Showing 33001 words to 36000 words out of 221574 words

Chapter 12 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

159

Islaha, har Ummin baza ta fita ba. Domin zamu je ayi rubutu nida iyayenta, duk abinda ya same ki wallahi sai na Waure ta. Kuma dole ki basu bayani mai gamsarwa akan maganar nan, baza a ?yale case Win ya tafi a banza ba wallahi, kin ji na rantse ko?."

Ta Wan girgiza kai cikin rashin mafita ta ce, "To Hamma."

Sai a sannan ya kalli Sadik da Saleem ya ce, "ku yi ha?uri, ashe bamu gaisa ba" ya faWa yana basu hannu.

Suka gaisa suna dariya, Safeera ta ce, "ta ya zamu gaisa, ka ga Islaha ai dole ka manta damu."

Ya yi murmushi ya ce, "Hankalina ne a tashe, sai da na baro ?asar nan sannan na samu nutsuwa. Ina labarin waWanda suka yi waya akan kuWin fansar ta?."

Sadik ya ce, "Amfani aka yi da Satanta aka kira dan a damfare mu, suma za a yi bincike a gano waWanda suka yi wayar."

Ya Waga kai ya ce, "babu wanda zai sha a cikim case Win nan wallahi, ko shi wanda ya Wauke ta Win ne sai mun yi shari'a dashi indai ina da rai."

"Hakan ne ya kamata daman" Saleem ya amsa yana kallon Islaha.

Saheer ya ce, "Ya kuWin aikin Baffa? An gama haWawa ne Sadik?."

Sadik ya Wan kalli Islaha yaga ta zuba masa ido alamun kar ya faWa, ya Wauke kai daga kallon ta ya ce, "uhum an samu, har an biya ma. Sai dai mu yi fatan Allah ya sa a yi a sa'a."

"Amin. Amma baka faWa min an gama ba."

"Ina gama biyan kuWin islaha ta bayyana shiyasa na manta."

Ya Waga kai, ya juyo yana kallon Islaha ganinta tsaf da ita kamar babu abinda ya faru da ita ya ce, "babu alamun wahala a tare dake, kin dai Wan rame kaWan, amma kwata-kwata baki yi kama da wacce aka sace ba."

Ta sunkuyar da kai ta ce, "kaina ciwo yake yi min Hamma" ta faWa dan ta kawar da waccan maganar.

Ya bita da kallo cike da kulawa ya ce, "muje ki huta" ya faWa yana mi?ewa, ya ri?e hannunta suka shiga ciki.

Sadik ya kalli Safeera ya ce, "?awar ki akwai abinda take Soyewa wanda bata so mu san dashi."

Safeera ta girgiza kai ta ce, "nima na gani, zan je naji ko meye, dan na tabbatar zata faWa min. Ina zuwa" ta faWa tana bin bayansu da sauri......

Nana Haleema.
[6/22, 9:42/ AM] KRBBK: RDB2P014
Nana Haleema

Rehaan yana zaune a falon Mamy yana danna wayarsa, magana yake akan sabuwar order da ya yi gabaWaya ya yi busy har su Mamy suka zauna bai sani ba. ?aramin tsaki ya yi yana dafe kai, sai kuma ya kira waya ya saka a kunne ya fara magana cikin turanci.

Ya fi mintina arba'in yana waya, sai ya sauke wayar ya yi ajiyar zuciya, sannan yaji Mamy ta ce, "Mr Busy."

Ya hankali ya juyo suka haWa ido, suna haWa ido ya yi murmushi ya Wan langwaSar da kai cikin shagwaSar da ya saba yi mata ya ce, "neman halak da wahala Mamy."

Ikram da take zaune ta ce, "awwwn! Bruh ashe ka iya karin magana?."

Ya Waga ido ya kalle ta suka haWa ido, a lokacin ta ?araso ta basa hannu alamun su gaisa. Bai musa ba ya bata hannu suka gaisa, ya Wan yi murmuahi ya ce, "Ikram, ya Mummy?."

Ta zauna a gefensa tana kallonsa ta ce, "tana gaishe ka." Ya Wan Waga kai yana kallon falon sannan ya ce, "Ina Riyya da Kiddo?."

A guje Kiddo ta taho ta zauna kusa dashi tana ri?e hannunsa tana kallonsa ta ce, "My love."

Ya shafa kanta ya ce, "My love bakya yi min waya."

Cikin shagwaSa ta ce, "na kira ka baka yi picking calls Win ba."

Ya Wan buWe ido, sai ya Wauki waya ya shiga recent calls Winsa, a nan ya yi karo da kiran ta har sau biyu. Ya Waga ido ya kalle ta, sai ta fara kukan shagwaSa kamar bata girma ba ta ce, "kana gani ka ?i ka Wauka. Ka daina sona."

Ya ri?o ta ya ce, "I'm sorry Kiddo, banga kiran ki ba, da zan yi pecking."

Ta turo baki ta ce, "ni dai a'a."

"Me ki ke so?."

"Mu tafi Jeddah tare."

"sai kin je Jeddah zaki ha?ura?."

"Eh."

"Kiddo ni kaWai ne a Jeddah, Jazy baya nan, in na tafi aiki da wa zaki zauna?."

Sai ta Wan yi jim kaWan ta ce, "to yaushe zaka je danii?." Ya ja hancinta ya ce, "zan turo a zo a tafi dake."

Ta Waga kai ya yi murmushi sannan ya ce, "Ina Riyya?." Banisha ta ce, "Tana school."

"Janan fa?."

"Tana wajan aiki."

Ya gyaWa kai bai ce komai ba, a lokacin Riyya ta dawo daga makaranta. Mamy ta mi?e ta ce, "tunda ga Riyya ta dawo muje muyi lunch gabaWaya."

Tare suka hau kan dining har Ikram aka fara cin abinci, rabin zaman nasa amsa waya yake yi, ko ka ji shigowar sa?o ya mayar da amsa ya cigaba da cin abincin. Mamy ta zuba masa wani abu ta mi?a masa, ya kalla yana kallonta ya ce, "meye wannan?."

Mamy ta ce, "moimoi."

"Moimoi!."

Mamy ta ce, "in baka ci ka daina harararsa."

Ya Wan ture ya ce, "bana so Mamy. Kema sun koya miki cin wannan abun" ya faWa yana cigaba da shan tea Winsa yana danna waya. Mamy ta ce, "Kai kuwa dole na koya ai, zaman da nayi a nan ban yi shi a inda aka haife ni ba."

Ikram aka kira a waya, ta Waga waya tana magana kafin ta kashe ta ce, "Mamy zan je gida yanzu, zan dawo in anjima." Mamy? bita da kallo tana murmushi ta ce, "To Ikram, a gaishe da Mummy."

"Zata ji. Byee Riyya, byee Hamma" ta faWa tana Waga masa hannu ta fita.

Mamy ta kalle sa a lokacin ya ce, "gobe zan yi tiyata Mamy, sannan a daren zan tafi Jeddah."

Riyya ta ce, "Jeddah!"

Ya kalle ta ya Waga kai alamun eh. Riyya ta ce, "Hamma why are you always traveling? We don't get enough time to spend with you. We really need you in our family. Daga Uk sai Jedda, kullum baka nan."

Ya kalle ta ganin cikin yanayin damuwa take maganar, hakan ya tabbatar masa har zuciyar ta take yi ba wasa take yi ba. Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Riyya akan aiki, zan je wani asibiti for three months contract."

Riyya ta yi fushi ta mi?e tsaye ta ce, "meyasa ko yaushe kana kan aiki? Meyasa baza ka tsaya a nan ba? meyasa lallai sai ka je can?."

Ya ri?o hannunta ta zauna ya ce, "calm down Riyya, ba abin Waga hankali bane." Idonta ya ciko da ?walla ta ce, "Muna son ka dinga zama a kusa damu, muna so mu dinga hira da kai. Kai kaWai ne Yayanmu, su Hamma Sameer yayansu su Janan ne, kaine namu. Don Allah ka dinga zama a kusa damu, ka ji?."

Rehaan ya kalli fuskar ta cikin damuwa ya ce, "ko yaushe muna tare, kar ki damu."

Riyya ta mi?e ta tafi Waki bata sake kula shi ba, ya bita da kallo cikin damuwa. GabaWaya ahlin Mamy babu wanda yake si yaga Waya yana fushi, sun fi so kowa ya kanace cikin farin ciki da walwala. Ba dan aiki ne zai kai shi Jeddah ba, tsaf zai iya fasa zuwa saboda fushin da Riyya ta yi, sun san darajar kansu, suna ?aunar junansu, suna yiwa juna abinda Waya yake so.

Mamy ta kalle shi ta ce, "su ma ?an uwanka basa son zaman ?asar wajen nan da ka ke yi, balle kuma ni mahaifiyar ka. Duk dani wani lokacin nafi son zaman ka a can Win, kafi zama lafiya kana sakewa fiye da zama a nan Win."

Ya yi shiru bai ce komai ba, dan baza su fahimta ba. Ita Mamy ta san baya son zaman ?asar gabaWaya, takura yake yi kuma baya sakewa, shiyasa da aka kawo masa contract Win ma ya karSa kawai, dan baya son abinda zai haWa shi da zama a nigeria ko kaWan. In haka akwai ne Abba baya bari ya zauna, amma in aiki yake yi bai cika takura masa akan ya dawo ba.

Mamy ta sake kallonsa ta ce, "Banisha tana son zama tare da kai, kaga da kana da aure sai ku je tare ku dawo."

Bai ce komai ba dan bai san amsar da zai faWawa Mamy a wannan maganar ba. Kamar ta fi kowa sanin bashi da aure, kuma bai yi niyar yi a nan kusa ba.

Mamy a tausashe ta ce, "meyasa baza ka yi aure ba?."

Ya kalli Mamy cike da gajiya da maganar ya ce, "Aure Mamy! Na auri wa?."

"Why Ikram?."

Ya Wan buWe ido cikin mamaki ya ce, "ikram!."

"eh ita. Tana sonka, kuma zaka iya aurenta, dan kaf cikin cousins Winka babu kamar gidansu Jafar. Suna sonka tsakani da Allah, ba dan wani abu da ka ke daahi ba. Kuma Ikram tana da kirki da hankali, zan yi farin cikin karSarta as my daugher inlaw."

Ya sake kallon Mamy yana girgiza kai ya ce, "i'm not interesting."

Mamy ta dafa kafaWarsa ta ce, "Why? Meye aibu dan ka auri Ikram?."

"Mamy a matsayin Riyya nake kallon ta, bazan iya kallonta a matsayin matata ba. Infact duk wata cousin sistera Wina bazan iya kallonsu a matsayin matan aure ba, ?an uwa ne kawai. Yadda babu aure tsakanina da Riyya ko Banisha, suma babu. Bazan iya kallon cousin sister as my wife ba."

Mamy ta girgiza ta ce, "Haka Jafar ma ya dinga cewa, amma yanzu saura few days bikinsa da Riyya. Zaka iya auren Ikram kaima, kamar yadda zai auri Riyya."

Ya girgiza kai ya ce, "shi ya ga zai iya Mamy, amma ni bazan iya ba. Dan zai auri Riyya ba hakan yana nufin zan auri Ikram ba."

"Amma ka san Ikram tana sonka ko?."

"Na sani, nima ina sonta as my sister, soyayyar da nake yiwa Riyya nake yi mata, ba wacce zan aura ba."

Mamy ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Zuwa yanzu ya kamata ace ka yi aure."

Ya kalli Mamy ya ce, "ba kin ce zaki zaSa min mata ba? Na baki dama kawai, ko wacece indai tayi miki nima tayi min, amma ban da cousins."

Mamy ta girgiza kai tana Wan murmushi ta ce, "Ga Ikram nan na faWa maka, itace zaSina."

"Mamy ban dasu."

"To ai gidan nan baza su yarda da zaSina ba, kuma kakarka ta zaSa maka matar aure."

"Wannan matar tana da mental issue fa, babu wata mata da zan aura daga wajanta Mamy. Ko an aura min sai na warware" ya faWa yana mi?ewa tsaye.

Mamy ta mi?e tana dariya ta ce, "Kai da Kakarka, wallahi babu ruwana, baza ka jawo a dinga ce min ni na zuga ka ba."

Ya Wan girgiza kai yana Waukar wayarsa ya ce, "matar aure indai ba daga wajan ki ba, bazan karSa ba.....Zan kwanta Mamy."

"Okay Baby. Kwana biyu baka yin azumi litinin da alhamis, meyasa?."

Ya Wan shafa kansa ya ce, "Zan yi, sai na je Jeddah."

"Yauwa, bana so ka daina, shine garkuwar da yake kare ka."

Ya Waga kai ya ce, "In sha Allah" ya faWa yana fita daga apartment Win ta bida sa kallon ?auna da soyayya.

Gab da zai shiga apartment Winsa ya hango Salman yana tahowa inda yake, ya tsaya cak duk da wajan akwai rana amma haka ya tsaya yana kallonsa har ya ?araso. Yana ?arasowa Salman ya ce, "Kai na Waukowa."

Ya faWa yana mi?a masa roba ta natural tamarind drink. Rehaan ya karSa yana murmuahi ya ce, "na gode sosai."

Shima murmushi ya yi yana kallonsa. Rehaan ya shiga ciki sai ya ga shima ya biyo bayansa. Bai hanasa ba ya bari ya ?arasa shigowa sannan ya kulle ?ofar. Suna shiga falon aka fata ?wan?wasa ?ofar, Rehaan ya dawo da baya ya buWe ?ofar ya ga Umma ce.

Ya Wan kalle ta a ta?aice ya ce, "ina yini."

Umma ta harare sa tana tsaki ta ce, "Sai yau ka san ya na yini?..." ta kalli Salman ta ce, "Salman fito" ta faWa tana shiga falon tana kallon Salman.

Salman ya ?i kallon ta ya ce, "a nan zan zauna." Ta yi tsaki ta shiga ciki ta ri?o hannunsa ta ce, "ina magana kana daWa gyara zama, dallah ta so."

Salman ya ?i tasowa ya fizge hannunsa ya yi bayan Rehaan yana neman ya cece sa. Shi kuma ya rasa ya zai yi, sai ya kalli Umman a sanyaye ya ce, "Umma ki bar shi a nan Win."

Umma ko kulasa bata yi ba sai da ta ri?o hannun Wanta sannan ta ce, "na bar shi ka cigaba da yi masa kallon mahaukaci ko? Har ka samu damar cewa zaka kai shi asibiti, kai ga mai kuWi ko...?" Ta ?arasa faWa tana hararar sa.

Ta kalli Salman ta ce, "Mu je" ta faWa tana jan hannunsa da ?arfi suka fita daga falon.Ya yi ajiyar zuciya yana kallonsu har suka fita daga wajan gabaWaya. Zai kulle ?ofar kenan ya ga kiran Abba yana zuwa wayarsa, ya Wauka da sallaama, Abba ya amsa ya ce, "ka same ni a falo" daga haka ya kashe wayar.

Rehaan ya Wan yi jim, kafin ya mayar da wayar aljihu yana ji kamar ya yi kuka, dan bai san me Abba zai ce masa ba. Babu yadda ta iya haka ya fito daga falon ya nufi wajan Abba.

A falo ya samu Abba da Mama a zaune, ya shiga da sallama suka amsa ya zauna, ya Wan kalli Mama ya ce, "ina yini."

Ta wani kalle sa kallon rainin wayo ta ce, "daman ina so na yi maka magana, wato nuna mana ka ke yi Nadira ce kaWai babar ka, mu ba iyayenka bane. Kwanan ka nawa baka gidan nan, da ka dawo ba sai ka shiga wajan kowa ka gaishe ta ba? Sai yanzu da ka ganni da Abba shine zaka wani ce ina yini? Gaisuwar ma sai a kan hanya za a yi?."

Shi dai ya yi shiru bai ce komai ba, sai Abba ne ya ce, "baka kyauta ba Rehaan."

Ya yi ?asa da kansa bai yi magana ba, dan bai san me zai ce ba. Abba ya ce, "akan maganar matar da Daada ta zaSa maka ne, na nemi unguwarsu kuma na ji labari akan iyayenta. Abinda ya dakatar dani an ce min mahaifinta yana asibiti bashi da lafiya, shine maganar ta dakata, da yanzu sai dai ka ji an tsayar da lokacin auren."

Rehaan ya kalli Abba cikin wani yanayi, Abba ya Waga masa kai ya ce, "Ka cigaba da shiri kawai, ku cigaba da shirye-shiryen auren ku kai da Jafar. In kana Jeddah zaka ji labarin an saka ranar aure, kar kace ban faWa maka ba. Ka fara shirye-shirye dan tare zaku angwance da Jafar......" ya faWa yana kallonsa kamar yadda shima yake kallon Abban.

Another banger=?%?=??=??=??

Nana Haleema.
[6/23, 11:47/ AM] KRBBK: RDB2P15
Nanahaleema.

Rehaan ya Wago yana kallon Abba jin abinda yake faWa, ransa ya Saci sosai, yana ji a ransa ko me zai faru bazai taSa auren zaSin Daada ba sai dai ko meye ya faru.

Rehaan ya kalli Abba ya ce, "Abba ban santa ba fa."

Abba ya Waga kai ya ce, "Na san baka santa ba, amma kafin auren ai zaka santa."

Rehaan ya ce, "Abba na faWa maka bana ra'ayin auren nan, meyasa zaka biyewa Daada don Allah?."

"Saboda uwata ce Rehaan, dole na biye mata nayi abinda take so."

"Wanne irin aure ne wannan? Ban san yarinya ba, itama bata sanni ba, ace za a aura min ita?. Kuma kowa ana basa dama ya kawo wacce yake so amma ni meyasa za a yi min haka?."

"Sai ha?uri, hakan za a yi Rehaan." Ya sauke numfashi bai ce komai ba zuciyarsa cike da jin haushi da takaici mai yawa.

Mama cike da makirci ta ce, "gaskiya dai Abba a duba lamarin nan, a bashi dama kamar yadda ake bawa ko wannen su dama ya kawo wacce yake so."

Rehaan ya kalle ta ya ce, "ki faWa masa please, bana son auren nan, meyasa ake so dole sai an yi min?."

Abba ya ce, "Rehaan gwara ka so auren nan, dan yin sa babu fashi, gwara ka daina ja kawai."

Ya Wan shafa kansa bai ce komai ba, Abba ya ce, "tashi ka je, na san lokacin yin baccin ka ne yanzu. Zamu ?arasa maganar in ka farka."

Ya gyaWa kai ya mi?e ya fita yana ji kamar yaje ya sha?e Daada ta mutu kowa ma ya huta, saboda haushinta ko gaishe ta bazai je ba ya yi shigewar sa apartment Winsa.

? ? ?? ******

Cikin lokaci kaWan labarin ganin Islaha ya zaga ko ina, ana ta yi mata addu'ar barka da dawowa da fatan Allah ya kiyaye gaba. Ita kuwa tana gida, tunda Saheer ya rakata Waki take baccin gajiya da baccin da ya taru a idonta. Dan ko da Safeera basu yi magana ba, ganin tana jin bacci ya saka ta ?yale ta.

Sai bayan sallar magrib ta farka, ta yi wanka ta yi sallah ta fito falon babu kowa alamun duk basa nan. Tana gab da shiga kitchen Saheer ya shigo da sallama, ta amsa ya bita da kallo ganin kanta babu Wankwali, gashinta ya sauka har baya, sannan gashin ya yi tudu daga sama, kamar wacce ta hargitsa shi da hannunta.

"Da daren nan ki ke yawo haka?."

Ta Wan yi murmushi ta ce, "abinci nake so na ci, sai na kira ka mu je asibiti."

Ya bita da kallo kafin ya tako inda take ya ce, "ki je ki saka Wankwali sai kizo ga abinci na siyo miki."

Ta Waga kai ta juya ya bi dogon gashinta da kallo, ta sauke numfashi, yana jin shau?i in ya tuna nan da lokaci kaWan ba gashinta kaWai ba, ita kanta nan gaba mallakinsa ce.

Ba jimawa ta dawo ta Waura Wankwali ta zauna ya bata pack Win abinci, ta karSa ta ga fried rice ce da chicken, an zuba mata sauce mai albasa sai ?hamshi take yi. Ta Wauki disposable spoon ta Webi ta fara ci.

Yadda bakinta yake moving Waukar hankalinsa yake yi, bakinta yana daga cikin abinda yake Waukar hankalinsa akan fuskarta. Bata san yana kallon ta ba abinci take ci, sai daga baya ta Wago suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login