Showing 102001 words to 105000 words out of 221574 words

Chapter 35 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

123

wayar sai ta faWa miki sunan Unguwar, ina so na zo na ganki."

A sanyaye Umma ta tambayi Hajiya Shafa, ta faWa mata itama ta faWawa Islaha.

Islaha ta ce, "In Allah ya yarda zan zo na ganki, duk da nima bana fita amma zan san yadda zan yi na zo."

Umma ta ce, "to Islaha, amma ki cewa ?awar ki ta daure ta yi magana dani kin ji?." Islaha ta amsa sannan suka kashe wayar.

Bayan sun gama wayar Hajiya Shafa ta bi Umma da kallo ta ce, "ya naga kin rame haka?."

Umma ta ce, "kullum a cikin fargaba nake kwana a gidan nan, kwana biyu hankalina ya kwanta saboda mai gidan baya nan, amma yanzu gabaWaya a ruWe nake saboda ya dawo yau."

Hajiya Shafa ta yi tsaki ta ce, "ke baki san yadda za ki kare kan ki daga wajan ba? In baki kame kan ki ba, kin nuna masa ke ba irinsa nace wallahi bazai ?yale ki ba wallahi."

Umma ta ce, "to ya zan yi?."

"Sai ki san abinda zaki yi. Kuma ki tashi na raka ki kije ki yi layin waya saboda ?an uwan ki, bazai yu na dinga zarwa a kan ki saboda waya ba."

Umma ta ce, "ai bani da kuWi."

"Mu je na ranta miki, in aka baki albashin ki sai ki biya ni." Babu yadda Umma ta iya haka ta tashi suka fita.

Tunda ta zo sai ranar ta fita, Umma sa kallon unguwar take yi cikin burgewa, ko ina shiru sai larabawa kaWan-kaWan kafin ta ce, "Hajiya a ina masallacin annabi yake?."

Ta kalli Umma ta ce, "da tafiya, sai kin hau mota."

Umma ta ce, "Allah ya bani iko wata ran na je na gano kabarin Annabi."

"Kina saka ran zaki je kenan?."

"Eh mana Hajiya, na zo har garin ace ban je ba, ai na yi asara babba."


"Ai ba ziyara ce ta kawo ki ba, aiki ne ya kawo ki."


"Duka biyun ne suka kawo ni wallahi."


"Ki cire ran zuwa wallahi, dan fitowa daga gidan nan ma babu lallai ki sake yi."

Umma ta yi shiru tana tunani, kenan burinta na zuwa masallacin bazai cika ba, gata a Madina amma ace kar ta saka ran zuwa ta yi ziyara? To meye amfanin zuwan ta ?asar in bata je ta ga masallacin ba? Ita da buri biyu tazo ?asar, ta tara kuWi kuma ta yi ziyara, gashi duka biyun basu yu ba. Bata ce komai ba suka je aka yi mata layin waya suka dawo gida ita kuma ta wuce.

Umma jin gidan shiru sai ta kwanta da niyar hutawa, bacci yana Wauke ta ta ji ana tashin ta, ta buWe ta ga matar gidan a tsaye tana yi mata nuni da tashi.

Umma ta mi?e tsaye ta biyo bayanta zuwa kichen. Abinda ta gani ya saka gabanta ya faWi, kaji ne masu yawa sosai, ta nuna mata alamun ta gyara.

Umma ta ji kamar ta kurma ihu saboda takaici, ta bi kajin da kallo dan a ?alla zasu kai hamsin. Matar ta ware wanda in aka gyara za a saka a fridge, da wanda Umma zata gasa.

Umma ta ?arasa ta fara gyarawa, tana yi tana hawaye saboda gajiya. Tana tsaka da yi aka ce ta zo ta gyara waje an Sata. Ta fito ta gyara ta koma ta cigaba da aikin.

Aikin sai da ya Wauke ta awa biyu da wani, ta gaji matu?a, bayanta kamar zai Salle saboda gajiya mai tarin yawa. Da?yar ta ke jan ?afa ta shiga Waki, ta cire kaya ta shiga wanka dan khamshin gashin kaza kawai take yi. Tana fitowa daga wanka ta ji an rufe ?ofa, tana juyowa ta ga mutuminta a tsaye yana kallon ta.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Umma ta faWa hawaye cikin tashin hankali.

Ya fara takowa zuwa inda take a hankali, Umma ta fara ja baya tana kalle kalle tana so ta samu wani abun da zai zamar mata makami.

Babu komai a wajan sai ta Wauki wayar ta tana muna masa, cikin turancinsu na manya ta ce, "Police, zan kira Police zu zo su kama ka wallahi, kar ka matso kusa dani." Jin ta ambaci police sai ya tsaya, kafin ya juya ya fita daga Wakin.

Umma ta zube a kan gado kwai ta fashe sa kukan takaici da sanasani. Whatsapp call Win Atika ne ya shigo, tana Wauka kawai ta fashe da kuka.

Atika daga can Sangaren ta ce, "Maimuna me ya faru ki ke kuka?."

Umma cikin kuka ta ce, "Na gaji Atika, gida nake son dawowa. Na gaji da zama a nan, aikin ya fita daga raina, ina so nazo na ri?e ?a?ana. Wahala nake sha, ga tsawa, ga aiki, ga raini. Na gaji wallahi."

Atika ta ce, "da wuri haka? GabaWaya kwanan ku nawa da tafiya da ki ke son dawowa? Ko har kin tara da yawa ne?."

"Wallahi babu abinda na tara, hasalima bani da ko sisi a hannuna. ?azu layin waya na je siya, sai ranta min kuWin aka yi dan bani da komai. Na gaji Atika, Ki ta ya ni da addu'a, Allah ya kuSutar dani daga hannunsu."

"Kin san dawowar ki yanzu bazai yu ba ko? Dole sai kin gama biyan waWanda suka kai ki kuWinsu ko?."

Kukan Umma ya ?aru ta ce, "na sani, shiyasa na ce ki taya ni da addu'a."

Atika ta ce, "ki yi ha?uri, zaki saba a hankali."

"baza ki gane halin da nake ciki ba. Ga wahala, ga fargaba, ga tsawa, ga aiki, ga raini. Haka kawai zan buWe ido na ga magidanci tsirarara a gabana. Ya zan yi?."

Atika ta ce, "ha?uri zaka yi, a hankali komai zai zama labari."

Umma ta ja numfashi ta ce, "Safeera har yanzu fushi take yi dani, ki bata ha?uri ki ce ko sau Waya ne ta yi magana dani."

Atika ta ce, "zan yi mata magana in na shiga gidan. Ki cigaba da ha?uri, ki ta addu'a, Allah ya kare ki daga sharrin shaiWanin can."

Umma? ta Waga kai kamar tana gabanta ta ce, "ki ta ya ni, ki saka su Rukayya su ta ya ni. Ina so na nemi afuwar su Yayan Katsina ban san ta ya zan fara ba."

Atika ta ce, "Allah zai kawo mafita, ki cigaba da ha?uri." Umma ta amsa suka yi sallama zuciyarta cike da abubuwa kala kala......

Nana Haleema.
[7/7, 6:25/ PM] KRBBK: RDB2P43
Nana Haleema.

_Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments Win ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link Win ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode Win baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/y7KtU9yRxrs?si=Q-KB7p8hKxcVfv1L

" " " " " " " " " " " "

*YOLA.*

"Ummi meyasa bakwa yin aiki yadda ya kamata ne? Har yanzu ?an kallo complain suke yi akan rashin Islaha, mun rasa mabiya da yawa saboda rashin ta. Da Saleem ya duba shafin mu na tiktok mutane sama da dubu uku sun yi unfllowing Winmu saboda rashin fuskar Islaha. In mu ka yi posting a ko yaushe magana Waya ce, su dai a dawo da Islaha ko su daina bibiyarmu. Shirin Rayuwatatalkshow views sun ragu sosai, lokacin da Islaha tana nan sai a samu masu kallo sama da dubu Wari biyar, amma tun bayan tafiyar ta ba a wuce dubu hamsin, wani har dubu ashirin. Me yake faruwa ne?."

Tunda ya fara magana Ummi da Jamila suka yi shiru, sai da ya gama sannan Jamila ta ce, "Chairman tsakani da Allah sun fi son fuskar Islaha, saboda son da masu kallo suke yi mata ya saka ta sama permanent a Sangaren interview da talkshow, sai ta ?ure ake canja ta a Sangaren. Ba laifin bane, mun iya aiki daidai ?arfinmu, kawai zuciyarsu tana tare da Islaha ne shiyasa ake samun matsala. Kuma baza mu maye gurbinta ba, sai dai mu yi abinda zamu iya."

Chairman ya ce, "Yanzu haka za a cigaba da zama kenan? Muna samun masu kallo dubu Wari uku zuwa Wari mun dawo dubu ashirin?. Ko interview Win da Muslim ya yi da minister tsaro akan satar yaran nan, har yafi interview Win Ummi views. Asara mu ke ta tafkawa, kwata-kwata bata yi sati uku da tafiya ba, amma muna ta samun na?asu akan harkokin mu."

Ummi ranta Saci yake yi, ba?in ciki da hassadarta suka sake ninkuwa fiye da baya, hassada ta Waure mata harshe ta kasa cewa komai balle ta yi magana.

Chairman ya ce, "ina magana Ummi kin yi yi shiru."

Da?yar ta buWe baki ta ce, "To Chairman na rasa me zan ce ba, gani ka ke kamar ba ma yin ?o?ari a aikin nan, ka manta tun kafin Islaha mu ne muke tafiyar da komai yadda ya kamata, zuwan ta ne ta asirici kowa ya zama babu mai son fuskar mu sai fuskar ta."

"Ke Ummi bana son shirme, wanne irin asiri kuma?."

Ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, shi kuma ya ce, "baza ki iya bakin ki ba? Baki daddara da abinda ya faru ba ko?."


"Chairman ai ba wani abun na ce ba, gaskiya ce ba wani abun ba."

Chairman ya ce, "ke ki ka sani kuma, ni dai in aka cigaba da samun akasi wallahi zan canja ku gabaWaya na zuba wasu. Bazai yu na dinga asara saboda ku ba."

Jamila a tausashe ta ce, "ka yi ha?uri Chairman."

Ya ja tsaki ya ce, "ku je. Sannan ku aiko min da Safeera."Basu jima da fita ba Sfeera ta shiga da sallama.

Ta ce, "Chairman gani."

Chairman ya ce, "Safeera ban tabbatar rashin ?awarki zai taSa mu har haka ba sai yanzu da mu ke ta samun raguwar mabiya. In ki ka duba comments section zancen Islaha ne, in bamu dawo da ita ba su dai zasu daina bibiyar mu."

Safeera ta ce, "ina lura da komai Chaairman."


"babu batun dawowar ?awar ki nan kusa Safeera? Kina gani bata rufe sati uku ba har yanzu, amma mun rasa mutane masu yawa. Ya ki ke ganin abinda zai kasance in ta sake kwanaki bata nan?."

Safeera ta ce, "In sha Allah baza a sake rasawa ba, zan tambaye ta in na koma na ji yaushe zata dawo, in sha Allah zata dawo a cigaba da komai kamar yadda aka sa ba."

"Don Allah ki tambayar mana ita, rashinta zai iya sakawa mu rasa abubuwa da yawa. Guest uku muka kaiwa katin gayyata amma sun bamu uzuri, abinda bai taSa faruwa damu ba kenan. Da zarar Islaha ta kaiwa mutum iv yake saka mana lokaci, wani ma shi zai ce ta saka lokacin da ya yi mata. Don Allah ku yi magana da ita."

Safeera ta ce, "in Allah ya yarda zamu yi magana, zata dawo komai zai dawo."

Chairman ya ce, "na gode Safeera, ki je ku cigaba da aiki."

Lokacin da ta fito office ta koma, tana shiga Saleem yan shigowa ta kalle sa ta ce, "Chairman ne ya yi min magana akan rashin Islaha, ba ka gani ba kamar ya yi kuka. Da yana da iko da ya yi fuffuke ya je ya Wauko Islaha ta dawo, ta Wora daga inda ta tsaya."

Ya yi murmushi ya ce, "Rashin ta ya taSa gidan gabaWaya, har bana son buWe tiktok saboda yadda za ki ga ana wula?anci dan ba ita bace."

Safeera ta yi dariya ta ce, "Hajiya Ummi uwar hassada, tana murna ta rabu da targaWe sai ga karaya ta samu. Bata rabu da bukar ba an haifi Habu."

Saleem ya yi dariya ya ce, "Ai na san ji zata yi kamar ta kashe Islaha ta huta."


"Ai da tana da dama wallahi zata iya. A haka zata ?are, babu abinda ta isa ta yiwa Islaha wallahi. Bara na koma gida na kira ta na bata labari." Saleem ya yi murmuahi suka cigaba da hirar su.

?? Ummi tana barin office Win Chairman office Win Muslim ta nufa, yadda ta shigo ya fahimci akwai damuwa, kuma daman ya san zata zo saboda irin cin kashin da ?an comments section suke yi mata. Kamar sun fi tsanar Ummi akan kowa, har gwara shi in ya yi ba a cewa a canjasa, amma in Ummi ce yanzu za a cika comments section da magana.

Ummi a firgice ta ce, "babu yadda za a yi a kashe Islaha ne? Babu wanda zamu biya ya kai ta har a shafe labarin ta daga duniya gabaWaya?."

Muslim bai ce komai ba, sai da ya mi?e ya buWe office Win ya le?a dama da haggu ya ga babu kowa sannan ya dawo ya saka mukulli ya ce, "me yake damun ki? Wannan Waga muryar da ki ke yi na meye? In wani ya ji abinda ki ke faWa fa?."

Ummi cikin ?unar zuciya ta ce, "Islaha! Ta tafi Win ma ban daina ?unsar ba?in ciki saboda ita ba, bata garin nan, bata cikin gidan nan amma tana bakin kowa, harda masu kallon mu. Ka kalli wula?ancin da aka yi min a hirar jiya? Ka kalli yadda ake saka hoton Islaha a commets section ana cewa in ba ita ba an daina kallon mu?."

Muslim ya ce, "na gani."

"Haukacewa ake so na yi ne? So ake na kashe kaina saboda ba?in cikin Islaha?. Chairman ne ya kira mu yanzu, wai faWa mana yake yi in aka cigaba da samun low views sai canja wasu presenters Win. Ya manta kafin Islaha ni ce highest presnter da ta fi kowa na gidan nan farin jini da samun views, ya manta ni na fara aiki a nam kafin ita?. Tunda ta zo na koma baya, yanzu akan rashinta yake cewa zai canja mu, ni Ummi ni za a canja na koma bayan camera saboda ita!. Wallahi bazan bar yarinyar nan ba, bazan ?yale ta ba, sai na yi mata abinda har ta mutu bazata manta dani ba."

Muslim a tausashe ya ce, "kwantar da hankalin ki, mafita ya kamata mu samu akan hakan ba wannan Waga muryar ba. Ki zauna mu yi magana."

Ta zauna kamar zata farka kujerar, sai jan numfashin mugunta take yi hassada da ba?in ciki suna nu?ur?usar zuciyata.

Muslim ya bita da kallo ya ce, "a hankali zamu yi maganinta, yadda ta bar aikin nan baza ta sake dawowa ba. Ba?in fenti ya kamata mu shafa mata, yadda ?an kallon ma zasu dinga son ganin fuskar ta ba balle har su ce suna son ganinta."

"Me zamu yi? Ni a ganina batun acid Win nan ya kamata a dawo dashi, da zarar ta dawo a lalata fuskar shegiya, sai na ga wacce fuskar za a dinga gani ana yabawa."

"Wannan ma shawara ce mai kyau. Bayan haka ma akwai abinda nake tunani, amma dole sai na yi bincike na ga ina ta tafi, me ta tafi yi, me ya kai ta garin, yaushe zata dawo?."

"Ka tambayi Salim, na san shi ya san inda take ai."

Ya yi murmushi ya ce, "ta yadda za ki san abun munafurci ne ya ?i faWa min, sai ya ce shi bai san inda take ba. Safeera ma da na tambaye ta sai ta ce min ta yi tafiya, nace zuwa ina, wai bata sani ba. Hakan ya jefa min zargi a zuciyata, ya tabbatar min akwai abinda aka ?ulla. Ko dai ba waje na gari ta tafi ba, ko kuma akwai abinda ya faru."

Ummi ta Wan daki table ta ce, "ya kamata ka samo mana inda take, jikina yana bani wani abu akan hakan."

Ya gyaWa kai ya ce, "dole zan nemo, wannam itace hanya ta farko ta ya?i da ita. In muka samo labari mara daWi a kanta, zamu yaWa sa ya shiga duniya gabaWaya. Iya wannan zai rage mata farin jini da masoya sosai."

Ummi ta ce, "yaushe zaka nemo Win?."

Ya bita da harara ya ce, "bana son gaggawa, na ce zan yi ai. Ki tashi ki koma, kar ace muna kulle ?ofa ni dake a office."

Ta mi?e ta ce, "meye in ance Win, mun kai mu kulle Win ai."

Ya Wan yi dariya bai ce komai ba ta fita. Ya jingina da kujera yana tunanin hanyar da zai bi ya gano inda Islaha ta tafi.

Safeera tana komawa gida ta tarar su Humaira suna nan, ta cire hijjab Winta, Rukayya ta shiga wajanta ta ce, "Adda Maman su Kausar ta aiko mana da dafaffiyar awara ta ce mu soya. Gata na soya in za ki ci."

Safeera ta murmusa ta ce, "bana jin yunwa Ruky, ki bari sai anjima. Baba ya dawo?."

"A'a bai dawo ba. Nima so nake ya dawo, Maman su Kausar ta ji ina maganar kuWin handout, shine ta bani kuWin ta ce na ?yale Baba ya huta. Kin gansu dubu biyu."

Safeera da mamaki ta ce, "Mamansu Kausar Win ce ta ba ki?."

Ta Waga kai ta ce, "itace wallahi."

Safeera ta ce, "Kai hidimar da take yi mana nan ta yi yawa sosai, ta bakin Baba ya kamata ta rage kar ta Worawa kanta nauyin mu."

Ruky ta ce, "Nima haka na ce Adda, amma bara ya dawo mu ji me zai ce."

Safeera ta Waga kai ta ce, "bara na Wan huta kafin lokacin sallah. Ko akwai abinda ku ke so?."

Ruky ta ce, "Babu komai Adda."

Safeera ta shiga Waki ta kwanta sai kuma ya jawo waya ta kira layin Islaha na saudia.

Tana Wauka ta ce, "ki hau whatsapp, yanzu za a janye min Wan katin nawa" tana faWa ta kashe wayar.

Ba jimawa sai ga kiran Islaha video call ya shigo, Safeera ta yi murmushi ta Wauka tana kallon Islaha da take zaune kanta babu Wankwali tana cin apple.

Safeera ta ce, "Lallai matar nan kina huta, kin ga yadda ki ka ?ara kyau? Ga wani haske, anya larabawa baza su ?wacewa Hamma ke ba?."

Islaha ta yi dariya ta ce, "ke yanzu kina tunanin akwai halittar da zata iya kasa Hamma? Duk kuWi da kyaun mutum bazai taSa kaiwa matsayin Hamma ba"

"Ban da cika baki dai, kar mu ga kin ma?alewa wani balaraben fa."

"Wuce wannan wallahi, Hamma shine farko kuma shine ?arshe."

"Amma duk da haka kin yi kyau. Waye ya yi miki kitson kan ki?."

"Ni na yi Safeera, ina yi ina kuka saboda sagewar hannu."

"Kema waye ya kai ki, wannan tulin gashin naki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login