sai dan dalilin Baffa. Rana tsaka ya aiko wanda yake bani abinci ya ce za a kai ni gida. Ni kuma a lokacin ina falon sa, ina ta tunanin kuWin aikin Baffa da nake mafarki har Baffa ya mutu saboda rashin kuWin. Kawai sai na ga kuWi akan sofa a ajjiye, kuWi ne masu yawa har rafar dala guda biyu....."

Sai ta dakata bata cigaba ba dan bata san ya zai Wauki maganar ba. Jazy yadda take naganar dariya take bashi sosai, a nutse take maganar amma cikin shagwaSa da nuna zallar gaskiya akan maganar.

Ganin ta yi shiru sai ya ce, "ina jin ki."


"Ni kuma a lokacin ban san me ya shiga kaina ba, rashin mafita ya ja ni, tunanin halin da Baffa yake ciki ya rufe min ido, na kasa tunanin abinda zan yi ba daidai bane, kawai na Wauki rafa Waya...."

Jazy ya wani ya zaro ido, sai ta yi sauri girgiza hannu ta ce, "wallahi ba sata na yi ba, bashi na Wauka, kuma na ce zan biya sa."

Jazy ya murmusa ganin yadda ta ruWe wai ba sata ta yi ba, Islaha ta ce, "har camera falon na kalla na faWa masa ni ban saci kuWinsa ba, rashin mafita ne ya saka na Wauka saboda na biya kuWin aikin Babana. A lokacin ban san me ya shiga kaina ba, amma wallahi ban taSa Waukar abin wani ba, shima ban san meyasa na yi ba a wannan lokacin. Tunda na Wauki kuWinsa na je aka biya kuWin aikin sai na kasa nutsuwa, da ina da burin na kai ?arar sa gaban hukuma, saboda a bi min ha??ina na sace ni da ya yi ban yi masa komai ba, amma saboda kuWinsa ya saka na fasa" ta ?arasa faWa tana wani karyar da murya.

"Ina ji"

Jazy ya faWa yana murmushi dan shi wallahi dariya take bashi.

Islaha ta ce, "tun daga ranar sai na fara mafarki akan kuWinsa, ko yaushe in na kwanta sai na ga yana cewa na biya sa kuWinsa. ?awata ta ce min sata na yi ba bashi bane, hankalina sai ya tashi, na fara neman hanyar da zan biya bashin. Na yi tunanin shiga film ta hana ni, sai kawai na yanke shawarar zuwa nan, dan kawai na tara kuWi na biya sa bashin da na Wauko. Bayan wannan ni babu wani abu a raina wallahi, ko sunansa ban sani ba."

Ya sauke numfashi yana wani irin murmushi ya ce, "Miss Islaha."

Ta Waga kai ta kalle sa suka haWa ido, ya Wan girgiza kai ya ce, "You are so funny."


"Ba wasa nake yi maka ba, da gaske ne abinda na faWa."

"Na san da gaske ki ke, kin bani dariya ne kawai."

Ta Wan sauke numfashi ta ce, "ban san tsautsayin da ya sake haWa ni dashi a nan ba, dan ni mugun haushinsa nake ji sosai wallahi. Ina zama a nan ne dan na tara kuWi na biyasa, daga nan na kai ?arar sa a bi min ha??ina, dan bazan bar case Win sace ni ya sha ruwa ba."

Ya yi dariya mai sauti, dan wallahi ?yal?yala dariya yake so ya yi, kawai ba ya son zubar da ajinsa ne.

Ya ce, "Miss Islaha yanzu kin fara tara masa kuWin na sa?."

Ta Waga kai ta ce, "na fara."

"Nawa ki ka tara?."

Ta Wago tana kallonsa, sai kuma ta chunkushe fuska ta ce, "basu da yawa, riyal dubu takwas ne, dubu bakwai a ciki....." sai ta dakata tana jin haushin abinda zata ce. Sai kuma ta sake kallonsa ta ce, "dubu bakwai a ciki, shine ya bani."

Jazy ya ?yal?yale da dariyar da take damunsa, yadda ta yi maganar ya bashi dariya matu?a, ya yi dariya son ransa yana kallon ta ganin ta sake haWe rai.

Ya dakata ya ce, "i'm sorry Miss, abin ne ya bani dariya sosai. Ya sace ki, kuma ki ka saci...."

Ta dakatar dashi ta ce, "bashi ne, ni ba sata na yi ba."

"Oh Sorry, kin ci bashin sa, kuma shine yake ba li kuWin da zaki fara biyansa?."

Ta kawar da kai ta ce, "ai ba kyauta ya bani ba, aiki na yi masa ya biya ni kuWin aikina."

Har lokacin murmushi yake yi yana kallonta, ya Wan girgiza kai ya ce, "Kina da sa'a Miss."

Ta Wago ido tana kallon Jazy ta ce, "dan ya bani kuWin?."

Ya girgiza kai ya ce, "haWuwa dashi gabaWaya sa a ce."

"Rashinta dai, ni a wajena rashin sa'a ne. Na faWa maka gaskiya Mr Jafar? Wallahi babu wanda nake jin haushinsa kamar sa."

Ya Wan yi clapping hannunsa yana gyaWa kai ya ce, "So ya batun interview ki da Mr Rehaan Yola?....." ya faWa yana kallom ta yana so ya ji me zata ce.

Nana Haleema.
[7/16, 12:11/ PM] KRBBK: RDB2P60
Nana Haleema.

Islaha ta kalle sa tana girgiza kai ta ce, "wannan yana hannunka, kai ka yi al?awari akan hakan."

Jafar ya ce, "To ai yanzu ai kina Jeddah, bakya Yola."

"Zan koma, in sha Allah."

Ya gyaWa kai ya ce, "ai yanzu kema kin san shi, bakya bu?atar taimakona. Kina da damar da za ki bashi invitation ke da shi."

Da mamaki take kallonsa ta ce, "A ina na san shi Win? Ni fa ban san shi ba, ban taSa ganinsa ba har yanzu."

Ya Wan yi murmushi kaWan yana girgiza kai cike da mamaki ya ce, "Unbelievable!."

Ya sake kallon ta sannan ya ce, "Wanda ku ka haWu a diamond hotel, ku ka haWu a asibiti, ya sace ki, ki ka ranci kuWinsa, ya yiwa babanki tiyata, ki fara aiki a gidan sa..." ya Waga kai yana kallon Rehaan da yake tsaye a upstairs yana amsa waya.

Jazy kalli Islaha ya yi mata alama da ta kalli inda ya kalla, ta Waga kai ta kalli Rehaan sannan ta kalli Jazy alamun na gani meye. Ya ce, "Rehaan AbdulAziz Yola, wanda ki ka fi sani da Ray!."

Wani irin dum Islaha ta ji a kanta da kunnenta, ta buWe ido sosai ta saka Waga kai tana kallon Rehaan da yake amasa waya yana murmushi.
Yana sanye da riga mai ?aramin hannu, sai dogon wando, ya saka hannu a aljihun yana zagayawa daga nan zuwa nan.

Ta sake kallin Jafar alamun tana son tabbatarwa, ya Wan murmusa yana Waga mata kai ya ce, "Ba ki yarda ba?."

Bata amsa ba dan mamaki ya kashe ta a zaune, Jazy ya Wan Waga murya ya ce, "Rehaan!."

Rehaan ya Wan zabura ya juyo yana kallonsa, ya yi masa alamun what kafin ya bar wajan.

Ya sake kallon Islaha da ta daskare a wajan, ta kalle sa dan har lokacin bata dawo daidai ba, mamaki take yi da ya kasance shine Rehaan Yola, zuciyarta bugawa take yi, dan kwata-kwata bata taSa wannan hasashen ba.

Ya ce, "har yanzu ba ki yarda ba? Ko dan kina ganin babu security kamar a Nigeria?."

Ta Wan sauke numfashi ta kasa magana, dan harshen ta ya sar?e, kamar an Waure sa ta kasa furta komai. Rehaan Yola kawai take maimaitawa a ranta, tana ganin abin kamar rainin hankali.

Jazy ya Wauki wayarsa a gefe kafin ya mi?a mata, ta karSi wayar tana kallo, ta sake jin faWuwatr gaba mai yawa, dan ta tabbatar shine Rehaan Yola. Ta kalli Jafar tana mi?a masa wayar sa, ta koma ta zauna tana ganin abin kamar wasa.

Jazy ganin ta shiga ruWani sosai ya ce, "Islaha nan gidan Rehaan, duk abinda ya faru ya faru tsakanin ki da Mr Ray. Shiyasa na ce kina da sa'a, babu macen da ta taSa rayuwa dashi kamar ki. Ke kam kin zauna dashi, kun yi magana, sannan ya yiwa mahaifin ki tiyata. Ta ko ina kin shiga rayuwarsa, shima ya shiga ta ki. Itace sa'ar da nake faWa miki, dan ni na san waye Rehaan, na san abinda zai yi da wanda bazai yi ba."

Ta Wan kalle sa ta ce, "Da gaske shine Mr Ray?."

Ya Waga mata kai ya ce, "a gidan Mr Ray ki ke, Miss Islaha."

Islaha ta gyaWa kai ta ce, "Ikon Allah! Wallahi ban taSa sani ba. Ban Wauka ma wannan yana jin hausa ba, har na gama zama a hannunsa Wauka nake yi ba bahaushe bane, dan sau Waya na ji ya yi magana, kuma ban san sunansa ba. A nan ma sai akan wannan baturiyar na ji ya yi min hausa."

Ya yi murmushi ya ce, "na san ba ki sani ba, shiyasa na faWa miki."

Ta sunkuyar da kai ta yi shiru bata ce komai ba, dan jikinta har rawa yake yi saboda mamaki.

Ya gyara zama ya ce, "kin san meyasa nake tambayar ki kuma nake faWa miki?."

Ta girgiza kai alamun bata sani ba, ya ce, "Tunda na yi bincike a kanki sai na ji na yarda dake, sai nake ji a raina aikin nan da ki ke yi kamar bai dace dake ba. Kina da carrier mai kyau, kina da farin jini, ana son fuskar ki a duniya, meyasa za ki zo nan ki dakusar da rayuwar ki?."

Ta Wan rausayar da kai ta ce, "na faWa maka ina nan saboda shi, wallahi ba dan kuWin nan ba da babu abinda zai kawo ni Jeddah da sunan aiki."


"Tun farko da kin faWa masa maganar kuWin da ba ki tsinci kan ki a nan ba. Na faWa miki shine ya yiwa mahaifinki tiyata, ranar da ya yi aikin ranar ya tawo nan, bai sake komawa ba har yanzu. Na tabbatar da bazai karSi komai na ki ba."

"Haka kawai ban san mutum ba sai na ro?e sa? Ni Waukar da na yi ma ban san dalili ba. Kuma wallahi da na san shine Mr Rehaan, da na san shine zai yiwa Baffa aiki, da bazan Waga hankalina na taho nan neman kuWin da zan bashi ba."

Jazy ya kalle ta, ta Waga kai ta ce, "Eh, da na san shine da bazan zo ba. Na ci bashin kuWinsa, kuma na ba da kuWin a asibitinsa. Na Wauko, kuma na mayar."

Jafar ya yi dariya yana kallon ta ya ce, "yanzu ki ajjiye batun nan, kina da asthma aiki irin wannan bai dace dake ba. Ki koma gida, ki cigaba da aikin jaridar ki, kamar zai fi miki."

Islaha ta ce, "ina son hakan, amma bazai yu ba sai na sauke nauyin da yake kaina. A nan ne zan iya haWa masa kuWin nan within one year, can kuwa fa?."

"Au ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login