Showing 213001 words to 216000 words out of 221574 words

Chapter 72 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

117

a kanta kamar an doka mata abu mai nauyi a tsakiyar kanta, sai da jinta da ganinta suka Wauke na wani lokaci, kafin ta dawo hayyacinta, jikinta ya fara rawa, ta koma da baya da hanzari ta Wauko hijjab, ta dawo ta samu Baffa da su Mama har sun fita daga falon ta rufa musu baya da sassarfa.

GabaWaya suka tafi asibitin da Saheer ya ke, suna shiga suka tarar da Sadik a tsaye yana amsa waya yana faWawa mutane an sa ki Saheer ya dawo.

Yana ganinsu ya kashe wayar, Baffa ya ?arasa ya ce, "Yana ina?."

Sadik ya ce, "an yi masa allurar bacci, yana ciki ana ba shi kulawar da ta kamata."

Islaha da ta fi kowa za?ewa ta ce, "Zan iya shiga na gansa?."

Hanan ta buWe baki ta ce, "ka ji wani abu, ga mahaifiyarsa bata shiga ta gansa ba sai ke?."

Islaha bata kula Hanan ba kallon Sadik take yi tana jiran amsa. Sadik ya ce, "an ce dai kar a tashe sa, amma za a iya shiga Waya bayan Waya a gansa."

Hanan ta yi caraf ta ce, "Mama mu je ki gansa, babu wata bare da zata fara shiga wajansa bayan ga ki. Ke ki ka haife sa ba, ba ita ba."

Islaha ta ja gefe ta jingina da bango ta bawa Mama hanya ta wuce, Mama da Hanan suka shiga. Babu jimawa Mama ta fito tana kuka tana faWin, "kun ga yadda ya koma? GabaWaya ya rame ya yi ba?i, jikinsa ya yi ?uraje. Allah ya isa! Allah ya isa! Allah ya isa!!. Allah ka shiga tsakaninmu da waWannan mutane, ka yi mana maganinsu cikin gaggawa.

Bafffa ya kalli Islaha da ta ke hawaya ya ce, "ki shiga ki gan shi Islaha."

Ta kalli Baffa jin abinda ya ce, muryar ta a sha?e ta ce, "ka shiga kawai Baffa."

Baffa ya murmusa ya ce, "ki shiga, Safeera ki raka ta." Safeera ta ri?e hannunta suka shiga ciki.

Suna shiga ta hange shi a kwance yana bacci, hawaye ya cigaba da ambaliyya daga idanunta, ganin yadda masoyinta ya canja kamar ba shi ba.

Ta ?arasa gaban gadon tana kallonsa, an saka masa ruwa yana shiga jijiyoyin jikinsa, kayan jikinsa duk sun lalace, fuskarsa ta yi duhu sosai, ga goshinsa an Waure da bandage, fatar jikinsa duk ta yi wasu ?ananun ba?a?en ?uraje.

Islaha ta mi?a hannu da niyar dafa kansa Safeera ta ri?e hannunta, duk da ba saba taSa shi ta yi ba, amma yanayin da ta gan shi a ciki ne ya saka take so ta dafa kansa. Ta juya suka haWa ido Safeera ta girgiza mata kai alamun kar ta taSa shi. Bata fahimci dalilin Safeera na hanata taSa shi ba, sai ta janye hannunta suka fito a sanyaye.

Ko da suka fito bata daina kuka ba, Safeera bata ce mata komai ba, sai da ta gama kukan son ranta sannan ta kalli Safeera ta ce, "meye dalilin da ya saka ki ka ri?e hannuna da zai taSa Hamma?."

Safeera ta ce, "saboda ke matar wani ce, taSa wanda ba muharramin ba babban zunubi ne da ba ki san girmansa ba."

Islaha ta yi sak tana kallon Safeera da ta kashe mata baki, ta kasa magana sai kallonta take yi, ta rasa wanne irin zagi zata yiwa Safeera da zata fahimci kuskurenta a cikin kalamanta.

Islaha ta ce, "Ina ma na iya zagi, ina ma na iya zagin maguzawa, zagin ?an iska, zagin karuwai, wallahi da sai na zage ki tas!......"

Ta nuna ta da yatsa ta ce, "Daman akan auren nan ki ka hana ni?."

Safeera ta ce, "Laifi ne hakan, ke ba matar auren ba ce?."

"Safeera meyasa ki ka yi min haka, Seyasa ki ka fara canja min tun yanzu?. Ni na Wauka saboda haramcin hakan ki ka hana ni, ashe akan wancan banzan auren da ban Wauke sa a matsayin aure ba ki ka hana ni taSa Hamma?."

Ganin ta fara fusata tana masifa a cikin mutane sai Safeera ta tausasa murya ta ce,? "Aure ya wuce ace masa banza aure, ki daina faWa, sunna annabi ne ba a zaginsa. Kuma akwai haramci a ciki taSa shi, ko babu aure a kan ki taSa Saheer haram ne balle ke matar aure....."

Hannu Islaha ta Waga kamar zata mare ta, sai Safeera ta yi shiru dan ta san a fusatar Islaha tsaf zata mare ta akan kalamanta. Islaha ta nuna ta da yatsa ta ce, "Na rantse da Allah in ki ka ?arasa sai na gaggaura miki da mari." Safeera ta yi murmushi bata ce mata komai ba.

Baffa ne ya ?araso wajan da suke tsaye, hakan ya hana Islaha magana.

Ya kalli Islaha ya ce, "Islaha."

Ta Waga kai ta kalle shi tana jiran ta ji me zai ce, a daidai lokacin Adda ta ?araso wajan ta tsaya a kusa da Baffa.

Baffa ya ce, "Yauwa ga Yayarki nan, ku je ta ta ya ki abubuwan da ya kamata ki yi, kafin gobe ki tare a gidan mijin ki."

Wani irin abu ya soki Islaha a zuciyarta, ta runtse ido da ?arfi tana jin yaji yana tasowa daga zuciyarta yana mamaye idanunta. Saboda zafin yajin har ruwa idonta ya tara, ta rasa inda zata saka kanta saboda ba?in ciki. Ga shi bata iya yiwa Baffa musu balle ta ce bazata je ba.

Adda ta kalli Baffa ta ce, "Baffa wai sai da aka yi auren nan, yanzu me za a faWawa Saheer?."

Baffa ya kalle ta ya ce, "wannan duk zai biyo baya, ya kamata ku fara shirin da ya kamata."

Islaha ta kalli Baffa tana hawaye ta ce, "Baffa don Allah ka bari zuwa anjima sai mu tafi, tunda ka ga sai gobe ne tafiyar ba yau ba."

Baffa ya murmusa yana kallon ta, yana karanto rauni da soyayyar Saheer a idanunta. Shi kuma wannan dalilin ne ya saka yake so ya nisanta ta a Saheer dan ita yanzu matar wani ce, zama inda Saheer yake bai kamace ta ba. In ya bar su tare za a tafka saSon Allah, ko iya magana ta yi da Saheer da fuskar masoya babban zunubi ne.

Baffa ya ce, "ku je Islaha, har shida na yamma ta yi. Ku tafi kawai." Babu yadda zata yi da Baffa, ta mi?e a sanyaye Safeea ma ta mi?e suka fito tare da Adda.

Ray tunda aka Waura aurensa ya daina walwala, yana sakewa ne kawai zaboda Jazy zai ji babu daWi in yana ?in sakewa a bikinsa, amma gabaWaya komai ya tsaya masa ba ya jin daWin komai. Yana zaune a falo ya canja kaya zuwa na shan iska, hannunsa ri?e da mug na tea yana sipping a hankali.

Jazy ya shigo yana hararsa ya ce, "Mamy tana ta neman ka, Wan family picture Win nan na biki baka tsaya an yi ba. Haba Ray, baka kyautawa Riyya ba, gabaWaya bata ji daWin haka ba."

Bai ce masa komai ba ya dai kalle sa kafin ya Wauke kai. Jazy ya zauna bayan ya cire babbar rigar jikinsa, ya Wauki wayar sa yana dannawa sannan ya ce, "media gabaWaya a kan ka take magana yau, hotunan ka kamar ruwa. Amma na yi mamaki da maganar auren ka bai fita ba."

Ya juyo ya kalle sa ya ce, "ka daina cewa aurena, please."

Ya yi murmushi ya ce, "Ray she is your wife, auren contract ne ko akasin wannan kai ta dama ba mu ba."

Bai ce masa komai ba ya kuma yi masa shiru dan bai san me zai ce ba. Jazy ya kalli agogo ya ce, "?arfe nawa zamu tafi dinner party?."

Ray ya buWe baki zai yi magana Jazy ya ce, "wallahi bazan karSi uzurin ka ce min baza ka je ba, gwara ma na faWa maka tun kafin ka furta. Kar ka wahalar da bakin ka ka ce min baza ka je ba."

Sai ya fasa faWar abinda zai faWa ya ajjiye kofin hannunsa ya mi?e ya shiga bedroom.

Bayan sallar magrib Jazy ya shirya cikin ash men lace, yana saka agogo a hannunsa ya shiga Wakin Ray ya same sa sanye da bathrobe ko kaya bai saka ba.

Ya bi shi da ya ce, "kasan akwai pictures before event ko?."

Ya yi tsaki ya ce, "kai wa da me zan ji ne? Ka ce sai na je, kuma ka ce min photoshoot?."

Jazy baice komai ba sai danna waya da yake yi, ya kira Riyya ya saka a speaker ya ce, "Riyya Wan uwanki ya ce ba zai yi attending event Win ki ba, ki yi masa magana yana jin ki."


Riyya ta ce, "Ray please, tunda ba ka tsaya an yi pictures Wazu ba yanzu ka zo mu yi, ka ji?."

Jin muryarta kamar zata yi masa kuka sai ya ce, "Riyya zan je event Win, meye wani pics brfore event?."

"Please!."

"Okay, i will be there"

"Thank you. I love you."

"I love you" ya furta yana kallon Jazykafin Jazy ya kashe wayar.

Ray ya yi ajiyar zuciya yana kallon Jazy da ya yi kyau cikin shigarsa ta angwaye. Kafin ya yi magana Jazy ya ce, "ka shirya mu je." Bai ce komai ba ya Wauke kansa sai wayarsa da ya Wauka jin ana kiransa.

Jazy ya ?wace wayar bai bari ya Wauka ba ya ce, "in ka fara waya akan business sai a tashi daga event Win ba ka gama ba. Don Allah ka tashi ka shirya."

Nan ma bai ce masa komai ba Jazy ya ce, "Abba ya ce na tura a Wauki Islaha ta je event Win, ni kuma na manta."

Sai lokacin ya ce, "wace?."

Ya wani kalle sa ya ce, "Wan rainin hankali, da ina yi maka magana ka yi banza amma ina ambato sunanta ka yi magana."

"Ita wa?."

"ba ka san ta ba?."

Ta girgiza kai alamun bai santa ba yana mi?ewa tsaye.

Jazy ya ce, "matarka nake nufi." Ya dakata daga kwance igiyar bathrobe Wun da yake niyar yi yana kallonsa, sai kuma ya ce, "point of correction, contract wife za ka ce, ba matata ba."

"Kai ka san wannan, ni a matarka nake kallon ta."

"As who will she go to the event?."

"Amaryar Ray."

Bai ce komai ya ?arasa yana kallon kayan da zai saka.

Jazy ya ce, "ni fa murna nake da auren nan, ko babu komai Alma zata ?yale ka." Ray ya sake yi masa shiru, sai da ambaci Alma ya tuna masa kwana biyu ko kiransa bata yi, yadda take damunsa da waya da texts yanzu duk bata yi.

Bai ce komai ba ya shirya cikin men lace amma na sa brown colour.

Jazy ya kalle shi bayan ya gama ya ce, "ka yi kyau fa." Bai ce masa komai ba wrist watch yake Waurawa sannan ya saka takalmi.

A hankali ya Wago yana yatsine fuska ya ce, "cikina."

Jazy ya buWe ido waje ya ce, "ciwo yake yi maka?."

Ya Wan girgiz kai ya ce, "ina jin alamun ciwon."

Jazy ya ce, "don Allah ka taimaka mana kar ciwon cikin nan ya tashi, in ya tashi a wannan lokacin ai mun shiga uku." Bai ce komai ba ya ?arasa shiryawa suka fito tare, suka hau mota suka tafi ayi hotunan kafin event.

Mama tana tsaye ta shirya cikin lace mai kyau, fuskar ta ta sha makeup kamar ba ita ba. A kan idanunta motar Mamy ta fita zuwa wajan event Win.

Ta girgiza kai ta ce, "an dai Waura aure, wannan aure shine target Wina na ganin bayan Rehaan. Wallahi indai ina da rai sai na ga bayan Rehaan, wallahi sai na kai shi ?asa."

"Mama" Sameer ya faWa yana shigowa.

Ta juya tana kallonsa ya ce, "Za mu tafi tare ne?."

Ta Waga kai ta ce, "mu je mu tafi tare kawai." Tare suka fito suka shiga mota zuwa wajan event Win.
[7/31, 11:42/ AM] KRBBK: RDB2P99
Nana Haleema..

Islaha tunda suka koma Adda ta saka a gaba da tambaya akan ya aka yi aka yi auren. Adda ta ce, "Ya aka yi? Me yasa Baffa ya yanke hukuncin aura miki wani ba Saheer ba?."

Islaha cikin rauni ta ce, "nima ban sani ba Adda."

"Meyasa ki ka amince bayan kin san wannan hukuncin nan na ki sai ya fi yiwa Saheer zafi fiye da zaman wajen masu garkuwa mutane? Aure fa Islaha."


"Adda babu yadda zan yi ne"

"Ban yarda ba Islaha; Da kin nunawa Baffa bakya son auren da bai yi ba miki ba. Yanzu da ki ka auri wani ya ki ke tunanin makomar Saheer zata kasance?. Daga wajen masu garkuwa da mutane ya fito, kuma dan rashin imani yana farfaWowa sai a ce masa kin auri wani?."

Adda ta Wora da cewa, "Gaskiya ba a kyautawa Saheer ba wallahi, yanzu shikenan duk yadda ya sakawa ransa auren ki sai dai ya ha?ura?."

Islaha bata ce komai ba ta yi shiru, tana so ta faWa mata babu wanda ya isa ya hanata auren Saheer, aurensa yana nan babu fashi. Tana so ta faWa mata duk wuya duk runtse sai ta fito daga gidan Rehaan ta zo ta aure shi, tana so ta faWa mata babu wanda zai rabata da Saheer. Sai dai kash! Bata so kowa ya san sirrin auren ta, bata so kowa ya san irin auren da ta ?ulla, dole ta ja bakinta ta yi shiru.

"Na san dai kuWi ba sa gaban ki, balle na ce dan Wan masu kuWi ne ya saka ki ka amince. Amma duk da haka kin dakusar da kan ki, ba kowa ne zai yarda ba auren kuWi ki ka yi ba Islaha. Mahaukaci ne fa aka ce, in ya kashe ki ya kashe banza, babu abinda aka isa ayi masa, tunda ba a shari'a da mahaukaci. Kin san da haka ka amince har aka Waura aure, ki ka bar Saheer da yake tsananin sonki, yake burin auren ki, yake burin ya ga ya samu kuWin da zai mallake ki. Ko yaushe maganar bikin ku ce akan harshensa, shine ginin gida, shine lefe, shine kyautata miki, amma ke kuma ba ki ri?e amana ba wallahi!."


Safeera jin Adda ta fara wuce gona da iri sai ta yi caraf ta ce, "Adda duk abinda Islaha ta yi har ki ke ganin laifinta ta yi ne dan taimakon Saheer, ke kin san baza ta zaSi kuWi ta bar Saheer ba. Masu kuWi nawa ne suka nuna suna sonta ta ?i basu dama? Sai yanzu da aski yazo gaban goshi zata juya masa baya?."

Adda kalli Safeera ta ce, "kamar ya saboda shi ta yi? Ban gane ba, kina so ki ce ta auri wani zata tare a gidansa gobe saboda Saheer? Wannan ma tana daga cikin soyayyar da take yi masa kenan ko?."

Safeera zata yi magana Islaha ta ce, "ni dai ki yi ha?uri kawai, duk abinda ki ke tunani ba haka bane, za ki fahimta nan gaba, amma ban da yanzu."

"Me zan fahimta Islaha? Ai kin riga kin goge min hadda, kin Sarar da duk yardar da na yi da ke, kin ri ga kin nuna min za ki iya zaSar kuWi akan Saheer. Meye Saheer bai yi miki ba?."

Mama da take shigowa falon ta ce, "faWa mata dai, yau kin tabbatar da tsintacciyar mage bata mage, in ina faWa miki halinta bakya ganewa, yau gashi ta nuna miki ita ?ar kunama ce. Ta zaSi auren mahaukaci akan Saheer."

Adda ta kalli Mama ta ce, "wallahi ta bani mamaki, ban yi tunanin zata zaSi mahaukaci akan Saheer ba. Kawai dan mahaifinsa yana da kuWi, kuma dan Wan uwan Rehaan Yola shikenan sai ta zaSi auresa ta bar Saherr? Yanzu in ya tashi me za a ce masa?."

Hanan ta ce, "a faWa masa gaskiya mana, ta zaSi Wan masu kuWi mai taSin hankali a kansa. Daman duk wanda ya siyi rariya ya san zata zubar da ruwa, duk wanda ya kalli Islaha ai ya san zata aikata goman haka."

Safeear fusace ta ce, "ke da ki ke maganar ba dan Islahan ba da yanzu..."

Islaha ta katse ta ta ce, "Safeera mu je gidan ku" ta faWa tana jan hannunta suka fita da ?arfi suka fita daga falon.

Suna fita harabar gidan ta fashe ta kuka, ta nemi waje ta zauna ta dafe kanta tana kuka mai tsuma zuciya wanda yake fita da sauti mai ratsa kunne.

Safeera ta tsaya a kanta ta ce, "ki bari a faWa mu su, ki bari su san kin sadaukar da rayuwar ki ne saboda Saheer, ki bari su san kin yi abinda su basu yi ba saboda shi, ki bari su san kanki ki ka Wauka ki ka kai wani waje saboda Saheer. Sai wani ?ananun mganganu suke yi, ai kowa ya san baza ki taSa zaSar mai kuWi ki bar Saheer ba. Ban taSa jin haushin Adda kamar yau ba, na Wauka zata yi shaidar ki, sai ga shi ta biyewa Mama. Ba dan ke ba da yanzu ai Saheer Win bai dawo ba."

Islaha dai bata ce komai ba, kuka kawai take yi tana jin ciwon auren da ta yi da ba Hamma ta aura ba. Tabbas kowa zai ce kwaWayi ta yi, musamman in aka san asalin wanda ta aura, kuma aka san ta bar Saheer ta aure sa, kowa ya san halaccin Saheer a gare ta, dole a faWa mata ba?a?en maganganu a kai.

Islaha kalli Safeera ta ce, "gaskiya ce maganar su, duk wanda ya ji asalin wanda na aura zai ce kuWi na zaSa na bar halacci. Na yi danasanin ?ulla yarjejeniyar nan, na yi danasani wallahi. Safeera In wayata?."

Safira ta ce, "me za ki yi da ita?."

"Zan kira Jafar ne."

"Ki ce masa me?."

"Ya haWa ni da Rehaan, zan yi canceling auren nan."

Ta yi mata kallon up and down ta ce, "kuWin sa da ki ka karSa fa? Ko kin manta ya ba ki kuWi dan ki zauna dashi har na wata biyar, ko kina da kuWin da za ki dawo masa da kuWinaa ne?."

Islaha ta dafe kai bata ce komai ba zuciyarta tana yi mata Waci, tana suya, tana zafi da raWaWi mai yawa. Sai a lokacin take danasanin aikata abinda ta aikata, sai a lokacin take tunanin ya Hamma zai ji, sai a lokacin take tunanin me mutane za su ce akan auren da ta yi?.

"Islaha lafiya ki ke kuka?."

Jin muryar Baffa duk sai suka juya a tare, Baffa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login